Showing 168001 words to 171000 words out of 190771 words

Chapter 57 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1562

su kadai suka rage a gidan domin harsu Maimoon suma sun wuce Maryam ce kawai a tareda ita sabon wanka suka sata tayi suka mata sabon shiri,
nan suka sata a tsakiya sukaci gaba da mata nasiha akan hakurin zaman gidan aure duk da sun san cewa zaman gidan miji ba sabon abu bane a wajen ta amma ai akwai banbanci sosai tsakanin wannan auren da zaman da tayi da Sarki,
ita abun ma wallahi dariya yake bata wai ita akema nasiha ko mantawa sukeyi cewa wannan shine aurenta na biyu oho itafa ji takeyi irin a dole tasan komai ko ba'a mata nasiha ba zata kula da komai yanda ya dace,

Sai dai bata da yanda zatayi haka ta Bude kunnuwa taci gaba da sauraran su, koda suka kira Mommy akan tazo ta mata nata nasihar wannan karon ma k'iyawa tayi saima cewa da tayi meya rage wanda basu fadamata ba kuma ita yanzun aiba karamar yarinya bane,
itadai ban biye mataba dan haka har inda take taje ta isketa ta rungumeta tana kuka dan wallahi jikinta yayi sanyi,
zata k'ara barin gidan zuwa gidan miji a karo na biyu.

"Allah ya muku albarkha, ya kuma baku zuri'a masu albarkha ki rik'e mijinki da auren ki da kyau Meenal kowa dai ya miki shedan hakuri dan haka kije kici gaba da hak'urin banda yawan k'orafi ko kuma kai k'arar shi wajen Hajiya dan kingan ki a kusa da ita duk da dai ba a gidan zaku dauwa maba ki kuma kula da yawan ibadan ki Allah ya baku zaman lafiya"
Ameen sauran jama'a suka amsa dashi sannan suka banbareta daga jikinta,
duk wani nasihar daya kamata iyaye maza suma sun mata shi tun d'azun a falon Malam.


Sai da suka k'ara shiryata suka Kara fesheta da turatuka masu sanyi marasa hayaniya Sannan Aunty hassana ta nad'a mata lafaya ta yane mata jikinta,
sannan suka rikota suka fito harabar gidan wajen yayi tsit kamar ba acikin shi aka tara mutanen d'azun ba,
wasu sun wuce wajen shagali wasu kuma gidajen su suka koma,
Mota 4ne kadai a wajen 3n dai Yay yenta maza ne ta tsakiyar da take nan fara tass sabanin sauran da suka kasance bakake aka bude mata,
Bayar motar suka sata Meelat ce a gaba gefen mai zaman banza yayin da Musty ke zaune a kujerar driver,
Tun sanda aka bud'e murfin motar kamshin turaren shi da baya buya shi ya tabbatar mata da wanzuwar shi a cikin motar dan haka tasha jinin jikinta,
duk da darene hakan bai boye kyau da tsaruwar motar ba allah kadai yasan nawa aka dandake kafin a mallaketa,
bata tab'a ganin AK da farar mota ba tun bayan waccan daya bata kyauta dan duk motocin shi masu duhuwar kala sunfi yawa sai yau duk da kowa yasan favorite color din shi sune black and white,
Dama yasha fadar cewa a farar mota za'a dauko mashi mata gashi ko ya tabbatar shi dai wallahi haka nan allah yayi shi mota da sutura bayajin kyashin kashe kudade masu nauyi wajen mallakar su,
tun sanin da tayi mashi a baya shi mutum ne mai son gayu Kamar mace, haka kuma yake da son kyale² domin kowa yasan komai nashi mai kyau da tsadane tun daga kan sutura takalmi hula agoge zobe komai nashi abun sone gwanin burgewa kamar yanda yake mai kyau shima, bata manta zamanin yarinta sanda take zuwa satan turare a dakin shiba, murmushi tayi
kuma wai dan rashin wayau tun daga can take feffesawa a jikinta kafin ta iso waje asirin ta ke tonuwa dan kanshin ke rigata isa waje,
satar turare ko tonon sililiii......
Sauran motacin suma suka shiga aka d'auki hanyan zuwa wajen shagali,
tun basu fita a cikin layin suba yake fad'ama Musty

"Dan allah ka rufamin asiri kayi tafiya a hankali dan batun yauba naji tsoffi na fadin amarya tsautsayi gareta balle kuma yanzun da take tareda angonta a gefen ta koba haka ba wife?"
Ya fada yana matsowa gefen da take ita dai bata amsa shiba dan tasan magana yake nema,

Shima kuma Musty din bai tanka mishi ba shima,
hannuwan ta ya riko yana wasa da dogayen yatsunta da suka sha xanen lalle ga kuma kwalliyar zobbunan da suka kara k'awata su,
Saitin bakin shi yakai hannun ya bashi sumba muah yaja tumbar mai sauti,
kokarin janyota zuwa cikin jikin shi yake ita kuma tana cijewa da hannu take mishi nuni dasu Meelat dake gaban motar suna nasu hirar,

" miye haka wai?" Ya fad'a kasa²,
" To Ai bamu kadai bane a cikin motar" ta fada tana kokarin turashi baya,
"to ke ina ruwan ki dasu? bakiga suma nasu soyayyar sukeyi bane?"

