Showing 63001 words to 66000 words out of 190771 words

Chapter 22 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1543

gaskiya bawai so na wasa ba, ki taimaka ki amshi tayin soyayya ta ki kuma bani dama ni kuma in gabatar da kaina a wajen iyayen mu su aura minke in tashi daga matakin tuzurun da kika dad'e kina kirana zuwa mijin auren ki.

Misalin k'arfe 8 da mintoci Salman ya iso kofar gidan AK domin yau bai samu damar zama a can gidan rasuwar ba gashi kuma yana ta cema Meenal d'in zai zo Allah baiyi ba kuma yasan gobe idan har suka koma Zaria to wuyan gani zata mishi,

Bai manta kwatancen da Meelat ta mishi ba dan haka koda zai taso bai kirata a waya ba har saida ya iso kofar gidan ya nemi waje yayi parking.

Kiran wayanta da yayi,
Hakan yayi dai dai da lokacin da AK yake durk'ushe a gaban ta yana koro mata kalaman da suke tsotse mata ruwan jiki,

Da kyar ta samu ta sanya hannun ta guda da yake free ya zaro wayar daga aljuhun wandon jikin ta jikinta na karkarwa.


No editing ๐Ÿฅณ


*Ummiee ce*โœ๐Ÿผ
[9/8, 2:20 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 22*


Batareda hannun ta ya dena rawa ba ta samu ta d'auki wayar ta dannata a speaker, shi kuma jin ta d'auka bayan yayi sallam dabai jira jin amsarta ba ya d'aura da cewa,

"Ranki ya dade gani a kofar gidan fa, Allah yamin isowa, hello! Hello!! Hello Meenal kina jina kuwa?"
Yayi ta maimaitawa jin tayi shiru bata amsa ba,

Hannu AK ya mik'a ya zare wayar dake cikin hannun nata ya yanke kiran kafin ya kashe wayar gaba d'aya,
Mikewa daga tsugunen da yake yayi sai ya kamo kafad'un ta da takufan hannayen shi ya k'arasa da ita gefen gadon shi ya zaunar, ita dai da ido kawai take bin shi kurrr ko kyaftawa bata son idon sunayi dan so take ta tantance shi d'in ne dai a gaban ta ko kuma wani shed'anin aljanine yayi suffa irin nashi dan taga alama yau gidan ruwan aljannu akeyi,

A k'asa inda kafafuwan ta suke ya nemi waje shima ya zauna bai yarda kuma ya saki sannayen ta ba yanzun d'in ma tafin hannun ta yana cikin nashi yana mamma tsa matasu yaci gaba da cewa,

"Karkiyi mamaki kokonto ko jin shakka akan dukan kalaman da zakiji daga gareni, I know that I am not perfect, niba kowa bane face d'an Adam wanda Allah kan iya jarabta a ko wani irin lokaci,
Ni ba d'an soyayya bane dan haka ban kasance cikin sahun mazaje masu wasa da zuciyar mata ba,
Na sani abu d'aya ke miki yawo akai shine yanda yan mata ke yawan bibiyata,
Sai dai ina so ki sani yakice su da nikeyi daga jikina hakan bawai yana nufin ina wulakanta su bane kawai saboda sun nuna suna sona,
Ah ah ita d'iya mace kaddara ce mai daraja, kasancewa ta namiji kuma bashine zai bani damar yin amfani da son da suke nuna min dan in wulakanta suba,
Domin ko da nike namiji ai ina da yayye da kuma k'anni mata kuma bazanji dad'i idan naga wani yana wulakanta min suba,
Wannan dalilin ne yasa duk mace da ta nuna min tana buk'atar kusanta kanta gareni ni kuma sai in nesanta kaina da ita,
Tarayya na tsakanin namiji da mace sun kasune kamar haka,
Kodai tarayya ta soyayya, ko kuma Abota na had'uwar jini ko kuma mummunar alaqar da addini ya haramta mana,
Idan naso zanyi amfani da damar makin da nike dashi akan su wajen bin son zuciya in shiga cikin rayuwar su in kuma yi amfani da son da suke min in cimma manufata ko wacce irice akan su batareda nasha wahala ba,
Amma kuma miye amfanin hakan wacce riba zanci idan na aikata hakan bayan a rubuce take cewa abunda kayi ma wani kaima shi za'a maka, ya zanji idan wani abu mara kyau ya faru da nawa ahalin?
Wannan dalilin shine yasa a kullum nike k'ara rik'e kaina nike kuma k'ara nesanta kaina dako wacce mace sai dai kuma ku dama sauran jama'a gurguwar fahimta kukamin a ganin ku kawai Ina amfani da damar da nike dashi ne wajen wulakanta mata,
Kun kasa hasaso cewa sufa matan ba nine nike gayyatar su zuwa duk inda nike ba, Kaini inda so samuna nane ace in rayu can wani wajen daban inda bazan dunga had'a ido da matan ba da hakan zaifi min saboda tsoron fad'awa halaka da nikeyi akoda yaushe,
Kin san meya canza ra'ayina akan mata?"

