Showing 150001 words to 153000 words out of 190771 words
hakuri abar batun d'aurin auren ko nan da zuwa ranar juma'a ne amma matar nan ta coge tace bata san zancen ba,
yau dai take bukatar a d'aura auren duk wanda zai mace shiya dad'e bai sha fiya fiya ya mutuba tunda har aka iya nuna mata bak'in ciki zallah ai ba iko da isa aka fita iyawaba,
Dama can da take bin abubuwan da sauk'i ba tsoro ne yasa take hakan ba,
Suna fitowa daga cikin falon Musty ya fara kiran wayar AK sai dai kira 4 ya mishi amma bai amsa ba dan haka saiya juya akalar kiran zuwa k'an Yusuf wase, bai tsaya jira su gaisa ba ya fara kora mishi bayani akan abinda ke faruwa,
"Hajiya ce tace dole sai dai a d'aura auren a yau?" Wase ya tambaya,
"Eh wallahi kuma anyi anyi da ita ta bari ma ko zuwa gobe ne wallahi tak'i yarda"Musty ya bashi amsa
"Turkashi to yanzun fa ya za'ayi kenan nidai kasan ko nace in taso daga Abuja yanzun indai ba layar b'ata zanyi ba bazan samu d'aurin auren ba, ga kuma Sadeeq shima yana nan, amma bari in kira sauran friend nasan baza'a rasa wadanda suke cikin gari ba kaima kayi kira ko za'a samu,zanyi maka transfer yanzun sai ku k'ara kud'in sadaki kasan tuntuni dama Ina fad'a muku cewa ni zan biya sadakin auren AK toga ranar tazo,insha Allah zan shigo ko zuwa dare ne dan yau dole ma in kwana a Zaria shi angon ka kira shi ka fad'a mishi halin da ake ciki ne? "
"Na kira shi Ina ganin baya tare da wayar kasan dai ko baya kusa zan gabatar da abinda ya dace balle kuma anan ma muna tare dasu Abba ga Kamal kuma a tareda ni"
Cikin mintunan da basu fi talatin ba sai ga kofar gidan Malam ya cika da jama'a wai a hakan ma ba kowa yasan da batun d'aurin auren ba domin da lasifikar masallaci akayi amfani wajen shelanta d'aurin auren wanda hakan yaba kowa mamaki matuk'a,
Manyan restaurant uku Musty ya kira yayi odar d'in abinci ya kuma ba su Hafees kud'i suka je suka sissiyo drinks din da za'a raba da abincin bayan an gama d'aurin aure.
An maida d'aurin auren karfe 5 na yamma wanda hakan ne kuma ya sa suka samu k'arin lokacin gabatar da abubuwa a tsanake,
Baba Adamu yasa yaran gidan sun sharo cikin masallacin kuma suka gyara harabar gidan saboda amsar bak'i,
Cikin gida ko ya rud'e da surutai domin su dai basu san me yake faruwa ba har saida taron falon Malam ya watse Hajiya ta shiga cikin gida suma sauran mazan gidan suka shiga acan ne labari ya isa kunnuwan mata,
Shi kuma Sheikh bayan fitar mutane a falon shida Baba Adamu ne sukabi Malam har cikin d'akin shi suka dunga bashi baki, akan cewa dama Allah ya nufa cewa Meenal ba matar Sheikh bace kuma Alhamdulillah tunda ashe shima Fauxieyerh yake so, inda kuma ace hakan bai faruba haka za'ayi auren koda ita tayi biyayya ta amshe shi zatayi zaman auren ne ba cikin dadin raiba shima kuma zai rasa abinda yakeso kunga dai kenan babu biyan buk'ata,
