Showing 153001 words to 156000 words out of 190771 words

Chapter 52 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1542

aure taci gaba da zama gaban iyayen ta da gaban shi zan koma in k'arasa rayuwata a tareda shi kamar yanda na faro ta,
Matsayin shi a wajena yafi k'arfin in tsaya a gaban wani namijin harya bud'e baki ya nemi ai banta shi ban dun kule hannu na naushi bakin ko waye ba koda ko ace shi d'in mai maganar yafi ni tsayi zanyi tsalle ko in nemo abinda zan cimma tsayin bakin shi in nausa kafin mu cigaba da bala'i,
balle kuma kai,
Ka sani da kazo kace kana sona harna amince bawai dan Ina tsoron ka bane ko kuma wani dalilin na da ban,
Ah ah na amshi sonka ne a zatona matsayin ka na d'an uwana zakaci gaba da tayani yin biyayya ga ubana ciki harda girmama sauran *DANGINA* shine tun ba'aje ko Ina ba kake ganin kamar har kana da zarrar da zaka tsaya a gabana ka nemi ai bata uban da bani da kamar shi,
a haka kake so incigaba da sonka har in aure ka bayan nasan bai zama dole ka girmama ubana wanda shine gatana ba,"

"Please Meenal karkice zaki min gurguwar fahimta, ki sani cewa wallahi ko waye ya fad'a miki cewa zai soki fiye da son da nike miki karya yake miki babu wanda zai had'a son shi da kaunar dani nike miki,
Ina sonki meenal shi yasa bazan so inga an k'ara rabani dake a wannan lokacin ba"

"Oh soyayyar ce tasa ka fara tunanin tsame ni a cikin *DANGINA* zuwa wata duniyar ta daban?
Kasan abinda yasa naji zan soka harma in rayu tareda kai a wancan lokacin?
Saboda tsubin nutsuwar da Allah ya maka na kuma yaba da kyawun halayyan ka,
Amma a yanzun daka fara fitomin da ainihin ka hakan yasa na gano rashin dacewar mu,
Abdul bazan aureka ba zan koma gida wajen Yayan babana wannan karon ma zan bashi dama ya k'ara zab'ar min miji a karo na biyu"

Tana gama fad'a mishi hakan ita kuma ta juya mishi baya ta fashe da kuka,
Allah ma ya sani kalaman AK sun bata haushi sun kuma kona mata rai,
Domin ko bai fito fili ya furta ba a cikin zancen shi ta shinshino rashin son da yake ma wanda ta d'auka a matsayin gatan ta, taya zata yarda so ya rufe mata ido harta tsaya a gaban shi yana neman zagin uban ta bata d'auki mata ki ba indai har itace so zaici amana irin haka to taci uwar son tasha ruwan kanwa maganin kwarnafin ciki,

Sanyi jikin shi yayi sosai shi kuma,
Shifa duk abinda ya fad'a bada mugun nufi ya furta suba yadai fad'ane kawai saboda ranshi da yake b'ace,
Ya ita kuma take neman juya zancen haka daga d'an magana kuma shine zatace wai ta dena son shi ta fasa auren shi,
Da sanyin jiki ya koma inda ta juya,
"Meenal "
ya kira sunan ta a sanyaye ita kuma sai ta k'ara juya mishi baya tana cigaba dayin kuka,

"Meenal Ina son ki karkice zaki juyamin baya a daidai lokacin da nike sa ran na kusa mallakar ki"

"Ni kuma nace bana sonka kuma ban auren ka tunda ka raina min uban da bani da kamar shi" ta karasa fad'a tana kara sautin kukan ta,

Wallahi jiri yaji yana neman maka shi da kansa,

"Ki rufa min asiri meenal bazan iya rasaki a wannan lokacin ba Ina sonki,
Kuma ni bada wata manufa nayi magana ba tsoro dai nikeji kar a maimaita abinda ya faru a baya kiyi hakuri ki fahimta"
Kara juyawa tayi ganin ya k'ara binta inda ta juya,
Haka sukaci gaba dayi duk inda ta juya shi kuma zai bita yana faman son ya fahimtar da ita cewa shifa bawai ya raina baban ta bane, kawai dai tsoro yakeji,