Ya tambaya a yayinda ya mik'a hannun shi ya gyara mata zaman gashinta daya zame daga cikin ribom d'in data d'aure shi ya maida mata shi ta gefen kunnenta,
Kafin ya d'anja hannun rigar shi ya fara tsane mata sauran ruwan da yake gangarowa daga cikin gashin ta yana Saukowa kan wuyanta,
Hannun ta ta mik'a ta rigo nashi saboda yanda takejin gab'obin jikin ta suna k'ara sanyayewa,
Saida ya shafa gefen fuskanta da tafin hannun shi kafin ya k'ara komawa gaban ta d'in yayi zaman d'alibi a gaban malamin shi kana ya d'aura da cewa,

"Kece macen da sonta ya fara narkamin dakakkiyar zuciyar da nike tak'amar cewa bata isa ta kamu da son kowata mace ba har sai wanda nid'in na duba naga ta cancanta,

Yes nasan na raina ajin mata saboda yanda suke bibiyata kullum kamar naman da aka kasa a mayanka,
Sai gashi kwatsam sonki yayi min shigar saurin ta yanda banyi zato ko tsammani ba,
Nayi zaton soyayya kamar karatu ne mataki mataki wanda za'a farashi daga k'aramin mataki zuwa matakin sakandire wanda in ka kaican kaike da damar zab'arma kanka hanyar da kake ganin zata bulle da kai,
Kodai ka d'auki fannin science ko kuma art,
Kin san me? "
Ya k'ara tambaya yana cigaba da binta da kallo ita d'ai ko motsin kwarai bata iyawa balle kuma ta samu kwarin gwuiwar amsa mishi,
Shima dai ganin bazata amsa d'inba sai kawai yaci gaba da cewa,

