Showing 183001 words to 186000 words out of 190771 words
kuma ka amsa"
Ihun dariyar sune ya tashi Hajiya daga bacci bayan ta farka ta d'an jima a kwance tana son ta tantance daga ina dariyar yake fitowa ko dai cikin bak'in da akayi ne wani ya kawo mata tsarabar aljanu masu dariya,
Jin dariyar yaki d'aukewa ne ta mik'e ta sauko daga gadonta tana karanta ayatul kursiyu a bayyane ta bud'e kofar d'akin ta fito,
Hasken wuta ta hango daga cikin d'akin meenal kuma daga nan takejin dariya dama k'ananan surutai,
"Wai yaron nan biyo yarinyar nan yayi ita kuma munafukan ta bud'e mishi kofa ya shigo suke min iya shege a cikin sashe?"
Kofar d'akin ta fara bugawa,
"Kai Abdul tattaro Matar ka kuzo ku barmin sashe bazaku hanani baccin dare ba wallahi,
Ke kuma badai ni zaki juya ma baya ina tausaya miki ke kuma bakyajin tausayin kanki ba?
Da kaina fa na kulle kofar falon nan saboda dama nasan tabbas zai biyo sahu wato shine ya kiraki kikaje kika bud'e mishi kofar ya shigo, to ku tattaro ku wuce can ku k'arata"
Shi dama ai da gayya ya aikata abunda yayi dan haka babu b'ata lokaci yama yar Matar shi d'aukar chak ya sauketa akan gadon,
"Ka gani ko shi yasa ai nace ka koma,
ka koma kai kuma kak'i tafiya gashi nan ai kaja ta ritsa mu"
Bai kulata ba sai da ya ciro Hijab yasa mata kafin ya k'ara mata daukar cak tana wutsul² da kai mishi duka akan ya sauketa yak'i sai ma gyara rikon ta da yayi ya bude kofar ita kuma sai ta cusa fuskarta a k'irjin shi saboda kunyar Hajiyar daya rufeta,
Duk surutan da hajiya keyi bai tanka taba har suka sauka k'asa ya bude kofar falon sai da ya fita kafin yace da Hajiya " Hajiya sai da safe kuma dan Allah goben nan dai in Allah ya kaimu a raye kar ayi saurin zuwa kawo mana breakfast da sassafe idan mun tashi zamu zo mu amsa"
Yana gama fadar hakan ya wuce abinshi yabar Hajiya naci gaba da sababi,
"Wani shegen ka ajiye dazai muku girki?
Ai kuma kunyi da y'a wallahi bacci kuma idan k'unso ku yini goma kunayi jarababbu kawai".
*UMMIEE CE*✍🏼
[10/18, 3:06 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA*👨👩👧👦🔱⚜️
*BOOK 2*
*INA MAI CIKE DA FARIN CIKI A YAU DA ALLAH YA BANI IKO NA GANIN NAKAI K'ARSHEN WANNAN LABARIN MAI SUNA A SAMA*
*NAGODA KWARAI GA MASOYA WAD'ANDA SUKAYI JIMIRIN BIBIYAR LABARIN TUN DAGA LITTAFI NA D'AYA HAR ZUWA YAU, KU SANI CEWA UMMIEE ZARIA NA KAUNAR KU KUMA NA YABA DAN HAKA NIKE MA KOWA FATAN ALKHAIRI,INA SONKU³ SAU A DADIN DA BAKI YA GAZA FURTAWA YAN GROUPS DINA FAMILY HOUSE DA DANGINA COMMENT SECTION DAMA SAURAN GROUPS NAGODE KWARAI INA FATAN ALLAH YA HAD'AMU A GABA CIKIN AMINCIN SA*
*BAYAN WASU KWANAKI*
Amarci sosai ake gurza tsakanin AK da Amaryar shi wanda tun Hajiya na yawan surutu in taga sunyi wani abun har dai yakai dan dole ita da kanta ta gaji ta shafama kanta lafiya ta kawo ido ta zuba musu,
kuma dan wulakanci basu tashi barbad'a ruwan rashin kunyar su ako ina sai sunzo sashen ta, tayi kora harta gaji amma sunk'i suyi zuciya su dena zuwa mata sashe, dan haka ta taso AK d'in a gaba da mita cewa yayi da jiki ya kammala gyaran gidan shi na Kaduna ya kwashi matar shi subar mata gida ita bazata iya gani ba dan kar suja mata makantar wuri,
shi kuma yace mata barin Zaria ba yanzun ba har sai sun bar mata d'an raino dan in suka bar gidan tun yanzun ciwon kewar su yana iya kamata.
