Showing 69001 words to 72000 words out of 190771 words
sallama a d'akin shi ta tura kofar ta shiga batare da ta jira mai dakin ya amsa ba,
juyowa yayi daga tsayen da yake a gaban wardrobe din Shi yana binta da kallo, bata ci burki a ko inaba sai da ta k'araso inda yake tsaye yana binta da kallon,
Manyan kayan daya tsiri sawa ne yauma a jikin shi, da alama dai shima shirin fitowa yakeyi dan wasu takardu ne a hannun shi yana dubawa,
Babu gaisuwa ba komai ta fara kora mishi abunda ke cikin zuciyar ta,
"Ya'ya ka fito ka fad'ama Hajiyan can su shirya subar maka gidan ka dan Allah"
"Saboda me?" Ya tambaya a yayinda
ya d'aura hannun shi d'aya daga kan goshin shi ya cusa yatsun nashi cikin gashin kanshi yayi baya dasu,
Saida yakai hannun zuwa k'eyar shi kafin ya k'arayo gaba dashi ya wani yamutsa gashin kan nashi,
"Oh Allah yayi dare gari ya waye,
Yanzun kuma mai aka miki daga waye war gari fisabilillahi waye ya tab'amin Soul mate d'ina?"
"To ba tunda na tashi da asuba nace ma Hajiya mu wuce gidan rasuwar can da wuri ba tunda yaune za'ayi addu'ar uku saboda mu kama musu aiki ita kuma sai tace wai bazamu tafi ba sai karfe 8,
To yanzun kuma na fito mu tafi shine naga duk kan su ma babu wacce take da niyyar tafiya sai yanzun nema zasu karya fa"
Ta k'arasa fada kamar zata fashe mishi da kuka,
Oh ya rabbi, shi dai wallahi aiki ya ganshi,
Wai dama haka yarinyar nan keda tab'ara kamar jinjirar goye ko kuma dai yanzun ne ta k'irkireta saboda ta k'arasa susuta shi?,
"Ina kwana!
Kin tashi lafiya!
ina fatan kin samuyin bacci cike da nutsuwa a daren jiya?"
Shiru tayi tana duk'ar da kai itafa batun gaisuwa ma gaba d'aya bai shigo mata cikin kaiba, bata san ma ya akayi idon ta ya rufe ta fad'o cikin d'akin ba alhalin tun d'azun saboda shi ta kunshe kanta a cikin d'akin tak'i fitowa,
Ita dai gidan ne kawai takejin ya isheta so take ta fita waje ta shak'i iskar da babu numfashin Sultana da shi Taubashin a waje d'aya,
A k'aqe take da son ganin sun bar gidan dan a yanda ta lura da cewa notikan kan Sultanan sun fice tofa tabbas tana iya tunkarar shi kai tsaye d'in ta fada mishi tana son shi, to kafin hakan ta fara gara ta d'auki matakin gaggawa,
Ku sani itafa a nata ganin bawai tana hakan saboda kishin shi AK din bane, ah ah ita tana hakan ne saboda bata son ita Sultanan tayi abunda zata zubarma da kanta aji a gaban Namiji kuma koda ba AK sultanan keso ba ita a ganin ta kalar matakin da zata d'auke kenan na ganin ta hana Sultanar aikata abunda zata zo daga baya tana dana sani.
Matsowa yayi kusa da ita ya tsaya shima, kafin yayi amfani da yatsar shi manuniya ya d'ago habarta yana ci gaba dabin fuskarta da kallo yace,
"Bud'e idonki ki kalleni!"
A hankali ta dunga bude idon nata data runtse har ta ware su gaba d'aya a saman fuskar shi,
"Oya take a deep breath"
Numfashin ta shak'a mai had'e da sassanyar kamshin turaren shi kamar yanda ya umarceta,
"Ok breath out a hankali"
A hankali ta sauke numfashin,
Sai da yasata yi hakan sau uku kafin yace mata,
"ya kikeji yanzun?" Ya tambaya da harshen turanci,
"Ina kwana "
Ta fad'a mai makon ta amsa tambayar shi,
"Lafiya lau ya kika tashi?"
