Showing 21001 words to 24000 words out of 190771 words
yajamin!"
Ta bata amsa tana tab'e baki,
"Ban gane yaja miki ba, miye had'aku?"
Meelat ta kara tambaya.
Dariya Maryam keyi kafin tace "wa yaga qawata a gaban Mr Emma tana rokon shi"
"Ke ai wallahi bama zani ba balle ya samu damar fadamin maganar banza irin yanda ya saba yima wadanda ya raina"
"Kingani koh aina fad'a miki da bakiyi mata ba to tsaf zata murje idone tace bazataje ta roke shiba"
Cewar Meelat,
"Lah wai Maryam dan Allah kin min da gaske? Kai masoyiya allah ya jefa min ke a cikin aljannah"
Ta fada fuskarta na washe wa,
Knock knock karar glass din window din gefen mai zaman banza,
Dukan su suka maida hankali a wajen,
"Kungani koh wallahi masu motar can ne ai dama nace muku mu suke bi gashi kuma kun gani๐คท๐ปโโ๏ธ"
"Kisan yanda zaki damk'o mana wuyar koma waye zuwa cikin shagon nan mu tatse mishi yan canjin dake jikin shi, Allah dai yasa ba yaron oga bane aka aika ya biyo bayan mu, aiko da na mishi rashin daraja wallahi"
Inji Meenal,
"Kee a wani dalilin zakice in kula shi bayan yanzun kika gama tunamin cewa ina da nawa mijin auren a hannu, in haka ne ai kece yan zun for sale"
Zuge glass d'in gefen nata Maryam tayi zuwa k'asa, kafin tace komai wanda yayi knocking din ya riga ta da cewa,
"Assalamu Alaikum yan mata kuyi hakuri please Allah yasa dai ban katse muku hanzari ba?"
Ya furta fuskar shi cike da fara'a,
"Eh to kusan hakan dan muma uzuri ne ya kawo mu nan gashi kuma ka tsaida mu Allah yasa dai lafiya?"
"Lafiya kalau Alhamdulillah, nace to ko za'a dan min alfarma a cikin lokacin naku ad'an d'iba min kad'an a ciki dan jin mai ke tafe dani? "
Maimakon Maryam ta bashi amsa sai ta juya fuskarta gefen da Meenal ke zaune tana faman latsa waya tamak'i d'agowa ta kalli ko waye gaba d'aya,
"Bebs kunji me yace"
"Meenal mu shiga daga ciki sai mu basu waje su tattauna koh"
Meelat tace a yayin da ta bud'e kofar motar ta fice hakan ne kuma yaba itama Meenal din damar ficewa daga motar da jakarta a hannu,
Koda suka fita a motar babu wacce ta kalli gefen da yake tsaye shida abokin shi da shima ya k'araso wajen, har suka shige katafaren shagon na Ya Mashkur,
har lokacin kuma gyalen na Meenal na nan saman kai ta d'aura shi ta mishi yafi irin na matan aure sab'anin d'azun da take tuk'in ko gyalen ma babu a jikin ta kuma ta sauke glass din gefen ta duk da bawai duka ta sauke ba amma tsaf wanda ke waje zai tantance ko wacece ita,
Suna shigewa cikin shagon Meelat ta fara maka mata harara,
"Ke wannan iskancin kuma fa kin wani kama gyale kin d'aura akai uwa wata matar mamaci, kefa ba matar aure bace yanzun, ko kina nufin a haka da zabga zabgan gyalen da kike yafawa ne zamu cinye sauran lokacin daya rage min a matsayin budurwa kafin zuwan lokacin bikin,
Gaskiya wannan cin amana ne wallahi dan haka daga nan gidan Hajiya zamu wallahi dole kima canza dressing kawata, duk tsoffin kayan ki kyauta zamuyi dasu ko kin manta wai ke din har yanzun budurwa ne? Kina wannan shigar fisabilillahi waye zai gani ya yaba?"
Shekek'e meenal ke kallon ta,
"Me kike nufi?
Oh wato ga yar iska tunda aurena na ya mutu sai in koma yawo da kaya half naked koh?"
