Showing 84001 words to 87000 words out of 190771 words

Chapter 29 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1559

bazai yuwuba dan nidai bazan iya tunkarar kowa da maganar nan ba, zaifi kyau idan kaima kaji zance Mahaifiyar ka ka hakura ka nemo wata can daban ba Meenal ba mu kuma zamu tsaya muga mun aura maka ita"
Shima tashi yayi ya shige ciki yabar din shi kad'ai a falon sai uwar zufan tashin hankali yake had'awa, akwai matsala fa gaskiya dan bayajin zaiyi saurin sarewa dole zaici gaba da gwada sa'an shi har su saurare shi in kuma basu saurare shiba shida kanshi zaije ya gabatar da kanshi a gaban Malam.

Tunda Meenal da Sultana suka koma gidan Hajiya sai ya zamana zuwa unguwar Malamai ya musu wahala dan hankalin Meenal yana kan surprise din da suke son hadama Meelat dan haka ko a tudun wadan ma ba zama sukeyi sosai ba,
Kuma tun dawowar su ko sau d'aya meenal tak'i yarda ta tsaya suyi magana da Hajiya akan AK dan da zarar Hajiya ta d'auko zancen ita kuma zata tsareta da cewa ai ita Hajiyar tayi alkawarin cewa wannan karan bazata yarda ayi mata aure irin wanda aka mata a baya ba dan haka su kyaleta ita ba yanzun zatayi aure ba, ko dan Hajiya taga AK jikan ta shi yasa take so ta matsa mata,
To ai itama jikar Hajiyar ne bai kamata kuma ta nuna banbanci ba,
Ita dai Hajiya ta kyaleta ne kawai amma tuni ta riga ta yanke hukunci suna gama hidimar bikin nan na Musty ita da kanta zata nemi Adamu akan maganar dan babu ruwan ta da Malam Almu.

Misalin k'arfe 3 na rana ya iso garin na ZARIA,
Yana mai d'aukin dawowa dan yayi tozali da muradin zuciyar shi, bai shaida ma kowa cewa yana hanya ba dan yasan idan tasan zaizo ba abun mamaki bane ta gudu ta koma Unguwar Malamai,
Sai dai dole murnar shi ta koma ciki a sanda ya iso gidan Hajiya ke shaida mishi cewa ai basa gida sun daiyi mata sallama akan zasuje Makaranta,
Sabon wanka yayi bayan da yaci abincin da Hajiya ta shirya mishi kananun kaya ya sanya,
Kai jama'a wallahi AK bayaji indai wajen iya d'aukar wanka ne koba dan Allah ba idan yayi wani wankan dole ka tsaya ka kalle shi,wankan na yau k'ananun kaya ne bak'ak'e ya sanya dogon wandon crazy jeans sai vest daya sanya a ciki mai fad'i dan sam bata kama jikin shiba ya d'auko wata jacket itama bak'a crazy wacce duk akabi jikinta aka Yayyan ka ta saboda tsabar iya shege tun daga gangar jikin rigar har hannayen duka Anbi an yayyanka sai tsintsiyar hannun ne kawai wajen inda aka makala botura sune ba'a yanka wajen ba,
Bandana bak'i ya d'aura akai haka ma a tsintsiyar hannun shi guda wanda ya nad'e hannun rigar zuwa sama suma sai ya sanya agogo da wasu yan hannu na gayu wanda maza ke sawa,
Takalmin kafar shi ko irin πŸ‘’ boot din nan ne mai tarin igiyoyi shima baki, bak'in glass ya sanya ya toshe idanuwan shi dasu bayan ya gama yima jiki shi wankan turare ya fito daga Sashen,
A farfajiyar gidan suka had'e da hajiya wacce ta fito itama wajen Dada Turai kakar billyn ya sa'eed take son zuwa,
Harta gifta shi ta dawo daga baya tana tafa hannu wa,