"Alhamdulillah"
"Waye ya b'ata miki rai kuma me yasa kike son ku tafi da wuri?"
"Ba komai"
"To muje ki karya kema kafin ku wuce d'in tunda tsoron zama anan d'in kikeji, zan gani zuwa gaba idan aka kawomin ke a matsayin mota ko ya zakiyi "
Gaba yayi ta bishi a baya har suka fice daga d'akin,
Sun iske su Hajiya nata k'aryawa hankali kwance kafin suma suka samu waje suka zauna,
Su Maryam ne suka dunga mik'a mishi gaisuwa domin shi da Hajiya sun gaisa d'azun daya shigo gidan, kunun gyad'ar Hajiya ta gabatar mishi ya kuma sha kamar yanda Hajiya ta fad'a.
"Hajiya nace ya kamata idan kun kammala muje kiga wancan gidan koh? Tunda yanzun dai idan kun koma ban san kuma sai yaushe zaki k'ara shigowa nan d'in ba,"
"Eh to kuma fa kaima kana da gaskiya tunda ya zama haka ai sai mu wuce yanzun daga can sai mu zarce gidan rasuwar basai mun dawo ta nan ba dan dama ita wannan a k'age take da mu wuce, amma dai kafin mu wuce ina buk'atar magana da kai"
Meenal data rage ita d'aya sai shi da Hajiya akan dinning din dan su Maryam sun tashi ta yunk'ura da niyyar basu waje ya riko hannun ta,
"Nima ina son magana dake Hajiya amma kafin nan ki yi hak'uri dai har ku koma gida idan na shigo sai muyi maganar a tsanake dan ina da abubuwan da zanyi masu mahimmanci yau d'in shine ma zai hana ni binku mu koma tare,
Amma insha Allah zanyi kokarin shigowa cikin satin nan sai muyi maganar "
Kauda kai hajiya tayi kamar bataga hannun Meenal daya rik'e cikin nashi ba tace,
"Madallah ni ai dama kasan tatsuniyar gizo bata wuce kok'i, komai zan fad'a kaima kasan bazai wuce akan batun auren da nike so inga kayi ba,
da fari dai zanso insan halin da kake ciki tsakanin ka da yarinyar da kacemin kana so kwanaki"
Sai da yad'an waiga ya kalli Meenal ta gefen ido kafin ya amsa ma Hajiya da cewa,
"Karki damu kanki da wannan maganar Hajiya dan na riga na gabatar da kaina a wajen yarinyar,
Addu'an da zaki tayani dashi yanzun kawai shine, Allah yasa taji tausayina ta amsa min da wuri kafin ciwon sonta ya ya k'arasa firgita miki ni.
*Ummiee ce*โ๐ผ
[9/10, 10:46 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*
*Page 24*
Yo Allah na tuba kai yanzun nan harma dan wata mace tace bata sonka har zaka wani d'aga hankali ka damu kanka bayan ba masoyan ka rasaba?... "
"Hajiya bafa cewa tayi bata sona ba, kin san bai yuwuwa daga fad'a mata cewa ina sonta ta amsa min dai take a lokacin"
"Koma dai yayane kawai ka fita sabgarta taje can ta k'arata da yawarta ita tayi ma kanta dan nidai banga abunda ka rasa daga cikin abunda ake buk'atar samun mijin aure dashi ba tunda ko kaga bata amsa maka ba son kane batayi gara ma haka wallahi dan
Kaga ni dama gata naso in maka kana gani dai gashi nan abokan ka sai harama suke shi dama Yusufu tuni yayi muku fintinkau dan haka indai zakaji ta nawa gara kabar batun yarinyar nan kawai kazo ga wata matar Allah ya kawo na fidda maka ita ka aura,
Gata kuma yar gida sannan na yaba da nutsuwa da hankalin ta kaga idan ka auri wannan d'in ita waccen yarinyar da kace kana so d'in ko zuwa gabane in Allah yasa ta amince sai kayi ta biyu da ita ko ya kagani?,
Dan nidai dama bana maka sha'awar zama da mace d'aya wallahi,"
Yunk'urawa Meenal tayi da niyyar tashi tabar musu wajen, shi kuma yaja hannun ta dake rik'e cikin nashi ya maidata zaune ya kuma maida hannun nasu dake had'e kan cinyarta ya danne saboda ya hanata mik'ewar ,
"Ke kuma ina kike shirin zuwa? Ai gara ki zauna dan dama ina gamawa dashi kanki zan dawo atoh bawai na manta dake bane,
Nace har yanzun duk wannan uwar wankan da fesa turaren da kikeyi a kullum kafin ki fita kar dai kice min asarar ruwan wanka da sabulu kikeyi kullum?,
To ga dai lokaci yana ta tafiya amma har yanzun ban fara ganin manyan motoci suna jera min layi a kofar gidaba,
Anya kuwa Yar wajen Jidda ba amanata kike ciba kuwa wajen k'in kula samarin da suke nuna ra'ayin su a kanki?