"Karkimin iskanci yaushe nace kiyi yawo halfnaked, amma dai kin san dole zaki komayin normal dressing ba kamar shigar da kikeyi lokacin da kike da aure ba, kar dai ki manta yan matan cin da kika rasa a baya shi zakiyi yanzun, ki gane mana so nike inga kina shiga irin na manyan yan matan da in maza suka gansu dole gaban su ya fad'i ai ba sai kinyi shiga kin fidda tsaraici bane yake nufin kin kai karshen wanka hajiya ta, shiga mai daga darajar ya mace nike nufi,"
"Mtwss yar rainin wayau kawai to in kinga dama daga yau karki k'ara fita dani tunda ban iya sa kaya ba"
Tana gama fadar hakan tayi gaba tabar Meelat a tsaye a wajen,
Bayau ne ranar farko da suka fara zuwa shagon ba domin kusan kaf yaran shagon sun san su,
Dan haka tuni ta shige gaba ta fara duba kayan da suke ta gabatar mata wadanda suke ganin zasu bada kala in aka fitar dasu a matsayin anko, Meelat na taya ta, har suka gama zab'en wadanda suke buk'ata kuma Maryam bata fito ba, shigowar Ya Mashkur ne kuma yasa suka k'ara shantakewa dan Meenal bata tuna cewa tana jin yunwa ba sai da ta ganshi, da yayi maganar ya aika a siyo musu abinci kuma sai cewa tayi ah ah bafa abinci ba domin a hanyar da suke zuwa ne ta hangi wani waje da ake ta faman gashin Hajiya kaza kuma ranta ya biya sai dai kuma bata tsaya bane dan ba a hannun ta wajen yake ba dole sai taje gaba tayo u turn in tana son zuwa wajen dalilin da yasa ta yanke shawarar biyawa kenan in zasu koma gida,
Kuma wallahi a ribar da Ya Mashkur din zaici dasu na siyayyar da sukayi zata fanshe,
"To me kike sonci uwar malam?"
"Kaga Yayan mu Allah kaza naga ana gasawa a can k'asa kafin mu iso nan shi nike son mu siya idan zamu koma"
"Kawai kice kwad'ayin ne ya motsa zaki sauke shi a kaina"
"To dan Allah in bamu tambayeka abunda muke so ka mana ba wa muke dashi anan da zamu nema a wajen shi?"
"Naji karki min wata doguwar farsafa in kun tashi tafiya zan baku"
Hannun ta tasa cikin juna tana dan jujjuya jikin ta irin yanda yara keyi in suna so a musu abu kafin tace,
"Nidai Allah Ya Mashkur ka bani kawai a hannuna kar in mun tashi tafiya ka manta ko kuma ni inji kunyar tuna maka"
Ta k'arasa fada tana dariya k'asa kasa,
"Oh Aminatu badai zaki tab'a canza waba wallahi, wai ma karkiji kunyar tambaya, wai kece zakiji kunyar amsar kud'i a hannuna ai ina ganin in ban baki kudin nan ba kina iya bina bashi sai na biya kafin in huta da mitan ki,"
Dan haka sai yasa hannu a aljihu ya ciro wallet din shi, dubu goma ya kirga kafin ya miko mata,
"Zasu iya ko a kara?"
Sai da ta mik'a hannu ta amsa kafin ta furta cewa.
"Ba komai yayan mu ko basu cika ba ai mu sai mu cika Allah dai ya k'ara arziki Allah kuma ya baka ikon k'ara aure wallahi"
Ta k'arasa fad'a da dariya, shima dariyar kawai yayi yasa kai ya wuce dan yasan magana kawai take son sashi.
Duk abunda sukeyi Meelat nacan ana buga mata lissafin kud'in kayan su,
Karasawa wurin ta Meenal tayi
"Wai kinga Maryam shiru dan mak'iyin ubanta har yanzun bata sallame suba balle ta shigo,"
Wayarta ta ciro daga cikin jaka ta dannama Maryam din kira,
Tana d'auka ta rufeta da sababin cewa,
"Ke wai me kikeyi ne a wajen har yanzun mun riga mun gama zab'a fa kuma wallahi baki isa kizo kice mana wanda muka d'auka basuyi ba tunda kika k'i zuwa ki tayamu zab'en"
"Yi hakuri gani nan zuwa"
"Na dai fad'a miki ki shak'o mana wuyan su suzo su biya kudin biyo bayan mu da sukayi koh? To wallahi karma ki fara ki shigo wajen nan ke d'aya atoh"
Sai gashi kamar jiran kiran nata Maryam keyi domin cikin kankanin lokaci sai gata da mazajen nan biyu a bayan ta d'ayan kusan a jere suke tafiya da ita shi kuma d'ayan yana bin su a baya,
Gefe meenal ta koma tana musu kallon kasan ido,
Bafa yara bane dan zama mu iya kiran su da suna magidan ta dan sun d'an fara manyan ta sai dai alamu sun nuna cewa dukan su biyun idon su a bud'e yake da ganin su kaga mayun mata,
"Aiko zakuci uban ku wallahi wato kun hango kyawawan yan mata wanke hannu ka tab'a shine kuka biyo bayan mu, to ai ba laifi dan motar da naga kun tuk'o ta isa shedar cewa kun tara"
Cewar meenal kasa kasa tana murmushin mugunta,
Suna k'ara dosowa inda suke a gaban kanta ita da Meelat da style ta sauke gyalen ta daga saman kai zuwa kafad'a ta yanda babu wanda zai gane cewa da gangan tayi hakan, nan danan kuwa ta aro murmushi ta yafa a fuskar nata,
"Wai har kun gama siyayyar da wuri haka?"