"Bana son..... " bai bari takai k'arsher kalmar ba da karfin tsiya ya jawota zuwa cikin k'irjin shi ya rungume a cikin jikin shi tsamtsam ya ta bude baki zataciga da masifa karaf ya had'e bakin ta da nashi ya fara aika mata da wasu irin mahaukatan zafafan kissing masu juya kwakwalen mata irinta wadanda basu saba keb'ewa da namiji ba,
Duka da yakushi ta dunga kai mishi a k'okarin ta na ganin ta kwace amma ko gezau baiyi ba,
Baya tayi da jikinta da karfi shi kuma ya biyota suka fad'a kan gadon dake kusa dasu yako k'ara danneta gaba d'aya batareda ya sarara daga aikin daya sa kanshi ba,

Astagfirullah astagfirullah
Astagfirullah yau dai duk yanda AK yake kai zuciyar shi nesa sai da bakin Yarinyar nan tasa hege shed'an ya kusa cin galaba akan shi domin dai rufe ido yayi ya tumurmushe ta saida ya murtsuke bakin rashin kunyar nan tsaf, itama dai tun tana ciccijewa tana tureshi har dan dole ta hakura ta nemi biye mishi dan jiki da jini atoh kuma itama dai a shekarun ta ai takai matakin da idan namiji yace mata kule zata maida mishi Cass ai wacce za'ayi wallahi, ๐Ÿ˜’
To dai ansha baki an kuma tsotsi kunne an lashe wuya kafin dai ayi batun kaima yan biyu da sauran sassan jiki hari Allah ya kwato mana gogan a hannun shed'an kila dai ya tuna cewa har yanzun ba'a d'aura auren bane dan haka a sanda jikinta ya amsa ta fara neman kai naushi itama shi kuma sai ya murgina gefe ya sauka a jikin ta yana faman maida numfashin dake neman d'auke mishi tun d'azun hakan ne kuma yabata damar jin kunyar kanta dan haka sai kawai ta dunkule itama taja bargo ta kudun dune a ciki dan bata da bakin magana,
To me zatace jama'a bayan saura kad'an ta mance kanta,
sai da yaji numfashin shi ya koma mishi dai dai kafin ya yunkura ya sauka a gadon,

"Tashi ki fita min a cikin d'aki tunda kin samu abida kike so, ban hanaki ba kuma in kinga dama anjima idan muka k'ara had'uwa shima ki k'ara fad'amin cewa bakya sona ni kuma bazan gaji da kawo ki nan inci gaba da ladafta bakin rashin kunya ba badai ni kika ce bakya soba?"

Yaye bargon tayi ta mik'e zaune,

"Ka daiji kunya wallahi mugu mai shan bakin mata kawai kuma nidai ban yafe tab'amin jiki da shan bakina da kayi ba"

"Ai saboda a iya bakin na tsaya shi yasa kika samu damar magana, duk ranar da hauka yasa kika kara cewa zaki rabu dani ko kuma bakya sona gonar ki zan shiga inyi b'arna wallahi an dad'e ba'a kaini kotun musulunci ba k'aramar yarinya kawai har nine ma zaki kalli idona kice bakya so dan kawai na fad'a miki gaskiya"

Kuka ta fashe dashi,
"eh din ba'a sonka kuma bana yin auren na fasa ko ko a k'afa aka daura min kai saina kwance na gudu inda bazaka k'ara ganina ba mai farin jinin mata kawai"

"Oh kice min dama kullum ashe target dina kikeyi shi yasa da nace idan kika k'ara cewa baki sona zanyi noma yanzun kika furta,
To bismillah inkin shirya nima na shirya k'aryar rashin kunya kikeyi"

Juyowa yayi ya nufo inda take, da wani irin zafin nama ita kuma tayi kifiya ta sauka a gadon kafin ya ankara harta bud'e kofa ta fice da shegen gudu ko d'an kwalin ta bata tsaya d'auka ba,