Naga dai ko shekarun baya a lokacin da kike kwailar ki ma maza sun nuna maitar su a kanki yanzun kuma da kika koma tubarkhallah maka Allah sai inji shiru, to wai in baki basu damar zuwa gidanba ta ina zan iya tantance su wajen gano miki wanda ya cancanci auren ki a cikin su?"
AK ya katse Hajiyar da cewa..
"Hajiya, amma dai na roki arzikin ki akan abar maganar nan koh?
ba komai amma tunda kin matsa bari in fito miki a mutum!,
Ita dai yarinyar da kike magana a kanta koma wacece bana buk'atar ta a cikin rayuwata, akwai maza da yawa a waje wad'anda suka fini quality da komai ma da kike ganin ina dashi, ni kuma ina mata fatan Allah ya had'ata da d'aya daga cikin su wanda zai sota har zuwa k'arshen numfashin su,
Batun wai in fara auren ta ko wani zancen mata biyu da kike kawowa ina so ki soke shi in ma a mafarki kika gani ina tabbatar miki da cewa bazai tab'a tabbata ba domin bana da ra'ayin su,
Naga dai kema naki mijin dake kad'ai ya rayu har zuwa karshen rayuwar shi, suma kuma yaran daya haifa har yanzun kaf cikin su banga wanda yayi mace sama da d'aya ba, oh sai nine kike ganin nafi kowa a cikin jikokin ki da kike kiran min auren mata biyu, Hajiya so kike ranar kiyama in tashi da shanyayyen gefen jiki ko ya?
Kedai kin san cewa bazan tab'a iya adalci a tsakanin abunda na gani ina so da kuma wanda nayi alfarmar amsa saboda an cusa min ita ba,
Aure dai ina kike so kiga nayi?
To in hakan ne gata d'aya nike so kimin wajen tayani yak'in kwato abunda nike so d'in har zuwa sanda zai zama mallakina,
Yar gida wanda kika san halinta kuma kika yaba da tarbiyar ta kike min sha'awar aura koh?
To gata ayau a yanzun zan gabatar miki da ita batare da b'ata lokaci ba nidai na riga na gabatar da kaina a wajen ta, Ina son ta ina kuma fatan in mallaketa ta zame min matar rufin asiri,
Gata nan zaune a gaban ki dan haka sai ki yanke hukuncin daya dace domin da ita dani dukan mu tarbiyar kine babu wanda baki san halin shiba a cikin mu,"
Mikewa yayi tsaye sannan ya d'ago meenal d'in tsaye itama,
wacce zaune kawai take amma ji takeyi da da ace tana da wani layan zanan da zata latsa tayi b'atan dabo a wajen da tayi saboda tsaka mai wuyar da take ganin su biyun sun jefata a ciki, wannan ai ita akama turke wallahi.
"Meenal meet my grandma Hajiya ta itace gatana tun ban san kaina ba, duk wani matakin nasarar da nataka a rayuwata zuwa yanzun da gudun mawarta na same shi,
Ina fatan zaki kula min da ita fiye da yanda nike kula da duk abunda ya shafeta bayan auren mu?"