"Kai bakajin kunyan sune?"

"Kunyan wa zanji a cikin su Ita koshi?
Baki ga su nasu rashin kunyar harda result sun samuba ko bakiga yanda yake neman kwakwume ta bane shima? To shida ya iyama matar shi nine bazan rungume mata taba nima?
Dan haka Banajin kunyar su "
ya bata amsa kai tsaye
"To ni inaji gaskiya"

"kin san allah in baki kiyayeni ba zansa Musty ya juyamin motar nan zuwa Tudun wada"
ya fada cikin dakakkiyar murya,
shiru tayi tana mishi hararar kasar ido babu bakin magana,

"kice tak kiga yanda akeyi yarinya! Marowaciya ma dake ko dan kissing din ma kin hanani, kina abu sam ba wayewa kamar ba budurwar ABU ba,
da watane tun a cikin motar nan zata fara tattalina kafin mu isa duk sai ta yamutse min kayana ta yanda kowa zai shaida cewa lallai ango nike a yau,
Amma ke mutum yana rungume kima kina tureshi kuma in ance dake yarinya kiji haushi"

Itadai tunda ta samu ya dena tattab'a tan da yake tayi tsit da bakinta jawota yayi ya rungume yana maida ajiyar zuciya,

***
A hankali Musty yaci gaba da jan motar kamar yanda AK ya umarta a hankali sukaci gaba da tafiya har zuwa wajen taron,
gaskiya sunyi kokari matuka wajen kawata wajen duk da darene amma ko ina cike yake da haske,kallo d'aya zakama d'akin taron kasan cewa bana talaka bane
koda suka iso su kadai ake jira dan haka ba wani b'ata lokaci Yayyen ta maza suka fito kwansu da kwarkwa duk da yanda AK yake wani nan nan da ita shi a dole ga mai mata haka suka sa su Musty suka mishi jagora zuwa cikin d'akin taron sai da suka tabbatar da cewa ya zauna kafin su kuma suka sa Meenal d'in a tsakiyar su wasu na gaba wasu kuma sun jeru a bayan ta haka suka mata jagora har cikin hall d'in suna tafe suna mata liqi wasu daga cikin su kuma suna feshe ta da turaruka masu k'amshi abin gwanin burgewa wallahi,
Saida suka kaita har inda AK yake kafin Ya Sa'eed ya rik'o hannun AK ya had'a dana Meenal din,
"Ga amanar kanwar mu nan mun baka"

"Allah ya taya rik'o yan cikin hall din suka amsa dashi, shi kuma bayan ya rik'e hannun ta tasowa yayi daga kan kujerar yana rik'e da hannunta saida zagaya suka gaggaisa da mutanen da suka zo wajen domin su musamman iyayen su mata da maza sannan abokan ango da kawayen ta suka musu jagora zuwa kujerar da aka tanada domin su,

lallai bikin Mai Jama'a ake dole kaga taron jama'a gaskiya tayi farin ciki sabida ganin mutanen da ke wajen da yawa daga cikin su wasu sunyi shekaru basuga juna ba wasu mate dinta ne na school wasu kuma childhood friends dinta ne da suka dade basuga juna ba sauran jama'ar kuma kunsan dan wa sukazo ita har mamaki take yanda akayi mutane sukaji labari har suka hallara haka,
gaskiya dai tayi farin cikin ganin yanda mutane suka taru saboda su musamman yanda yayyen ta maza suka nuna ma kowa yanda suke ji da ita duk da lura da uban gayyar yanda yake wani jajjanye ta daga cikin su.
Sai fatan allah ya maida kowa gidan shi lafiya ameen.

Bayan Bude taro da addu'ane kuma aka ba iyaye dama wajen tofa albarkhacin bakin su, kuma alhmadulillahi sunyi jan kunne sosai kuma sun fadakar
unyi bayani sosai akan aure, hakkin miji akan mata, da kuma hakkin itama matar akan mijinta wanda baba Adamu ne yayi wannan jan kunnen sannan kuma yakara jan hankali akan mahimmancin hakuri da abokin zama daga nan akaci gaba da shagali, kai gaskiya dai taron dinner din ya kayatar anci ansha kuma anyi rabon abubuwa kala²a wajen bayan an rufe taro da addu'a ne kuma aka fara watsewa dan karfe 10 dai dai aka tashi,
masu wayau dai basu yarda sun bar wajen ba saida sukayi sallan ishsha'i,