"Na dade ina hasaso kalar macen da zan nema aduk sanda na shirya fara gudanar da soyayya, ko sau daya ban tab'a hango kaina cewa wai ni ABDUL KHAREEM AHMAD MAI JAMA'A, zan k'are akan son k'aramar yarinya ba sai da zuciyata ta butulce min wajen nuna min isarta a kaina ta fad'a sonki da karfin tuwo,
Na d'auka cewa soyayyar kamar wasan kwaikwayo ne yanda kaso haka zaka tsara ka shiryata kuma ka gabatar,
Sai da na fara sonki na gane cewa ita soyyaya afkuwa kawai takeyi kai tsaye bawai mu ke k'irk'irarta ba, sai da nayi nisa a cikin soyayyar ki kafin na tabbatar da cewa zuciya tana da matsanan cin son kanta ita kawai ta samu wanda take so shi tafiso amma shi lokaci yafi adalci wanda ya cancanta shi yake bawa, kamar yanda abunda yake faruwa tsakanina dake,
Kinga a shekarun baya inda na furta miki kalmar so bana da tabbacin cewa ko zaki aminta sai dai kuma koda baki amince ba nasan zan samu goyon bayan mutane da dama wanda kuma hakan yana iya tab'a zumunci dan duka gefen biyu kowa zaiso ya gwada ikon da yake dashi ne a kanki,
Amma da yike shi lokaci yafi yima kowa adalci sai gashi lokacin yazo kuma komai ya warware batareda wani abu ya shiga tsakanin zumunci ba.
Meenal ki sani ko ina numfashi ko banayi bazan tab'acin amanar soyyaya ta dake ba.
Shin kinsan cewa duk yawan jama'ar mutanen danake mu'amalanta kad'an daga cikin sune suka samu kusanci da zuciyata?
Misali iyayena saboda ina samun kariya daga garesu, kema haka naji akanki tun daga sanda na gano kishin ki a kaina, tundaga sannan kuma ban k'ara tunanin kowacce mace ba saike,
Kawai a kullum burina shine na k'are rayuwata tareda ke a cikin shi,
Ki sani ko ki soni ko kada ki soni har abada bazan tab'a dena sonki zan k'ara mai maita miki a karo mara adadi cewa, ni AKA Mai Jama'a *INA SONKI*ยณ.
Meenal bana so na sakeyin saken da zaki kufcemin ki amince dani na miki alkawarin cewa bazakiyi dana sanin bani amanar kankiba,
Nayarda ko bakya sona wallahi zan zauna dake dan kaunar da nike miki kad'ai ta isa ta riqe auren mu,
Nidai kawai ki amince min akan kaunar da nike miki dan yardar ki kad'ai nike nema.
Ban tab'a sarewa ba dai dai dana sa'a guda tun ranar dana rasaki a kullum cikin addu'a nike idan har son da zuciyata ke miki alhairine a tsakanin mu allah ya tabbatar min dashi,
Sai gashi yanzun bayan shekararun da har na sare nafara cire raina akanki Allah ya k'arbi addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata,
Dan Allah karki sake jefa zuciyata a cikin quncin data rayu a ciki tsayin shekarun da kikayi nesa dani,
Ban sani ba ko k'ila a cikin zuciyar ki akwai wanda kikejin soyayyar shi, amma ni a wajena hakan bai isa yasamin linzami ba domin ko son wani bashi ne ba a soka shine muradin ko wani mai so, bazanyi gaggawa wajen sonjin ra'ayin ki a kaina ba,
Dole zan baki dama kije kiyi tunani akan hakan."

"Mik'ewa yayi tsaye sannan ya wuce gaba zuwa wajen k'aramin pridge din dake cikin d'akin ya ciro mata ruwan gora mara sanyi sosai kamar yasan tana buk'atar jik'a makoshin ta da takejin ya bushe mata qamas,
Sai da ya bud'e murfin goran sannan yakai hannushi guda daya ya tallafe kanta yakai mata ruwan a baki,
Sai da tasha kusan rabin goran sannan ya cire goran daga bakin ta ya maida kan nashi bakin ya shanye sauran, jefar da goran yayi anan tsakiyar d'akin ya kamo hannun ta,

"Muje kici abinci nasan mu suke jira tun d'azun"
Ya fad'a a yayinda yake cigaba da mata jagora da niyyar barin d'akin,

Abin takaici abin dariya da gudu yan gulman da suka lab'e daga bakin kofar d'akin suka bar wajen suka koma cikin falon ko wacce na neman wajen zama suka wani fuska suna kama wata hirar,

*Abinda ya faru bayan Meenak taja Ak zuwa d'akin kuwa shine*.......

Suna shigewa kusan a tare Maryam da Meelat suka fito Maryam daga kitchen ta kwaso sauran kayan abincin da bata gama kawowa kan dinning ba ita kuma Meelat sai yanzun ta gama shiri shi yasa ta fito,
Suna ganin sun shige duk sai suka dawo tsakar falon sukayi tsai-tsaye gulma na cin su sai dai kuma ganin Hajiya sai suka so su fuske,

"Ku kuma wannan tsayuwar zakarun damben da kukazo kuka min a tsakar kai na menene?"
Hajiya ta tambaya a yayinda take bin fuskokin su da kallo,

