Showing 144001 words to 147000 words out of 190771 words
ake gabatar wa a yayin sa rana suka hango domin harda su tabarma da kafet ga kuma setin akwati mai guda uku da kit tarin kwalayen dake wajen da drinks ko kasa kirgawa sukayi suna da yawa, kus kus suka farayi a tsakanin su babu dai damar fitowa a ganar ma ido dan Baba Malam yana gida,
Sai da aka sauke komai kafin Baba Usman yake cema Hajiya,
"Zamu sa ayi mana iso ne ko zamu shiga ciki ne dan naga k'ofar falon na Malam a bud'e?"
"Wani iso kuma Usmanu? bayan mun riga mun kawo kan mu ai munyi mai wuyar"
Juyawa tayi inda yaran ta basu umarnin kwasar kayan zuwa falon Malam suko dama umarni suke jira dan haka tuni suka fara aiki,
Yaran gidan manya maza dake zaune a falon Mommy Hauwa wato su Sa'eed dasu Farouq ne suka fito daga falon suna ma su Baba Usman Barka da zuwa, ita dai Hajiya bata bi takan kowa ba tayi gaba tabi sahun yaran da suka kwashi kaya zuwa sashen Malam,
Da sallama yaran gidan suka d'uru cikin falon na Malam ko wannen su d'auke yake da abinda yake iya d'auka na daga kayan da hajiya tasa su kwasowa zuwa nan d'in,
Wasu huhun goro suka kwaso, wasu kwalayen biscuits wasu kuma na sweet kaya ne dai gashi nan kamar masu shirin bud'e shago,
"Kai daga ina wannan kayan kuma?
Waye yace muku ku shigo dashi nan?"
Malam ya tambaya a tsawace,
Alhassan yaron ya sa'eed ne ya amsa ma malam da cewa,
"Hajiyar tudun wada ne sukazo ita da wasu bak'i kuma ma itace tace mu shigo da kayan nan falon ka"
Yaron yana rufe baki hajiya ta shigo falon da sallama ayarin ta suna biye da ita a baya suma sallama d'auke a bakunan su,
Gyara zama Baba Adamu yayi daga inda yake zaune yana amsa sallamar masu shigowar, a cikin zuciyar shi ko cewa yake aiki ga maiyin ka, wato Hajiya taji shiru shine tayo mai gaba d'aya, satan kallon Malam yayi sai yaga fuskar nashi da d'an sauk'i yanzun sab'anin d'azun daya d'aureta yasan kuma sakewar fuskar dan zuwan bak'in da baiyi zato ko tsammani bane a yanzun, lallai ranar yau Allah ne kad'ai yasan abinda ya boye a cikin ta sai fatan Allah ya mana mafi alkhairi kawai.
"Barkan da zuwa" daga Baba Adamu har Malam suka dungayi ma su Abba Ahmad su kuma suna amsawa,
"Bismillah ku zazzauna ga wajen zama" cewar Baba Adamu a sanda ya mik'e tsaye daga inda yake zaune yana taron su,
Zazzaunawan sukayi dan akwai isashen kujerun zama a falon su Ya Farouq da suka kwaso sauran kayan suka shigo dashi suma suka jera a tsakiyar falon inda yaran suka zuba nasu, gaisuwar su suka gabatar ga bak'in kafin suka mik'e,
"Kai Abdul shiga cikin gida wajen iyayen ka su baka ruwa ka kawo masu kawun nan ka"
Cewar Baba Adamu,
Ficewa Abdul din tayi, su kuma su Ya Sa'eed sai suka koma gefe can ta wajen kofar falon sukayi zazzaune,
Saida aka gama jerin gwanon gaishe gaishen da za'ayi kafin Hajiya ta jefo nata zancen cike da barkwanci take mai cewa da Baba Adamu,
"Haba Malam Adamu kai kuma hakayi daga cewa idan ka dawo zaka samu Yayan ka da zancen shi kenan kuma sai muji shiru kamar dai an aiki bawa garin su,"
"Ayimin aikin gafara Hajiya abubuwa ne suka d'an shamin kai amma yanzun haka maganar da muka gama tattaunawa da Yaya kenan dan dama yau nike son zuwa can gida akan maganar"