To dai Malam a babu yanda zaiyi haka ya hakura shima ya shiga cikin sahu wajen kiran nashi mutanen yana sheda musu d'aurin auren daza ayi karfe 5 tunda dai ita magajiyar hakan ta yanke,
A can falon mommy Hauwa ko Hajiya cike da farin ciki ta shiga tana zuwa bata zauna ba tace a bata ruwa a buta dan farin cikin da take ciki dole nema ta gabatar da nafila kafin ta sauke farilla na nuna godiyar ta a wajen Allah Subhanahu wata'alah daya nuna mata wannan ranar da zata aurar da Meenal ga AK Ina ma ace Prof yana raye tasan dasai yafi kowa yin farin ciki da wanzuwar hakan,
Kafin ta idar da Sallah su Farouq suka shaida ma Jidda abinda yake faruwa, to ya zatayi tunda har Malam ya zubda makaman aiki ai kuma ita ba'a bakin komai take ba,
Yadai tabbata cewa daga ita har Baba Auta basu data cewa akan al'amarin yaran da suka haifa tunda gashi yau ma dai isa aka k'ara nuna mata akan yaran nata har biyu bama d'aya ba,
Itafa kwata² bata san cewa alaqar soyayyar da ake ambatawa a tsakanin AK da Meenal yakai matakin da har za'ayi zancen aure ba,
to na Fauxieyerh da Sheikh ma bata tab'a lura ba inba yau da ake batun cewa kila ita Fauxieyerh ce malam yaba Sheikh d'inba,
*Mu tafi a gurguje*
Karfe 5 dai dai tarin jama'ar da suka taru a kofar gidan Malam suka shaida d'aurin auren Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a tareda Amaryar shi Aminatu Al Mustapha Umar Farouq, akan sadaqi mai daraja,
Haka kuma aka d'aura nasu sheikh da Fauxieyerh shima, an rarraba ma bak'i abincin dasu Musty sukayi order dasu drinks sai snacks da sauran su,
Ango AK dai bai samu damar halartar wajen d'aurin auren ba dan har akaci aka sid'e bashi da labari su musty ne keta amsa fatan alkhairin da mutane keyi a madadin shi,
Salman dai yayi kuka kamar zai tsiyaye kwayar idon shi,
bai tabbatar da cewa ya rasa Meenal ba sai da aka gama sanar da d'aurin aure yaga ana ta taya su Abba Ahmad murna wai harda Sarki fa a wajen d'aurin aure yana taya mutane murna wato dai shine ba'a so,
Fauxieyerh dai koda ta samu labari bata wani damu kanta ba, dan dama dai itama tad'an fola ma Sheikh d'in bata dai bayyana bane kawai yanzun kuma daya tabbata cewa shima d'in yana son ta mai zai dameta.
Bayan gama d'aurin aure Hajiya tabi ayarin ta sun koma tudun wada bayan ta k'ira waya ta sheda ma Dada abida ya faru ta kuma bada umarnin cewa a d'aura abinci saboda masu zuwa yi musu fatan alkhairi,
Alhamdulillah aure dai ya tabbata yan ciki bak'i kuma sai su mace atoh, mudai bari mu koma tudun wada mu gani ko AK ya iso in kuma bai iso ba mu bishi hanya mu taro kayan mu😜.
