Showing 9001 words to 12000 words out of 190771 words

Chapter 4 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1528

kuma ya zama dole ita Jamilan basai suje ita da Maryam su fito da ankon ba, cire anko dai ba wata tsiya ba,"

"Hajiya kasuwa kawai fa zamu awa nawa ne mun siyo mun dawo?"
Cewar Meenal.

"Eh fa kasuwar koma minti daya ne nidai nace a'a dan dole inyi kaffa kaffa dan kar kiyi mamaki ace ubanki yana nan yasa masu kula mishi da shiga da fitan ki dan kinsan dole na mishi kike zaune a gidan nan badan yana so ba kamar wani shine yama yata nakudar ki"

Cike da haushi ta tashi fuuuu kamar wata kububuwa ta haye sama tana turo baki,

"Ai sai dai Kiyi ta fushin ki amma babu abunda zai canza in fad'a miki, aini kuma shi kenan na d'auko ma kaina jangwam magana daya biyu ki wani dunga turomin baki dan kaniyar ki, da dai ina zamana abuna baki na Alaikum yanzun banda halin in zauna shiru a cikin gidan nan sai dai in kina makaranta, ai dole ma Kiyi aure da wuri wallahi tun kafin a ganmu a rana a mana gwai Allah"

Ita fa Meenal bawai saboda abunda Hajiya tace bane yasa ta wuce sama ah ah tadai tuna cewa bata da pad din da zata canza cikin dare ne dan a kayan data kwaso a gidan Sarki pad guda daya kawai ta gani,
Dan haka koda ta shiga cikin dakin kudi taso d'aukowa domin ta fita shagon dake waje ta siyo saboda gidan na hajiya dai babu yara balle ta aiki wani daga cikin su,
Sai dai kuma tana shiga dakin kira ya shigo wayar ta koda ta duba kuma sai taga malam ne ya dawo mata da kiran da tayi mishi d'azun bai dauka ba dan tunda ta dawo gidan kullum ne zai kirata dan ya tambayi ya take da fatan hajiya bata matsa mata kamar wata wacce hajiyar zata dafa ta cinye,
To anyi rashin sa'a yau din gaba daya basuyi yawa ba dan tayi sammakon zuwa makaranta wanda hakan yaja harta mance da wayarta data kashe tasa a caji,
Sun dade suna hira bayan sunyi gaisuwa kafin ya mata saida safe ya kashe wayar,
Gyalen dake kanta kwai ta gyara ta d'auko kudin ta sauko, babu kowa a falon sai Sadeeq dake waya, AK da Musty duk bata san ina sukayi ba garama hajiya taji motsin bude kofar dakin ta d'azun da alama ciki ta shige,

"Ah ah an matan Hajiya sai ina kuma?"
Sadeeq ya tambaya yana dan kauda wayar daga bakin shi,

"Kofar gida zani zan d'an siyo abu a shagone yanzun zan dawo"

"Kawo in amso miki Kiyi zaman ki dare ya farayi"

Kai๐Ÿ˜ณ" ta furta tana zaro ido, ina ita ina aiken Sadeeq siyo pad fisabilillahi,

"Ya akayi ?"ya tambaya
"Ah ah ka barshi dan Allah wallahi yanzun zan dawo kaga ai waya kakeyi"

"Kawarkice ko in baki ku gaisa ne?"

Bata tsaya ba tana ficewa daga falon take cewa "ah ah kace ina gaisheta"
Koda ta fito babu kowa a harabar gidan sai hasken wutar lantarkin daya haska ko ina ya fito fes kamar ba dare ba, daga can bakin gate kuma masu gadine zaune suna hira a tsakanin su,
Karasawan da tayi kusan sune kuma hakan yasa daya daga cikin su mai suna Isah tasowa,

"Zakiyi aike ne Hajiya?"

