Showing 57001 words to 60000 words out of 190771 words

Chapter 20 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1592

din dan tasan wallahi badan Allah su Maryam suka dawo falon suka zauna ba, ganin tana b'atama kanta lokaci a cikin kitchen din ne yasata fito fuska d'aure bata kalli ko gefen da suka zaunen ba duk da kiran da suke mata na iya shege kin kulasu tayi tayi shigewar ta d'aki to itama dai kamar shi din tana shiga kayan jikin ta ta cire ta fad'a ban d'aki sai da ta gabatar da duk wani al'adar ta na kafin kwanciyar bacci sannan ta koma kan kujerar 3sitter guda d'aya wacce ke cikin d'akin ta kwanta ta rufe kafafuwan ta da dogon hijjabin ta, ganin ta kasa sakewa a kan kujerar dan bata saba kwana a kujera ba sai kawai ta mike ta fito daga d'akin zuwa wanda Hajiya ke ciki,

Duk yanda su Meelat ke kiranta kin kulasu tayi ta shige d'akin ta kulle kofar da key ta k'arasa kan gadon gefen Hajiya ta kwanta,
Ta dade a kwance tana hasaso kalaman AK sai dai kuma ta rasa irin fassarar da zata musu daga k'arshe dai ture tunanin tayi a gefe ta gabatar da addu'ar bacci ta shafe jikin ta dashi sannan ta rufe idon ta tana ci gaba da istigfarin da take gabatar wa aduk sanda tazo kwanciya bacci har zuwa sanda baccin yayi nasarar d'auketa,

Suko su Meelat tun fitar da tayi zuwa kaima AK abinci tana fita Maryam ce ta fara cewa,

"Bebs wallahi AK son Meenal yakeyi, amma kuga ita ko a jikin ta kamar ma bata gane halin da yake ciki ba,ko kuma ta gane tana basarwa ne kawai oho mata"

Meelat ce ta gyara zaman ta kafin ta amsa ma Maryam din da cewa,

"Tabbas hakan take kamar yanda kika hasaso dan ni (Love sunan da suke kiran juna ita da Musty)...
Shi ya fad'a min hakan da kanshi kwana biyu bamu samu zama ni dakeba shi yasa ban miki bayani ba dan shima AK d'in tsabar zurfin ciki wallahi da kyar ya iya fad'ama Yusuf gaskiyar abinda yakeji akan Meenal d'in sannan kuma har yanzun bai iya fitowa fili ya fad'a mata cewa yana sonta ba sai faman kame kame yake ita kuma nasan bazata tab'a kawo zancen wani soyayya a tsakanin suba dan bashi bane a gaban ta,
Love ya rok'i arzikina akan mu d'an janyo musu hankalin ita Meenal din dan shi Mai Jama'a har yanzun tsoron tunkaranta da batun yake, shi yasa kikaga d'azun na tabbar mishi da cewa wasu ne suka biyo mu dan ina son in k'ara tabbar wa, kuma gashi kema kin tabbatar, kedai shaida ce cewa mutumin nan bashi da wani mugun halin da mace zatak'i shi saboda su, kuma koba komai shi d'in d'an uwanta ne kuma wallahi da ace ba son nata yakeyi da gaske ba bazai yarda har su Abokan shi Susan da batun ba dan bai tab'a nuna shaukin shi akan ko wacce mace ba shi yasa suma suke girmama tarin kaunar da suka tabbatar yana mata kuma na mishi alkawarin cewa muma zamuyi bakin kokarin mu wajen ganin mun saita ta a hanya ta yanda cikin sauk'i zata gane son da AK yake mata kafin wani yazo ya mishi shigar sauri"