"Ke dawo ki d'auki d'an kwalin ki karkisa a fara yimin kallon d'an iska dan duk wanda ya ganki a haka ko nace ban tab'a kiba bazasu yarda ba mara kunyar karya dake kawai"
Ina itafa tuni ta haye sama abinta shi yasa ko jiyo shi batayi ba,

Su kuma su Sultana tun d'azun suka wuce sashen su Moon wajen Umma dan ita da kanta ta leko tayi kiran su Bayan da Hajiya ta bada sallahun a d'aura abinci kafin su dawo gidan acan ne kuma sukaji labarin d'aurin auren AK da Meenal din da akayi, dan haka Sultana ta sato jiki ta dawo falon dan ta fesa ma AK labari sai dai kuma tana shigowa ta hango Meenal ta haye sama da gudu bata gama tunanin dalilin gudun da Meenal keyi ba sai kuma ta hango AK kuma duk maganganun da yayi taji su rass dan haka sai zuciyar ta ya bata ko shima ya samu labarin d'aurin auren ne, shi yasa ya fara celebrating
D'aga murya tayi ta kira sunan shi
"Ya AK"
Bai amsa ba sai dai ya juyo yana kallon ta har ta isa gareshi,

"Congrats angon Meenal Ubangiji Allah yasa ace gara da akayi, muma yan baya Allah ya aurar damu" ta fad'a da fara'a sosai a murya da fuskar ta,
"Wai Yaya dama ashe ana d'aura aure ko ango baije wajen ba? Ni wallahi ban tab'a jin daga zuwa tambaya ace an d'aura aure ba sai yau, dan Allah kaje kayi wanka kasa manya kaya kaima kafin su Hajiya su dawo inba haka ba ai baza'a wani gane cewa kaine angon ba"

"Me kike cewa ne Sultana auren wa aka d'aura ne?"

"Lah wai basu kiraka sunce maka an d'aura ba? Tsaya ka gani"

Shifa shirme ya d'auki zancen ta ko kuma dai kila tana mishi wasa ne, dan haka sai kawai ya tsaya yana kallon ta harta d'aga wayarta ta d'anna kira, Number din ya Sheikh ta kira yana d'auka ko bayan tayi sallama ya amsa ta jefa mishi tambaya kamar haka,
"Ya Sheikh da gaskene wai an an d'aura auren ka da Fauxieyerh ita kuma Meenal da Mai Jama'a?"

"Ke kina Ina ne da kike kirana a yanzun? Bakya gida kenan"

"Nidai dan Allah ka amsa min tabbaci nike son samu kuma nasan kai baka k'arya"

"Eh Sultana Allah yayi a yau nasamu k'aruwar aure nima na zama ma gidanci"
Kit ta yanke wayar,

"Kaji koh Wallahi da gaske an d'aura dan ya Sheikh baya k'arya"

Kofar d'akin AK ya bud'e ya fito a tsakiyar falon ya yi sujudur shakur bayan ya d'ago sai da ya d'aga hannuwa sama yayi addu'o'i harda hawaye yana shafawa kuma baibi takan Sultana ba ya fice da gudu
Sashen Abba Ahmad ya shiga,
Akwai mata a falon amma bai damu daya tsaya gaishe su ba ya wuce da sauri yana kwala kiran Ummi,

"Kai lafiyar ka zaka fad'omin cikin gida kana wani kwala kiran sunana uwa dai sabon makaho"

Maman su Bilkisu daya wuce su a falon ne tace "bashshi Amina ke koh ango nefa"

"Da gaske ne an d'aura aurena da mai sunan ki ummi?"

"Da gaske ne mana ba abinda kake buri kenan ba dama?"

