Showing 33001 words to 36000 words out of 190771 words

Chapter 12 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1578

ta amso abincin a hannun Larai ganin ta biye ma Hajiya ita kuma wallahi yunwa takeji,

Bayan Larai ta koma kitchen shiru Hajiya tayi har saida Meenal din ta gama cin abincin,

"Hajiya wai ya akayi ne hala kiran me kike min to wani abun ya faru ne bayan na fita?"

"Ah ah komai bai faruba son jin muryar kine yasa na yi ta kira kamar wata shashasha ke kuma kika k'i dauka"

"Yi hak'uri to ai kin san in lafiya lau ne bazan k'i d'aukar miki waya ba wallahi ban san kin kiraba"

jakarta ta jawo ta fito da wayar daga ciki tana nuna ma Hajiya tarin miss call din da aka mata wanda ko bud'esu batayi ba balle taga ko su waye,
"Kin gani koh Hajiya wallahi ban duba ko su waye suka kiraba kiyi hakuri"

"To ki shiga ciki ki shirya tunda akwai sauran lokaci mu wuce kaduna, dan bayan fitan ki na samu kira daga wajen Jidda cewar Allah yayi ma mijin yar uwar ki Raheenat Rasuwa a safiyar yau kuma itama Raheenat din ta Haife cikin dake jikinta wanda sakamakon sak'on mutuwar daya iske sune yasa nakudar dole taso mata ta haihu an samu d'a namiji, shi yasa nike ta kiran ki nasan kuma suma mutanen can gidan naku sun neme ki a waya"

"Innalillahi wa'innah ilairir raju'unยณ"
Shi meenal tayi ta maimaita wa tana hango irin tashin hankalin da Raheenat take ciki na rasuwar miji kwatsam babu jinya ba komai, kuka ta fashe dashi sosai dan Wallahi mutuwar ta dake ta, mutuwa farat daya irin haka kona wanda baka sani bane sai ya tab'aka balle kuma mijin yar uwarta.

"Wai yayi rashin lafiya ne dama Hajiya ko hatsari yayi?"ta tambaya da muryar kuka

"Babu ko d'aya kedai wallahi ajaline kawai ya riske shi dan sunce lafiya lau ya tashi har anyi sallan asuba dashi lafiya lau ma sukayi karin safe da iyalan shi kafin ya shige cikin dan yin sallan walha ita uwar gidan ne ta shiga ta iske shi kwance a kan daddumar da yayi Sallah ita a zaton ta ma ko bacci yake yi ashe tuni lokaci yayi ya tafi yabar musu duniyar daduk abunda ke cikin ta"

Hajiya ta k'arasa fad'a da hawaye itama,
zuwa wannan lokacin ko kuka shab'e shab'e Meenal keyi dan sosai mutuwar ta dake ta,

"Ke ai ba kuka zakiyi ba tashi zakiyi ki shirya muzo mu kama hanya tun yamma batayi sosai ba"

Wayar ta da ta lalubo number din Mommy Hauwa ta dannawa kira ta kara akunne tana kuma cigaba da kukan, koda mommy ta dauki wayar tambaya ta jefo mata da cewa,

"Kun iso ne Meenal kuna ta ina ne? Mu muna Sashen uwar gidan bari inzo in same ku"
Katseta Meenal tayi da cewa,
"Mommy wai da gaske ne ya rasu?"

"Ya rasu mana Meenal ana wasa da mutuwa ne?"
Ta tambaya tana yanke wayan, wanda hakan ne kuma yasa Meenal din kara yawan kukan da takeyi,

"Kai amma yarinyar nan ban san kallon mak'aryaciya kikemin ba tsayin zamana dake sai yau, ni ince miki mijin yar uwar ki ya rasu amma baki yarda ba shine sai da kika kira uwar ki kika tabbatar tukun, to yanzun da kika tabbatar da mutuwar dawo mishi da ran zakiyi ko k'ak'ah?"

Ita dai Meenal kukan ta kawai takeyi, yanzun fisabilillahi shi kenan Raheenat ta rasa mijinta yaranta kuma sun zama marayu ciki harda wanda yazo duniya ayau shi ko damar sanin baban shi ma bai samu ba,
Allah sarki Alhaji Saminu ubangiji Allah ya jikan ka"

Suna cikin wannan jimamin ne biyu daga cikin masu gadin gidan sukayi sallama a kofar falon, Hajiya ce ta amsa musu,

"Ya akayi ne Isah?"

