Showing 108001 words to 111000 words out of 190771 words

Chapter 37 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1580

fatali da duk sauran samarin da suke ta mata naci a baya,
Sai yanzun data riga ta gama Koran kowa ne kuma za'ace a cikin sati d'aya ake buk'atar ta fidda mijin aure?

A wannan ranar ma Sarki yazo wajen ta hira sai dai kuma tun zuwan shi ya gane akwai abunda ke damun ta amma juyin duniya yayi da ita akan ta fad'a mishi mike damunta tak'i, hirar ranar dai babu armashi haka suka rabu ya mata Sallama akan sai sun had'u a zaria.

Shi kuma sarki tsakanin shi da Teemah yanzun kam komai zam zam dan bakin kokari Teemah tanayi wajen bashi kulawa abinda baiyi tsammanin cewa zata iya yinsu a shekarun baya ba shi takeyi mishi a yanzun, idan kaga yanda suke rayuwa bazakayi zaton cewa ba haka suka rayu tun farko ba, shi kanshi saboda kwanciyar hankalin daya samu harda wata yar k'iba yayi, batun gyaran gidan su na KD ko tuni Salman yayi tsaye komai ya kammala kayan su wanda teemah ke buk'ata tuni aka tura su zuwa KD duk wani shiri na tashi sun riga sun gamayi, kasuwancin Teemah din kuma ta mik'a shi a hannun Azizah ranar da Moon zata wuce Zaria suma shine ranar da zasu wuce KD,

Ita Moon daga gidan su kanin ta imran ne ya kaita airports a wajen shiga jirgine kuma suka had'e da Sarki da nashi iyalan wato matar shi da kannin ta wad'anda zasu mata rakiya zuwa sabon gida,
Sam Sarki bai shaida mata cewa shima wannan jirgin zaibi ba duk da cewa shine ya biya mata kudin jirgin, kai jama'a wallahi maza dai sun kware a wajen iya munafunci wai ita Moon itace Sarki zai nuna kamar bai Santa ba balle yasan daga inda ta fito a cikin jirgin nan tafa ganshi ya ganta amma sai ya wani d'auke kai sai wani iyayi yakeyi yana wani faman tarairayo tsohuwar matar shi zuwa jikin shi ita kuma sai wani k'ara langwabewa takeyi a jikin shi kamar dai a kanta aka vara d'aukan cikin haihuwa, zama na awan nine amma ji Moon tayi uwa kwana sukayi suna tafiya saboda tsabar kishi gashi kuma duk yanda taso d'auke kanta daga kallon shida matar nashi hakan ya gagara sai dai dasun had'a ido ita kuma take jifan shi da harara,
Wallahi mutumin nan ma ya raina ma kanshi wayau dama yasan yana son matar shi har haka shine kuma zaizo yace yana son ta bai kuma ji kunyar idon taba yake kwantar da matar nashi a jikin shi wato hummm ba komai ai wallahi yayi da ya,
Ba karamin Hamdala tayi ba a sanda jirgin su ya sauka, bayan saukan su dama so tayi ta d'auki drop kawai ya wuce da ita Zaria kai tsaye sai gashi wai dan munafunci suna sauka Sarki ya fad'a kiranta a waya, tana kallon kiran ita kuma tayi mishi banza,
Ganin bata dauki wayar ba shi kuma sai ya tura mata messages yana shaida mata cewa ta jira akwai wanda zaizo ya kaita zaria,
Tsaki tayi bayan ta karanta a bayyane ta furta cewa, Allah ya kyauta tahau motar shi ko jirgin nan inda tasan cewa dashi da matar shi a ciki da bata hauba,

Duk abinda takeyi yana lura da ita hakan nema yasa bayan su Teemah sun shiga mota ita koma ya koma inda take tana shirin shiga motar da zai kaita zaria, mai da k'ofar data bude yayi ya rufe,

"Ba nace miki akwai wanda zaizo ya kaiki ba me yasa bakyajin magana ne, Kwaro kai"
Ya kira sunan kwaron bayan yaja hannun ta,