Acan unguwar malamai ko maganar gidan Malam da Meenal ta bashi ko ana watse bikin Meenal d'in yaran gidan mazan su da mata kowa ya bada nashi gudun mawar wajen sanyama gidan kayan furniture da sauran su ana kammala gyaran gidan kuwa suka shirya walima gangariya Malam yanaji yana gani dai haka shida iyalan shi suka koma sabon gida aka bar Baba Adamu da Baba Auta a family house suda sauran ahalin,
Soyayya tsakanin Bash sa Sultana kuwa abu dai kamar wasa tun tana basar dashi tana nuna ita batayi har dai da taimakon su Meelat, Maryam, Moon da ita kanta Meenal din wanda suka tayashi yak'in neman zab'e a fadar Sultanar daga k'arshe dai sunci nasara ta amsa sai gashi a hankali abubuwa sun kankama dan koda Bash ya k'ara tura iyayen shi wajen Malam a karo na biyu Malam bai b'ata musu lokaci ba a gaban iyayen nashi ya kira Sultanan ya zaunar ya kuma tambaye ta shin ko tana son Bash d'in? kuma da yardar ta ya turo a nema mishi auren ta?"
Bata tsaya ba sharia wahala ba itama ta amsa da cewa eh, bayan ya sallameta tabar falon mahaifin ta ya kira ya mishi bayanin halin da ake ciki kuma yarinya ta amsa cewa eh tana so dan haka yana so a basu dama suje can Abuja su nemo auren ta,
Alhaji Mahmoud yaso ace Malam ya zartar da komai amma sai Malam din ya zame akan gara dai ya basu ranar da zasu je shi sai yayi ma iyayen bash din jagora,
To dai da yike magana ne na manya babu wani kolo² ya basu ranar da zasuje dan haka iyayen Bash suka bar gidan Malam cike da farin ciki *wannan kenan*,
Itama Maryam a gefen ta ana gama bikin su AK Sadeeq ya sata a gaba da cewa shima fa a yanzun ya fasa wani jira har saita kammala karatun,
Tunda dai yan watan ni ne suka rage musu kawai tayi hak'uri ta k'arasa a cikin d'akin ta itama kamar dai sauran kawayen ta,
Taso ta bujire sai dai da wuri ya taka mata burki wajen kai maganar gaban manya babu b'ata lokaci kuma aka sa bikinsu sati d'aya tsakanin su da nasu Moon ita kuma Sultana bayan zuwan su Malam Abuja wata d'aya kachal akasa nata bikin dan haka nasu Sultanan za'a farayi kafin nasu Moon da Maryam d'in,
AK tuni ya koma KD yaci gaba da gudanar da abubuwan shi sai dai yanzun a maimakon weak ends da yake dawowa zaria sai ya mai dashi duk bayan kwana d'aya ko biyu, wani lokacin ma bazai fad'a mata cewa yana hanyar zuwa ba sai dai kawai ta ganshi kwatsam duk da bako yaushe yake tareda ita ba hakan bai rage komai na daga kauna da kulawar da suke ba junan suba.
***
Bayan wani lokaci da bikin su Meenal hutun yan makaranta ya k'are dan haka bak'in gidan Hajiya suka fara haramar komawa gidajen su akan sai bikin Moon kuma idan Allah yakai rai zasu dawo,
Dan haka ana gobe zasu tafi suna zaune a falon Hajiya suna hirar dare Hajiya ta kawo nata batun da cewa,
"To dai gashi naga sai shirin barin gari gobe kukeyi amma kaf cikin ku har yanzun banga wanda ya dunk'ulo yan kud'ad'en shi yace min Hajiya ga wannan gudunmawa naba,"
"Gudun mawar me kuma Hajiya? Akwai wani sha'anin da za'ayi ne bamu da labari?"
