Showing 141001 words to 144000 words out of 190771 words
wacce ke magana dakai kuma bazawara ce wacce tayi aure shekuru masu dan tsayi wacce da ace tana da rabon ciki da haihuwa da tuni an sakata cikin matan da ake kira iyaye,
Alaqa ta ganin girma da mutunci ne ta had'ani da kai a baya kafin alaqar tamu ta rikid'e ta koma soyayya,
Na soka sosai a wancan lokacin ban kuma tab'a kawo rabuwa a tsakanin mu ba sai dai kuma ba haka Allah ya tsara ba, bayan aurena kuma ban tab'a tunanin rabuwa da Yayana na duk kuwa da irin zaman da mukeyi na kalar na sauran ma'aurata bane, ina so ka sani nayi yak'i da zuciyata sosai a kanka ban sarara ba har saida nayi iyayina wajen ganin na cire soyayyar ka dama duk wata damuwar da zata hanani karatu domin shi kad'ai nasa a gabana ba komai ba, banyi tunanin ajiye sauran sanka a zuciyata ba dan ban tab'a hango ranar mutuwar aurena zaizo ba, komai ya afku da sauri ta yanda auren ya mutu har na zamana ya dawo nan,
Nasan zakaji babu dad'i idan nace maka koda aurena ya mutu ban kawo ka a raina balle in neme ka,
Ka sani na riga nayi rami tuni na riga na burne komai dan haka sabon babin rayuwa na gina ma kaina, a hakan ne kuma d'an uwana ya gabatar da soyayyar shi gareni, abinda banyi zato ko tsammani ba"
Shiru tayi shi kuma sai ya mik'a hannu a sanyaye ya mika mata ruwa, sai da ta amsa tasha kafin taci gaba,
"Bash ina matuk'ar son Mai Jama'a, son da ban tab'a zaton cewa zanyi ma wani namiji ha irin son nike mishi, ina farin ciki idan nagan shi cikin farin ciki ina kuma jin rashin dadi idan ni ko wani ya b'ata mishi rai, ina son shi bawai dan yana matsayin d'an uwana ba, ah ah ina son shine kawai saboda shi zuciyata ta zab'a kayi hakuriΒ³"
Sai da ta maimata mishi kalmar kayi hakuri har sau uku kafin taci gaba dacewa,
"Bazan iya raba zuciyata da son shi in zab'e kaba, hakan kuma bawai yana nufin ina k'in ka bane ah ah har yanzun kallon ka nike a matsayin makusanci na domin ma baka matsayi na musamman a zuciyata batun soyayya nedai nike so mu barta komai ya faru akwai dalilin faruwar shi ni dakai Allah bai k'addara zamu zamo mata da mijiba"
Tunda taci gaba da bayani ya maida kanshi k'asa harta gama,
"Ba komai Meenal hakan ma nagode, kuma ina ma Dan mai k'arfin murna"
Murmushin yak'e,
"Baka manta sunan da muke kiran shi dashi ha ashe?"
"Taya zan manta kuwa? Yanzun dai muje ki takamin in wuce, yauwa kuma Hajiya tace tana gaisheki, muje ki takamin in wuce"
"Nagode Bash nima ina gaisheda Hajiya, amma kasan bani da number dinka kuma kake batun tafiya baka bani ba? "
"Kina buk'atar number na?"
"Eh mana ka sani ko a cikin yan Matan gidan mu in baka d'aya! Kuma koba ma haka ba aidai kasan na dad'e ban tambaye ka kudin anko da kaza ba,
Wai kasan me?"
Yana dariyar maganar ta yace ina zan sani yar Malam, ko yanzun ma kud'in kazar za'a amsa ne?"
"Ah ah wallahi badai kud'in kaza ba aini nafiso a siyo min kazar a gashen ta, dama zance maka ne yanzun fa nima k'atotuwar Hajiya ce wallahi motocina dai dai har uku"
Ta fad'a tana kad'a kai cike da kurari,
Fashewa yayi da dariya sosai,
Ita kuma sai ta d'aure fuska,
"Auw dariya ma kake min mai makon ka tayani murna duk masu tsada nefa yan yayi"
"Sorry sorry nifa dariyar murna nike miki tunda Allah yasa burin ki na mallakan manyan motoci ya cika saura wanne kuma, uhumm dama burin uku ne ai zama likita, matoci manya, sai ginama malam gida koh?"