"To ai nidai gajiya nayi da jira nace gara dai in tuso keyar su mu taho ayi mai yiwuwa shi yasa ka ganni da rana fatse fatse kasan yan hausa na cewa zuwa dakai yafi sak'o yau dai nace da kaina zanyo jagora inzo ayi komai a gaban idona dan su kullum idan na tambaye su ya ake ciki saidai suce min kai suke saurare baka tab'osu akan maganar ba,
Niko naga ai mai nema da zafin nema akan sanshi to dai ka ganmu da shirin tsaff muka taho wallahi dan nidai sam banga abinda zamu tsaya muna jeka ka dawo akan shiba kai koh abune ya zama duk na gida zan aura ma takwarata miji dole inyi da jiki,
Yanzun dai ya ake ciki ? Injin dai riga ka gabatar ma dashi Malam zancen neman? dan nidai ka gani ganin idon ka da shirina tsaf na taho dan in koma gida da daddad'an labarin bayarwa"
Faffad'ar murmushi ya k'awata fuskar shi dashi,
"Hajiya karkiji komai tun farko ma da nasan kuna hanya dani zance kiyi zaman kine basai kin wani wahalar da kanki zuwa nan d'inba abinda yar nan dai kuma takuce ko kufa kuna da hurumin da zaku iya aurar da ita ba lallai sai mu ba"
Wannan karon Baba Usman ne ya amshi zancen da cewa,
"Ah ah Malam Adamu ai hakkin kune muzo mu nemi auren ta a wajen ku, kaga koh ai komin nisa dole mu taso zuwa inda kuke dan neman izini da yardar ku balle kuma nan da nan dai ga baki ga hanci,"
"Kwarai kuwa ko ga gida ga gida ne dole muzo mu nema ma d'an mu balle kuma nan sha'anin neman aure ai ba abin wasa bane"
Wannan k'aran Alhaji Musa ne ya amsa wato Mahaifin Billyn Ya Sa'eed ina fatan kun gane shima dai sirikin Malam ne tunda Yarshi tana aure a gidan.
Su dai su Farouq dake tare da Musty da wani abokin su AK Kamal ata wajen kofa k'asa² su Farouq d'in ke tambaya akan wa akazo nemar ma aure kuma wace Yarinyar ake son auren?
Musty ne ke musu bayani k'asa k'asa nan kuma jikin su yayi sanyi ta wani gefen sunyi ma Meenal murna ta wani gefen kuma suna jimamin abinda zai faru ne, yau dai su basu da abinda zasu iya cewa domin Allah ne kad'ai yasan abinda ya b'oye yasa abubuwan sukazo a haka,
Gyaran murya Alhaji Sani yayi wato Yayan Alhaji Hamza, kafin yaci gaba da magana a yayinda yaga kowa ya natsu ana sauraron abinda zaice,
Taron ya bud'e da addu'a kamar yanda addini ya koyar sai bayan da kowa ya shafa sannan ya k'ara gyara zama ya fara magana kamar haka,
"To Alhamdulillah anan dai koda ace bamuyi wani dogon bayani ba alamomin da kuma suffar da muka shigo da ita kad'ai ta isa bayyana ma kowa abinda yake tafe damu gareku,
Amma duk da haka mu masu nema Bazamuyi shiru ba,
Masha Allah kamar dai yanda aka saba tunda dai wannan ba shine alaqar farko da zamu kulla a tsakanin mu ba domin alaqa ta dade da kulluwa a tsakanin mu tun daga lokacin da kukaje kuka nemi auren Hauwa'u Jidda a wajen mu kuma muka baku"
"Kwarai kuwa wannan hakan yake" jam'ar wajen suka amsa banda su Ya Sa'eed dake can gefe,
Sai da akayi shiru shi kuma yaci gaba da cewa,
"Bayan Auren Jidda a cikin ahalin nan alaqa tsakanin mu daku taci gaba da habbaka ne daga sanda ta samu k'aruwar ta na farko,
Tana ci gaba da samun k'aruwar arziki alaqa na dad'a hab'aka, koba haka ba?"
