Showing 126001 words to 129000 words out of 190771 words
mata da gidan a matsayin kyauta daga gareka ba,
Kasan halin Meenal sarai yar tutsuce tana sanin cewa daga wajen Kane kyautar gidan tana iya murje ido tace bata buk'ata shi yasa kawai na yanke hukuncin cewa zan bata ne a matsayin cewa kayan d'akin ta dana siyar ne na had'a da kudin daka bata nayi mata ciko na siya mata gidan nasan zatafi yin farin ciki da haka,
Daga baya idan ta gabatar ma da uban nata idan komai ya lafa sai in bud'e mata gaskiyar zancen, Sa'eed kuma ya fad'amin cewa baka son asan cewa kaine ka siya gidan da sunan ta dan haka ka kwantar da hankalin ka wannan sirrin babu maijin shi daga nan wajena kuma shima nasan bazai tona ba,
Sai batun Moon kuma nidai na baka goyon baya dari bisa dari sai dai bazan gaji dayi maka tuni ba nasan dai zuwa yanzun kasan kalar matar da kake aure atoh dan haka a daure a cigaba da kiyaye azkar sadaqa da kyauta a kuma dunga shan tsarin jiki duk da allah ke tsarewa amma kula da kaya dai yafi ban cigiya, ban kuma ce wai dan zaka auri jikata ita na gidan ka wulakanta taba koba komai ka dunga duba matsayin ta na uwar yaranta idan tayi ba dai daiba ka tsawatar mata kaine sama da ita, ita kuma Allah ya shirye ta tabar duk wasu abubuwan da basu dace ba Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakanin ku,
Na fad'a maka dai da wuri nike son ayi komai dan had'awa nike so ayi dana shi wannan yayan nasu daya gama zazzageni a gaban ka, dan shike neman auren Kanwarka Aminatu shin ko wajen ka zamuzo neman auren nema kai Babban yaya?"
Hajiya ta tambaya da dariya a muryar ta,
"Ai hajiya indai shine na bashi Meenal ko gobe ya shirya yazo da goro kawai ni kuma zan d'aura musu aure,"
"Oh kace kaima gaban kanka zakayi kamar yanda shima ya daki k'irji wai shi mai k'anwa zai aura mata wanda take so, to ai shi nashi maganar bata shiga gida ba tukun amma da iyayen shi sun iso zasu kai zancen can gidan su, ai ka gane ita waccen da suka haura sama tare dasu Meenal din ko?"
"Ah ah ban ganeta ba gaskiya"
"Ash sha to kanwar kace itama d'iyar mamarku ta Abuja ce tunda sukazo da rasuwar mijin Raheenat ita bata koma ba ta tare a wajen takwarar ta Aminatu, idan kaje gidan Malam ma zakaga d'an uwan ta yana nan wani ustazu suna ce mishi Sheikh Naseer yaro mai hankali dashi ni burgeni yake da farko har nayi sha'awar had'ashi da Moon fa ashe ba rabon shi bace"
Dan murmushi Sarki "eh nasan shi Sheikh d'in ita ce dai ban wayeta ba,
Hirar ne sosai ya b'arke tsakanin Hajiya da Sarki suna zaune a falon har karfe 11 na dare ya gota, sai da Ak ya fito daga d'aki yake ce mishi,
"Sarki idan ka biyema Hajiya fa zaku kwana kuna hira ne idan kuma ka shirya kwanan gidan sirikai ga d'akina nan idan kun gama hirar sai ka shigo mu kwana tare,"
Agoge Sarki ya kalla yana mik'ewa tsaye, "kasan kwata kwata banyi zaton lokaci yaja haka ba ashe dare ya farayi ban sani ba kuma ko gida ban shiba, Hajiya bari in wuce nagode kwarai Allah ya k'ara girma da jinkiri mai albarkha"
"Ameen ta amsa dashi tana mai cewa ka gaishe min da uwar gida kwana biyu bamu had'u ba,
Ficewa sukayi shida AK daga falon sai da AK ya raka shi har wajen motar shi sukayi sallama ya tada motar ya fice daga gidan duk da cewa AK yace mishi ko ya kira mishi Moon suyi sallama ne shi kuma Sarkin yace ah ah ya barta kawai tagama hutun kukan son shi da tayi d'azun,
Falon ya koma bayan wucewar Sarki sai da ya kulle kofa kafin shima ya shige ciki kamar ya haura sama ga k'ara gano Meenal sai kuma ya hana kanshi ya wuce nashi d'akin shima ya rufe k'ofa.