Baba Usman ya tambaya
Amsa mishi tayi da cewa,
"Sha'ani kai !
inace nan har akaci aka sid'e bikin d'anku babu wanda a cikin ku hankalin shi ya bashi cewa bari ya bani gudun mawa zan aurar da jikata ah ah ko koh dan kuma kuna aurar da d'a,
shi kenan ni kuma bazaku bani nawa gudun mawar na auren jikata ba,
In takamar ku shine kun ba uwarta gudun mawa naga dai uwarta daban ni kaka marigiya daban,
Kuna ganin dai yanda suka bugi k'irji suka gyarama yarinyar nan takwarata sashenta komai acan acan wallahi babu ne kawai basu siyo sun kawo ba,
To yanzun kuma dashi naku d'an ya kammala ginin gidan shi so kuke in saka ido su iyayen nata ne zasu k'ara zuba mata kaya a cikin wancan gidan shima?"
"Hajiya nifa na riga nayi oder d'in komai da za'asa a cikin gidan ban fad'a miki bane dama naso sai komai ya kammala sai in kaiki ki duba abubuwan da babu sai a k'arasa kafin mu tare acan..... "Cewar Ak
Katseshi Hajiya tayi da cewa,
"Kai dallah can matsa bani waje ina magana da iyayen ka kana samun baki ko kaji na kira sunan ka a zance nane?,
In kayi hakuri ai dana gama dasu kanka zan dawo ko ce maka akayi na manta da kaine?
Da kake zancen sa kaya a gida kuma Allah ya kyauta jikata ta dogara da kayan da miji ya siya salon wata rana kai ko yan uwanka kuyi mata gori ah ah wallahi,"
"Haba Hajiya waye zai mata gori kuma?"AK ya tambaya yana b'ata rai,
"To bari kaji in ma siya zakayi sai dai ka tabbatar da cewa da sunan ta ka siya,
kayan nata ne halak malak ta yanda ko yau ka fad'i ka mutu babu mai sanya su cikin sahun kayan gado atoh namiji kuma da gadara ko koh salon in yan uwanka suka san cewa kaine ka siya su dunga zuwa gidan suna mata abubuwa isa²? halin dangin miji kuma ni wanne ne za'a layance min ni Aminatu"
Umma ne ta amshi zancen da cewa,
"Hajiya ai ba laifi bane idan yace zaisa kayan daya siya a gidan tunda ai koda ace aure bai had'asu ba shid'in ai yana da halin da zai d'auke ma iyayen shi kayan d'akin k'annen shi mata kuma ita Meenal din ai bata da banbanci da kannen shi tunda dai Jidda ce ta haifeta kamar dai sauran jikokin gidan"
Katseta Hajiya tayi da cewa,
"Shi yasa ma nima yanzun a gaban ku na shaida mishi cewa zai zuba kayan ne da sharad'in cewa kayan mallakar meenal ne ba nashi ba,
Yo nawa akayi da zarar k'addarar da ba'a fata ta gifta tsakanin miji da mata sai gori ya tashi, ko kuma in mijin ya mutu yan uwa sai suzo suyi bake² suna kurin cewa ai nasu ne ya siya kayan ba daga gidan su ita matar ta kawo ba,
Kuma ni koma dai menene bazai hanani amsar kudin gudun mawa a hannun kuba garama ku had'a ku bani tun yanzun basai zuwa gaba idan wasu hidimomin sun taso ku fara min kame² ba ni ban yanke ko nawa nike buk'ata ba balle kuce na tsanan ta kar kuma mutum ya fara nufo ni da wasu yan kud'ad'en da basu fi k'arfin in dunkula inyi kyautar su tashi d'aya ba"
Yanda Hajiya ta kafe dole sai da kowa ya sauke mata nashi gudun mawar mai nauyi in ma baka da cash zatace kayi mata transfer,
Wadanda kuma sukace sai sun koma zasu tura mata tasa an rubuta mata sunan su a cikin yan bashi,
Bayan tafiyar mutanen gidan kuma tabi AK har can Kadunan inda suka tafi tareda Hassana suka duba sauran abubuwan da gidan ke buk'ata aka siyo akasa, sai dai koda AK ya tambayeta akan yaushe Meenal zata tare anan din sai cewa tayi wani tarewa kuma ai hak'uri kawai zaiyi daga nan har zuwa lokacin bikin Moon zuwa lokacin itama Meenal ta gama jigilar zuwa makarantar da takeyi in yaso sai ta dawo gaba d'aya.