Rungume ta yayi yana dariya,
Dan haka sai itama ta rungume shi tana cewa "na tayaka murna Ina fatan kuma zaka riketa amana, Allah ya baku zaman lafiya da zuria masu albarka"

"Ameen Matan falon suka amsa shi kuma sai ya saketa daga rungumar daya mata ya juya ya fice daga sashen gaba d'aya tsabar farin cikin da yake cikine yasa bai tuna da wayar shiba tun d'azun sai yanzun, aljihunan shi ya fara lalube sai dai kuma baiji wayar ba, kenan dai a kaduna ya barta, komawa cikin sashen Ummi ya karayi da gud'a, Wayarta ya amso ya k'ara fitowa number din musty ya fara kira,
"Kana ina? "Ya tambaya bayan musty ya d'auka,

"Kai kana Ina yanzun haka?" Shima musty ya tambaya,

"Ina gidan Hajiya kazo yanzun please"

"Fito kofar gida ka jirani"

Yanke wayar yayi shi kuma AK mai makon ya fita wajen sai ya koma sashen Hajiya gaskiya fa Sultana ta fad'a mishi gara yaje yayi sabon wanka yasa manyan kaya shima ya fito a matsayin ango sak,

Kafin ya shiga d'akin shi har ya fara tunanin haurawa sama yaje yama Yarinyar nan albishir amma sai ya fasa,
Zaiyi lokacin tane anjima badai shi tayi ma rashin kunya ba hummm,

Bayan ya fito daga wanka cikin sabbin manyan kayan daya d'in ka da bikin Musty ya zab'o wata lafiyayyar farar shadda mai had'e da malum malum wacce akayi ma aiki blue din zare ya sanya, tsaf ya shirya ya fito a angon kafin ya fito daga d'akin hula a hannu sai zabgaga kamshin turaren dayayi ma jikin shi wanka yakeyi,

Kawayen Hajiya data kira ta shaida ma batun auren ya tarar a zaune a falon cikin su kuma harda Dadah turai,
Su kuma kamar masu jiran fitowar shi haka suka lullubeshi suna gud'a,

Gidan hajiya fa ya cika da makota mata suna cikin gida suna aikin abinci suna kuma jiran dawowar yan d'aurin aure,


Tunda su Musty suka dawo tudun wada suke wasa da motoci a majalisar su dan haka wajen ya cika dam da mata sa harda wad'anda basu samu zuwa can wajen d'aurin auren ba shagali kawai sukeyi abin su, dan haka sai shi kuma ya janye jikin shi yayi cikin gida,
Sasan AK din ya fara zuwa ganin kofar ya kulle yasan baya wajen dan haka sai ya wuce sashen Hajiya kai tsaye, a falon nata ya sameshi mata sun dabaibaye shi suna mishi gud'a yana Karasawa shi kuma ya ciro kud'i daga cikin aljihun shi ya farayima Ak manni dasu dariya.


*Ummiee ce*
[10/10, 8:51 AM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA *๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 46*

*My Aleesah where are you? Ki sani tundaga kan wannan page din har zuw karshen labarin na sadaukar dashi a gareki domin kin cancanta na yaba kwarai da kokorin ki*๐Ÿ˜....


Da kyal suka samu suka fice daga cikin falon suna dariyar Dadah wacce ta d'age akan cewa sam bata yarda da shigo shigo ba zurfin da aka mata kishiya da yamma sakaliya ba,
Haka kawai tana zaune daga zuwa tambaya sai taji tashin zancen wai an rangad'a mata kishiya ba notice,
Su kuma k'awayen Hajiya suna taya ta da cewa tabbas suma suna tayata kishi,


A harabar gidan sukaci burki bayan fitowar s daga falon suka nufi inda su Baba Usman suke, domin su Musty sun rigasu barin can gidan Malam shi yasa su sai yanzun suke isowa tareda uwar garken wato Hajiya.