"Ka d'auko kayanta kasa a mota ka kuma sallami shi wannan mutumin"
Ya k'arasa fad'a yana cigaba da jan hannun ta zuwa motar da kwaro wanda bai dade da isowa wajen ba ya faka a kusa dasu,
"Ok Sir" shi kuma kwaro ya furta sai da ya sallami mai motan da wasu yan kud'ad'e kafin mutumin da kanshi ya maida kayan nata zuwa motar kwaron,

"Ni dai ka sake min hannu ina ruwanka dani ne wai,ina ce jirgi d'aya muka hawo tun daga Lagos zuwa nan amma ka fuske ka nuna kamar baka tab'a ganina ba sai yanzun ne idanuwan ka suka shaida maka ni?"
Ta tambaya cikin fushi tana kwace hannun ta,

"Too haka akayi?" Ya tambaya yana dafe gemu,

"Ah ah ba haka akayi ba kuma ni bazan bi motar kaba tunda ba kai ka kawoni ba kasa ya maida min kayana cikin motar daya cirosu"
Ta fad'a tana dafe kugu bayan ta b'ata fuska ta zunburo baki tana jijjige jijjige,

Shi dai kwaro lallab'awa yayi ya shige gefen direba ya zauna cike da mamaki,
Shifa yarinyar nan kallon idon sani yake mata sai dai kuma ya kasa gano a inda ya Santa amma kam tabbas ya Santa,
To wai ma da Sarki yake ta wani lallab'ata kar dai ace Sarki wani auren zai k'ara,
Kashe kunne yayi yana sauraren hirar su a yayinda Sarki yake cewa,

"Moon please ki adana rikicin ki ba yanzun ba, naji nayi laifi kiyi hakuri kibi kwaro ya tafi dake idan nazo zan amshi hukuncina"

"Moon "kwaro ya maimaita a bayyane, k'ara lekowa yayi, a bayyane ya k'ara cewa,

"Wallahi itace, Moon dai k'awar Meenal, Meenal fa matar da Sarki ya saka tome ya had'ashi da Moon kuma?.


*Ummiee ce*
[9/28, 8:44 PM] zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️
*BOOK 2*

*PAGE 35*


Tanaji tana gani haka Sarki ya juya zuwa wajen motar da matar shi take ciki ya shige ciki abinshi bayanda yasata a motar Kwaro ya kulle duk rikicin datakeyi na cewa ita bazata hau motar ba haka yayi kunnen uwar shegu da ita bai k'ara kulata ba tun bayan da yace mata ta adana rikicin ta har su had'u a Zaria ,
Kallo mai cike da madaukakin mamaki tabi bayan shi da shi har zuwa sanda mota biyun da akazo daukar su dashi suka fice daga cikin airports ɗin,
Hummm Namiji dan baban shi,
Bata san ya zata kwatanta abinda taji a cikin zuciyarta a dai dai wannan lokacin ba, abunda tasani kawai shine bataji dadin halin ko in kula ɗin daya nuna mata a cikin jirgin ba, to amma idan tace tayi fushi wani dalili take dashi nayin fushin alhalin iya kalmar I LOVE YOU ne kaɗai ya shiga tsakanin su, bayan shi kuma har yanzun ta kasa bashi damar da zai gabatar da kanshi a gidan su balle ya tantance matsayin shi,
To ma wai me yasa zataji zafi dan ya nuna kulawan shi akan matar shi? zuciyarta ta tambayeta, ance kasowa dan uwanka abinda kake soma kanka ai itama bazataji dad'i ace mijinta ya kula wata budurwa a gaban idonta ba,
Itafa laifin shi kawai take son gani ba kuma komai ya kawo hakan ba sai tsabar kishin shi, batayi zaton zataji kishi irin haka dan kawai ta ganshi tareda matar shiba,
"To amma ai yasan ina son shi dan haka dole yasan zanji kishi", sai da ta tura baki gaba kafin murya ƙasa² cike da ƙunƙuni ta Kara cewa "kuma wallahi nima sai na rama"

"Na'am kina magana ne?"kwaro dake tuƙi ya tambaya,
"Ni ba dakai nakeyi ba"ta amsa mishi tana kauda kanta gefe, shima sai bai ƙara bi takan taba sukaci gaba da tafiya.