"Kayane zamu shigo dashi Hajiya"

"Kaya kuma! To bismillah ku shigo,"

Rik'i rik'i suka shiga d'auke da buhun dankalin turawa,

"Mai Jama'a ne ya dawo hala?"

"Eh shine Hajiya shigowar shi kenan"

"To ai da kun min bayani sai ince ku shiga da kayan tacan kofar kitchen din baya zaifi muku sauki,Larai zoki nuna musu inda zasu ajiye wannan d'in"

Bayan sun shige dashi basu fito ta falon ba sai kawai suka fuce ta kofar bayan, tacan suka cigaba da shigewa da kayan har suka gama,
Hajiya kuma ta haura sama tana k'ara jaddama ma Meenal cewa ta tashi taje ta shirya fa su kama hanya dan bata son tafiyar dare,

Sai dai har Hajiyar ta k'ule bata motsa ba, Malam ta kira ta farayi ma gaisuwa cike da muryar kuka,

"Mamana yanzun ne kikaji sakon rasuwar nashi hala? Shi yasa kike ta kuka bayan kin san mamaci ba kuka yake buk'ata ba"

Sai da ta yi kokarin share hawayen dake ci gaba da biyo fuskanta kafin ta amsa da cewa,

"Naje makaranta da wuri yau kuma banje da wancan wayar ba, wannan kuma ana ta kira a fad'amin sai dai itama na cire mata k'ara shi yasa duk banji kiran ba,"
Sai da taja majina sannan ta d'aura da cewa,

"Yanzun ne dana dawo Hajiya take fad'amin rasuwar nashi, ubangiji Allah ya jikan shi Allah kuma ya raya abunda ya bari yaba iyalai hakurin rashi"

"Ameen Ameen Mamana Allah yayi albarka, amma dai zaki bari har zuwa gobe ne sai ki tafi kije kima yar uwar naki gaisuwa koh? tunda kinga yamma tayi yanzun ana neman k'arfe biyar ne yanzun"

"Aiba ni kadai zan tafi ba Hajiya ta shirya tun d'azun dawowana dama take jira nasan direban ta ne zai kaimu"

"To masha Allah ubangiji Allah ya tsare suma iyayen naki suna can ai nidai na dawo gida tun bayan da aka gama jana'izah"
Sallama sukayi ta yanke wayar,

Tunda suke wayar hancin ta ke shak'o mata kamshin da ko bata tambaya ba tasan mallakin waye balle kuma shigowar su Isah ya k'ara tabbatar mata da cewa shid'in ne,

A hankali yaci gaba da takowa bayan yayi sallama daga bakin kofar da yake tsaye, bata yarda ta d'agoba kanta a duke ta amsa sallamar tana laluben number din Meelat a wayar dake hannun ta kuma bawai kukan da takeyi ya dauke bane gaba d'aya ah ah har zuwa lokacin hawaye basu dauke a idonta ba ga kuma shashshek'an da takeyi kasa kasa,
Gefen ta ya k'arasa ya zauna yana binta da mayen kallo hankalin shi a tashe sakamakon ganin hawaye shab'eยฒ a fuskar da ya dawo da burin gani wanda kyanta ke karuwa aduk sanda ta k'awata fuskar nata da murmushi shine daga shigowa zai sameta tana kuka kuma,

"Maiya sameki kike zaune anan ke kadai kina kuka? Kukan ne kikeyi?"

Sai da ta tab'e bakin ta irin yanda yara keyi idan suna kuka sannan ta dago idanuwan ta wanda suka fara burkicewa kalan su ya canza daga farare zuwa jajaye ta zuba mishi,

"Fad'amin mana meya same ki ko baki da lafiya ne?
Kai ta girgiza mishi alamun ah ah,

"Lafiyar ki kalau kenan?"

"Eh"
Ta bashi amsa,
"To me ya faru?" Ya kara tambaya.

"Rasuwa akayi"

"Innalillahi wa'innah ilairir raju'un ubangiji Allah ya jikan musulmi"

"Ameen"
Ta amsa dashi, sai shi kuma ya kara tambayar ta cewa,
"Waye ya rasu?"