"Kai Abdul me nike shirin gani haka wannan shigar da kayi kuma irin ta d'iyan anna ina kake shirin zuwa ni Aminatu?
Wannan ai kirama kai tsiya ne wallahi ka rasa suturar sawa sai wannan shegiyar riga ko ina a yayyage kamar wani sabon mahaukaci, fisabilillahi wa zai kalleka in bacin wannan tabon sallan dake goshin kaba ai sai ace k'atoton Anne ne kai wallahi,
Ji takalmin da kasa ka tamke k'afa wannan kafin ka cire kace zakayi alwallah an liman ya idar da sallah tuni,
Ni ko ina ce kwanaki naga duk ka zubar da wannan shigar naka na banza ka koma shigar hausawa sak,
To yau kuma watan iya shege ne ya tsaya daga dawowan ka ka shiga ka cire suturar mutane kawai kayo shiga irin ta annan legos ka fito a haka zaka fita gari kana yawo a dunga nuna ka da baki ana cewa ai jikan prof ne,"

"Hajiya Birthday din friend dina zani fa taya zan je wajen da kananun kaya?
Nidai kiyi hakuri sai na dawo"

"Muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun a haka kake son in shige maka gaba a baka auren jikata kana Wannan shigar anya kuwa Abdul Khareem"

Bai saurare ta ba ya shige motar shi yabarta a wajen tana faman surutai daga karshe fasa fita tayi ta wuce wajen jummai kai karan AK din.

Shiko tun a hanya ya kira Sultana ya tambayeta suna ina ne ita kuma ta shaida mishi inda suke,
Makarantar ba bak'on shi bane dan haka baisha wahalar gano inda suke ba,
A can wani cafeteria suke ita da su Maryam da alamar sun gama tattauna wa ne suka isa wajen dan cin abinci,
A kujerar da suke zaune ita da wani abokin su ne tana k'ara jaddada mishi abubuwan da take buk'ata,
Sultana ce ta fara hango shi dan haka sai tayi ma su Maryam signal akan subar wajen, zare jikin su sukayi suka koma can gefe ita kuma tana duk'e ne sai faman list na abubuwa take rubutawa,

Yana K'arasowa da Sallama yaja kujera guda d'aya a gefe ya ajiye a gefen ta ya zauna yana binta da mayen kallo,

Muryar shi da kuma kamshin turaren shi data shaqa ne yasa ta d'ago kai babu shiri,
Idanuwan sune suka fad'a cikin na juna sai ko ya wani d'age mata girar shi guda d'aya,

K'asa sosai ta amsa sallamar ta maida kanta k'asa sai dai kuma ta gagara ci gaba da rubutun saboda yanda idanuwan shi ke yawo a jikin ta,

Gayen dake zaune a gefe ne bayan ya amsa sallamar AK din yake tambayar shi da cewa,

"Malam lafiya? Ko akwai wani abun da zamu taimaka maka dashi ne?"

Wani irin kallo AK ya jefe mishi kafin a dake da jefa mishi tambaya da cewa,
"Waye Kai?"

"Ah ah ya zaka zo waje ka samu sannan ka kama tambaya na waye ni, ai sai dai ni in tambaye ka ko waye kai daka zo ka zauna a inda muke ba tareda izini ba"

"Oh haka ne fa, na zauna ban tambayi izini ba koh?
Koda yake ai babu buk'atar masoyi ya tambayi masoyiyar shi izinin zama a inda take, koba haka ba Soulmate?"

Bata dago ba ta amsa da cewa,

"Ina ganin ai mun kammala lissafin komai na buk'ata zaka iya tafiya yanzun dan muma wuce wa zamuyi"
Ta fadi hakan tana mik'a ma gayen takardar data gama rubutu a ciki yanzun,
Shima baija zancen da tsaho ba ya amshi paper din ya mik'e ya isa can inda su Maryam suke, ya rage daga ita sai AK a zaune a wajen.

"Soulmate ba gaisuwa ko baki farin ciki da zuwana bane? Kinga niko tunda na iso na kasa jure rashin ganin ki shi yasa na biyoki nan.