"Aiko in haka ya tabbata ba k'aramin farin ciki zanyi ba, sai dai kuma ba anan gizo ke sakar ba dan ita dai kin kwana da salin halin ta, wallahi nasan koya fad'a mata cewa yana son ta d'in bai zama lallai ta d'auki abun da mahimmanci ba kina jin tana cewa wai ita ba yanzun zata k'ara aure ba karatu zataci gaba dayi, ban san uban miye zataci da karatun ba, kuma ni tsoro nikeji kar Baba Malam yazo ya maimaita mata wani auren irin wancan a karo na biyu dan kin san dai yanzun batun auren su Fauxieyerh akeyi Suda suka kammala Secondary to wallahi yana iya cewa zai had'a harda ita,inta tsaya wasa sai dai taji shelar d'aurin auren ta amma ita ko ka tsaya ka mata bayani ba lallai bane ta maka kyakyawan fahimta ba,
Sai dai kuma abunda muke hasashe zai tabbata cikin sauk'i ne idan ya zamana shi din yayi gaggawar gabatar da kanshi saboda kinga a yanzun dai babu wani jajirtaccen da zan nuna ince shi take so kinga idan ya fada mata gaskiyar shi koba komai duk wanda zai kawo nashi kokon barar soyayyar to bayan shi zai biyo, dan kinga Ya Salman wallahi ina kula da takun shi muna zaune zakiji yazo yace son Meenal yakeyi, ke nifa hatta da Ya Sa'eed dan dai nasan yanayin kusancin dake tsakanin shi da Meenal tun zamanin yarinta ne amma da nace sonta yakeyi a yanzun saboda yanda naga yana shishshige mata, ke tsaya wai kin san ma cewa Dan Gidan Master ya dawo Kasar nan kuwa?๐Ÿค”".

"Wani d'an gidan master din badai Bash ba?" Meelat ta tambaya

"Shi dai Bash tsohon saurayin Meenal din dai da kika sani, wallahi mun had'u ni dashi ranar alhamis d'in nan daya wuce a kofar doka na tsaya a asibitin Dr Meerah ina fitowa shi kuma yana Saukowa daga benen dake saman nan kin gane wannan plaza d'in nasu dai?"

"Kwarai na gane cigaba da bayanin ki sai me ya faru?"

"Ke Qawata kinga yanda ya dawo kamar wani bak'on balarabe kuwa kinsan dai ko dacan dama shid'in masha Allah balle kuma yanzun an k'ara girma kud'i da hutu sun kara bin jiki,
Ina fad'a miki nidai ina ta sauri dan gida nike son isa da wuri sai naji ana kiran sunana daga baya,
Koda na waiga na rantse miki da allah daga farko ban gane shiba, sai da yace min,
(Baki ganeni bane 3ple M)
kin san Allah koda ya kira sunan da yake kiran mu dashi a wancan lokacin k'ara jefani yayi a cikin rud'ani har sai da shi da kanshi yace min,
(Suna na El Bashir Al Hassan Master).
Allah naji kunya amma na maze dan ya riga ya gane cewa ban gane shiba, mun gaisa dai a tsai-tsaye kafin muyi sallama kuma ya tabbatar min da cewa zaimin har gida mu gaisa, kuma na tabbata cewa zaizo din tunda in baki manta ba Ada can ma bai tab'a cewa zai ma abu kuma ya kasa cikawa ba"

"Turkashi lailai to akwai matsala inhar muka sake Bash ya bayyana kanshi a wajen Meenal ba tareda AK ya bayyana kanshi ba, duk da dai bani da tabbacin cewa har yanzun tana son shi amma dai abun bazaiyi dad'i ba sam idan ya dawo, kin san dai yasan gidan Hajiya kuma zuwa can d'in bazai mishi wahala ba"

"To wai me yasa bazata so shi AK dinba bayan kuma naga alamar akwai fahimtar juna a tsakanin su?" Sultana ta tambaya.