Dariya Sultana ta fashe dashi mara k'ara sosai tana nuna kofar d'akin na AK take cewa,

"Kunga abunda na fad'a muku koh? Wallahi da gaske itama tana son shi, ai naso ace kuna kusa d'azun kuga a yanda ta iya kai kanta d'aki da kyar"

"Ya akayi ne mutuniyar?"
Meelat ta tambayi sultanan tana dafa kafad'arta,

"Ke Beb dan Allah bamu musha wai ya akayi ne anci ancinye bamu da labari tun d'azun da naga kin d'au wanka naso inyi magana sai kuma dai na share"

Waje dukan su suka nema suka zauna akan 3sitter din da Hajiya ke zaune duk da kujerar ta musu kad'an basu damuba,

Tsaf Sultana ta shaida musu abunda ta fad'ama Hajiyan a gaban Meenal d'in tun kafin takai k'arshe suke dariya,

Hajiya ko da mamaki take kallon su sai can ta bud'e baki tace,

"Oh wai kuma kenan kun gane cewa shi Yayan naku son Meenal d'in yake?"

"Haba Hajiya waye ma zai zauna dasu yace bai fahimci komai dake gudana a cikin zukatan su ba!"inji Meelat,
Sultana kuma ta d'aura da cewa
" Wallahi itama son shi take Hajiya ba gashi ba dai yanzun kinga komai daya faru a gaban idon ki,

"To kenan ke da kikazo kina min kukan cewa kina son shi wannan d'in ma duk shirin kune a kansu ko ya abun yake?๐Ÿค”"
Hajiya ta tambaya cike da mamakin su ta yanda suka gudanar da komai gashi tun ba'aje ko ina ba su wad'anda aka ma gadar zaren sun fad'a,

"To wai yayan nan kenan kuna nufin wayau kuka fini shi yasa tuntuni ni na kasa zarge su waje d'aya ko yayane?"

"Ah Hajiya wane mu mu miki yawau kawai gani mukayi dukan su inba hakan aka musu ba bazasu fito fili su amayar da abunda ke cikin zukatan suba musamman ma dai shi da yakeyi kamar yana shakkarta wallahi,

Sad'af sad'af Sultana ta cire takalmin kafarta ta k'arasa bakin kofar d'akin AK d'in da turawa kawai Meenal tayi kuma bai wani rufu da kyau ba ta kafa kunne tana jiyo hirar dake gudana tsakanin AK da Meenal d'in ganin hakan ne kuma suma Maryam da Meelat suka rufa mata baya,
Basai ga Hajiya itama ta rashi tinkis tinkis tabi sahun suba,

Kaf hirar daya gudana tsakanin su a cikin kunnuwan su babu abunda basuji ba,
Hajiya ce ta fara komawa kan kujerar data dawo cike da Mamakin AK sai faman gyacci da gyad'a kai take saboda tsabar mamakin kalaman da kunnuwan ta sukajiyo mata sun fito daga bakin AK din,
Intayi tayi sai ta tafa hannu ta rik'e hab'a tana sauke ajiyar zuciya,
Har zuwa sanda motsin fitowar su yasa su Sultana baro bakin k'ofar,

Su Ak na fitowa dama bai tsaya sauraran kowa ba ya wuce da Meenal d'in can wajen dinning yaja mata kujera kafin ya zaunar da ita,
Ganin hakan ne kuma yasa suma su Maryam tasowa suka iso wajen,

Sultana ce da rawar jiki ta fara saving d'insu sai da ta fara zuba ma Hajiya ta ajiye mata a gabanta kafin ta koma gefen AK da niyyar zuba mishi suma, filet din ta fara ajiyewa a gaban shi,