"Ah ah ya Isah ba bu wani abu jeka zauna kawai zan amso da kaina"

"Haba Hajiya gamu zaune ba wani abun mukeyi ba ai da nauyi mu barki kije siyan wani abu da kanki da girman kujeran ki ranki ya dade"

Da murmushi a fuskanta ta amsa mishi da cewa,
"Allah kuwa ka koma ni da kaina zanje ai ba zama zanyi ba kafin ka sani na siyo na dawo"

"To shi kenan ranki ya dade tunda kince haka a dawo lafiya"
Ya k'arasa ya bude mata kofar ita kuma ta fice a gidan,
Duk da cewa a wasu unguwan nin za'a iya cewa dare ya farayi ta yanda zirga zirgan mutane zakaga ya ragu su nan ba haka abun yake ba domin yawancin darare a cike wajen yake kasancewa da mutane sakamakon wadannan shagunan da suke raya unguwar akoda yaushe baya rabo da jama'a inba tsakiyar dare ba,
Bata tsaya bata lokaci ba taje chemist din dake nan ta siyo pad din guda d'aya kafin idan taje asibiti gobe zata dibo wasu,
Tana siya din kuma ta dawo gida, wannan karan ma Isah ne ya bude mata domin tana tsaye harta je ta dawo,

AK ta hango zaune a cikin motar shi ya kunna fitilar cikin motar sautin kid'a na tashi kadan kadan shi kuma yana zaune a mazaunin driver sai dai bai kulle kofar motar ba domin kafar duka biyun ma ata wajen motar suke yana danna waya,

Murmushi tayi, kasa kasa take cewa,
"Mutum bashi da aiki sai na cire manyan kudade yana siyan manyan motoci to muma dai baza'a mana Kuri ba atoh,"
Key din motar ta na wajen Sarki dake rike a hannun ta wanda dama ta fito dashi ne da niyyar idan zaka koma ciki ta bud'e kofar motar akwai sakon da Meelat ta bata d'azun a makaranta shi take son dauka a cikin motar,
Sai da ta jinjina mukullin da kyau sannan ta matsa luck daga inda take tayi unlucky din motar, har wani canza tafiya take a yayin da take k'arasa wa zuwa wajen motar,

Shi kuma AK dake zaune yana amsa waya ta Bluetooth din dake kunnen shi daya wayar dake hannun shi kuma yana duba sakon ni karar da motar tayi ne yaja hankalin shi zuwa gareta dan sam bai san da wanzuwar ta a wajen ba,

Kallo yake binta dashi cike da burgewa domin shi dai a yanzun kam allah ya sani babu wani abun halittan da baya gajiya da kallo wanda kullum yake fatan ya dauwama yana kallo kodan samuwar farin cikin zuciyar shi irin yarinyar nan,
Shi dai yasan bai taba jin son wata yarinya irin yanda yake jin sonta a cikin ko wani fitar numfashin shi,
Ji yakeyi kamar inbai sameta yana iya rasa numfashin shi,
Wallahi ko nawa za'a nema a wajen shi zai bada koda ko kafatanin dukiyar shine dan dai kawai ta zama mallakin shi.

Dan haka da kallo yaci gaba da binta yana jin wani yanayi mafi kololuwar dadi na lullube shi, har zuwa sanda ta isa wajen motar ta wani bude ta da still,
Murmushi yayi a bayyane ya furta cewa "da alama dai yar kauye tayi agogo shine ake mana kaud'i"
Kallon ta yaci gaba dayi yayin da ita kuma ta shiga cikin motar ta zauna, saida tayi warming motar da kyau kafin ta fito daga ciki ba tareda ta kashe motar ba ta zagaya ta bud'e bayan motar ta cire sakon da take son d'auka sannan ta maida booth din ta rufe ta Kara komawa cikin motar ta zauna itama kafafuwan duka guda biyun suna waje kamar yanda ya zauna,

"I will call you back John please excuse me"
Ya furta cikin harshen turanci bai kuma jira amsar John din ba ya yanke wayar,
Takowa yayi zuwa inda nata motar yake bayan ya tura murfin nashi kofar motar ba tareda ya kashe ba har ya iso inda take,
Tun tasowar shi idanuwan ta ke kanshi tana mishi kallon kasan ido ba tareda tayi yanda zai gane cewa kallon nashi takeyi ba, har ya iso inda take, yana karasawo kuwa kamshin turaren shi gaba d'aya ya lullube wajen, wanda dole saida ta runtse ido tana mai bude kofofin hancin ta dan taba turaren nashi damar isa cikin kwalwarta da kyau......