"Hummm kishi ne ke damun ta ba tareda ta sani ba, saboda shi dai mai makon ace idon shi akan mata, sai ya zamana su matan ne idon su yake kanshi ita kuma haushin hakan takeji, yanzun kina tambayar ta zatace miki ai yafiye kyaune shi yasa matan ke binshi ita kuma bazata iya auren mijin da yake da kyau ba bayan itama kullum cikin bibiyar ta mazan keyi cewa suna sonta, amma ah ah ita bata ganin nata kyan kullum nashi kadai ne ya tsole mata ido dan haka shi kad'ai take hangowa,
Kin san tsohon mijinta a tsayin shekarun zaman da tayi gidan shi a matsayin matar shi ban tab'ajin ta yaba kyan shi ko sau d'aya ba duk da shima yana da kalan nashi kyan,
sau tarima bata son muna sako shi koda hira mukeyi, amma da zarar ana hirar farin jini sunan mai jama'an shine na farko da zakuji ta ambata, dan allah ku fad'amin hakan da takeyi shi din ba soyayya bane? Amma ita shegen taurin kai gareta"

"Ku tsaya kuji ni ina da shawara indai har zaku bani goyon baya to tabbas kwalliya zata biya kud'in sabulu komai zaizo cikin sauk'i"

" Shawarar me kike dashi Sultana?"
Suka tambaya a tare suna maida hankalin su a kanta, taso wa tayi daga inda take zaune ta koma tsakiyar su ta zauna,
Kasa kasa sosai tace,

"Kishi ko wanne namiji yana kishin abunda yake so kamar dai yanda shi din ya nuna, haka kuma itama duk da tana nuna batajin komai a kanshi amma dole ai kishin ta akan shi zai tona asirin zuciyar ta dan haka daga gobe wasan zai soma ni zanji da ita ta gefen shi, ku kuma sai kuji da ita ta nashi gefen sai dai kuma in har abunda nike fata ya tafi akan yanda muka tsara to dole zai zama nid'in zan kasance a inda take, ina nufin mai makon in zauna a family house dole zan zauna ne a gidan Hajiya inda shi da ita suke rayuwa ina fatan kun fahimci abinda nike nufi?"

Mun gane mu kuma menene abunda zamuyi?,

Dariya tayi kafin tace,

"Hirar samarin da suke bibiyarta zaku dunga yi da gayya kuna ruruta abun aduk san yake kusa ina nufin kamar yanda kukayi d'azun dafatan dai kun fahimci me nike nufi?"

Dariya suka fashe dashi suna tafa hannu a tare,

"Oh Sultana gaskiya nagode Allah daya kawo mana ke a daidai sanda muke buk'atar ki, dan haka kamar yanda aikin mu ya fara daga yau haka zamu cigaba da d'aurashi a gobe ma har zuwa ranar da hak'ar mu zata cimma ruwa"

Sun dad'e suna tufka da warwara akan yanda zasu tafiyar da Meenal dama shi kanshi gogan kafin suka tashi suma sukaje suka nemi wajen bacci.


*washe gari*

koda suka idar da Sallah komawa sukayi suka ci gaba da bacci,
Hajiya dai mai karin Sassafe ita kad'aice ta fito falon ta k'arya da nata kayan dad'in da Meenal ta ware mata tun jiyan,
To shima Dan mai karfi dai tun fitar da yayi masallaci bai dawo gidan ba, Hajiya kuma ganin su d'in basu da niyyar barin gidan sai kawai bayan ta shirya ta amshi key d'in Motar Meenal taba Mansoor shi ya kaita gidan gaisuwar ya dawo ma da Meenal d'in da key din,
Suko basu suka tashi daga baccin ba sai wajen karfe 10, koda suka fito kuma raba aikin sukayi, Meenal ce ta tsaya gyaran d'akunan baccin su wanda suka kwana ita da Hajiya da kuma wanda su Meelat suka kwana a ciki batayi yunkurin lek'a d'akin mai jama'an ba duk da bawai tasan baya gidan bane, Meelat ce tayi gyaran falo su kuma Maryam da Sultana suka shiga kitchen,
Nan da nan suka kammala aiyukan su kowaccen su taje tayi wanka kafin suka dawo falon suka fara shirin karin safe kafin subar gida,

Suna zaune suna karyawa,
Sadeeq ne ya fara shigowa falon da sallama kafin AK dake biyoshi a baya,

Amsawa sukayi, kafin Meelat dake kallon Sadeeq tana dariya tace,
"Anya kuwa ya Sadeeq in ka zarge wuyar Qawata da igiyoyin auren ka zaka dunga bari tana nisa dakai kuwa?
Dubi fa jiya ne kawai amma har ka biyo bayan ta yau, Allah sarki ni nawa mijin ko yana ina oho, yau ko wayar safen ma bamuyi ba bawan Allah"

Wuce wa ciki AK yayi tun bayan daya gama amsa gaisuwar su shiko Sadeeq gefen da Maryam ke zaune ya nema ya zauna, yana ma Meelat dariyar maganar ta,

"Baby ko dai bakiyi murnar ganina bane in koma inda na fito naga sai wani k'ara duk'ar da kai kikeyi?"