*UMMIEE ce*✍🏼
[9/15, 8:39 AM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 28*


Ina yini"
Ta fad'a a sanyaye tana d'an satar kallon gefen dasu Maryam suke,
sai dai ga mamakin ta sai taga kusan gaba d'aya yan matan dake wajen hankalin su ya karkata ne akan kallon AK,
Ita wallahi dama tasan za'ayi haka, wai mema ya sashi biyota har makaranta ne?

"Lafiya lau Dr ya kike, ya school d'in naku?"

"School Alhamdulillah barka da zuwa ya hanya?"

"Alhamdulillah na iso lafiya, hanya kuma yana can mun baro musu,
Me kuke shiryawa ne haka naga kina tayin dogon list?"

"Surprise zamuyi ma amaryar ku, abubuwan da muke buk'ata na program din da muka shirya zamuyi anan cikin school ne nike rubutawa saboda karmu mance da wasu abubuwan,
Me za'a kawo maka ?"

"Ni bana buk'atar komai naci anan wajen balle kuma kafin in fito ma sai da Hajiya ta bani abinci naci, ke kawai nazo gani dan bazan iya jira har sai kin koma gida kafin in samu damar kallon wannan kyakyawar fuskar taki ba tashi muje wajen nan babu dad'in zama sam!"
Ya fad'a a yayinda ya kai yatsar shi ya lakaci gefen kuma tun ta,

"Ina zamu kuma?"

"Kaiki zanyi in siyar dake"

"To ni ai nazo cin abinci ne anan yunwa fa nike ji!"

"Naga alaman hakan shi yasa nake son in kaiki inda zakici abincin a tsanake ba nan wajen da yake da hayaniyar mutane da yawa ba,
Yama zaki zauna cin abinci anan bayan ga maza nan da yawa duk sai kallon ki sukeyi,
Baki san hakan yana da had'ari ba ai baima dace ki zauna kina tauna abinci a bakin ki maza na kallon yanda bakin naki ke taunar abincin ba dan ba kowa bane yake da tsarkakakkiyar zuciya ba, kenan haka kike zuwa nan kullum da sunan cin abinci? "

K'asa yayi da murya sosai ta yanda bai zama lallai taji mai zaiceba kafin ya k'arasa maganar shi da cewa,
"Yarinya baki san wani jarababben daga kallon yanayin yanda bakin ki ke motsi ma kad'ai yana iya samun gamsuwa ba"

"Na'am me kace?"

"Cewa nayi kenan kullum anan kuke zuwa cin abinci?"

"Ah ah ba kullum ba lokaci lokaci dai"

"To na kashe zuwa wajen nan da sunan cin abinci daga yau,
Bazan hanaki kizo kiyi take away ba amma dai ban yarda kizo ki zauna kici anan d'inba kinji na fad'a miki"

"To saboda me zaka ce haka ai bani kad'ai nike zuwa ba, in ma kallo ne ba gashi nan ba kaima daga zuwan ka duk kabi ka d'auke hankalin yan matan wajen kalle su ka gani fa dukan su idanuwan su akanka yake ni ban san ma mi yasa ka biyoni nan ba"
Ta fad'a tana juya idanuwan ta gefe da gefe harda wani tura baki,

"Koma ke da waye ni dai ina rokon alfarma kiji tausayina ki rufamin asiri ki dena zaman cin abinci a wajen nan,
Nifa inda hali ma gara ki dunga zuwa da abinci daga gida kinga nifa in abun ya zama haka zan ma Hajiya magana ta d'auki wata sabuwar mai aikin da zata dunga tashi da sassafe tana had'a miki abincin da zaki dunga zuwa dashi makaranta tunda naga aikin yana son yama Aunty Larai yawa amma bazan yarda kici gaba da zuwa irin wajen nan cin abinci ba nagode Allah ma kun kusa kammala karatun madai mutum ya huta "
Yana karasa fad'in hakan ya mik'e ta bayan kujeran ta ya koma ya tsaya kafin ya sanya hannayen shi yaja kujerar da take kai din a zaune baya,
Zabura tayi ta mik'e tsaye daga zaunen da take dan tasan dan k'ank'ani ne cikin aiyukan da zai iya aikata wa wato yace zai kama kafadar ta ya mik'ar da ita tsaye ko kuma dai wani abun makamancin hakan,