Koda kirar wayar Sultana ya isa ga AK lokacin yana marafa can gidan shi dan yanzun ne ya tada aikin gyaran gidan tuk'uru dan yana tsammanin bikin dai ko za'a sashi bazai wuce ace a had'a ayi gaba d'aya tareda nasu Sarki ba,
dan Allah yasa ma dama tuni anci k'arfin aikin abubuwan da ba'a k'arasa bane akeyin su a yanzun,
Dan haka bayan gama wayar shi da sultana motar shi ya shiga kawai ya juya zuwa Malali can gidan shi koda ya isa a k'ofar gida yayi parking ya sauka da k'afa ya karasa cikin gidan bai tsaya bata lokaci ba ya cire wandon 3quiter din dake jikin shi ya canza shi da wani farin wandon jeans crazy ya cire polo din dake jikin shi ya d'auko waya rigar bak'a mai kamar na sanyi ya d'aurata akan farar vest din dake jikinshi ko zip din rigar bai rufe ba ya juya ya fice daga falon garin sauri yabar gidan ne kuma ya manta da wayar shi wanda yake cikin aljuhun wandon daya cire yana fitowa ya mik'ama Mansoor key din sashen shi dan bai sani ba ko kila ya kwana ko kuma ya dawo ko zuwa dare,
Normal dama idan yana tuk'i baya tafiyar nawa yau kuma da yake cikin hanzari sai gudun motar nashi ya k'aru Allah allah kawai yake yaga Allah ya kaishi Zaria lafiya yaje ya amayar da abinda ke cikin zuciyar shi,
To Allah dai ya tsare taubashi,
Tunda su Sultana suka k'ara komawa suka zauna zaman hira a tsakar gidan bayan wucewar Bash basu tashi ba har saida rana ya kawo inda suke kafin suka tattara suka koma cikin falon na Hajiya ita dai Sultana labari take jira na abinda yake faruwa acan unguwar malamai ita kuma Moon ta samu kira daga Sarki akan cewa ya shigo gari dan haka zai shigo nan gidan ya ganta zuwa anjima,
Ita kuma Meenal duk da halin faduwar gaban da take ciki haka ta matse ta d'auki wayar Meelat wacce ta kira take rok'on ta akan dan Allah ta taimaka taje gidan ta Meelat d'in tana neman ta ita kuma tace mata wallahi bata zuwa,
"Bani da lafiya fa Besty" cewar Meelat,
Ita kuma Meenal ta bata amsa da cewa,
"Kisha magani in kuma yaji miki ciwo ne ai kinsan yanda zaki gyara kanki dan nidai bazan zo inyi gyaran b'arnar da mai sunan Malam yayi ba wallahi garama ki kama jikin ki"
K'asa kasa suke maganar amma tsabar gulma sai da Sultana ta jiyo bata iya yin shiru ba kuma sai da tasa baki,
"Wai Meenal badai kuna nufin sai yanzun Meelat ta sauke gammon dake kanta ba🤔? Ni ai nayi zaton tuni ta wuce babbak'u ta shiga mai wasali"
"Ina ruwan ki da gammon data d'auka!
Kuma ba mai wasali ba mai tafiya ta shiga😕"
"Ke tsakani da allah mamaki nikeyi ke koh kwana nawa dakai mishi ita shiko bawan Allah yakawai sai yasa mata ido kawai yaci gaba da kallo duk da cewa rai naso amma yayi ta had'iye yawu gaskiya Musty waliyyine ko a cikin maza abudai kamar rainon tsoffi bawan Allah abunshi,
Tana gidane ko asibiti?"
Sultana ta k'arasa maganar da tambaya,
Moon ce ta amshi zancen da cewa,
"Haba ke kuwa me zaikaita asibiti ana zaune k'alau?"
"Ai wai kina ganin hakan bazai iya faruwa bane? Na rantse miki tunda har kikaga tayi kiran Meenal tofa tabbas ta had'u da hatsarin maza allah dai ya bata lafiya oh Allah Yasin ta bani tausayi"
Hirar Meelat sultana da moon suka cigaba da kacal calawa ita kuma Meenal ganin iskancin su bana karau bane kawai saita tashi daga kusa dasu ta koma can gefe a cewar ta wai bazasu lalace d'iyar malam ba tunda su sun zama fanko ki iska kawai suke busawa,
Number din AK ta kira dan tun asuba basu k'ara yin waya ba, tasan yayi busy shi yasa bai kirataba dan haka ita kuma ta kira dan taji ya yake, sai dai harta gama ringing ta katse ba'a d'auka ba tasan da ace yana kusa da zai yanke kiran nata ne shi sai ya biyo bayan kiran dan haka sai ta shiga cikin message tayi typing kamar haka,
"Heart kana can kana aiki nasan k'ila ko abinci baka nema kaci ba,
Call me back if you are less busy I miss you 😍"
Ta tura mishi,
"Sister shirya muje gidan Meelat please" inji Sultana,
"Wallahi bazanje ba shi da yayi barnar shi zai gyara kuma babu inda zakuje"
"To idan kuma tana buk'atar taimako fa?" Moon ta tambaya tana dariya,
"Inma uban taimako take buk'ata dai babu inda zaku dan dukan ku dai babu likita balle ta dubata kuma ita ai nasan kafin ma ta naimi taimakon sai ta fara taimaka ma kanta dan haka baku zuwa"
Fad'owa cikin falon yayi kosu dake zaune basuji sallamar shiba dan iyashi da yayi kayan shi shi yasan yayi abinshi,
Babu wacce ya Kala tsakanin Sultana da Moon balle susa ran zai amsa gaisuwar su, ita kuma tun kallon farko datayi ma fuskar shi tasan cewa akwai matsala yanda taga fuskar nashi a d'aure irinta shanu har fiyema da yanda yake daure musu ita a dah,
Hannun ta ya kamo batayi musu ba ta mik'e ta bishi a sanda ya jata zuwa cikin d'akin daya maida nashi anan kasan dan itama tana buk'atar keb'ewa dashi dan taji abunda ya same shi ya koma haka,
Maida kofar d'akin yayi ya rufe sai faman huci mai zafi yake fesarwa,
Kallon shi takeyi hankali a tashe jin baice mata komai ba bayan shigar su d'akin,
"Ya'ya maiya sameka?