"Baka manta ko d'aya ba yanzun biyu sun cika saura d'aya insha Allah shima saura kiris"
"To Allah ya sanya alkhairi kawo wayar ki in sa miki number din"
Mika wayar tayi ya amsa ya zuba nashi number din yayi saving da sunan shi kafin ya kira, saida kirar ya shiga ya yanke sannan ya mika mata wayar,
Fitowa harabar gidan sukayi fuskar su d'auke da murmushi Sultana wacce duk hirar da suke da Moon hankalin ta yana kan kofar falon ne ta taso,
"Kai murmushi fa naga kanayi?" Ta tambaya tana zagaye shi,
"Karki k'ara kulani ina ruwan ki dani?"
"Ke Meenal baki fad'a mishi gaskiya bane duk shawarar dana baki"
"Na fad'a mishi"
"Kuma shine naga ya fito yana murmushi?"
"Moon zoki janye yar tsanar nan a gaba na kafin inyi ball da ita"cewar bash,
"Wai nice zakayi ball dani kawai dan nayi tambaya,
To wai kai bakaji kishi bane ai kamata yayi inga ka fito fuska a d'aure kana cin magani"
"Amma kamar kina da ciwon mantuwa koh? Ina ce d'azun nan nace miki zan tayata son abinda take so? To abinda nike yi a yanzun kenan"
"Wai dama da gaske kakeyi? π³ ashe dai kana da kirki har haka, sannu to Allah ya k'ara hakuri"
"Ka dena biyema Sultana inba haka ba ko kwana zakuyi bazata dena saka kanayin surutu ba,
Nidai muje in nuna maka motocina karma kayi zaton labarin kanzon kurege na baka"
Can parking space suka wuce ta nuna mishi motocin sai da ya zagaye su duka ya kuma yaba, kafin yayi sallama dasu ya shiga motar shi yabar gidan su koma suka koma harabar gidan suka dasa sabon hira anan ne kuma takejin cewa wai ashe Hajiya ta kwashi bataliyan ta sun wuce gidan Malam,
Ita dai ranar yau bata san ko wacce kalar rana zata kirata ta, allah dai ya isa tsakanin ta da mutum uku, Salman Hashim da Aliyu duk su suka jawo mata koma menene suna dai zaune suna jiran jin sabon update daga gidan Malam.
A gidan Malam ko fitowar su Bash da iyayen shi yayi dai dai da dawowar Baba Adamu gida a wannan lokacin dan haka lafiya lau sukayi gaisuwa a tsakanin su, yana tareda gajiya shi yasa bai tsaya ba kawai ya wuce nashi sashen sai bayan da yayi wanka yaci abinci ne Aunty Murja take shaida mishi abubuwan da suka faru yau a cikin gidan na zuwa neman auren dasu Salman sukayi wajen Malam har zuwa kan su Bash da suka bar gidan a yanzun,
Dafe kai yayi cike da jimami,
"Akwai matsala ne?" Ta tambaya tana jiran jin amsar shi,
"Hajiya da su Usman sun nemi auren Meenal a wajena suna nema ma Mai Jama'a nasu tun ranar da mukaje nema ma Sarki auren yarsu ni kuma na shaida musu cewa zan yi ma Malam bayani sai yasa ranar da zasu zo ayi magana,
Wallahi abubuwa ne suka shamin kai banyi zaton cewa hakan zai iya tasowa a yanzun ba kuma, yanzun me zance ma Hajiya idan taji zancen nan bayan kuma su suna da yak'ini akai na shi yasa nasan basu taso sun taho wajen Malam ba tun lokacin"
Mikewa yayi ya fice daga falon dan gara yaje ma malam da batun tun yanzun kafin abubuwa su tab'arb'are Allah yasa dai sanarwar da Malam yaba Sheikh mata ba Meenal din yake nufi ba!
