Showing 42001 words to 45000 words out of 190771 words
ka shigo cikin gida sai ka wani d'aure fuska"
Dariya ma ta bashi sai dai baiyi dariyar ba sai yayi karamin murmushi kawai,
"To yarinya ko dai kina kishi ne kinga yan mafa nata faman folawa?" Ya tambaya shima yana dage mata gira irin yanda ta mishi dazun,
"Allah ya kyauta to wacece zanyi kishi da ita a cikin su bayan ba saurayina sukace suna soba, nidai dan Allah kayi aure kona samu in dunga zuwa maka gidan nan hutu"
"Ke bafa gidana bane"
"Gidan waye", ta tambaya tana b'ata fuska,
"Haya nikeyi anan d'in kafin in k'arasa nawa ginin da nikeyi a marafa ki bari kafin ku tafi zan kaiki kiga gidan inda baiyi ba sai ki fad'a a gyara ko yar zuwa hutu"
"Kai taubashi wai dan Allah duk kyan gidan nan na hayane? Ikon Allah amma dai gaskiya gidan yana da kyau nasan kuma hayar shi sai yayi tsada gaskiya gara ka gina naka kawai ka tare abunka wallahi, nifa abun baya burgeni ace mutum yana da halin da zai siya ma kanshi muhalli amma kaga yana yawon haya, wallahi kuma wani zakaga ga mata ga tarin yara duka a gidan hayan ana batun hidimar abincin da za'aci kudin makaranta kudin hayan dana hidimar yau da kullum amma a hakan sai kaga mijin sai yayi ta faman hawan manyan motoci yana yawo a gari alhalin ko fili taki d'aya bai mallaka ba sai ya mutu kaga ahali duk sun watse tunda babu muhallin zama.
Suna wannan hirar har suka fita waje ya kwaso musu kayan nata dana Hajiyan ita kuma tana bin shi a baya, sai da yakai musu kayan har d'aki sannan ya dawo falon, ya samu tayi zaune tana cin chips din,
"Ya'ya amma abincin nan yayi yawa fa Allah sai dai musa sauran a fridge gobe muyi breakfast dashi"
"Shi yasa na siyo da tawa aI kici ki ture, kafin ki koma gida kina cewa kinzo kaduna ko ruwan sha ban siya miki ba"
Ya k'arasa fad'a shima yana zama k'asa inda take zaune, cokali ya d'auka yasa a cikin chips din da take ci sukaci gaba da cin abincin tare suna hira,
Kai shidai yau wallahi bazai ce komai ba sai dai yace Alhamdulillah wallahi me yafi wannan dad'i ace gaka ga abunda kake so kuna cin abinci da hora cike da soyayya,
Ji yake kamar su dauwama a haka kar wani abu na sab'ani ya shigo tsakanin su, wallahi sai yakeji kawai kamar irin ai an riga an daura musu aure ita din matar shice take zaune a gaban shi, baiyi yunkurin bata abincin a baki ko sau daya ba sai dai kuma shi da kanshi ya dunga cire mishi tsokokin kajin yana tara mata a gefe d'aya ita kuma tana d'auka tana ci a haka har sai da ta koshi dam, sannan shima yaci wanda zai iyaci suka tattara sauran suka kai cikin fridge lodojin kuma suka sasu a cikin Bola, sai da ta raka shi har kitchen din ya wanke hannu sannan suka fito ya kulle kofar falon ya kashe wutar falon kuma,
"Ina ne d'akin ka?"
"Ya akayi?"
"So nike in lek'a mana"
"Kiyi me a cikin?"
"Kalla fa kawai zanyi sai nima inje in kwanta!"
"Ah ah kije dai ki kwanta dare yayi kya gani da safen in Allah ya kaimu"
"Kai yaya lek'awa fa kawai zanyi"
Daure fuska yayi ya koma mata AK din data sani a da can baya,
"Ke wai ina wasa dake ne nace kije ki kwanta dare yayi koh bakiji me nace bane, kin san dai bana son inyi ta maimaita magana a lokaci guda koh?"