Baka da lafiya ne?
ko wani ne ya b'ata maka rai?
Meya faru?"
Sai da yasa hannu ya yamutsa gashin kanshi kafin yayi taku biyu ya matso inda take,
"Meenal Ina sonki"ya fad'a da karamar murya
"Nima Ina sonka"
"Kullum fatana da burina akan ki shine ki zama mallaki na"
"Nima Ina burin ganin hakan ya kasance a tsakanin mu"
"Ke k'adaice a cikin zuciyata tunda kika shiga cikin ta kuma na rufeta ruf ta yanda babu wata macen da zata k'ara shiga ciki bare tayi kwadayin samun gurbin zama kin san da haka?"
"Nima kai kad'ai nake so dakai kuma Nike fatan in rayu har gaban abada"
"Idan nayi addu'a zaki amsa min?"
"Eh mai zai hana!"
"Allah ya miki Albarka Hajiyata,"
"Ameen" ta amsa
"Allah ya cika miki duka burin ki na alkhairi ciki harda zamowa matata,"
"Ameen"ta k'ara amsawa tana rufe fuska da tafin hannun ta
"Ina addu'a allah ya tsone idon mak'iyan mu ya kuma toshe idon duk wata macen da zata ganni tace tana so balle kuma ta kawo mana wata tangard'a a tarayyar mu"
"Ameen" ta k'ara amsawa cike da shauk'i tana jin ta acan saman gajimaren soyayya,
"Kema kuma Ina addu'a da fatan Allah ya nakasa duk wani namijin da idan ya ganki zaiji yana sonki ko kuma yayi burin mallakar ki balle kuma har yace zai gabatar da kanshi a gaban iyayen ki da sunan yana son auren ki,
Ina kuma rok'on Allah duk wanda zai kawo ma aurena dake tangarda allah ya kashe shi ya mutu ya huta muma mu huta"
"Ameen" ta amsa dashi sai kuma can kamar wacce aka zabga ma mari ta zaro ido,
"Heart wannan wace irin addu'a ce haka, babu kyau fa musulmi yayi ma d'an uwan shi musulmi mugun baki balle kuma fatan mutuwa"
Ta fad'a a shagwabe,
"Amma ai dani nace allah ya to she idon duk macen da zata ganni tace tana so kin amsa da ameen"
"To ai wannan daban"
"Ok in wancan daban kenan wannan ma d'aya ne da wancan insha Allah duk wanda zai kawo min matsala a maganar aurena dake sai ya mutu idan bai janye ba dan inaji a jikina kedin rabona ce "
"Gaskiya nidai ba amin ba, oh dama saboda kazo kayi ma yan uwana muguwar addu'a shi yasa ka taso tun daga kaduna kazo nan Ina ta kiran ka baka iya d'aukar wayata ba, wani munafukin ne ya kiraka ya baka labarin abinda yake faruwa ne ma?"
"Oh ashe dai akwai masu yin bakin cikin aurena dake d'in kenan tunda har kin ma sansu?"