Dan in har ita yake nufi tofa akwai matsala gaskiya dan koshi bazai goyi bayan abunba indai yarinyar ta nuna bata so koda ko babu zancen AK a hannun shi balle kuma su yasan dashi suka dogara,
Malam kad'ai ya tarar a falon nashi saida suka gaisa kafin Malam din ya kora mishi bayani akan zuwan iyalan gidan Master wadanda ya gani, kafin ya koma baya kuma ya bashi labarin zuwan su Salman kamar dai yanda yasamu labari daga wajen matar shi, sai da malam ya gama nashi jawabin duk da ajawabin na Malam ya gane cewa su Salman maganar su bai d'ad'a Malam da k'asa ba,
Bayani shima ya gyara zama ya kora ma Malam din na auren dasu Baba Usman suka nema a wajen shi.
*UMMIEE*
[10/5, 11:23 PM] Ummiee Zaria: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 44*
Ya'ya ina ganin dai wannan karan ya dace muba Yarinyar nan dama ta zabi mijin aurenta da kanta! basai munyi mata zab'i kamar yanda aka saba yiba,
Duba da cewa dukan su wad'anda suka nuna muradin auren nata a yanzun yan uwa ne idan ka cire shi wannan da sukazo daga baya, wad'ancan ukun tun daga kan Salman har Aliyu duk wanda akaba ita d'an uwan shi zaiga cewa shi ba'ayi mishi adalci ba, amma kaga idan muka bata zab'i ta fidda wanda take so a cikin su da kanta dole sauran zasuyi hak'uri kuma baza'ayi kananun magan ganu akan hakan ba!,
Maganar shi d'ayan d'an uwan nata d'an gidan Ahmad kuma shima kaga ba abune wanda za'a ture ba tunda iyayen shine da kansu suka tareni da maganar saboda sun san cewa ina da damar dazan iya aurar da Meenal d'in,
Sannan kuma a bayanin su sun nuna min cewa su Yaran sun riga sun dai daita kansu dan haka kaga zancen mu muce zamuyi mata shishshigi wajen zab'ar mata miji wannan k'aran bai taso ba,"
Sai da Malam ya k'ank'ance idanuwan shi kafin ya jefoma Baba Adamu tambaya kamar haka,
"Wato Adamu dai so kake kace ni bazan zab'ar mata mijin daya dace da ita ba kenan?"
"Subhanallah haba Yaya yaza kace haka, wallahi ko kusa ko alama ba abinda nike nufi ba kenan taya zan kalli idon ka ince haka bayan duk yaran gidan nan tun daga kan yayyen ta mata har zuwa yan k'asa da ita kaine ka zab'ar musu mijin kuma suke zaune lafiya lau a gidajen auren su,
Itama abinda yasa nace haka saboda a yanda nata neman auren a yanzun ya kasance ne al'amarin ya dangana da duka ahalin ta biyu mu nan gefen uba da kuma can gefen uwa,
kaga dai kai yanzun tsakani da Allah idan kace kaine zaka mata zab'i kamar yanda ka saba na sani Ya'ya bazaka ce zaka bata shi d'an gidan Ahmad ba,
Idan kayi haka kuma su yan uwan Jidda bazasuji dad'i ba zasu kalleka a matsayin mai son kanka wato kak'i su kaba naka kuma idan aka duba kusancin duk abu d'aya ne,... "
Kara yanke shi Malam yayi wannan karon ma yana mai cewa,
"Dama ce maka akayi akwai wanda nike shakka ko tsoro a cikin su idan na tashi yin hukunci ga abinda nike da iko akan shine?,
ai ba tsoron surutun mutane nikeyi ba abinda ya dace nike aiwatar wa koba komai kafin in yanke hukuncin sai nayi hangen yaya goben su yaran zai kasance kuma Alhamdulillah ina alfahari da hakan domin kaf yaran dana aurar babu wacce take da matsala da mijinta suna can zaune a d'akunan su babu rashin ci balle nasha kaga auren miji mai ilimin addini ko tanan ya musu rana dan ni ban damu da aura ma yata wayayyen mutumin daku kuke hange ba mutum mai tsoron Allah nike buk'ata wanda zai riketa amana "
"Na sani Yaya kuma nima bawai na k'alubalance ka bane akan hakan sai dai su jama'a kallon da zasuyi ma hakan da ban, arziki dai nike roko dan Allah wannan karon ka bata damar zab'e a cikin su saboda ayi ma kowa adalci nidai bana son ayi abinda za'azo ana ganin laifin juna ko kuma zumunci ya tab'u"
"Adamu wai wakakeyi ma kamfe a cikin su? Shin a tsagina kake?