"Ina zaka kaini to?
Nidai ban zuwa ko ina gida kawai zan tafiπŸ˜’"

"Ni kuma nace ba gida ba wani waje zaki rakani"

Jakarta ya mik'a hannu zai d'auka tayi saurin d'auke Jakar ta rataya a kafad'a,
"Ok muje to tunda bazaki bari in rik'e miki Jakar ba"

Karasawa inda su Maryam suke sukayi,

Sultana ce ta fara gaishe shi da cewa, "barka da zuwa Brother ya hanya?"

"Alhamdulillah Sultana ya kike?"

"Ina lafiya! "

Ganin haka yasa sauran yan matan dake wajen suma suka dunga tasowa suna mik'o gaisuwa bai damuba haka yaci gaba da amsa musu sai dai tsaf yake lura da yanda yanayin fuskar Meenal ya canza dan haka sai kawai ya waske da cema Sultana d'in idan ta gama abinda takeyi tazo su tafi,

"Ah ah Brother kuje kawai nida Maryam zamu wuce unguwar Malamai ne daga nan zamuyi amfani da motar Meenal din kai sai ka wuce da ita"

"Alright to ba damuwa sai kun dawo muje koh!

"Nidai dan Allah ka tafi nima zan bisu muje can din tare kaji"

"Ai kinji abinda Sultana tace dan haka kodai ki taka mu tafi ko kuma in nad'e hannun rigana in miki irin d'aukar da akema Jarirai, wai bana ce miki saboda ke na shigo cikin school din nan yauba, to wallahi in ma bakya so su kawayen naki su gane alaqar dake tsakanin mune gara tun wuri ki bini mu tafi salin alin sab'anin hakan kuma bazan bar nan ba har sai na tabbatar da nabar musu labari mai armashin da zasu dad'e suna tattaunawa akai kafin in tafi,"

Bata da wani zab'i wanda ya wuce ta bishi d'in,

Dan haka badan taso ba haka su Sultana suka musu rakiya har zuwa inda yayi parking motar shi,
shi da kanshi ya bud'e mata gidan gaba ta zauna kafin ya zagaya ta gefen driver yaja motar suka fice daga cikin school din.

Maryam da Sultana dake tsaye a wajen har yanzun sun juya da niyyar komawa dan akwai sak'on da Maryam zata amsa kafin su wuce juyawar da Maryam tayi idonta ya sauka akan Bash jingine da motar dake gefen su kad'an hannuwan shi rungume a k'irji idanuwan shi kyar a kansu,

Basarwa taso tayi ta nuna kamar bata ganshi ba sai dai kuma shi d'in duk da halin shock d'in da yake ciki na ganin Meenal hakan bai hana shi kiran sunan ta ba domin koba komai yana buk'atar tabbatar wa akan abunda idanuwan shi suka gano mishi,

"Maryam"
Ya kira sunan yana takowa da d'an sauran karfin daya rage mishi zuwa inda take,

Bata iya amsawa ba har ya cin musu,

"Maryam fad'amin dagaske Meenal ne idanuwa na suka gane min ko wata daban?
Meenal na gani yanzun nan fa tare da wannan yayan nasu me nene ma sunan da ake kiran shi dashi?
Uhmm uhmm mai jama'a, eh mai jama'a shifa, wallahi da idona na gansu yanzun nan ya bud'e mata murfin mota bayan ta shiga shi kuma ya shiga gefen direba yaja motar suka tafi,
Mai yake faruwa ne? Dama shine mijin da aka aura mata ko ya abin yake shin ko dai gizo ne ko kuma mai Kama da ita na gani?
Fadamin dan Allah kicemin ba ita bace mai kama da ita na gani ayau, inba haka ba mai zaisa inga Meenal anan bayan an tabbatar min da cewa wani d'an uwanta soja aka aura mata kuma ba anan zasu zauna ba?miye had'inta da mai jama'a kuma? "