"Dama to kace min zakazo nan ne? Ina fa d'azun ma munyi waya kuma bakace min zakazo ba"
Ta fad'a tana tura baki da kauda kanta gefe,

Sai da ya mik'a hannu ya d'auko kofin shayin da take sha ya kurb'a kafin ya ajiye yana mai cewa,

"Kiyi hakuri nima banyi zaton zan samu damar isowa nan d'inba Mai Jama'a ne ya tattago ni ko bakiyi murnar ganina ba? "

" Nayi wallahi sosai ma,"

"To ki shirya mu wuce Zaria anjima!"

"Ah ah wallahi ai bamuyi haka da kaiba mukam sai gobe zamu koma gida kai dai Allah ya kiyaye hanya,"

"Haka zamuyi Baby?"
Ya tambaya yana marairaice mata,

Fitowa AK yayi shima ya nemi waje ya zauna, a gefen Sadeeq sai ya zamana suna kallon juna shida Meenal,

Ita ko Sultana dama tana ganin fitowar shi ta tashi tsam ta koma cikin d'akin da suka kwana Meelat ma ta rufa mata baya tana cemata bari tazo ta nuna mata wani abu,sai ya rage daga AK da Meenal sai Maryam da Sadeeq wadanda ke hirar su kamar ma sun manta da wanzuwar su AK a wajen, saida su Meelat suka share kusan minti goma sannan suka k'ara dawowa falon,
Suna fitowa tun basu zauna ba Sultana ta fara cewa,

"Sister Meenal wannan guy din naki wanda yace zaizo miki yawo jiya ya kira wayar ki na d'auka, nace mishi bakya kusa yadai tambayeni Address d'in gidan nan Meelat kuma ta mishi kwatance yace zaizo kafin mu wuce gidan rasuwar"

"Waye yace ki tab'amin waya to?"

"Kiyi hakuri nima dan naga tun jiya kuna ta waya dashi nasan saurayin kine shi yasa na d'auka, to miye tun yace zai zo dama batun jiya yaso zuwa ba"

"Dallah can ni bani wayata, shegen karambani kawai meya kaiki tab'amin waya yanzun yana zuwa zai dameni da surutu"

"Nifa ban fito da wayar ba tana can na saka miki a caji"

Tunda Sultana ta fara maganar wai wani guy ya kira Meenal a waya, daga AK har Sadeeq suka bar abincin da suke ci, shi Sadeeq Sultana yake kallo kamar a cikin fuskarta ne zai hango fuskar saurayin daya kira Meenal din shiko AK meenal din ya kafe da kallo,

"Waye shi kike shirin gayyato min shi gidan nan?"

"Eh gaskiya kam waye shi?" shima Sadeeq ya tambaya fuska a daure,

Maryam ce tayi saurin amsawa da cewa,

"Kai Baby ba wani bane fa Ya Salman ne yake ta k'ok'arin ganen ya maye gurbin Yayan shi,
Kaga muma muna ta tayashi yak'i amma ita Gimbiyar sai yanga take mana niko banga abunk'i a jikin shiba wallahi, in Babban yaya yaja baya shi k'arami basai ya shigo ciki ba sun mafi dacewa da Salman d'in wallahi"

"Maryam kin san dai bana son haka koh! Ni da yau she mukayi dake cewa sona Ya Salman yakeyi harda zaki min sharri"

"Oh bai fad'a miki ba wai dama? To nima ai ba fadamin yayi ba kawai alamun hakan na gani shi yasa ni kuma nike mishi kamun k'afa"

"Ke Baby Salman SS Ladan kike magana k'anin Sarki? Kowa?"