*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ
[8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*~{{MY FAMILY}}~ BOOK 2.*
ยฉยฎ *UZ-2023.*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*

*Page 5.*


Ke farar kura wai me yasa kika raina nine?"

"Ni kuma fisabilillahi to me kuma nayi maka yau daga dawowar ka?"
Itama ta maida mishi da tambaya.

"Oh baki ma san me kikayi min ba kike cewa?"

"Eh"
ta bashi amsa a takaice.

"Da kyau amma kin san dai tunda na shigo ko gaisuwa bai had'ani dake ba koh?
Ko shima gaisuwar ban kai darajar da zan same shi daga gareki bane?"
Ya k'ara tambaya yana kureta da kallo.

A yayinda ita kuma kunya ya rufeta, dan sosai taji rashin kyautawar hakan,

"Kayi hakuri na manta ne ban gaisheka ba,Ina wuni ya hanya dafatan ka dawo lafiya?"

"Lafiya kalau alhamdulillah, ko kefa!"

"kuma ma ai laifin Kane tunda kaine ka shigo ta kofar baya ka bani tsoro yasin nayi zaton aljanine!"

"Oh shi yasa kika kirani da suna fatalwa dan kawai na biyo ta kofar kitchen? Kuma ai nayi sallama keda kakarki da kuke ta surutu ne bakuji ba"

Sai da ta maida kanta k'asa saboda abunda take son fadi tasan bazata iya fadar shi a yayinda take kallon cikin idon shiba kafin tace.

"To ai manyan kaya naga kasa kuma fa sai faman murmushi kake tayi shi yasa kawai nayi zaton ba kai bane, amma da kayi magana aina gane cewa kai din ne dai da gaske,"

"Manyan kaya!
Murmushi?"

Ya tambaya yana dage mata giran shi guda daya a yayinda ta d'an d'ago nata kan tana kallon shi kad'an kad'an,

Sai da tayi yar karamar murmushin ta dake bala'in burgeshi kafin ta amsa mishi da cewa...

"Eh mana Allah kuwa nidai banfa tab'a ganin kasa manyan kaya harda hula irin yauba, ko lokacin bikin su Aunty Sas da Anty Fati duk kana nan kaya kasa, kuma kai ai kullum fuskarka a murd'e take"

"Kamar fuskar shanu ko?"
Ya tambaya yana tsare ta da ido,
Sai da ta kauda kai kafin ta amsa da cewa,
"Eh mana sai yau kawai naga kanata murmushi harda dariya da kyakyatawa ka dunga yifa,shi yasa ni kuma nace fatalwa.
Dan ma ba kaga yanda manyan kayan da murmushin fuskar ka suka sa ka k'ara kyau kamar wani ango bane, allah da kullum bazaka yarda ka dunga d'aure fuska ba,"

"Ango dai!"
Ya tambaya da mamaki,
Ita kuma ta amsa da cewa
"Allah kuwa koda yike kuma gara dai ka dunga d'aure fuskan naka saboda yan matan dake nacin binka kamar wani namar kasuwa"

Ta k'ara furucin ta da d'aure fuska sab'anin farkon zancen data d'auko shi da murmushi a fuskar nata,

Murmushi yaci gaba dayi, yana jin wani irin farin ciki da dad'i mara musaltuwa, domin dama ai shi abunda yake muradine wato ta yaba kwalliyar kuma gashi ta yaba d'in duk da dai cewa ita bata san manufar shi nayin kwalliyar ba, in ko haka ne ai shi abubuwa zasu zo mishi da sauk'i koba komai ai gashi yanzun ma ta bashi wani k'arin haske, akan yanda zai samu damar kwamushe zuciyar ta a saukake,
Dan haka a can kasan zuciyar shi ya tsinci kanshi da furta cewa,
"Anything for you my โค๏ธ love "
Dan haka fuska cike da murmushi kana kuma yana girgiza kanshi ya nunata da yatsar shi manuniya duk a lokaci d'aya.