ko koh tsagin dangin matar kanin ka masu tak'ama da dukiyar da Allah ya basu?"
"Ko d'aya ina dai ganin laifin kainane sakama kon jin kirin da nayi ban samu damar gabatar maka da nasu batun atun sanda suka buk'aci hakan ba,
dan na tabbatar da ace tun lokacin na Kawo maganar gaban ka da hakan bata faru ba, koba komai kuma ai ido da kunya ace su nema mu kasa basu duba da cewa kwanan nan suma sukaba namu d'an auren yarsu duk da sunfi kowa sanin kusancin dake tsakanin ya'yan,
ka dai duba al amarin nan kafin kace zakayi hukunci Ya'ya idan kuma ba haka ba ni zanyi tunanin ko har yanzun baka son had'a zuria dasu ne kamar dai yanda ka nuna shekarun baya kafin auren Jidda da auta da kuma yanda ka dunga mu'amalantar ta bayan auren wanda kowa yasan baka sake mata ba sai bayan data haifo mana Meenal a cikin gidan nan, idan kuma abun nan ya tabbata nasan da yawan mutane suma irin hasashen da nayi zasuyi itama kuma kanta uwar Meenal d'in da ahalin ta zasu hasaso hakan dan haka nike rokon ka tsaya ka duba magana ta da kyau kafin ka yanke hukunci,
kayi hakuri kuma dan naji zancen sanarwar da kayi naba Shehi auren d'aya daga cikin yaran nan ina fatan dai ba ita Mama ka bashi ba?"
"AdamuΒ³"
Sai da Malam ya kira sunan shi sau uku yana amsawa kafin Malam din yaci gaba da cewa,
"Ka dai fad'amin abinda ya Kawo ka nan koh?"
"Eh yaya, amma ai baka bani amsa ba dan yanzun haka dai ban san me zance dasu Ahmad ba, shin in basu damar zuwa gareka ne ko koh dai wannan k'aran ka bani damar gabatar da abinda ya dace? Kar suji shirun yayi yawa su suce zasu zo nan dan bana son labarin nan yaje musu batareda sunji daga gareni ba"
"Adamu akwai wani abunda zaku iyayi ne a yanzun idan nace na riga na yanke hukuncin bada auren Meenal ga wani?"
Malam ya tambaya fuskar nan tashi a d'aure kamar tasowar hadarin kaka,
Shiko Baba Adamu d'an murmushi yayi shima yana gyad'a kai,
"Eh to idan ita Yarinyar tace taji ta gani tana son shi zab'in naka falillahil hamdu bani da abin cewa dan dama abinda take so shi nike mata fatan samu wannan karon,
Akasin hakan kuma inaga sai dai kayi hakuri a duba cikin k'annen ta sai abashi in baya muradi kuma sai ya hak'ura,
indai kuma Shehin ne kamar yanda nike hasashe ai duk d'aya ne nasan koshi bazai so ayi mata dole ta zauna dashi kamar yanda akayi mata dole ta zauna da Sarki a baya ba, ni dama tunda naji zancen nasan bazaka goyi bayan aura ma d'aya daga cikin su Salman Aliyu ko Hashim ita ba,
Shehin dai shine zab'in ka gareta kamar zuciyata ta bani, dan haka kafin ni dakai mu yanke hukuncin zan kirata in zauna da ita ta fad'a min gaskiyar wanda take so a cikin su biyu shehin ne ko shi Mai Jama'a dan ni nacire zancen wadannan bak'in da sukazo nan wurin ka d'azun tuni basu a lissafina"
Kallon mamaki Malam kebin Adamu dashi,
Wai shine yau Adamu keson ya k'alubalance shi akan auren Meenal?