Da yawa daga cikin abokanshi da bata san suba ya gabatar mata dasu wasun su sun mata kyauta a wajen yayin da wasu sukace sai sunzo gida,
Sun daiyi sallama da wadanda zasu koma garuruwan su wadanda sukazo daga nesa,

Sai dai tana kasa tana dabo domin tun zuwan su wajen take an kare da tawagar wasu mata wanda ko shakka babu gasan suna cikin gayyar mai Jama'a kuma ko yanzun haka da mutane ke watsewa su suna ciki, tun dazun taso ta tanka amma dai ta danne to yasin bata barin wajen nan ta bar mijinta cikin kuraye duk da tasan halin kayanta Amma kula da kaya yafi ban cigiya,

Ba tawagar kowa bane face tawagar Hafsat ita din kuma tsohuwar budurwar AK ce tun zamanin yarinta nasan baku manta da ita ba mijin data aure mutuwa yayi tun bayan data gama takaba kuma take ta faman bikon AK din sai dai kun san mai hali, kafin ta ankara kuma kawai sai labarin d'aurin aure taji har yanzun kuma bawai ta dena son AK din bane a wautar ta wai ko a mata ta biyu ne sai ta shiga gidan Mai Jama'a inba batar basira ba shidin dabai aureta tun tuntuni ba wai yanzun ne zai aureta,

" Lallai dani suke wasan to wallahi sai naci musu uwa kana inbi da ruwan kanwa maganin kwarnafin ciki, kuma shima Zai fadamin dalilin da yasa yayomin gayyar karuwai,"

Tunda suka fito take cika tana batsewa, tayi² ta danne kishin dake yunkuro mata amma abun yana neman ya faskara.........
Matsowa kusa da ita yayi,
"meya sameki?"ya tambaya ganin yanda take ta wani kunbure kunbure,
" Ai dole kace meya sameni tunda kayomin gayya harda na karuwai wajen tarona,"

"Ke waye ya miki gayyar karuwan?"
Tura baki tayi bata amsa mishi ba
"To bari kiji ni ban gayyace suba kuma ita Hafsan da kike magana a kanta in baki manta ba tun baki da wayau nike tare da ita kin san da ina ra'ayin ta daba wannan maganar akeyi yanzun ba,"

"To da baka ra'ayin ta basai ka fada mata ta fita a sabgar kaba,
Shine kuma dan maita duk inda kake haka zata dunga binka Kamar karya to wallahi nikam a kiyayeni idan da nayi shiru yanzun ba abunda zai gagareni,"
haka nan ta dunga warwarewa tana yab'a maganganu gaba daya kishi yabi ya rufemata ido,
kai jama'a gaskiya kishi jidaline shi dai daga karshe ido ya zubamata dan ba amfanin yin kace nace da ita a yanzun saida ta gaji dan kainta tayi shiru,
ruwa yasa aka miko mashi shi kuma ya budemata ya kafamata ruwan a baki wai tasha,

Kuma da tasha taji saukin tukukin da zuciyarta ke mata,

"Nagode"
Tace dashi bayan ya cire gorar a bakinta,

Aunty hassana ce ta karaso inda suke ta cire hannunta a cikin nashi tana mishi tsiyar kodai su wucene shi zai wuce da amaryar shi da kanshi?
AK fa ba kunyace ta wadace shiba Dan haka da sauri ya amsa mata

"Eh aunty kuje kawai tunda dama ai da yawa sunje sunga daki kinga gobe sai suzo suma amaryar sallama kafin su wuce"

" Kai 😳" ta fada tana zaro ido fincike hannunta dake cikin nashi tayi da gudu ta koma bayanta ta b'uya daga bayan Aunty Hassanan ta leko kanta tana fadin "wallahi ban yarda ba,"
Dariya jama'ar dake wajen sukayi shiko yasin ko a jikin shi sai ma kara matsowa da yayi yana neman kamota
"Dan Allah kizo idan na sallami bak'i sai mu wuce tare"
wata katuwar harara ta watsa mishi tana mak'e kafada alamar bata yarda ba,
" Fine " shima ya fada yana dage kafadun shi wani shegen kallon kasar ido ya bita dashi alamar zaki shigo hannu yarinya,

Ita kuma ta mishi gwalo tana murmushi, hannun shi manuniya ya nuna zuwa kirjin shi alamun "ni koh?"
Had'e hannu tayi alamun ban hakuri 🙏.

Motar da Musty ya d'auko su a ciki ita ta mai dasu sabanin d'azun da suka taho su hudu a cikin motar yanzun kam sun kara yawa,
ita da Aunty hassana da Maimoon a baya sai Maryam da Sultana ne a gaban motar bata san ko miye sultanar take nunama Maryam din a waya ba kuma Faisal ne kejan motar,
A haka suka jera tare da sauran motocin suna tafe suna hira har zuwa gidan Hajiya wanda yake matsayin gidan auren Meenal din a yanzun...