*Ummiee ce*
[10/2, 10:46 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 40*
No editing ๐
A wannan daren su Moon sun dad'e basuyi bacci ba domin Sarki yana barin gidan ya kira wayarta yana mata tsiyar cewa "ashe har haka yayi nisa a cikin zuciyar ta bai sani ba tunda gashi harta kasa rik'ewa ko kunya batajiba taje tana kukan tana son shi a gaban Hajiya, ai shi bai san cewa shi d'in d'an baiwa bane sai yau dan haka ta bar kuka tunda dai ta nuna tana so to jira kad'an kawai zatayi kafin ya canza mata suna daga Maimoon Usman Abdul Khareem,
Zuwa Maimoon Usman Sufyaan,
Tun yana hanya suke magana da ita bai yanke wayar ba har saida yakai gidan shi kafin ya mata sallama kuma sai da yasa ta had'ashi da Meenal,
"Kanwata nace wato da yike kin samu wani Yayan makwafina shi yasa ko tunawa dani ma bakyayi yanzun koh?"
"Ah ah wallahi Ya Sarki ba haka bane, kaga ga hidimar karatu da kuma shirye shiryen bikin besty Meelat da muke tayi shi ya d'auke min hankali yasa ban kira kaba amma kayi hakuri na manta kuma ban tayaka murnar sabon gidaba Allah yasa alkhairi ina kuma tayaka murnar samun soyayyar yar uwata allah dai ya nuna mana ranar "
"Ameen ya rabbi nagode da addu'a ai nasan dama bai wuce kice inyi hakurin ba bayan kin ware ni a gefe kuna biki babu sanarwa balle insa rai da goron gayyata, bana ma ko kud'in ankon ba'a nema a hannu naba nace too abun har yakai haka? anya ba'a canza min matsayi ba kuwa uwar malam?"
Dariya tayi kafin tace
"ah ah wallahi ba haka bane yayan mu karkayi fushi ai ba'a gama bikin ba bama a fara ba tunda gaka ka iso aini kuma nasan daga daren yau na tashi daga Meenal na koma Hajiya Ameena mai uwa a gindin murhu ai bayacin tuwon shi gaya allah dai ya k'ara arziki Ya maimartaba angon Maimunatu"
"Wannan irin kod'awa da kikamin Meenal ai dole a baki kyauta yanzun fad'amin cash kike so ko kuma transfer dan gudun mawar da kika bayar yau dama kin cancanci tukuici mai tsokama kuwa, dan haka ko nawa kike buk'ata ki nemi Salman gobe ya baki kamar yanda aka saba... "
"Wai Salman Yayan mu? Ah ah nidai karka had'ani da Salman fad'a mukeyi dashi gobe dai idan na shigo unguwar zan aiko ko kuma in amsa sakon ta hannun mutuniyar ka" sallama sukayi ta maida ma moon wayar,
ikon Allah wato dai kusancin da basu samu a baya tsakanin shida itaba shine yake son wanzuwa a yanzun a sanda take gidan shifa ita zata iya rantsuwa da Allah cewa basu tab'a zaman hira a tsakanin suba koda ya kirata a waya kawai zai tambayeta lafiyar tane sannan kuma yaji ko akwai wani abunda take buk'ata, itama kuma bata neman shi sai in tana da wani buk'ata na kud'i ko kuma idan fita zuwa wani wajen ya kama zata kira ta nemi izini amma kun gani tun bayan rabuwar su komai ya canza yanda yake mata wallahi kamar dai ba Yayan su Sufyaan mai karnukan nan data sani a shekarun baya ba wanda ko muryar shi kaji dole ka kama kanka,
haka Sultana tasa Meenal a gaba da tarin tambayoyi dan itafa tayi mamaki bata tab'a zaton cewa haka zataga Sarki ba dan haka ta gaza hakuri sai da ta tanka,
"Wai dama wannan shine Ya Sarkin?"