Gaba tayi tana tura baki ta bud'e kofar d'akin da Hajiya ke ciki ta shiga tana tura baki,
"Ku da ke kukeyi a falon tun d'azun?" Hajiya ta tambaya wacce ke zaune akan gadon hannun ta rike da littafin addu'a da alamun itama sai da tayi wankan dan ta canza kayan jikinta ma zuwa na bacci,
"Mun tsaya cin abinci nefa Hajiya tunda ke kince kin koshi"
Cewar Meenal shiko sai da safe kawai yayi ma Hajiyar daga bakin kofar daya coge ya koma da baya bayan ya rufe musu kofar ya shige d'akin shi.
********
Teemah amma dai tsayin shekarun zamana dake ina ganin kamar ai ban tab'ayi miki alkawari cewa zan zauna dake ke kad'aiba har zuwa karshen rayuwa na,
Ya kamata ki gane cewa shi karin aure a wajen namiji kaddara ce idan Allah ya tsara cewa zan kara auro wasu matan bayan ke bai kamata kiyi mamaki ko jayayya ba,
Miye ma wani abun damuwa ko tashin hankali bayan kinsan cewa ina son ki, duk wacce zan auro fa ke din dai ke zata tarar a matsayin uwar gidan ta, ya kamata ace kin shaideni kodan yanda nake kokarin wajen baki hakkin ki ba tareda na tauye kiba,
Ni bance zanyi aure yanzun ba, amma ki sani niba nine nike da zab'in yanda kaddara zatayi da rayuwata ba idan Allah ya nufa cewa nan gaba zan k'arayin wani auren dole zakiyi hakuri ne kwatankwacin hakurin da kikayi a baya,
Sannan ina mai maki ishara da ki kasance mace mai tsoron Allah aduk abunda zata aikata kiji tsoron Allah ki sani duk wani abun da zakiyi a sarari ko a fili koda ace ni da sauran jama'a bamu gani ba, tofa ubangijin daya halitto mu dan mu bauta masa yana daga sama yana kallon mu, sannan babu mara rabo a duniya irin wanda yake had'a Allah da wani masu biye biyen wajen boka ko malaman tsubbu dan suyi musu maganin damuwar su, ki sani in kika tauye wani kema Allah bazai barki ba sai ya saka ma wanda kika zalinta,
Nidai ina son ki har gobe kuma ina kaunar ki a matsayina kuma na uban yaran ki bazan so inga kin tashi ranar lahira cikin mutanen da Allah yake fushi dasu ba dan haka nike son in k'ara jan hankalin ki ki sani ita mutuwa bata sanarwa a yayin zuwanta Allah yaga dama a yanzun da kike kwancen nan kike ganin cewa kin samu sauk'i akan a sallame ki gobe ki koma gidan ki, in Allah yaso sai ya aiko mala'ikun shi suzo su zare miki ran da kike takama dashi wanda ni ko mahaifan ki bamu isa mu dakatar da hakan ba,
Teemah nasan ni duk abunda kika aikata kin yi shine saboda son da kike min,
Amma kuma ni bazanyi akfahari da son ba alhalin son nawa ne yake ta neman jefa min ke a cikin wuta,
Ki fadamin maina tauye miki a tsawon zamana dake mai kika nema wanda ni ban miki ba? Wacce kalar soyayya kike so wacce ban nuna miki ba?