Koda suka isa sun samu da yawa daga cikin motocin da suka kawo mutane sun wuce sai tsiraru wadanda suka tsaya tarbar amarya,

Bayan sun faka a harabar gidan Hajiya ce da kanta ta fito ta tarbe su da sabuwar butan ta wanda ta ciko shi da ruwa ta fito dan haka saida ta umarce Meenal din da tayi alwallah da ruwan cikin butan,
bayan ta idar Hajiyar ce ta k'ara rike hannunta sai da ta zaga da ita kaf sashen gidan iyayen ta su Baba Usman suka sa ma auren albarka kafin suka nufi sashen Meenal din,
Sai da Hajiyar tayi mata umarni da ta shiga da kafar dama bayan sun gabatar da addu'o'in a kofar shiga sashen,
haka suka rakata da addu'ar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma zuria masu albarkha,
sun kumayi addu'ar yanda suka kawota cikin aminci ubangiji yasa mutuwa ce kadai zata fiddata daga gidan aure ta,
Basu zauna a falon ba kai tsaye sama suka haura da ita zuwa dakinta suka mata masauki akan gadonta,
Itadai fuskarta tana lullube dan haka bata samu damar karema gidan kallo ba, a bakunan mutane takejin yanda suke zuzuta kyawu da tsaruwar da gidan yayi, kun san dai yanda akeyi in ankai amarya dan haka itama mutane sukaci gaba da shigowa kallon ta duk da kasancewar fuskarta na rufe wasu sukan mata sallama akan sai sun dawo suna,
wasu kuma sukance sai sun shigo gobe, a haka dai yawancin mutanen suka watse, Dan baba Malam yace bamai kwana ita dai taso ace sun kwana amma ba yanda zatayi tunda babane ya yanke hukunci itada tace bazata tare yanzun ba karshen magana dai to gashi har sun kawota sun barta na bakin AK,
Hafees ne ya shigo dakin da sallama karasowa kusa da ita yayi "matar Ina wayata?"

Da hannu ta mishi nuni da Sultana ba tareda tayi magana ba, shima baija maganar da tsayi ba ya juya inda Sultana din take mikewa tayi tace
"muje waje wayar tana cikin jakata a mota,"
Oh ni y'asu wai ita zasu maida karamar yarinya da zata fita shine tama Maryam signal itama ta rufa mata baya kujifa Dan sun raina ta wai a tunanin su wayau sukama Meenal irin bari su gudu sai dai inji shiru din nan ni wallahi dariya ma suka bani,
bayan sun fice ne Maimoon ta rufe kofar gyalenta ta cire sannan ta matso kusa da Meenal din,
"kawata" ta fada tana mai mikar da ita tsaye daga zaunen da Meenal din take, lafayar dake jikinta ta warware ninkeshi tayi ta sashi cikin wardrobe,
"tashi kiyi wanka na hada miki ruwa a ciki,"ta fada yayinda taci gaba da kakkabe² tana kara kimtsa dakin ta kara feffesa room freshener dan sun kunna turaren wuta dama tun kafin su Meenal su shigo,
Mikewa tayi tana mita "Nidai gaskiya gaba daya yau kun takuramin kun mai dani Kamar wata agwagwa, haba bini² kadan kuce inyi wanka, dazun nan fa nayi wanka!"
Barin abunda takeyi tayi ta juyo tana kallon Meenal din,
"To wallahi sai kinyi shi kinjima na rantse kin maci uwar rainin wayau wato mun miki mai wuyar ai Bari kimin iskanci......."

" Eh din to me yasa baku barni a gida ba" rike baki tayi tana kallonta da mamaki,
Kayan baccin da Moon ta ciro ta ajiyemata akan gadon ta mika hannu na kwasa,
Juyawa fayi cikin bayin tana tafe tana murguda mata mazaunai,
"Yar rainin wayau in zakiyi murgud'e² ki sai ki jira har shi ya shigo dan nidai in kin min kinyi ne a banza"
wanka sosai tayi da ruwa mai dumi dan wallahi gajiya takeji sosai a jikinta dan baccine taf cike da idonta,
bata fito ba saida ga dauro alwallah,
Koda ta fito ta samu Moon ta canza zanin gadon ta sanya wani kayan data fito dasu a hannunta Moon ta amsa sai da ta feshesu da turare sannan ta ninke ta adana,
Gaban mirrow ita kuma Meenal din ta karasa ta mutstsuka mai sannan tadan bi fuskarta da hoda yar kadan dan ta kashe maskin man,

"Baza kiyi kwalliya ba?" Ta tambaya
" ke dan allah rabani da wani kwalliya da daren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login