"Ke wallahi yarinyar nan fitinan niyace, oh kice k'aremin kallo kawai kikayi a d'azun din bawai tsoron fatalwa ba, to tunda har kika samu damar kallona a arha sai kin biya farashin kallon,
Toma wai waye yace miki nid'in bana dariya neh? Inda bana dariya zakiga mutane na bina ne? Ko kin manta in kiyata ne *MAI JAMA'A*? "

K'ara matsar da jikin shi zuwa kofar motar yayi ya wani jingina kafadar shi da kofar motar ta inda take zaune yayi tsayuwar a karkace gamida d'an rage tsayin shi ta yanda tsayin nashi zai dai da ita da ita dake zaune, hannun shi duka biyun kuma goye suke a kirjin shi, ya kuma karkato gaba daya ya rufe ta kafin yace..

"Fad'amin yarinya kenan dai na miki kyau, koda yike ai kin riga kin fad'ama miye nawa na tambaya kuma"

Dariya ta fashe dashi irin dariyar ban haushin nan tana nuna shi tace.

"To sai me dan nace kayi kyau ko bakayi kyau ba,halan baka yarda da kanka bane? ai dai kasan ni ba abokiyar adawar ka bace ba kuma zanyi maka hassada ba koba komai ai nima mai kyan ce ba kuma fina kyau d'in kayi ba,balle inyi kishi dan kawai nace manyan kaya da murmushi na maka kyau bawai yana nufin na yaba bane, kawai dai ka d'auki hakan a matsayin shawara ina ganin idan ka rike hakan a gaba zaiyi tasiri ga matar da zaka nema kasan wasu matan sun iya jefa kansu a had'ari wajen auren abu mai kyau"

Katseta yayi da cewa
"Kefa? Ke baki son abu mai kyau d'in ne?"

"Tab aini matsala na da namiji mai kyau bai tab'a zama mijin mace d'aya, domin ko bai nemi mace ba su matan zasu neme shi kaga kuma ni mijina nike da burin aure bawai mijin wata ba dan haka babu maza masu kyau a lissafina sai wanda na tabbatar da cewa shi d'in zai kasance nawa ne bana kowa ba๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€๏ธ ina nufin bazan tab'a rabashi da wata macen ba zai dauwama ne a matsayin mijina ni kadai"

"Hummm" ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi,

"Kenan in irina ya nuna yana sonki ba zaki amince ba?"

"Zan amince idan na tabbatar da gasken gaske yake son nawa kuma bashi bayi min kishiya"
ta k'arasa fad'a tana karkata kai,

Dariya ma ta bashi wallahi dan haka yako kama dariyar abunshi dan ya tabbatar har yanzun da yarinta sosai akan yarinyar nan, a cikin dariyar nashi ne yake cewa.

"Ashema karamar kwalwa gareki yarinya tunda har zaki yarda idan namiji ya miki dadin bakin cewa dake kadai zai dauwama har karshen rayuwar shi, to ma idan ya miki alkawarin kuma zuwa gaba allah ya kaddara cewa dole saiya k'ara auren ya kenan zakiyi?"

"Sai ince ya sakeni" ta fad'a tana bata fuska da turo baki.

"Ai kaji matsalar yarintar ba, to idan kin fito kina da tabbacin samun wani mijin single wanda bai da mata kuma shima kina da tabbacin zai iya zama bai miki kishiya ba? Ko koh haka zakiyi ta aure kina fitowa da zarar miji yace zai k'ara aure?
Koda yike muma bar hirar nan dan bazaki gane me nike nufi ba, yanzun fad'amin ya zaman gidan ina fatan kina jin dadin shi tunda kika zab'i dawowa cikin shi ki zauna? "

"To wai kai dan Allah laifina kake gani?" Ta tambaya muryar ta cike da rauni,

"Ah ah ni bance ba, nasan dai zama da Hajiya ne kamar yanda zuwa yanzun nasan kin fara tantancewa"