Saboda ita dai ba sanin shi tayi ba kuma a yanda take jin su Maryam na bada labarin shi tayi zaton cewa zatagan shi wani dattijo ne irin kamar dai wanda yake nemar shekaru 40 da wasu hayaniya a sama haka,
amma sab'anin hakan sai ta ganshi wani wankakken d'an gayu dashi wanda kai a kallo d'aya ma wallahi bazaka ce yana da yara har 4 har sun fara zama yan mata ba sai dai kace saurayi ne irin wanda baiyi aure da wuri ba d'in nan dan sam jikin shi bai nuna adadin shekarun shiba,
Koda tayi tambayar Meenal shareta tayi dan haka taci gaba da cewa
"Ke Meenal wai wani irin zama ne kukayi kukoh harna tsayin shekaru har 6 amma aka kasa samun cigaba?
Daga ke harshi kukayi ma kanku bak'in ciki wato yanda yasa miki na mujiya kema haka kika sa mishi saboda tsabar rashin sanin ciwon kai, Ni wallahi in fad'a miki gaskiya babu ta yanda za'ayi in rayu da irin wannan mijin irin rayuwar da kukayi gida d'aya kuma kuna ganin juna ace in sa mishi ido inyi ta kallo ban kai mishi cafka ba yo dan Allah kwace goruba a hannun kuturu har wani abunda za'a tsaya ana ba kai wahala ne, na rantse da Allah shida kanshi ma zai kawo kan shi har inda nike koda dad'in rai ko babu batareda ya tsaya shawara da kowa ba,
koda yike bari dai inyi shiru tunda mai afkuwa ta riga ta afku harta wuce inaga dai Allah yasan abunda ya shirya shi yasa ban bayyana a zaria ba a wancan lokacin su kuma wadanda ke tare dake suka kasa baki mafitar daya dace,
ke kuma Moon bari kiji in fad'a miki wallahi idan har kika sake kikace kema irin wutar da yar uwarki tayi a baya zakiyi to ki sani koni nan sai na miki Allah ya isa idan ita rashin rabone ya rabasu to ke ki d'auka cewa dama can kece mai rabon ba ita ba, zan kuma baki shawara daga yau daga ita harshi karki k'ara musu kallo a matsayin wadanda suka tab'a rayuwa karkashin inuwar aure ki d'auka cewa ita d'in dai kawai k'anwa take a gareshi kamar yanda nidake dama kowa ya shaida hakan,
Sarki dai yana sonki kema kuma kina son shi dan haka nemo zanin goyo kiyi d'amara ki goye abinki tsaf wallahi, karki sake koda wasa kice zaki dunga tunawa cewa yana da wata matar bayan ke a duk sanda kuka kasance tare, nuna mishi cewa shi shikadan shi shi kika sani shi kika waya kike kuma gani a gaban ki da bayanki dan shi din dai shine duniyar ki ,
Ki nuna mishi kauna ta hanyar nuna kulawar ki akan dukan abunda ya nuna miki yana da mahimmanci a wajen shi, ki tayashi son iyayen shi, yan uwan shi da yaran da ya haifa, bance ki nuna soyayyar ki ga matar shiba dan ba dolen ki bace ita, sai dai kiyi kokari ki dunga danne kishin ta a gaban shi karki yarda in kina hira dashi kice zaki dunga sakota a cikin hirar ku haka kuma shima karki yarda ya dunga kawo miki hirar ta kowacce ta tsaya matsayin ta ki kuma dunga kiyayewa karki yarda kice zaki shiga hakkin ta wato misali kiran waya a sanda kika san yana gida,