Mai ya rage a tsakanin mu iyeh, kefa matatace ni mijinki hakan bai wadatar ba, naga dai tun kafin ki aureni kin sani cewa ahalina ba masu zama da mace d'aya bane kuma a hakan kika aureni to miye kuma na tashin hankalin a yanzun, ko wani mutum yana samun dama na domin ya gyara kuskuren daya aikata a rayuwar shi ta baya dan haka kema zan baki wannan damar kamar yanda nima lokaci ya bani damar gyara kuskuren da nayi a baya tun ina raye,
Ni bazan tab'a iya rabuwa dake ba saboda son da nike miki darajar yaran da kika haifamin da kuma na iyayen ki da kullum suke d'aukata a matsayin d'an su,
Dan haka zan baki zab'i, indai har kina sona kamar yanda kike fad'a a kullum to zanso ki tattara komai da kike buk'ata ki bini mu koma Kaduna muci gaba da rayuwa ni kuma zan nema miki gida dai dai da ra'ayin ki wanda zaki zauna keda yaranki wadanda zan amso miki su ku zauna tare,
Sannan maganar aikin ki bazan tab'a hanaki ba sai dai kuma dole ne ki nemi transfer daga nan zuwa can inya so kici gaba da aikin acan bayan mun koma can, maganar kasuwancin ki kuma dama ai bake ke gudanar dashi ba akwai masu kula mishi dashi dan haka kibar mu ni kuma na miki alkawarin cewa ko wani kasuwancin sabo kike buk'atar budewa a kadunan zan baki kudaden da zasu isheki wajen gudanar dashi,
Sab'anin hakan kuma ina ga sai dai muyi hak'uri mu rungumi kaddarar rabuwa dan gaskiya bazan iya jele kullum ina raba hankali na bana kaduna bana Lagos bana zaria sannan bana sauran guraren da aiki ke Kaini ba, dan haka na baki zab'i ko ki bani mu koma can gaba daya ko kuma kiyi zaman ki kici gaba da al'amuranki amma bada igiyar aurena a kanki ba, sati d'aya zanyi anan dan haka kiyi tunani ki kuma yanke shawara cikin kwana kin da zanyi kafin in koma dan in san a wata matsayar muke,"
Yana gama karanta mata hakan ya sauka daga gadon ya d'auki pillow da bargon da nurse din nan ta kawo mishi ya koma kan kujera yayi kwance bai k'ara bi takan ta ba,
Ita ko zaune take kawai amma idan tace hankalin ta baya tare da ita tabbas ba tayi karya ba,
Bazatace bataji abunda ya fada mata ba, sai dai ta rasa tantancewa shin mafarki takeyi ne ko a farke take Sarki ya ajiyeta ya rattafo mata wadan nan kalaman masu kama da sukar mashi ko yankar takobi,
Infa kunnen ta ya jiye mata abinda ya fad'a da kyau kamar maganar rabuwa taji yanayi a tsakanin su bayan ya shimfid'a mata sharadin da in batabi suba rabuwar ce zata biyo baya,
To me yake shirin mafuwa ne ga mutumin da a yanzun yanzun ya gama maimaita mata kalaman tarin kaunar da yake mata,
Daren yau daya kamata ta kwana cikin farin ciki na samun yanci cewa mijinta ya dawo mata shine kuma tun ba'a kwana ba yake neman rusa mata duk lissafin dako farawa batayi ba,
Da kallo ta bishi tana rasa abin cewa harya kwanta mai kuma ya tuna sai taga ya tashi ya fad'a toilet alwallah ya d'auro bayan ya fito ya d'auko daddumar da yake gefen gadon nata ya shimfid'a ya tada Sallah ita dai bata k'irga ko raka'a nawa yayi ba tana kallo dai harya sallame yayi addu'a ya taso ya nad'e daddumar ya koma ya kwanta kuma baice mata k'alaba duk da yanda ta kafe shi da kallo kuwa,
To itama dai jiki a sanyaye ta kwanta tana tariyo maganganun daya furta wadanda sukaci gaba da maimaituwa a cikin kunnen ta kamar yanzun yake furta mata su,
To kenan hakan yana nufin cewa Sarki yasan abubuwan da take aikatawa a kanshi shi yasa ya mata wa'azi kenan ko kuma me ya faru?