Meenal fa ake magana ba sauran yaran gidan ba, to harshi zai fad'a mishi abinda ya dace da Meenal dama wanda bai dace da ita ba? Shida ko uwar data haifi Meenal din bazata nuna mishi son Meenal din ba,
Minene aibun Sheikh da har shi Adamun yake tunanin cewa Meenal zata k'ishi bayan tarin nasabar da yake dashi,
ai shi abun alfahari ne a wajen shi had'a zuri'a da Shehi kuma lissafin shi bai hango kowa ba sai Meenal yasan kuma itama zatayi alfahari dashi wannan karon,
"Yaya bari inje duk yanda ake ciki zuwa dare zan dawo in labarta maka"
(Nasan wasu zasuce Baba Adamu yayi tsaurin ido, sai dai in baku manta ba tun a farkon littafin na shaida muku cewa Malam da Adamu sak'o da sak'o ne sannan tun farko yanda Baba Auta yake tsoron Malam shi Baba Adamu baya tsoron shi haka, kuma kaf cikin ahalin babu wanda yake iya tsayawa a gaban Malam ya tsage mishi gaskiya irin shi Adamun, duk irin mulkin mallaka da Malam yakeyi akan kowa Adamun baya magana dan yasan cewa Malam ya isa dasu balle kuma yaran da suka haifa,
Amma abinda ya faru na mutuwar auren Meenal da kuma mutuwar mijin Raheenat hakan yasa yake ganin ya dace afara ba yaran gidan damar zab'arma kansu abokan rayuwa domin dai tun farko inda ace ita Meenal an barta tayi ma kanta zab'i da ba haka ba,
itama kuma Raheenat da aka d'auki tsoho mai tarin shekaru aka had'ata aure dashi ko sakandire bata gama ba da ace an jira ta gama aka bata dama da yanzun ba cikin taka ba take ba, duk da cewa yasan komai daya samu bawa Allah ne yakeyin shi amma lokaci yayi da za'a kawo canji a gidan kuma zaiyi amfani da kaunar da malam yake ma Meenal ne wajen cin nasara akan Malam d'in, bawai baya son ta da Sheikh bane ah ah in ta zab'i sheikh zaiyi murna da hakan kodan samu k'aruwar d'ankon zumunci a tsakanin su da yar uwar su, amma fa ya shirya tsaf wajen bata goyon baya a yayinda zata nuna bata ra'ayin shi Shehin.
A can harabar gidan ko motocin su Abba Ahmad ne ya shigo gidan a jere bayan an bud'e musu gate,
Dan haka suka layu a harabar gidan mota 3 ne sai Hilux cikon ta 4 wacce ke d'auke da tarin kaya mak'are a bayan ta,
Kasancewar yau gidan ya uni idanuwa da kunnen yan gidan a bude rass wajen ji da ganin kayan ban mamakin dake ta gudana a cikin gidan yau dan haka tsayuwar motocin babu d'ad'ewa yaran gidan suka fara fitowa dan suga waye yazo gidan yanzun kuma,
Suma sirikan gidan mata ba'a barsu a baya ba wajen yin dogon lek'e daga nasu sashen, ba duka yaran gidan ne suka san su Baba Usman ba dan haka su da suka fara fitowa daga cikin mota sai yaran basu wani waye su ba, har sai da Hajiya ta fito tukun suka baibayeta suna mata oyoyo,
Aka bar matan gidan cikin mamakin mai kuma ya kawo Hajiyar gidan ita da wad'annan mutanen ga kuma kayan da suke hange anata saukowa daga bayan mota sun kasa tantance ko kayan miye daga farko har sai da aka sauke kayan tass aka loda su a gefe, ganin idan su su dai kayan da