Ya tambaya,
"Haka ne" suka amsa dashi suna gyad'a kai alamun tabbatar wa a gareshi,
"Alhamdulillah Allah yayi cewar silar shigowarta gidan nan shine silar kulluwar alaqa mai k'arfi a tsakanin mu domin yanda kuka rik'e mana ita da amana shi ya bamu kwarin gwuiwa wajen baku wata Y'ar namu a sanda kukaje nema ma d'anku auren ta koba haka ba? Dan da ace baku rike Jidda da mutunci ba bazamu baku auren Bilkisu ba"
"Wannan haka yake" suka k'ara maimaita wa, a cikin masu amsawar kuma harda Malam wanda yake amsawa cike da alfaharin an yabe su,
Cigaba yayi da cewa, "baku tsaya anan ba bayan Bilkisu kuka k'ara d'aukar yarmu kuka ba naku yaron, eh saboda ai itama Meenal din da kuke tak'amar takuce muma tamu ce kamar yanda kai Malam Adamu ka fad'a a d'azun"
Yar k'aramar dariyar raha akayi, Baba Adamu kuma ya amsa da cewa "kwarai Meenal taku ce Alhaji"
"To kaji gaskiya dai gashi kuma bayan ita yanzun kuma kun k'ara biyomu kun nemawa d'an gatan d'anku auren Yar mu Maimunatu wanda muna sa ran insha Allah nan da yan watanni ne za'a gabatar da nasu bikin koba haka ba kunga ko ai alaqa tsakanin mu daku takai kololuwar da ko yaro ya d'aga kai bai iya hango wa, dan haka ne yanzun bamuyi shayin zuwa nan d'in tafe da kayan mu ba dan mun san wuyarta dai mu nema ne a wajen ku mun san bazaku hana ba"
"Wannan haka yake" Baba Adamu ya amsa dashi shida Alhaji Kamal shiko Malam kauda kanshi yayi gefe,
"To yau dai zuwa mukayi dan mu nemarwa takwarar marigayi Abdul Khareem auren Yarku mai Babban suna munzo gareku da yak'ini muna kuma fatan Allah yasa wani bayyi mana shigar sauri ba?"
Tsit falon yayi shi Baba Adamu yayi shiru ne dan a ganin shi an kai gab'ar daya kamata ace Malam yayi magana yanzun kam,
Su kuma sauran yan falon sunyi shirune suna jiran jin amsa daga bakin mutum biyu ko dai Malam ya amsa musu ko kuma Baba Adamu,
Kafe Malam Baba Adamu yayi da ido dan haka dole badan Malam yaso ba ya fara magana kamar haka bayan yayi gyarar muryar daya saba,
"Alhamdulillah muna yi muku Barka da zuwa kuma duk munji bayanan da aka gabatar,
Kafin ku shigo mun zauna mun d'an tattauna da shi Adamu domin shi da kuka ba Sallahu shine ya d'anyi nauyin baki wajen isar min da sak'on ni kuma rashin sanin abinda yake faruwa yasa a jiya bayan mun gama karatun da muke gabatar wa a masallaci na gabatar da sanarwar bada auren ita Mamana ga Sheikh Naseer malamin dake mana karatu wanda ya kasance d'ane a wajen k'anwata Zahra wacce uwa d'aya uba d'aya suka haifemu kamar dai yanda kuka san bamu da yan uba,"
K'ananun maganganu ne suka fara tashi daga can bakin k'ofa inda su Sa'eed ke zaune, inda suke tabbatar ma juna da zargin su dan su dama tun jiya sun zargi cewa Meenal ce Malam yaba Shehi ba kowa ba, lallai ko akwai gwarama yau,
Gyaran murya Malam ya k'arayi, kafin ya d'aura da cewa,