In fad'a miki gaskiya wannan had'i naku yamin dad'i dan tsakanina da Allah dama tunanin wacce zata shige cikin gidan nan tayi luff a matsayin matar gidan madadin Meenal kullum shike cimin tuwo a kwarya ke gidan nan fa Yasin duk wacce ta shige shi matsayin mata to ta kwantar da kai tayi luf taci arzikin ta hankali kwance abinta kinga ni dama ban tab'a shiga ba kullum dai idan nazo wuce shi sai na yaba a cikin zuciyata yanzun kuma ga dama ta samu kina shigewa gidan nan ai mu shar abunmu wallahi ,
bari in baki wata shawara ban sani ba ko zaki d'auka kinga zama gida d'aya keda kishiya na rantse miki da Allah sai kin kai zuciyar ki kololuwar nesa dan yau da gobe duk yanda zata takale ki ku raba hali sai tayi ke wani abun ma da gayya zatayi dan dai kawai taga ta b'ata miki rai balle kuma kishiya irin matar shi da naji labarin nata kishin yake a sarari dan haka nidai a nawa hangen gara ki lallab'o shi ya ajiye ki a wannan gidan nashi na garin nan ita kuma taci gaba da zama a Kaduna,
Falalane mai girma raba gari da kishiya domin idan dai tana inda take kema kina naki wajen wata rana ma mantawa zaki dungayi cewa bake kad'ai bane domin idan yana wajen ta gani zakiyi kamar tafiya yayi ya dawo gareki, tana da masaukin ta anan cikin gidan iyayen shi dan haka baki da fargaba cewa idan tazo zata sauka a gidan ki, zuwa Kaduna ki tare ba dole bane a gareki in kinso dai kina iya zuwa can din lokaci bayan lokaci amma dai ya zamana cewa nan dai kece mai iko dashi, wallahi nayi miki murna kwarai kekam Allah dai ya sanya alkhairi yasa ace gara da akayi barkan ki da shigowa cikin ahalin mu duk da dai naji babu dad'i kad'an a sanda naji Hajiya tace da taso ne ta badaki ga d'an uwana ya Sheikh amma ba komai na hakura dan bazan miki bakin ciki ba".
Hira sosai suka sha a wannan dare kafi bacci ya nuna musu fin k'arfi wajen yi gaba da kowacce a cikin su, yau dai rana na farko da Moon ta samu damar yin bacci cikin salama sab'anin sauran ranakun da suka wuce wad'anda ta dunga lissafin yanda abubuwa zasu kasance sai gashi Allah da ikon shi komai ya tafi a saukake ba tareda an samu rarrabuwar kawuna ba.
*WASHE GARI*
Gidan Hajiya mak'il ya cika da bak'i na nesa dana kusa kowa ya hallara sai faman hadaยฒ kawai akeyi, cikar gidan kuma ya k'aru ne kasancewar ba iya ahalin gidan ne kad'ai suka samu damar isowa a wannan rana ba harda abokanan su Musty kamar yanda AK yace anan zasu sauka anan d'in suka sauka,abokan sune wasu tun na yarinta wasu kuma anyi makaranta tare sai dai kuma kai mai kallo da zarar ka gansu ko baka tambaya ba kasan babu sakarai a cikin su domin duk kan su kowa yana da abun hannun shi duk wanda ka kalla dole sai kaji kamar karka dena kallon shi dan sun san hannun su gashi ko wannen su sunsha wanka sun gaji kamshin ko har baka tantance na wani ga kuma giyar kud'i dake d'ibar su sai suka zama abun sha'awa a wajen sauran matasa sai dai sunji babi dad'i bayan isowar su da suka samu labarin cewa babu wani shagalin da aka shirya na cashewa a bikin na abokin su domin fa sunzo da niyyar su warwasa biki dai na rana d'aya dan haka suka tada balli cewa basu yarda ba ko ba'ayi komai ba su zasu shirya ma amarya da ango dinner,
da kyar suka samu Mai Jama'a yasa baki aka tsaida batun dinner d'in dan shi da Musty cewa yayi baya buk'atar bidi'a su bisu da addu'a kawai.