To amma ai inda bai sani ba da bazai tada maganar ba,
Ta dade tana tufka da warwara itafa tana son mijinta dan son nashi ne ma yasata aikata komai da ake ganin ta aikata masu kyau da marasa kyau, to shine sai yanzun kuma da abubuwa suka dai dai ta zai bata zab'i, kenan idan harta sake ta zab'i cigaba da zama a Lagos da kuma aikin ta anan din duk yak'in da tayi a can baya saboda shi sun tashi a banza kenan, to ita da take fatan Allah yasa cikin yan biyun gareta me zai Hana bazata amince su koma can din ba ta rungumi sauran yaranta tunda komai yazo karshe su gina sabuwar rayuwar su abunsu,
Sai da ta gama yanke shawara tsaf sannan ta sauko daga kan gadon ta nufi kujerar da yake kwance dan shi har bacci ya d'auke shi tuni,
Dukawa tayi a dai dai fuskar shi tana shafa kanshi da hannun ta guda,
Daya hannun kuma tana dan tsetstsefe gemun da baida wani tsayi sosai dashi tana kuma kiran sunan shi k'asa k'asa,
Bud'e idon shi yayi a hankali yana kallon ta,
"Mi kikeyi bakiyi bacci ba? Dare fa yayi jeki kwanta"
"Sarki na yarda zan bika mu koma can Kadunar kamar yanda ka buk'ata amma dan Allah kar kace zaka rabu dani wallahi ina son ka, bazan iya yin rayuwa dako wani namiji bayan kaina a duniyar nan, kuma wallahi duk abunda na aikata nayi sune sakamakon kishi da kuma son ka da suka rufemin ido, amma insha Allah bazan k'ara ba"
"Nifa bance kiyi saurin yanke hukunci kai tsaye ba shi yasama na baki dama saboda kiyi nazari sosai a tsayin kwanaki 7 din dana baki, saboda bana son in miki dole"
"Na amince Sarki zan bika duk inda kake son Kaini bazan k'arayin maka musu ba dan Allah karka k'ara cewa zaka rabu dani wallahi zuciya ta zafi takemin"
"Kin tabbata?"
"Eh nayi alqawari"
"To jeki kwanta zamu k'arasa maganar da safe bacci nikeji yanzun"
Kwantowa take shirin yi a kujeran da yake kwance,
"Ke miye haka bayan kin san nan wajen ba isar mu zaiyi ba so kike ki matse min baby ne?"
"To ka tashi mu koma can sai mu kwanta yanda bazamu takura ba"
"Kin san dai bana son musu koh"
Ya fada yana rufe kanshi da bargo har saman kanshi,
Dire dire ta fara tana kananan kuka cewa ita wallahi bata yarda ba sai dai ya tashi su koma can din su kwanta gaba d'aya, a babu yanda zaiyi haka ya tashi, yana mik'ewa ko ya mata d'aukar cak irin wanda akema jarirai bai direta a ko ina ba sai akan gadon, yana sauke ta ko ta sanya duka hannuwan ta guda biyu ta kamo fuskar shi a cikin tafin hannun ta, yana shirin yin magana ta had'e bakin su tana aikata mishi da kiss jikinta har rawa yake tsabar yanda jikin nata ke amsa kewar shi da tayi,
To dai shima dama d'aurewa ce kawai yake bawai dan baya buk'atar matar tashi ba dan haka tuni ya sadaqar wajen biye mata suka raya daren suna farantawa juna rai,
Asuba ta gari Sarki da Gimbiyar shi,
Washe gari Sarki ya nema mata sallama, haka ko Dr din ya rubuta musu takardar sallama bayan sun gindaya mata sharad'od'i akan abubuwan da zata kiyaye har zuwa sanda cikin zai kai lokacin haihuwa ne suka kwasa suka koma gidan su,