Haka rayuwa yaci gaba da gudu babu k'ak'kautawa,
Raheenat ta gama wanka tuni dan haka Malam yace ta dawo gida tunda dai ai ba zaman takaba zatayi ba, dan haka ya tura aka d'aukota ita da kayanta tana kuka mutanen gidan nayi haka suka rabu tunda mai rabawa ya raba,
Bayan komawar ta Zaria
a lokacin ne shi kuma kanin mijin ta ya bijiro da batun cewa yana son Malam ya bashi auren ta saboda ta koma taci gaba da kula da d'an data Haifa dama sauran da suke wajen shi a Abuja,
Malam baik'i ba sai dai ya nemi jin ta bakin Raheenat d'in a zaton kowa sun d'auka zatayi murna da hakan kodan saboda rik'on yaranta sai dai ita kuma ta buga k'asa akan cewa bata auren shi,
Kuma yarama da ake magana ai tun kafin uban su ya mutu ya kwashe su ya basu shida matar shi tana musu fatan Allah ya tayasu rik'o,
Dan kowa yaga yaran yasan basu rasa komai a wajen suba dan dashi da matar shi sun rik'esu kamar sune asalin iyayen su ba Raheenat da marigayi ba,
sai yanzun dan k'asa ya rufe idon mijin ta shine shi k'anin shi zai lallab'o yace wani wai zai maye mata gurbin yayan shi saboda yaran ta,
To inda ace kuma itace ta mutun ba mijin bafa?dole dai ai a gefen uba yaran zasu rayu
Haka dai akayi ta cakalkala zance dan dole dai kowa ya shafama kanshi lafiya bayan abubuwan sun lafa ne kuma Ya Abakar tsohon saurayin Raheenat d'in ya yunk'uro ya fara nuna kulawan shi a kanta da d'an da take goyo duk da cewa bawai ya fito mata fili akan yana son maida Soyayyar su na baya ne sai dai duk mai hankali in ya kalli abun yasan me ake nufi,
shima dai tun bayan daya rabu da Raheenat din a wancan shekarun k'asar ya bari yaje yana cigaba da k'aratu bai dad'e sosai da dawowa ba kuma tunda ya dawo ake mishi zancen aure amma bai maida hankali ba can Abuja yake zaune a yanzun haka yana aikine da central bank,
To dai zamu iya cewa tsohuwar soyayyar da aka binne ce ake kokarin tono ta domin shi dai bayan da yaga cewa boye boye bayayi dole ya fito tsaya tsayin daka cewa yaji ya gani Raheenat dai yake so bai damu da cewa ai tayi aure harda rabon yara uku ga kuma wani tana shayarwa yanzun ba,
Shifa a yanda yaso so yayi a d'aura auren su ta tare a gidan shi taje can taci gaba da rainon Umar sunan yaronta wanda sukai ma lakabi da Khalifa itace tak'i akan ya daiyi hakuri ba yanzun ba har sai ta yaye,
Sultana ma ta koma Abuja inda ake ta shirye shiryen gabatar da bikin ta dan acan Abujan za'ayi komai kuma acan zasu zauna ita da Bash d'inta,
*Bari mu lek'a gefen Teemah matar Sarki*
Tun bayan tarewar ta a sabon gida babu wani abu wanda yake d'aga mata hankali domin dai ko babu komai gata tare da yayan ta wadanda a yanzun ne take k'okarin nuna musu kulawa dan ta gyara kuskuren da tayi a baya,dan bayan dawowar su hannunta sam haka sukak'i sakin jikin su da ita kamar dai ba uwar data haife suba, babu shiri ta fara kokarin jansu a jiki ta hanyar daukan su su fita shopping a tare ko wajen wasannin yara, wani lokacin ma tare dasu take kwana a d'akin su,