"Aiba laifi bane idan d'an uwa yaso yar uwar shi, da kai dasu dukan ku *DANGINA* ne yanda kake takamar kana da alaqa dani haka suma dan haka banga dalilin da zai sa kabi su da muguwar addu'a ba, idan addu'a ne ai nice ya dace inyita akan ka tunda nasan yanda kake da farin jini a wajen mata amma na rintse ido nace bana ganin kowa sai kai bayan nasan ko auren ka nayi ban isa in hana wasu Matan son ka ba"
A matuk'ar fusace kamar dai wanda ta kalli girman shi ta zaga cike da hayagaga ya fara maida mata martani da cewa,
"Wallahi³,
Sai da ya maimaita rantsuwar wallahi sau uku kafin ya d'aura da cewa,
"Kinji rantsuwar musulmi, to wallahi ki bud'e kunne kiji da kyau ko sun k'i ko sun so saina aure ki, bawan shi wancan Yayan baban naki da yake nuna ikon shi a kanki kullum ba kinaji koda ace duka *DANGINA* da naki dangin ne a yanzun sukace zasu k'alubalance zancen aurena dake kuma su juya min baya ni nan AK sai na aure ki sai dai duk wanda bazai iya gani ba yasha poison ya mutu,
Dan haka kodai kije ki fad'ama wancan yayan Baban naki cewa ni dai ni kike so kika kuma fitar a matsayin mijin aure ba wad'ancan lusaran da suka gabatar da kan su a wajen shi ba,
ya aura miki ni kowa ya samu kwanciyar hankali ko kuma wallahi in saceki in d'aukeki daga k'asar gaba d'aya babu mai k'ara ganin mu ko jin labarin mu har sai ranar dani naga dama na dawo dake,
Shawara nike baki kodai kije ki fad'a mishi gaskiyar cewa ni kike ra'ayi kike kuma burin aure,
Ko kuma ni in d'auke ki ta yanda bazai k'ara ganin ki ko jin labarin inda kike ba balle yayi tunanin k'ara had'aki aure da wani sakaran, shawara ya rage ga mai shiga rijiya, nayi sake a shekarun baya wanda saken nawa ne kuma yasa na rasaki a wancan lokacin,
A zaton ki mahaukaci neni dazan sa ido Ina kallo shi Yayan baban naki ya k'ara ba wani can da bai cancanta ba auren ki kamar dai ke kad'aice Ya mace a cikin ahalin ku?
Wallahi tunda har kika sake na sauke girman kaina na iya fitowa na shaida ma duniya cewa Ina sonki to a yanzun dai banga uban da zai fito yace zaiyi takara dani wajen neman auren ki ba, ki d'auka cewa wancan auren da aka miki a baya a mafarki kawai ya faru kamar yanda nima na d'auke shi matsayin mummunar mafarki, yanzu ne zakiyi aure kuma ni d'in nan nine mijin ki"
Hannu ta d'aga mishi
"Dakata Malam idan zakayi maganar ka kayi shi iya tsakanina ni dakai amma kar ka sake kayi zaton cewa dan kace kana sona hakan zaisa in zuba ido ka raina min ahali balle kuma har rainin wayau yasa ka tab'o shi wanda kake kallo a matsayin yayan babana,
To bari kaji shi din ni ban tab'a mishi kallo a matsayin yayan ubaba tunda nayi wayau a ubana nike kallon shi har yau da gobe da jibina zuwa karshen numfashi haka zanci gaba da kallon shi,
Shi dai da kake son aibatawa shine ni domin shi yayi tsaye wajen samar min da gatan da har kai dama wasu kuka gani kukayi sha'awa dan haka ina son in tabbatar maka da cewa shi din dai akalar rayuwata duka na damk'a mishi ita a hannun shi yanda duk ya juyani haka zanbi shi ba tareda tambayar dalili ba dan duk wanda zai nuna min so ko kauna harma da kulawan dakai kake ganin kana bani to a bayan nashi ka biyo,
Wallahi da ace an halatta wa mace kin yin