A gefen su Meenal ko suma dai tun wayewar gari suka fice daga gidan domin agenda dinsu na yau shine kunshi da gyaran gashi da yamma kuma zasu gabatar da bridal shower wanda iyasu mata ne zasu halarta gobe kuma shine zasu gabatar da kwarya kwaryar walimar da suka shirya wanda maza da matan dukan su zasu halarta, kud'i masu nauyi AK ya sauke ma sultana kafin fitar su a matsayin kudin kunshi dana gyaran kai nasu dana amaryar su, su kuma sauran abokan sosai suka nuna nasu bajintar wajen saukema k'awayen na amarya komai zasu buk'ata dan haka suma kawayen babu tausayi haka suka dunga lissafo musu abubuwan da suke buk'ata harda wad'anda basu zama dole ba, Safiyya matar Yusuf wase itama a ranar ta iso dan haka itama gidan Hajiya ta ajiye su Affan ta shige cikin su Moon aka cigaba da gudanar da abubuwa da ita, kuma shima Sarki kamar yanda yayi alkawari ya sauke ma Meenal d'in Alert mai nauyi a cikin wayarta wanda har saida Sultana ta dunga mamaki wai sudai mazan zaria idan zasuyi kyauta a dunkule sukeyin shi kamar basu san zafin nema ba, ita ma dai Allah ya had'ata da wanda zata shak'o wuyar shi tayi ta goge mishi hadda.
****
A jiya kasancewar koda Sarki ya isa unguwar na malamai dare ya riga yayi sai kawai ya wuce gidan shi ya nemi wajen bacci,
Bayan gari ya waye kuma yana dawowa daga sallan asuba yayi wanka ya shirya ya wuce gidan su, kowa yayi mamakin irin sammakon daya bugo daga Kaduna dan haka sai uwar gida ta fara tambayar shi da cewa "lafiya kuwa wannan irin tafiya na sassafe"
Kai ya maida k'asa cike da rashin gaskiya yana non nokewa ya amsa mata da cewa, "lafiya lau"
"Ko wani abu ya farune?" Ta k'ara tambaya,
"Ah ah babu abunda ya faru, da yike nayi shigowar dare ne a jiyan shi yasa ban shigo nan din ba," sai da ya k'ara duk'ar dakai kafin yace,
"Ina son zan k'ara aure!"
Shiru yayi yana jiran jin amsar da zata bashi,
Ita ko sai tayi shiru abinta kamar ma bataji mai yace d'in ba,
D'aurawa yayi da cewa,
"Na tura can gidan su yarinyar wajen iyayen ta a Lagos sai dai kuma a lokacin shi mahaifin ta bayan sunyi magana da wanda na tura yace a dakace su saboda waliyin dazai bada auren ta baya k'asar idan ya dawo sai su koma ayi magana, to jiya dana iso naje na gaisheda kakarta ita kuma ta shaida min cewa indai na shirya to suma a shirye suke dan basa son abin ya d'auki lokaci, tana dai nufin idan za'aje a tafi da komai na neman aure kawai dan a cewarta bata son a wuce nan da wata d'aya yau iyayen yarinyar zasu shigo gari shi yasa nace bari in zo in muku bayani"
"To ubana mai kake nema a gunmu kuma tunda ka riga ka shirya harka riga ka tura magabatan ka mu nan bamu da labari daka kawo min zancen yanzun mi kake so ni kuma ince ne? Ai ni kuma bani data cewa sai dai in muku fatan Alkhairi tunda kai dai ka zama d'an kanka har kayi girman da zaka tura wasu can daban nema