Cewar wanda suka jero tare da Maryam ita kuma Maryam din kayan take dubawa tana yaba kyan su,
Dan haka Meenal ce ta amsa mishi da cewa,
"Eh wallahi yallabai, mun kammala fa, kayi hakuri na katse muku hira bana son mu gama bata zo ta duba bane shi yasa na kirata ina fatan ban shiga hakkin kaba?"
"Ah haba dai ai girman kine wallahi aini godiya ma ya kamata in miki na aron kawarki da kika bani"
"Babu komai wallahi yallaibai, Maryam in kin gama dubawan ku biya su kudin su had'a mana kayan mu tafi dan Allah wallahi na gaji zan kuma tsaya in siya abinci a hanya dan bazan iya d'aura wani abunci idan na koma gida ba wallahi"
Daga Maryam din har Meelat kallon mamaki suke mata, ita ko ta wani fuske abunta, daga inda take tana ankare da kallon da d'ayan mutumin yake binta dashi tunda ya shigo kuma baice ma kowa komai ba har yanzun.
"Ah haba ayi haka kuma maza na tsaye subar mata da biyan kudin siyayyar da bata taka kara ta karya ba, ai sai girma ya fad'i, malam ka gama lissafa kudin kayan nasu?"
Ya tambayi yaron shagon dake lissafin kudin kayan,
"Eh na gama"
Wuf tayi ta matsa kusa dashi tana cewa "haba Yayana ya haka daga zuwa kuma zakace zaka biya mana kud'in kayan bayan kasan cewa tunda mukazo shagon da niyyar siyayya dole zamu riko kudin biyan kayan ai, ya kuma zamu d'aura maka wata dawainiya daga had'uwa.
Oh ya Allah jama'a farawa da iyawa yar malam zata fara cin kudin samari tun bata gama iddah ba,
Kuyi hakuri naso page din yafi haka tsayi sai dai kuma kallon film ya d'auke min hankali.
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[8/23, 6:57 PM] Ummiee Zaria: ๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆโ๏ธ๐ฑ
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โ๐ผ
,,, *Page 9*
Mai makon shi wanda suke magana da Meenal d'in ya biya kud'in kamar yanda ya buk'ata, ah ah sai gashi abokin tafiyar shi dake gefe shine ya matsa wajen biyan kud'in ya biya tun su Meenal basu gama nasu muhawaran ba,
Babu b'ata lokaci haka mutumin nan ya lale kud'ad'en kayan da suka siya tsaf ya biya kud'in,
Ita ko Meelat kallon Meenal kawai takeyi cike da mamaki,
Dan batun yau ba zadu iya cewa Meenal itace hatimin nasarar su dan ata dalilin ta sun dad'e suna cin yan kud'ad'e na samari tun kafin auren ta, bayan auren kuma da suka fara karatu duk wanda ya yunk'uro idan suka ce matar aure ne sai ya nemi lab'ewa a tsakanin ita Meelat d'in ko Maryam a haka zasuyi ta musu hidima har sai in sun gaji dasu sanemi hanyar sallama su salin alin,
Kai itafa idan ma tace batayi farin cikin mutuwar Meenal yasin k'arya takeyi sai dai kawai dan darajar dake cikin aure yafi k'arfin ace za'a nuna mad'aukakin farin ciki a fili bayan mutuwar shi,
Amma ba komai tasan cewa yanzun kam qawarta zata samu damar data rasa a shekarun baya na tsaya ta zab'ar ma kanta abokin rayuwar da take ganin ya dace da tsarin ta, hakan nema yasa take ganin wannan lokacin na musamman ne a awaken su da zasu kasance a tare dukan su babu wacce keda igiyar auren wani akan ta balle hakan ya musu shamaki akan wani abun,
To gashi tun daga yau da alama wasar zai fara, idan suka had'a ido sai Meelat d'in ta girgiza kai ita kuma Meenal k'asa kasa take binta da murmushi,
Tsaf aka had'e musu kayan da suka siya yaran shagon suka raka su dashi har mota ko Sallama Meenal bata yarda d'aya daga cikin su tama Ya Mashkur ba dan allah ma sheda ne cewa Allah Allah kawai takeyi akan suyi subar wajen kafin ya fito dan tasan mawuyaci ne idan Maryam ta fad'a ma mutanen sunan su na gaskiya dan haka sukeyi dama batun yau ba in suka had'u da samari irin haka to suna da inkiyar da suke kiran sunan junan su sab'anin ainihin sunayen su na gaskiya.