"Sannan kuma bayan sanar war da nayi daren jiya safen yau ma na samu bakuntar mutum uku wadanda dukan su sunzo min har nan cikin falon nawa sun kuma gabatar da kansu a matsayin masu son neman auren Meenal din wadanda dukan su dangin tane na kusa, mutum na farko da yaxo akan maganar Yayan tane domin dai k'anin mijin da muka aura mata da farko ne shima yaxo yana rokon mu aura mishi ita yana son ta ya kuma yi alkawarin riketa da amana,
Mutum na biyu kuma shima yaro yayan tane domin da uban shi damu yaran wa da Kane muke,
Na ukun su kuma shima d'ana ne domin yaron k'anwar muce wacce ita kebin Adamu wato kunga ko dukan su ukun makusanta ne na kusa wanda in akace abi cancan ta dukan su sun cancanci a aura musu Meenal"
Dan shiru yayi sai dai kuma babu wanda ya amsa harya gama sauke ajiyar zuciyar shi yaci gaba da cewa,
"Bayan su ukun can kuma d'azun nan da azahar kafin isowar ku na k'ara samun bukuncin wasu manema auren nata inda suke shaida min cewa d'ansu yaso ita Meenal din tun kafin wancan auren nata amma itace a lokacin batayi saurin bashi dama ba acewar ta sai ta gama makaranta zatayi aure, suma dai fitaccin ahaline wadanda koba niba kowa zaiso had'a zuria dasu,
To gaku kuma kunzo kuma duka dai buk'atar d'aya ce daku da sauran duka dai auren uwata kuke nema...."
Katse shi Hajiya tayi saurin yi tun kafin ya gama feso maganar dake cikin bakin shi,
"Duk wannan lissafe lissafen da kayo ni basu ne damuwata ba domin duk cikin su ban cire mijin da zan iya sadaukar wa ita ba,
Shi Salman d'in in yana da kunya ai ko hanyar falon nan bazai biyo ka da zancen son auren matar da d'an uwan shi uwa d'aya uba d'aya ya saka ba, ko ya manta irin rikon sakainar kashin da d'an uwan shi yayi mata ne? Da badun jajircewa naba da kila har yanzun tana gidan shi a girke tana cigaba dayi mishi shara da wanke wanke,
Anji ba haramun bane amma dai ko babu komai ana barin halas dan kunya dan haka cire shi a lissafi wannan ba mijin Aminatu bane,
Mu gangara kan shi Hashimu yake kowa? Oho koma da miye sunan shi shima bai cancanci auren Meenal ba dan bazan yarda daga hannun mai mata d'aya ta fad'a hannun mai mata biyu da tarin yara ba sannan kuma ba wani darajar ta yake gani ba barin in baka labarin yanda hirar su ta kasance a gidana kafin yazo maka da zancen"
A gurguje ta labarta musu hirar Hashim da Meenal na ranar da yaje tudun wada kafin ta gangaro kan Aliyu,
"Shi kuma Aliyun in ba neman fitina da shegen kwad'ayi irin na maza ba ina shi ina batun k'ara aure?
Auren ma ya rasa wacce zaice yana so sai Meenal dan Allah kun tab'a ganin inda aka had'a gudun jirgin sama dana mota? Ina ai bama zai yuwuba dan haka shima na cire shi a lissafi,
Allah sarki bawan Allah Sheikh shikam wannan dai da ace bada jikana ya had'a nema ba wallah dako ni ina iya yi mishi tsaye wajen ganin an bashi mata!