Hijjabin dake sanye a jikin Meenal d'in taja da duk'unkune kanta gaba d'aya a cikin shi saboda tsabar kunyar daya lullub'eta,
"Hajiya ga Ameenatu takwarar ki, zanyi amfani da wannan damar dana samu wajen gabatar miki da ita a matsayin macen da zuciyata ta zab'amin wacce nike fatan in k'arasa sauran rayuwata a tare da ita k'ark'ashin inuwar aure, Ina fatan zaki tayani yak'in neman amincewar ta akan maganar auren mu,
Domin kamar yanda na shaida miki ne, na riga na gabatar da takardar barar soyayyata a gareta amsar ta kawai nike da buk'atar ji a yanzun wanda shine zai bani kwarin gwuiwar takawa zuwa mataki na gaba wato gabatar da kaina a wajen iyayen ta a matsayin mane min auren ta,
Hajiya Ina sonta, so irin wanda ban tab'a zaton zanyi ma wata y'a mace shi ba,"
"Sadaqallahul Azeem! Allahu akbar ! Allahu akbar!
Allahu akbar,,,
Ashe ni Aminatu zanga wannan ranar a raye tun k'asa bai rufemin idon ganiba,
Oh oh Allah Sarki duniya... "
Batakai k'arshen surutan da takeyi ba ta fara sheshek'a tana shirin fashe mishi da kuka,
Daga can cikin falon ko su Meelat da tun d'azun suka kashe kunne suna sauraron tattaunawar nasu, Sultana ce ta matso kusa saida ta k'arasa inda Hajiya take kafin ta tak'ark'are ta rangad'a gud'a uwa wacce ke taryar Amarya,
"Ayyiriri yirie yiriii yirrrriiieee dukan su suka had'u suna yarawa,
Hajiya dake sheshekar kuka basai gata itama ta biye musu suna rangad'a gud'ar atare dasu ba,
Da baya ya koma ya shige d'akin shi ya barsu a falon dan shifa tsakani da Allah ya manta cewa ba iya su bane kawai a gidan akwai wasu ukun a gefe tare dasu,
Sai dai ko kad'an baiji kunya ba shi a zuciyar shi ma dad'i yaji dan yasan suma zasu sa baki tunda a gaban su akai komai,
Suko yana shigewa suka zagaye Meenal d'in data d'uke kanta dake duk'un kune cikin hijjabi akan table din dinning d'in tak'i d'agowa balle su samu damar ganin yanayin fuskarta,
Basu damu da yanda tayin ba suka cigaba da tsokanarta da cewa,
"Allah yabar mana jikar Hajjaju sirikar Hajjaju, zaman ki lafiya tashin ki lafiya yar gaban goshin Malam...
Hajiya ce ta matso tana katsesu da cewa
"ku matsa ku bama sirikata waje karku samin ita a gaba da tsokana, yoni ina nasan cewa kanshi yake ma kiwo ashe!
Niko nike ta k'okarin yi mishi shishshigi, to ke Sultana kin daiji komai dan haka sai kija please ki rungumi sorry kiyi fatan Allah ya baki wanda ya fishi d'in kamar yanda shima ya rok'a miki, dan tunda ya iya kallon tsabar idona yace min ita yake so tofa bazai tab'a amsar naki soyayyar ba,
To amma Takwara haka ake rayuwa ayi ta abubuwa bani da labari ko dai da gaske bakyason shi d'in ne shi yasa kika kasa amsawa?