"Kai ku matsa ku bani hanya in isaga mijin Aminatu Abdul Khareem d'ina haba jama'a haka akeyi duk kunbi dai kun yanyame min jika kamar wani naman kasuwa bazaku barshi ya iso gareni mu taya juna murna bayan kowa yasan cewa nice kashin bayan arzikin daya samu na auren jikata,
Nice nan fa k'ashin bayan nasarar shi wai a hakan ma dan auren yazo ne babu zato amma ji yanda aka cika min gidan dama unguwar kamar dai wad'anda akayo ma shela,
Zonan kaji mai Babban suna zo wajena kaji yau dai Alhamdulillah alkawarin Allah ya cika masu murna suyi akasin haka kuma mutum sai ya rufe kanshi a daki inyaso karya fito sai ranar kiyama"

Janye jikin shi yayi daga cikin abokan shi da suka baibaye shi suna mishi mishi murna da fatan alkhairi ya k'arasa wajen Hajiya da iyayen shi yana isa baiyi wata wataba yabata kyakyawan runguma,

"Hajiyata da gaske kun amso min auren ta? " ya tambaya cike da mad'aukakin fara'a a fuska da muryar shi,

Itama da fara'a sosai ta amsa da cewa..
"Da gaske ne mana Abdul ana wasa da igiyoyin aure ne dama?
Kai dai yau Allah ya nufa cewa rana bazata fito harta fad'i batareda igiyar auren ka ya hau kan mai suna naba,
Ka daiga ikon Allah koh!
Inda ace ayau din nan wani zai tareni yace min ke Amina ki shirya yau za'a daura auren jikokin ki tofa ina fad'a maka da sai na kalli kwayar idon mutum kafin in kirashi da suna mugun makaryaci,
Eh mana kaikoh tunda mudai nan mun saba komai sai an bishi daki daki kafin a kaiga batun daurin aure, kaga dai ayi tambaya na angani Ana so,
Idan an amince aba saurayi dama ayi zancen baiko dasa rana amma mu babu d'aya da muka gabatar tun bayan dai da iyayen ka suka ma wancan d'ayan uban nata batun shi kuma da yafi kowa iya shiririta yaje yayi ta sha'anin gaban shi bai tada zancen ba,
ai dole kowa yayi mamaki dajin batun auren nan tunda dukan mufa saida muka sallaci sallan azahar kafin mu fita zuwa can gidan,
To da Allah dai ya kaddara cewa yaune ranar kamar yanda yan magana ke cewa mutuwa,
Aure da haihuwa dukan su lokaci garesu to kaima dai yau naka ranar yazo amma kaga kai da yike Allah yana sonka shi yasama ya baka ni a matsayin kakarka gashi munje da batun sa rana amma mai makon hakan mun amso maka auren gaba d'aya"

Kara rungume ta yayi tsam tsam hawayen farin ciki na cika mishi idanu dan kamar yanda Hajiya tace ne koshi yau kam ya jinjina ma girmar kudurar ubangiji lallai Allah ne kad'ai keyi inyaso kuma babu mai hanawa tunda gashi yau allah ya mallaka mishi Meenal a dai dai sanda take cikin tutsu, dazun nan fa ta gama mishi rikicin cewa bata auren shi ashe daga shi har ita basu san cewa aure ya tabbata akan su a daidai lokacin ba, to kodai shaukin auren nema ya kwashe shi yau yakusa sab'a lamba?, murmushi mai fad'i yayi hawaye na zirarowa daga cikin idon shi,

"Nagode Hajiya,
Nagode kwarai ubangiji Allah ya bada lada,
Allah ya kara miki lafiya ya kuma raya manake kiyi jinkiri mai amfani da albarka ameen nagode kwarai kuma nayi miki alkawari insha Allah zan rike mai sunan ki da amana bazan taba yin abunda zaisa tayi kuka dani ba zan cigaba da sonta har zuwa sanda zanja numfashina na karshe a doron k'asa "

*Ameen!
Ameen
Ameen Abdul Khareem ubangiji Allah yasa albarka a cikin auren ku Allah ya zaunar daku lafiya Allah kuma ya baku ikon sauke hakkin juna hakika nafi kowa murna da faruwar wannan al'amari, Allah ya baka ikon rike Amina kamar yanda mai sunan ka ya rikeni har zuwa sanda mutuwa ce ta rabamu"

Ta k'arasa fad'a da muryar kuka idanuwan ta na zubda hawayen itama kamar dai shi,

Ameen jama'ar dake wajen suka amsa,
Bayan ya raba jikin shi dana Hajiya wajen su Baba Usman ya koma suma kuma saida ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login