"Mijin k'anwata Raheenat dake aure a kaduna"

"Allah ya jikan shi yasa mutuwa ta zama hutu a gareshi, ku kuma Allah ya k'ara muku hakuri"

"Ameen"

"To ki dena kukan hakan bakiga idon ki har sunyi jaba, kiyi mishi addu'a kinji" yana fad'in hakan ya kai tattausan hannun shi kan fuskar nata yana share mata hawayen da suke zubowa,

"Ki dena kukan please fuskarki bata kyau da kuka tafi yin kyau idan kina murmushi, ita kuma mutuwa lokaci ne duk wanda nashi lokacin yayi zai tafine ko da bai shirya ma zuwan lokacin ba, ni da ke da kowama lokaci muke jira sai dai muyi fatan Allah yasa mu cika da kyau da imani yasa mu gama da duniyar lafiya mu tafi ana kewar mu masoyan mu kuma suci gaba da bin mu da addu'a, kiyi shiru kukan ya isa haka"

'To Nagode"
ta amsa dashi harta mik'e da niyyar haurawa sama ya jefo mata tambaya da cewa
"Hajiya fa?"

"Tana d'aki tana shiryawa tace nima in shirya zamu tafi kadunan yanzun,"

"Ku dawa?"
"Mu biyu"
"Waye zaija motar nike nufi bawai ku nawa nike son sani ba"

"Oho to ai nima ban sani ba amma in direbanta baya nan aini ke tuk'ata"

"Eh amma ai baki tab'a tuk'a kanki zuwa Kaduna ba, jeki shirya ku fito sai mu wuce gaba d'aya dan dama nima gobe ne zan koma can din"

"To basai ka zauna mu mu tafi ba, nifa da mota ta zanje"

"Ai kindaiji abunda nace miki tunda niba mahaukaci bane da zan barki kiyi tuk'i a tsakankanin manyan motoci, kije ku shirya ku fito nace yamma nayi"

Yana gama fad'in hakan ya juya ya barta nan tsaye tana cigaba da binshi da kallon mamaki,
" Kuji min karfin hali fa mutum daga dawowar shi zai fara gindayawa mutane sharad'od'i ko waye ma ya gayyace shi zuwa gaisuwan",

to in suka bishi zuwa can in fita ya kamata zuwa wani wajen da motar waye zata fita,
Ganin ya juya ya fice abunshi itama sai ta haye saman jiki a sanyaye,

Tubewa tayi ta fad'a toilet ta sakar ma jikin ta ruwa sabulu kawai ta goga ma jikinta ko soso bata saba tayi wankan ta fito, a gurguje ta shirya ko mai bata tsaya shafawa ba ta harhad'a yan kayanta kala uku a cikin karamin akwati ta d'auko wayarta data bari a gida ta kunna,

"To in kin gama ki sauko mu tafi ni na riga na fito"

Cewar Hajiya dake bakin kofa,

"Gani nan fitowa nima na gama ai,"
Ta fad'a tana zura hijjabin ta dogo har kasa, koda ta fito hajiya bata saman a kasa ta sameta tana ba Larai sallahun ta kula da gida sai sun dawo,

A can haraban gidan ko kafin su fito tuni AK ya kunna mota fitowar su kawai yake jira,

"Ah ah kai kuma daga shigowar ka garin shine zaka k'ara kwasan mu kuma bazaka zauna ka huta ba ko ita ai tana iya tuk'amu zuwa can din ka shigo nasan ko abunci bakaci ba"
Hajiya take fad'a ganin ya amshi kayan hannun Meenal yasa a cikin booth din motar shi harda ma nata kayan,

"Bana tare da gajiya Hajiya dan bani na tuk'o kaina ba, ina wuni ya k'arin hakuri Allah ya jikan shi"