Kuma ko yanzun ma karkuyi zaton cewa son kaine zai sa in zabi nawa jikan in barshi, ah ah wallahi ita dai Yarinyar ne na tabbatar da cewa jikana take so bashi wanda babanta ya k'ara zab'ar mata a karo na biyu matsayin mijin da zata aura ba, amma idan ana musu ana iya kiran ta dan aji nata ra'ayin aka su biyu,
Yauwa batun shi wancan yaron Bashar ne ko Bashir shi dai d'an gidan Master Wanda ake cewa suma sunzo d'azun to ku nasan kune baku san shiba tun a wancan lokacin amma ni nasan shi dan har suma yayi a falona ranar da aka d'aura mata aure shakarun baya,
Shima na cire shi a jerin masu neman aure dan koba komai wannan sha'anin na cikin gida ne bazamu kawo bare ba,
Yauwa ina magana akan Shehi da kuma Jikana Abdul,
Wannan dai ni kaf banga abunda za'a tsaya ba kai wahala ba, shi dai jikana shi yaga yar uwar shi saboda ra'ayin kanshi bawai dan wani ya tallata ko kuma a cusa mishi ita bisa dole ba, ah ah shi yaji ya gani cewa kaf fad'in garin nan k'asa dama duniyar gaba d'aya ita dai yaji ya gani yake so,
Duk kunyar dana san yaron nan dashi haka ya murtsiketa tass ya tareni za zancen cewa yana son yar uwar shi, wanda ni kuma dama tun kafin ma ya furta alamomin da yake nunawa sun tona mishi asiri a wajena kafin kuma ya furta mata abokan shi ya fara fesama su kuma suka sameni har cikin d'akina aminin shi ya shaida min halin da shi Abdul din yake ciki,
Inda ace naso to da tun lokacin zansa a shige gaba a nemar mishi auren ta a lokacin tunda bayan mutuwar auren ta ni daku duk munsan cewa bata tareda idda a kanta amma banyi Hakan ba,
Kunsan me yasa?"
"Ah ah Hajiya" da yawa daga cikin su da suka natsu suna sauraron ta suka amsa,
Ita kuma sai taci gaba da cewa,
"Saboda so nike ya tantance abinda yake ji akan ta, ni kuma so nike in gane zurfin da Soyayyar ta yayi a cikin nashi zuciyar,
Bana son inyi saurin shigewa gaba akan maganar ne saboda koda yake jikana bazan so ya sameta salin alin ba dan so nike yasan zafin ta yanda ko bayan auren zai riketa da kyau ba rikon sakainar kashin da wasu mazan sukeyi ma mata ba"
Dan dago kanshi malam yayi yana kallon hajiyar dan yasan dai maganar ta na k'arshe da biyu tayi shi,
Ita ko bata damu ba taci gaba da cewa,
"Dan haka sai nakau dakai ban nuna na gane komai ba har zuwa sanda ya gaji da nuk'u nuk'u dan yakeyi ya furta mata,
Tun lokacin daya furta kullum bashi da magana saina shidai in tura a nemo mishi auren ta surutun shi kuma bai sa nayi hakan ba duk da cewa duk da iyayen shi basa gari ina da damar dazan wakilta wasu su nemo mishi auren kuma a bashi amma banyi hakan ba, saboda so nike ya d'and'ana zafin da akeji a yayinda zakaga wasu mazan suna kaima abinda kai kake farauta cafka, hakan zai sa kaima ka jajirce, to Alhamdulillah duk wasu abubuwan da nike buk'atar tantancewa a tsakanin su na kammala ina kuma da tabbacin cewa ko yanzun aka d'aura auren su zasu rike junan su su kuma rayu cike da soyyaya shi yasa na had'o kan duk wad'anda suka dace a gabatar da komai a gaban su muka taho,
Mun taho da komai daya kamata tun daga kan kud'in gaisuwar uwa da uba har zuwa komai da ake buk'ata wajen gabatar da neman aure, domin a sanya mana rana, to amma yanzun zuwa na da kuma jawaban da naji daga bakin ku hakan yasa na canza ra'ayi bayan gabatar wa Ina so Uban shi ya biya kud'in sadaki kawai a wannan taron a d'aura aure gaba d'aya domin hakan ne kad'ai zai sa hankalina ya kwanta, jikana dai ba d'an iska bane baya shaye shaye baya sata, haka kuma baya caca balle yabi Matan banza duk inda aka shiga ko ina nasan jam'a zasu shede shi dan ba abanza yaci sunan da kakan shi yasa miba Mai Jama'a,
Kai Usmanu kun fito da kud'i a jikin ku ko nice zan biya mishi sadakin?"
Daga can bakin k'ofa kusan mutum hudu suka had'a baki