Shiko Sarki a gefen shi dariya ma moon ɗin ta bashi, wai me yasa su mata basa son zaman lafiya ne wai?
Ita yanzun tana fushi dashi cewa bai kulata ba duk da cewa ya ganta, to fisabilillah wani irin neman magana ne wannan? To so tayi shikenan kawai daya ganta d'in sai yabar matar shi da nata ahalin ya dawo gefen ta ya tare bayan kowa yana da mazaunin shi ko me take so yayi?
To idan ma ya kulata me take so yayi matane? Ita da kullum take nuna cewa babu komai a tsakanin su tunda KO zuwan da yakeyi gidan su a sace take fitowa bata son asan cewa yana zuwa wajenta,
Humm gaskiya rikicin mata sai su ita nata ma wasa ne bata san cewa inda ace matar shi tasan abinda yake tsakanin shi da itaba da Allah kad'ai yasan kalar tashin hankalin da zasuyi, shi bai shirya yin fitina dako wacce daga cikin suba in jarumta take son nunawa ta bari tukun har zancen auren su ya tabbata sai ya tabbatar da jarumace ita.

Sak'o ya tura ma Moon d'in kamar haka "Kar kiyi fushi Baby zan kiraki idan Allah yasa kun sauka lafiya, ya kike"

Koda saƙon shi ya isa cikin wayarta sai da ta karanta shi ta ƙara mai maita shi kusan sau uku, to mema yake nufi da cewa kar tayi fushi? To in tace tayi fushi ma ai bata da dalilin yin fushin wacece ita a wajen shi? menene matsayin ta? sune tambayoyin da take buƙatar amsar su daga gareshi, to dan Allah a yanda yake nunawa ne zata wani fito kai tsaye tace mishi iyayenta sun bata sati d'aya ta fidda mijin aure kuma ita shi zuciyarta ta zab'a,
Tunda harta yarda ta kula mai mata ai dama tasan dole zata fuskanci abubuwa fiye ma da wanda yayi mata a yau,
"Nace kiyi hakuri" ya kara tura mata,

Ita kuma sai ta tura mishi amsa kamar haka,
"don't Baby me, i am not your Baby😒"
Bai ƙara tura mata ko wani saƙo ba tun bayan daya karanta amsar data tura mishi , dan yaga alaman rikici takeji da gaske,

Acan gidan Sarki kuwa yan Zaria ne maƙil waɗanda sukazo domin tarewar tun daga kan iyalan gidan Malam yan gidan su da kuma yan uwan Uwar gida sun kammala gyaran gidan tsaf sai isowar masu gidan kadai sukeyi, dan haka koda suka isa babu ɓata lokaci akaci gaba da gabatar da walima yan Zaria basu bar gidan ba sai yamma sukabar masu gidan suna huta gajiyar tafiyar da sukayi kafin wucewar su kuma saida Malam Sulaiman suka zaunar dasu suka musu nasiha akan hak'uri da kuma zaman lafiya a tsakanin su especially its Teemah da bata da kowa a garin sai Mijinta da yaranta Uku wadanda Uwar gida ta dawo mata dasu hannun ta, to muma dai sai muce Allah ya zaunar dasu lafiya.