"Lafiya lau ya hanya? hakuri da godiya, ameen ameen,"
Juyawa tayi ta kalli Larai ki shiga ciki ki d'ibo mishi kayan fulawan da kika had'a dazun koshi sai ya samu yaci a hanya ki dibo da dan dama kin san itama Meenal tana so"
Da sauri Larai ta juya cikin bayan ta amsawa Hajiya sai gata ta dawo harda zungura zunguran gorunan exotic guda biyu ta mik'ama Meenal, Hajiya Jummai bata gidan ta tafi kano dan haka basuyi sallama da ita ba tun safen dai Hajiya ta fad'a mata rasuwar da cewa Meenal take jira idan ta dawo zasu kama hanyar Kadunan,
hakan name yasa babu b'ata lokaci suka kama Hanya Meenal ce a gaba gefen mai zaman Banza hajiya kuma ta kame a baya shi kuma shi da kanshi yake tuk'in, Hajiya na zaune a baya take bashi labarin irin yanda rasuwar na mijin Raheenat din ya kasance babu ciwon fari bare na bak'i sai gawa iyalin shi ta tarar Allah kadai yasan yanda abun ya faru ko yana cikin sallan ne aka cire ran ko kuma sai da ya idarne allah masani,
Koma dai menene ai shi kam Alhamdulillah ya tafi cike da nasara wallahi,

muma dai allah yasa mu dace da kyakyawar karshe ameen,

suna tafiya a motar ne kuma Meenal tayi kiran su Maryam a waya ta shaida musu batun rasuwar cewar yanzun haka sun kama hanyar wucewa can Kadunan sun mata gaisuwa da addu'ar Allah ya jikan musulmi suma kuma insha zasu yi kokari su shigo kadunan a gobe suma Raheenat gaisuwa,

A gefen AK ko zai iya cewa wannan tafiyar tafiya ce mafi dad'i a wajen shi duk da dai bawai tafiya ce wacce aka shirya ta cikin dad'in raiba,
Koba komai wannan shine karo na farko daya d'auki Meenal a cikin motar shi har zasuyi tafiya daga Zaria Zuwa Kaduna, dan haka zaiyi amfani da wannan damar ya cusa ma Hajiya ra'ayin zama a gidan nashi in yaso kullum shi yaji ya gani zai dunga kaisu can gidan gaisuwar yana d'auko su dan yasan in suka tare a gidan gaisuwar gani Meenal din zai mishi wahala,

Sai da suka fice daga cikin zaria har sun d'an fara nisa tukun ya daga kanshi ta mirror din gaban motan yana kallon Hajiya,
"Hajiya ina abincin da kika ce a dibo min yunwa fa nike ji wallahi"
Ya fadi hakan yana satan kallon Meenal ta gefen ido,

"To ai ga irinta nan shi yasa nace ka zauna a gida ka samu kaima ka huta, shikenan ayi rayuwar mutum ba hutu ba kanan ba kanan kamar kai kafi kowa son kud'i fisabilillahi wani kud'ine kake nema kuma bayan wanda ka tara iyee gashi nan duk ka fara zabgewa kana ramewa a tsaye tunda nasan ba wani cin abincin kake samun yi yanda ya kamata ba"

"Nidai Hajiya yunwa dai nace miki ina ji"

"Ke Meenal ina ce ke Larai ta damk'ama kayan fulawan ki bashi mana"

"Hajiya gashi nan fa a gefen shi ai yana kallo,"

"Hajiya nida nike tuk'i to da wani hannun zan dunga d'auka ina kaiwa baki ina ci?"

"To ni kake so in dawo gaban in dunga baka a baki kenan?"

"Ah ah Hajiya ki dai mata magana ita ta dunga bani a bakin har in koshi kinga idan nace in tsaya sai na gama ci muci gaba da tafiya lokaci zamu b'ata kuma yamma na k'arayi"

"To ai gata nan a gefen ta kunfi kusa"

Hajiya na gama fad'in haka ta gyara zaman ta bayan ta ciro wani littafin addu'o'i shi taci gaba da karantawa bata k'ara bi takan suba,

"To yane An mata a taimaka a bani abinci yunwa nike ji wallahi bakiga yanda cikina ya lafe ba"
Ya k'arasa fad'a dayin k'asa da kwayar idon shi ya mai da kallon shi zuwa wajen cikin shi,
Cikin nashi dake lafe cikin rigar dake sanye a jikin shi polo shirt fara tabi da kallo kafin ta kauda kai,

"Please mana ko so kike ulcer ya kama ma future wife d'ina nine?" Yake tambaya k'asa kasa,