"Shifa Baby ashe ka gane shi, wallahi sonta yakeyi amma ita sai wani basar dashi takeyi bayan kuma auren ta dashi bai haramta ba ko a musulunce"

"To ke tunda tace ba haka ba ai sai ki kyaleta koh, tunda ta nuna bata ra'ayi soyayya aiba dole bane, koh koh haka kawai dan su sukafi kowa gata ta auri yayan yanzun kuma sai ta k'ara auren k'anin to allah ya kyauta amma ai ana barin halak kodan kunya'

"To Baby gani nayi gida bai koshi ba ai ba'aba dawa nama ba, tunda shi ya nuna ra'ayi ai gara ta bada kai kawai"

"Meenal kina son shine?"
Ya tambayi meenal din,

AK da bashine wanda yayi tambayar ba har yafi Sadeeq din k'aguwan son jin amsar da zata bayar,

"Allah ya kyauta min mai zanyi dashi"
Ta bashi amsa tana cigaba da cin abincin ta,

Wata k'atuwar ajiyar zuciya ce ta kwacewa AK
Ba tareda ya d'auke idon shi akanta ba yace,

"Ki kirashi ki dakatar dashi da zuwa min gida, kuma ko kin koma ban yarda inji ance yana zuwa wajen ki a gidan Hajiya ba kinji dai na fad'a miki"

Suna gama karyawa suka kimtsa wajen suka fice daga gidan,

Ita dai unin ranar rasa gane kan su Maryam tayi dan lokaci lokaci sai taga sun had'a kai suna k'us da Dariya a tsakanin su,

ga kuma Sultana data isheta da shegen tambaya akan wai lallai sai ta bata Labarin waye AK,
Wai ita dai wallahi yana burgeta, haka tasa ta a gaba sai uban kod'a shi take kamar shi kadai ne namijin daya rage a doron k'asa,

duk yanda ake cika ciki yau yan matan nan uku sun cika ta, gidan mutuwa suke shi yasa ta d'aga musu kafa ita kuma sultana taga alaman sai ta ci mata uwa k'ila idan ta nuna mata true colors dinta zata kiyaye ta a lokacin, Allah ma dai yasa gobe za'ayi addu'ar uku kowa ya kama gaban shi masu zama sai anyi bakwai kuma su bada himma ita dai gobe kam Zaria zata kwana koda motar Haya zatabi ta koma gida kuwa,

Yauma kamar jiya anayin Magrib suka koma gidan AK dan tunda yamma dama ya kira Maryam akan su dawo gida da wuri.



*Ummiee ce*โœ๐Ÿผ[9/7, 9:27 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 21*


Yau dai duk yanda Meenal taci burin su fita yawo hakan bai samu ba domin dai koda suka dawo gidan sun iske Mai Jama'a ya rigasu dawowa gida, ko bai fad'aba tasan da gayya yazo ya kafa ya tsare dan dai kawai karsu fitan tunda ya dawo daga sallan ishsha'i ko bakin gate bai k'ara lek'awa ba,
harma da wani ba Mansoor Umarnin cewa ya kulle gate d'in kawai shima ya wuce ciki wajen nashi iyalan saboda babu mai k'ara fita a gidan.

Da wuri ta mishi magana akan fitan da zasuyi, saboda kar yace yauma basu nemi izinin fitan ba amma sai wani cewa yayi ai dama abinci suke fita siya koh?,
Dan haka in dai dan abinci ne su shiga kitchen su girka duk abunda suke son ci ya riga ya tanadar musu da komai,
Duk yanda tasa shi a gaba da magiya k'iyawa yayi, sudai su Meelat tunda yace ba'a zuwa ko ina dama suka shafa ma kansu lafiya,

Hajiya najin Meenal d'in na ta faman magiya amma bata sa baki ba har saida shi d'in yabar wajen ya shige d'akin shi saboda yanda ta dameshi, sannan hajiya tace,

"Ina kuke batun zuwa yanzun da daren nan Meenal?"

"Hajiya wani shago muka gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login