To bari kiji in baki shawara na gaskiya da gaske, dan ma karkice shid'in jikana ne shi yasa nike son taya shi yak'i ah ah wallahi ko d'aya dan kin sani duk wanda naga yana shirin yi miki dole akan auren wanda bakyaso sai inda k'arfina ya k'are,
Amma shi dai tsakani da Allah zan fad'a miki idan har kikayi saken daya kucce miki tofa ba lallai bane ki samu mafiyin shi ko kuma wanda ya kaishi,
Amma kinga in shine babu ta inda zanji fargaba dan na bashi auren ki domin dai dake dashi duka ina da iko daku kuma nasan bazai tab'a miki rik'on sakainar kashiba tunda yana sonki,
Na tabbata cewa yana sonki naki so na hak'ika tunda har ya iya gabatar dake a gaba na yanzun, bazance ki amince mishi dole ba,
Sai dai koda ace a yanzun bakya jin komai akan shi zan so ki bashi dama ko allah zaisa ki soshi d'in zuwa gaba, ni kuma na miki alkawarin inhar bakiji cewa kina son shi har cikin zuciyar kiba to bazan yarda kowa ya matsa miki cewa sai kin aure shi dole ba, wannan alkawarina ne kuma ku tayani sheda"
Ta k'arasa fad'a tana kallon su Maryam,
Insha Allahu kuwa zamuyi shedar ki Hajiyar mu, suka had'a baki wajen amsawa,
"To amma Hajiya ai Sultana tana son shi!"
Meenal ta fad'a batareda ta d'ago kanta ba,
"Ke Sister ni wallahi ba dagaske nike yiba inma dan abunda kikaji na fad'ama Hajiya jiyane to kisa ranki a inuwa Ya AK naki ne ke kad'ai, ina tayaki murna ubangiji Allah ya sanya alkhairi sai dai dan Allah karkija mana aji ki bada gari kawai musha biki a wuce wajen"
"Ni bazan auri mijin da tun baiyi auren farko ba kakar shi ke fad'in cewa tana mishi sha'awar auren mata biyu ba"
Ta k'ara fad'a tana juya kanta da har yanzun bata d'ago shi daga kan table d'in ba,
"Ah ah ha, Allah ya tsareni yi miki fatan zama da kishiya wallahi,
To dai koni da nike matsayin kakarki mijina har ya kwanta dama bai tab'a ambata min sunan kishiya a cikin gida ba,
Kuma dai har yanzun kina jin shima Yayan naki abinda yace dan suma dai nawa yaran babu mai kishiya a cikin su har yanzun, to wani mugun abun ne ni kuwa zaisa in so miki zama da kishiya yar nan!
Kwantar da hankali indai wancan ne Allah ya nufa zai zama mijin auren ki ina tabbatar miki da cewa kishiya sai dai ki gani a mak'ota ko baki lura da d'abi'un shi bane kaf nasara sun gamayin tasiri akan shi... "
Meelat dake dariya ne ta katse Hajiyar da cewa,
"To Hajiya mai yasa wancan lokacin baki hana auren ta da Sarki ba bayan kun san yana da mata?"
"Yanzun yar nan har kya tambayeni dalilin wannan aure?
Yo shi wannan auren yana da dalilin da za'a danganta shi dashi ne bayan k'addara, ke dai ki bari kawai Allah dai yasa kaffara ne ya bata ladan zaman kuma, gashi dai tun ba'aje ko ina ba Allah ya mata canji na alkhairi ai ni wannan abu koshi uban gayyar bazai fini farin ciki ba allah dai ya kaimu lokaci,"
Da ameen dukan su suka amsa sunaci gaba dayi ma Meenal din tsiya,
Daga nan gidan AK unguwan dosa suka wuce kai tsaye domin sun Riga sun gama cinye lokaci a gidan dan basu suka fitoba sai karfe 10 saura sakamakon hirar daya d'auke musu hankali,
Hakan ne kuma ya shashantar da batun zuwa marafa dubo gidan AK da sukaso zuwa.
An gabatar da addu'ar kwana uku ga mamacin lafiya, tun daga nan kuma bak'in da suka zo saboda a gudanar da addu'a dasu suka fara juyawa suna komawa gidajen su, wad'ansu yan garine wasu kuma bak'i,
Yan zaria ma dai da yawan su sun koma Malam yayi magana akan komawar Raheenat gida idan yaso sai ta k'arasa wankan ta a can, amma kuma sai iyayen Mamacin wad'anda a gidan suke zaune suma suka rok'i alfarmar abarta a gidan