Jawo roban da Larai ta zuba su samosa donut da meat pie din tayi sai taga harda Pepe chicken ta had'o musu,
Mutuniyar ku dai kun san amanar dake tsakanin ta da nama balle kuma Hajiya kaza fa ake magana anan, dan haka tuni ta manta da batun shi ta d'auko wani d'an kwalelen cinya ta gyara zama ta fara ci,

"Amma dai yarinyar nan kin iya d'aukar alhaki wallahi, abincin nan nawa nefa kuma yunwa nace miki inaji amma kin wani gyara zama kina ci ke kad'ai wato dad'i kawai hajiya da Larai suke baki shi yasa ashe naga sai k'ara kyau kikeyi abinki ni kuma bawan Allah sai faman rama nikeyi, to nidai a taimaka a sammun inci nima kar a ci da hakkina,"



*Ummiee Zaria*โœ๐Ÿผ
[8/28, 9:28 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*BOOK 2*

*PAGE 14*


Kadai jira ita future wife d'in taka tazo sai ta baka a bakin badai niba"
ta fad'a hankali kwance tana ci gaba da cin naman ta,

"Tunda gaki aiko kema kina iya zama wakiliyarta, Allah kuwa seriously ina jin yunwa,in kuma bazaki bani ba bari in faka a gefe ke sai ki amshi driving d'in ni kuma sai inci abincin tunda abun ya zama haka,"

"Allah ni ba wani tukin da zanyi ai tun farko saida nace kayi zaman ka mu tafi da mota na kak'i, tunda ko ka matsa haka nan zaka jamu ka kaimu"

"To abincin fa?"

"Ba gashi nan na ajiye maka a tsakanin mu ba hannu zaka dunga zirowa kana d'auka kana ci"
Ta fad'a bayan ta ajiye abincin a gefen ta,
Bai k'ara tanka mata ba har sai da suka shiga Zango sannan ya gangara gefe yana niyyar faka motar,

"Me zakayi wai?"

"Kina tambaya ne bayan ba makancewa idanuwan ki sukayi ba, to fakawa zanyi idan na gama cin abincin sai muci gaba da tafiyan"

"Dan Allah karka tsaya wallahi yamma tayi"

"Sai kince kin yarda zaki bani a baki"

"Na yarda"
yago naman tayi takai mishi baki,
"Haaa" tace tana bud'e mishi nata bakin kamar wata wacce zataba yaro abinci,

Cafka ya kaima naman data kawo kusa da bakin nashi ya had'a harda yatsarta ya d'an ciza kad'an yanda bazataji zafi ba, amma dan sharri irin na Meenal sai da ta tak'ark'are ta kwala ihu,

"Ke miye haka?"
Hajiya dake baya ta tambaya,

"To bashi bane kawai ya cijeni a yatsa taba"

"Cizo kuma kamar wasu k'ana nan yara, kaga nidai ka rufamin asiri ka lallab'a ka kaini ka sauke lafiya kafin kasa a sanya sunan mu a labaran dare cewa mun taso daga garin Zaria zamuje garin Kaduna gaisuwar mutuwa muma kuma munyi hatsari mun mutu, kar kaga na tara y'ay'a da jikoki kayi zaton kona shirya ma zuwan mutuwar ne duk da dai ita ba shiri ake mata ba amma dai zanso in k'ara mik'a takwarata d'akin mijinta a karo na biyu dan nidai ba takai nikeyi ba atoh yanzun idan tsautsayi ya gifta ai shi kenan sai ayi d'a kwance uwa kwance gara nima na bar baya ku kofa? "

"Yi hak'uri Hajiya insha Allahu lafiya lau zamu isa, kuma aure ba namu ba har yaran mu sai kin aurar Allah dai ya k'ara miki lafiya Hajiya ta"
Maida motar yayi kan titi sukaci gaba da tafiya, kin yarda ta k'ara bashi naman Meenal tayi har saida yayi mata alkawarin cewa bazai k'ara cizon taba,

a hakan ma sai taci a kalla sau uku kafin ta bashi sau d'aya lemun da,
da yike ta zura mishi stro a ciki shi da kanshi yake ja yana sha,
A haka suna tafe suna hira har suka isa kawo,

"Wani unguwa ne gidan nata yake?"

"Unguwan Dosa ta can k'asa wajen yan majalisu"
Ta bashi amsa,

Juyawa yayi gefen Hajiya,

"Hajiya nace a can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login