Juyawa tayi bayan ta damk'o hannun Sultana da niyyar subar wajen ganin yana shirin janyo hankalin mutane kan su,
Da sauri yasha gaban su yana had'a hannuwan shi,
"Please Maryam dan Allah ki tsaya kibani amsar tambayoyi na kaina ya d'aure da yawa,
Meenal fa idanuwa na suka gane min bayan tsayin shekarun dana d'auka ban sata a cikin kwayar idona ba"

Sultana ce ta katse shi da cewa,

"Da kata dan Allah bawan Allah ya zaka zo ka taremu a hanya cikin mutane haka, duba kaga yanda kasa jama'a ke kallon mu in ma maganar da kake son yi da ita ya zama dole ai ba anan ya kamata ka tsareta da tambayoyin ka ba sai dai bari ni in sauk'ak'a mata wasu rud'anin da kake ciki a yanzun,
Eh ita Meenal din dai ita ka gani sun fita tare da mijin da zata aura a yanzun duk yanda akayi alamu sun nuna cewa kana cikin samarin ta da aka kasa a shekarun baya, to ko yanzun din ma bana tunanin zaka samu galaba ko nasara a kanta domin kamar yanda wancan karan d'an uwanta ne yayi nasara a kanka wannan karan ma hakan ce zata k'ara faruwa dan haka gara ka shafama kanka lafiya Kaje kaci gaba da zama da yar matar ka ina ga hakan zaifi,
Meenal ba rabon ka bace shi yasa take ta kucce maka,
Maryam idan kin gama abinda kikeyi muna iya tafiya."

Kusan sumewa yayi a tsaye bai iya motsawa ba har suka kule ya dena ganin su,

"Ke wai waye wancan d'in?"
Sultana ta tambaya,

"Bash ne bash din da nace muku mun had'u dashi s kofar doka shine tsohon saurayin Meenal kafin auren ta da Sarki,
Ban san meya shigo yi cikin makarantar nan yauba gashi duk addu'ar da mukeyi na kar Allah yasa ya bayyana to yau dai gashi ya ganta, na kuma tabbatar da cewa wallahi sai ya nemo ta"

"Bash.... "
Sultana ta maimaita sunan tana jin jina kai,

"To ai ya riga ya makaro ko yanzun muke da nasara akan duk ma wanda zai bayyana bayan shi,
Domin dai koda bata riga ta furta ma AK cewa itama tana son shiba ina tabbatar miki da cewa akwai son shi a cikin zuciyar ta dan haka kowa ya iya allon sa ya wankeπŸ€·πŸ»β€β™€οΈ"

Basu b'ata lokaci mai tsayi a makarantar ba suna amsan abunda Maryam zata amsa suka bar makarantar, kamar yanda shima Bash yabar makarantar ba tareda yayi abinda ya kawo shi ba, dan ganin daya ma Meenal yasa komai ya kwance mishi,

Tsayin shekarun nan yayi hakuri da sonta ne kawai tun daga ranar da akace an d'aura mata aure da wanin shi,
Ba k'aramin gwagwar maya yayi tsakanin shi da zuciyar shi kafin ya samu damar mai da son Meenal din can k'asar zuciyar shi ya nemi waje ya birne son nata a ciki ba,
Yasa wuya yasha jinya yasha fama har sai da yayi jinya na watan ni saboda yanda batun auren ta ya mishi mugun bugun da dole ya kaishi k'asa war was,
Yaci buri akan ta burin auren ta wanda a wancan lokacin shine buri mafi girman da yake kwana ya kuma tashi dashi a cikin zuciyar shi, sai gashi kwatsam wai bai tashi jin cewa ita d'in za'a d'aurama aure da wani ba har sai ranar d'aurin auren,
Da badan yana da tabbacin cewa ita ma kanta bata da masaniya ba toda tabbas zaice babu namijin da aka ma mummunar yaudara irin shi,
Saurayin daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login