Zaman shiru akayi a cikin mota tsakanin Kwaro da Moon babu wanda ya kula Wani har sai da suka isa jaji, fakawa yayi a kofar wani shagon da ake saida snacks a cikin motar ya barta ya shiga cikin shagon, bai jima ba ya dawo ya bud'e gefen shi ya shiga saida zauna kafin ya juya baya ta gefen da take ya mik'a mata ledar hannun shi, "Sarki yace bakici komai ba"
Amsar ledar tayi bayan ta mishi godiya, shidai har yanzun bai dena mamaki ba, bai k'ara tabbatar da cewa lallai Moon din da yake hasashe bane har sai da bayan isar su Zaria ya tambayeta Ina suka nufa ita kuma ta shaida mishi da cewa unguwar malamai zai kaita, a gidan Baba Malam ta sauka wajen Mommy Hauwa saida taci abinci ta huta kafin ta kira Meelat ta tambayeta suna inane? Ita kuma taje ta same su. Wannan shine abinda ya faru, tunda ta sauka kuma taki d'aukar wayar da Sarki yake ta faman jera mata kira da tarin sak'onni,

*****

"Yanzun Meenal idan Bash yazo wajen ki wani irin tarba zaki mishi? "
Maryam ce ta k'ara jefo tambayar jin dukan su sunyi shiru,
Ajiyar zuciya mai nauyi Meenal din ta sauke,
"Zanyi murna da ganin shi mana, koba komai nasan ya damu dani sai dai ni kuma a yanzun bana jin komai a kanshi, ba kuma wai Ina kinshi bane ah ah Bebs please let's close this chapter I really don't want to think about it anymore, ke Moon wai ma uban me ya wani kaiki zuwa ki sauka a unguwar malamai bayan kin san cewa ni ina nan?"

"Saboda bikina tazo shi yasa dole zata zauna kusa dani har a gama komai idan ta kaini gidan mijina saita dawo nan"
Meelat taba Meenal amsa tana hararar ta.
Washe garin ranar ne kuma suka gabatar da event din da suka shirya ma Meelat a school ,

kamar yanda suka shirya surprising dinta takoyi mamaki kwarai ta yanda har suka shirya komai na program din batareda sanin taba, hakan kuma bai hanata nuna dad'in taba sosai domin ba iya friends dinsu na cikin makaranta bane kawai suka samu damar halartar wajen harma da wasu daga cikin tsoffin k'awayen su na primary secondary dama yan uwa na kusa, sun shirya abun ya tsaru sosai kuma Meelart din ta samu tarin kyaututtuka daga abokanan arziki, anci ansha anyi raha haka kuma anyi ma Amarya fatan Allah ya basu zaman lafiya ita da mijinta a gidan auren su, daga school da aka watse taro dukan su unguwar malamai suka wuce, wanda hakan kuma yasa Meenal bata samu damar komawa gidaba dole a nan unguwar malaman suka kwana.

Shiko AK a gefen shi tun rana yake faman jerama wayarta kira sai dai kuma ga mamakin shi wayar zatayi ta karane kawai har zuwa sanda zata gaji ta yanke batareda an d'auki kirar ba,
Yasan cewa dole zatayi busy saboda program d'in dan haka sai ya mata uzuri da zaton ko idan tazo taga tarin missed call dinshi ita ma zata neme shi daga baya,
Sai dai kuma abin haushi haka aka wuni zungur ko sau d'aya bata kira ba shima kuma daya gaji da jiran kiran nata ya k'ara kira bata dauka ba daga karshe ma sai aka dunga fada mishi cewa wayar tana kashe,
Yaji fushi sosai dan ya shak'a domin dai ta fita gidane yau d'in da sassafe ko neman shi batayi ba balle suyi sallama,
Messages din safe daya tura mata ma bata bashi reply ba koba komai ai yaci ace ta kira shi taji ya yake amma batayi hakan ba, shi kuma ya yarda girman ya kirata tak'i d'aukar wayar d'auriya ya aro ya d'aura ma kanshi dan so yake yaga iya gudun ruwan ta in har ba itace ta kira shiba to bazai nemeta ba wannan shine hukuncin ta. (Bari mu koma gefe mu gani zai iya k'in kiran🤷🏻‍♀️)