"Ya'ya mai zakaci in zuba maka?"
Ta tambaya da k'aramar murya tana kallon shi,

Nashi kallon shi kuma ya maida kan Meenal dake zaune a gefen shi,
Sultana bata jira jin ta bakin shiba ganin ya basar sai kawai ta mik'a hannu da niyyar d'auko kulan da yake gefe wanda ke d'auke da tuwon semo wanda aka tuk'ashi da kyau aka mulmula shi a cikin farar leda,
Hannu itama Meenal takai ta fincike kulan mik'ewa tsaye tayi bata yarda ta kalli fuskar kowa a cikin suba har shi kanshi Ak d'in, tuwon guda biyu ta d'aura mishi a plate din data d'auko bayan ta d'auke Wanda Sultana ta ajiye ta maida gaban ta,
Sai da ta had'a mishi komai da tasan yana buk'ata ta jera mishi a gaban shi kafin ta koma itama ta zauna,

Faten dankalin turawa ta zuba a nata plate d'in itama ta faraci,
Abu biyu suka zaunar da ita akan dinning din na farko yunwar cikin ta na biyu kuma gani takeyi kamar idan ta tashi sultana zata samu damar cusa kanta a wajen AK ne,

A hankali take cin abincin su kuma su Maryam da ido suke gulmar su,
Domin dai shi gogan nunawa yayi kamar bai san da zaman kowa a wajen ba daga shi sai gimbiyar shi kawai yake gani, dan lokaci lokaci zai juya wajen ta namomin data tara mishi a plate ma kusan kwashewa yayi ya maida mata cikin nata plate din,

"Kici wannan kiji yanda yayi dad'i,"
Ya fad'a a sanda ya gutsuro leman tuwon samo din da yake ci ya dangwali miya ya had'a da namar kazar dake cikin miyan ya kai bakin ta,

"Ci mana Allah kuwa yayi dad'i sosai"
Ya k'ara furta hakan ganin tana kauda kai bata son ci daga hannun shi,
Hannun shi d'aya yasa ya matse bakinta ya cusa mata tuwon yana dariya yake cewa,
"Wallahi sai kinci shi gara in koya miki cin tuwo tun yanzun"

Tafa hannuwa Hajiya ta fara tana salati da sallallami,

"Kai Abdul Kahareemu!
Oh ni Aminatu yau nikam nike ganin abunda yafi zare tsayi ganin idona,
Nace wai ana cin tuwo dole ne yarinya tace kasan bason tuwo take ba amma harda wani matse mata baki ka d'ura mata uwa dai wanda akayi ma dole,
Nace ana dole ne nikam,
Ke wai tsaya ma, ina ce nan da kikaja shi zuwa cikin d'aki cewa kikayi zaki amso takardun mota, yanzun da kuka fito hannu na dukan cinya takardun suna ina? Ko koh ah ah dama tsabar gulma ne ya kaiku d'akin bayan kun gama gulmar ne kuka fito?"

Daga shi har Meenal d'in babu wanda yayi gigin tankame Hajiya ke cewa, ita dai Allah take ta gama cin nata abincin ma ta bar musu falon,
Dan haka ita ta fara gamawa ta mik'e shima kamar jiran tashinta yake sai ya rufa mata baya yana tambayan ta
"Bacci zakiyi?"
"Eh ta amsa dashi batareda ta tsaya ba,

"Ok ga wayar ki,"ya zaro wayar daga aljihun shi yasa mata a cikin tafin hannun ta,

"Karki kunna tafa sai da safe"

Wucewa tayi zuwa d'aki shima ya shige bayan ya juyo yama hajiya sai da safe,

Mamaki kusan sumar da Hajiya yayi daga zaunen da take tana kallon ikon Allah,

"Jama'a wai dama haka maza ke komawa duk su makance idan suka fad'a soyayya?"
Ta ke tambayar su Meelat da tashin su AK d'in ya basu damar fitar da nasu maganganun suma,

"Ai hajiya yanzun dai sai dai mu baki irin shawarar da akeba sabuwar amarya,
Kiji kik'i ji,
Ki gani kiki gani, atoh"
Cewar Sultana tana dariya.
Sabon hirar gulman su Meenal din suka bud'e suna k'ara tabbatar ma da Hajiya irin alaqar soyayyar dake tsakanin jikokin nata wanda a kalaman sune itama ta dunga tuna wasu abubuwan da suka shud'e wanda tun wancan lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login