Da Alama dai kamar yanda tace ta tuba to tuban na gaskiya tayi bawai tuban muzuru ba dan wallahi sosai ta canza halayyanta da kuma yanda take mu'amala da mutane a yanzun,
Bata da damuwar komai dan babu abinda Sarki ya rageta dashi na daga soyayya da kulawar da yake bata sai dai lafiyan jikin ta ne kawai da yayi k'aranci yau lafiya gobe ciwo laulayi dai irin na masu ciki a haka dai take jurewa tana kula da iyalan ta iya iyawarta,
A sanda zancen neman auren Sarki ya bayyana a cikin dangi kowa ya sani yan gulma sun so sukai mata labarin kamar yanda suka saba labarta mata abubuwan dake gudana a cikin ahalin tun ma tana zama a Lagos,
Sai dai abinda basu sani ba shine tun a ranar da brigadier ya sauka a kadunan kafin su isa Zaria gidan ta ya fara biyawa ya sauka shida abokan shi,
Ya kumayi amfani da wannan damar wajen yima ita Teemah din nasiha a matsayin shi na mahaifin ta,
Ya lissafo mata tarin damar makin data samu a baya amma tayi fatali dasu saboda kawai tana tak'amar cewa mijin ta yana sonta yana fatan cewa a yanzu zata an kare wajen ganin ta gara kurakuren ta dan samun nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, dan yana sane da yanda tayi amfani da son mijin ta gareta ta taka mishi darajar Dangi ciki harda iyayen shi,
Ya kuma bud'e mata gaskiyar zancen cewa kar tayi zaton ko jama'a basu san abinda ta aikata na ganin ta tarwatsa auren da mijinta yayi a baya ba,
Ah ah kowa ya sani an dai juyama zancen baya ne saboda darajar su iyayen ta da kuma yayan data haifa,
Amma kar tayi zaton ko dan ta aikata hakan shine zai hanashi k'ara neman wani auren tama gode Allah da yasa har yanzun mijin nata bai canza daga matsayin daya bata a baya ba sai dai ta sani yanzun hakan ma zancen auren mijin nata ne ya kawo shi garin shine kuma wanda zai jagoranci auren,
Ya kumayi mata nuni da cewa taji tsoron Allah wannan karan kartace zata k'ara jefa kanta ga aikata shirka domin dama ne Allah ya bata nata gyara kuskuren data dad'e tana aikatawa, yanzun ne lokacin da zatayi yak'i da tsohon halinta na mugunta da kuma son kai,
kar tace zatayi mugunta domin dai in muguntar da tayi bai dawo kanta ba tofa yana iya afkawa kan yayan data haifa dan gasu nan dai har sun fara zama yan mata,
sannan babu laifi mai girma irin shirka ta duba ta gani cewa da tana da cikakkiyar lafiyar da take gudanar da rayuwar ta yanda take so amma sai gashi a yanzu dududu wata nawa ne data nemi lafiyar nata ta rasa?
Aiko wannan ya isa taji tsoron Allah tasan cewa shine ke tsarama bawa kaddara ta faru kuma a yanda shi Allah yaso tunda gashi rabuwar Sarki da Meenal hakan bai hanashi yace zai k'ara neman wani auren ba kuma tayi hankali idan har tace zata matsa ko kuma ta tada hankali k'aramin aikin ubangiji ne ya kauda ita a cikin duniyar kuma mutuwar ta bazai sa a fasa komai ba iya kacin bayan an haka k'asa an burneta ayi zaman makoki na kwanaki kadan bayan hakan kuma shi