Ita KO gaba d'aya yau d'in yanda abubuwan suka sha mata kaine yasa dole ta fita daga wani batun d'aukar wayarta ta duba ko ya kirata ba kuma wai dan ta manta da batun shi bane ah ah komai takeyi yana nan mak'ale a cikin zuciyar ta kawai dai bata son ta raba hankalin ta biyu ne dan shi idan ya kira waya bai san yayi magana na minti d'aya ko biyu ya yanke kira ba, ah ah ko bazaice komai ba haka zai ajiye wayar kuma yace dole sai ita ta mishi hira,
yar karamar wayarta ce a tareda ita wayar da shi AK yaketa kira a cikin mota ta barta k'aramar kuma shi bashi da wannan number din,
Bata waiwayi babbar wayar ba sai da dare, koda ta d'auko ta kuma ta dad'e da mutuwa dan haka sai bata damu da kunnawa ba kawai sai ta mak'alata a caji sukaci gaba da hirar yanda taron ya k'ayatar ita dasu Moon.

Duk yanda ranshi ya b'aci na rashin kunna wayar nata haka ya daure da dare yayi kuma kasawa yayi ya tsare yana jiran ta dawo gidan ta fad'amishi dalilin ta na kama ta kashe amma har k'arfe 10 na dare ya wuce basu ba alamar su, gaza hak'uri yayi yana ciccjiwa haka dai ya daure ya kira wayar Sultana, bayan ta amsa kiran ko gaisuwar da take mishi bai amsa ba ya jefo mata tambaya kamar haka,

"Ina Dr take?"
koda bai kira suna ba tasan Meenal yake nufi, dan haka sai ta amsa mishi da cewa "tana falon Baba Malam in kai mata wayar ne?"

"Me takeyi acan d'in ne? Ita Ina takai wayarta Nike ta kira a kashe? "

"Wayarta ya mutu babu caji bari in kai mata wayar"

"OK kuma idan kin shiga bance ki bata wayar ba, kawai dai ki zauna kusa da itane yanda zanji muryarta"

Amsawa tayi da cewa to kafin ta tashi ta wuce falon Malam d'in,

Ya Sa'eed, Ya Sheikh, Ya Naseer sai Meenal cikon na 4 sune zaune a falon suna hira a tsakanin su Meenal da Ya Sa'eed su nasu hirar suna tattaunawa ne inda yake tambayar ta cewa ya suke ciki tsakanin ta dasu Aliyu, wayarta dake caji a gefenta ta d'auko saida ta kunna wayar kafin ta shiga cikin WhatsApp ta nuna mishi chat d'inta da Ya Hashim inda yake fad'amata cewar yana son ta bashi ranar da zaizo gida ya sameta yana son su tattauna wani magana a tsakanin su, ita kuma ta dai bud'e sak'on ne kawai ta karanta amma bata bashi amsa ba saboda bata riga ta yanke inda zasu had'uba,
Bata son ya sameta a gidan hajiya ne saboda tana tsoron AK,
Eh mana dole tace tana tsoron shi tunda tasan idan yaga Hashim din kai tsaye cewa zaiyi saurayin tane ita bata son ma yaga Hashim din dan tsakani da Allah Hashim dai ya mata tsufa wallahi tasan idan AK ya ganshi ma dariya zai mata, shifa yanzun saboda tsabar samun waje wai har itane zai kafama masu gadin gidan dokar cewa duk wanda yazo gidan su fara tambayan shi wajen wa yazo inhar mutum yace wajen ta yazo to karsu barshi ya shiga su fad'ama kowa waye cewa bata nan, dan Allah jama'a kuji wani k'arfin halifa irin na AK FISABILILLAH haka ake rayuwa gaskiya saurayi a cikin gida baiyi ba wallahi,

"To me yasa baki bashi amsa ba, Meenal Ina jiye miki abinda zaije ya dawo fa," ya fad'a murya k'asa² kamar yanda suke magana shida ita d'in tun d'azun babu maijin abinda suke tattauna wa,

"Zanyi kokari gobe idan na koma gida ince mishi yazo"
"Ah ah kawo wayarki dai ki tura mishi sak'on yanzun"
Badan taso ba haka tayi typing ta tura ma Hashim din cewa yazo tudun wada gobe ya sameta da rana dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login