A cikin satin tattata batun zuwaga Moon Sarki yaci gaba da kulawa da Teemah wacce gaba d'aya ta canza mishi take binshi sau da k'afa tamkar ba Teemah da kowa ya sani ba wacce sai abunda take so takeyi, domin zagewa tayi wajen bashi kulawa kamar wasu sabbin ma'aurata ganin hakan shima sai ya sake mata a satin kuma yasa ta fara neman transfer shi kuma a gefen shi inda zata zauna a kaduna ya fara neman mata dan yasan cewa bata son zaman cikin bariki kuma shima ba muradin shi bane ajiye mata a cikin barikin,
Satin shi na farko a Lagos duk wajen kula da matar shi ya cinye su sati na biyu ne ya fara kokarin ganin sun had'u da Moon domin ya duba takardun binciken da Joseph ya kawo mishi ranar da matar Joseph din zata haihu, Allah yayi itama matar Joseph din ta haihu lafiya a asibitin dan washe garin ranar ma kusan tare dukan su aka sallame su,
A cikin binciken da Joseph din yayi akwai inda yaga ya sa sunan wajen shakatawar da Moon ke zuwa kusan kullum idan ta fito daga wajen aikin ta sai ta tsaya a wajen ta huta taci abunda take muradi wata rana kuma take away takeyi ta wuce dashi gida, kuma kullum tana isa wajen ne da misalin karfe 5 da mintoci na yamma wani lokaci ita d'aya wani lokacin ita da kawayen ta,
Dan haka tun bayan daya dawo daga Sallan la'asar ya shirya cikin tsararriyar shigar data boye yawan shekarun shi da suka fara nunawa, wanda har sai da Teemah ta tanka a yayinda taga fitowar shi.
"Abban Boy ina zuwa haka naga kaci gayu da yawa?"
Ya danji wani irin domin dai babu halin da zai fito ya fad'a mata gaskiyar inda zashi dan haka sai kawai yace mata,
"Muna da wani Meeting da karfe biyar shi nike son inyi attending kar inyi latti, sai na dawo ki kula da kanki"
Sai da ya k'arasa inda take ya mata kiss a goshi sannan ya fice daga gidan yana jin wani iri, kamar dai bai kyauta ba haka yakeji,
Tunda ya isa wajen ya nemi wajen zama ta inda zai iya kallon duk wani wanda zai shigo wajen dama duk wanda zai fita abinsha kawai yayi order ya zauna yana ci gaba da amsa kiran dake shigowa cikin wayar shi yana kuma jiran tsammani,
Kamar yanda Joseph din yace kuwa hakane ya tabbata dan karfe 5 da mintoci Moon ta shigo wajen,
Hadaddiyar yarinyar da tunda ta doso wajen ta kayar mishi da gaba saboda tsabar kwarjinin ta daya cika shi, tafiya take d'as d'as d'as abunta tasha wanka ta wanku kamar wacce bata fita cikin rana saboda tsabar hutu da gayun da suka bayyana kansu a tare da ita,
Ita kad'ai ta shigo wajen babu d'an rakiya, allah da ikon shi kuma sai yaga kamar inda yake zaune ma take nufowa, koda wasa baiyi sakacin dauke idon shi a kanta ba har sanda tazo ta d'an gota shi ta wuce ta gaban shi ta zauna a kujerar da yake gaban shi kadan tana baza kamshi, yana ci gaba da kallon ta harta zauna waiter din wajen yazo ya tambayeta abunda take so ita kuma ta fad'a mishi shi kuma ya juya dan ya kawo mata,
Gyara zama Sarki yayi yana k'ara gyara aye glass din dake sanye a fuskar shi,
Sunyi zama na mintoci baiyi yunkurin zuwa inda take ba yana zaune a inda yaken yaga wani saurayi wanda shima tunda ta shigo ya lura da yanda ta d'auke mishi hankali, sai dai kuma ga mamakin shi saurayin yana zama a kujerar dake gefen ta ita kuma ta mik'e bai daiji abunda tace ma gayen ba, lura da yayi cewar fita zatayi sai shima yayi azamar ficewa daga cikin wajen dan ya jirayi fitowar ta,