Dariya tayi sannan ta daura da cewa
"Hajiya hooo wannan matar Allah dai ya yafe mata yanda duk tabi tasa min ido bani da katabus harta abincin da zanci so take tace sai wanda ta zab'amin zanci kamar a cikinta zansa abincin, nama gode Allah daba uni nikeyi a gidan ba, kasan Allah da naga ta fara sababin ta nike sulalewa inyi makaranta koda ko bani da lecture"

Dariya suka sa dukan su ita dashi din,

"Hajiyar ce yar sa ido koh? Aiko sai na fad'a mata,"

"Amma aini dai kaine ka tambayeni ni kuma na baka amsa"
Ta fada tana tab'e baki a shagwabe,

"Wai akwai bak'in da akayi a cikin gidan nan ne?"
Ya tambaya
"Babu kowa fa daga ni sai Hajiya dan Hajiya Jummai ma ta tafi Abuja jiya, me kagani ne kake tambaya hala?"

"Ok nayi zaton ko anyi bak'ine danaga wannan motar ai"

"Wannan motar wai? Mota tace fa bayan tafiyar ka aka kawo min!"

"Motar ki๐Ÿ˜ณ?" Ya tambaya da mamaki a cikin muryar shi zuwa kan fuskar shi duba da yanda yayi tambayar yana k'ara ma idanuwan shi girma.

"Eh tawa kuwa ko ance maka dama kaine kad'ai aka yarjema hawa manyan motoci ka dunga yawo a gari,"

Ta fadi hakan kasa kasa sosai ta yanda a zatonta bazaiji maita furta ba sai dai kuma cikin rashin sa'a tsaf yaji me tace d'in.

"Waya siya miki mota?"

"Lallai ma kenan da kai kallon talaka kake min bani da kudin siyan mota kome?"

"Ki dai bani amsa tukun, eh kuma nasan baki da kudin siyan motar tunda kika kasa iya siyan turare da kudin ki uwar mak'o dake ne zaki cire kud'i masu nauyin da zasu siya motar nan?"

"Nagode tunda gorin turaren da kake siyamin ina fesawa yau kake min, kuma tunda abun ya zama haka ka fad'amin kud'in turaren naka dana fesa ni kuma zanyi lissafin adadin kwalaben daka siyamin in biyaka kudin ka, dan in tabbatar maka da cewa nima mai arziki ce,"

Ta fad'a fuska a daure, kana kuma sai ta gyara zaman ta ta maida duka kafafuwan ta duka biyun cikin motar ta mik'a hannu ta kwaso sakon data ciro a booth d'in motar da pad d'in data ajiye duka a kujerar mai zaman banza,
Key d'in motar ta cire bayan ta kashe motar, tana kokarin fita sai dai kuma shid'in da a yanzun ya mik'e daga kishingid'ar da yayi a jikin motar a d'azun yanzun saiya zamana gaba d'aya ya babbake bakin kofar,

"Kabani hanya zan shige ciki dare yayi"

"To ya muna hira zaki shige ciki kuma ko kinyi fushine dan na tambayi wanda ya siya miki mota?"

"Eh nayi fushin ai wannan ma tambayar rainin wayau ne, wato ni gidan mu babu mai arzikin da zai iya siyamin mota ya bani kenan kake nufi, naga dai kafin wannan motar na hau wasu wancan ma in baka manta ba motatace"
Ta fad'a tana nuna d'ayar motar ta.
"Kuma kafin ita nahau wata, in kuma son sanin wanda ya siya min kake to mai sona ne ya siyamin dan wanda keson Kane kadai yake maka kyautar da har abada bazai maka gori ba"

"Ke wai ya kike wasu maganganu kamar wacce dama take jirana ne, nifa kawai tambaya nayi, laifine dan nayi tambaya akan motar da ban san da zaman ta a inda nike da iko ba? Shine zaki kalli idona kice min wani wai mai sonki ne ya siya miki motar to kenan ni kallon mak'iyi kike min, kawai daga tambaya duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login