Har wani ajiyar zuciya ta sauke yayinda taga sun fito daga shagon salin alin ba tareda an samu matsala ba, shiko wancan mutumin da suka shigo tare da Maryam bakin shi ko gajiya bayayi da surutu, d'ayan dai da alama miskiline dan bai iya tanka musu ba sai bayan sun fito ne sannan ya matso inda suke,
"Sannu koh yan mata!"
"Yauwa sannu Maryam da Meelat suka amsa mishi dashi domin ita gwanar ko kallo bai isheta ba saima gaba da tayi abunta bayan ta kulle booth din motar ta da aka sa kayan da suka siyo, ta juya da niyar shiga motar kenan shi kuma ya tare ta da cewa,
"Yan mata nace ba!"
Ya fad'i hakan a yayinda yasha gabanta ya tare hanyar da zata wuce,
D'aga kai tayi batareda ta kalli fuskar shiba ta amsa mishi da cewa,
"Kace me? Oh na manta ban maka godiyar dawainiyar da kayi damu yanzun ba, mun gode fa Allah ya k'ara arziki ya jikan iyaye"
"Ameen nagode da addu'a duk da dai bawai nayi bane dan a gode min d'in ba,
Bama wannan ba shinko zan samu gimbiyar tad'an bani aron lokacin ta In ba damuwa ina son mud'an tattauna,"
Sai da tasa hannu ta gyara zaman gyalenta zuwa saman kai kafin ta bashi amsa da cewa,
"Yar uwata bata gaya maka cewa ina da aure bane hala?"
"Hakan dai tace min da farko kafin daga baya kuma sai ta fad'amin cewa tadai fad'ane kawai amma baki da aure,"
Ya k'arasa fad'a yana kureta da kallo,
Turo baki tayi ita kuma tana juya mishi baya
"Oh da gaske dai baki da auren kenan?"ya k'ara tambaya
"Injiwa yace maka? Nidai ai nace maka ina da aure koh"
"Yanda kikayin ne ya nuna min cewa da gaske d'in baki da aure, dan haka in babu damuwa ko zaki bani dama mu k'arasa zuwa gidan ku, dan gaskiya ina buk'atar magana dake kinga kuma dani dake duka ba girman mu bane mu tsaya muna hira a titi, shine nike ganin ko zaku mana jagora in yaso mu sai ku biyo ku a baya zuwa gidan ku ?
Dan yau nike son komawa Abuja bazan so kuma in wuce bamu tattauna ba gaskiya please ๐"
Kam buhu yau Allah ya had'ani da d'an anace daga taimako shine saboda tsabar maita wato bazai yarda mu rabu anan ba shine yake son lallai sai ya rakamu har gida,
jama'a ina ma laifin yace ta bashi number in yaso koma dai miye alakar ta tsaya a iya waya kawai in yaso sai ta bashi koda number din wayarta da ba kullum take amfani dashi ba,
"Kinyi shiru?"
"Umm umm to aini tsoro nikeji dan mu a gidan mu ba'a barin namiji zuwa wajen mace sai ya nemi izini kaga kuma ni karatu fa nikeyi a yanzun shi yasa ba'a barni na fara tsayuwa da kowa ba tukun"ta k'arasa fad'a tana wik'i wik'i da ido,
"To yanzun ya kenan?"
"Kayi hakuri sai dai muyi waya zuwa wani lokacin idan ka k'ara shigowa ni kuma zan san yanda zamuga juna koda a gidan d'aya daga cikin yayye nane, zaka iya zuwa ka sameni ai"
"Mai zai hana kuwa kin tab'a ganin inda mai nema yayi fushi ne?
Kafin nan dai bari in gabatar miki da kaina,
Suna na Al'ameen Adam Rano, bakano neni amma kuma mazaunin abuja"
"Allah sarki ni kuma suna na Zubaidat Ibrahim amma Ikram ake kirana, kamar yanda ka gani kuma ni d'in yar Zaria ce mazauniyar cikin ta kuma"
"To karmu b'ata muku lokaci ga wannan katina ne dan Allah kiyi kokari idan kun isa gida ki kirani,"
Ya fad'a bayan ya mik'a mata katin nashi ita kuma ta amsa,
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke dan da alama ta tsira.
"Mu zamu wuce nagode da lokacin da kika bani"
"Ah haba Yallabai ai muke da godiya da dawainiyar da akayi damu"
Sai da ya rakata har bakin motar ta ya bud'e mata ta shiga ya kuma maida mata kofar ya rufe sannan sukayi sallama da su Meelat ita kuma taja motar sukayi gaba suka bar su anan wajen suna d'aga masu hannu,
Sai da sukayi nisa da sosai kafin dukan su suka fashe da dariya,
"Kun san abunda ake cema dakyar nasha yafi ace da kyar aka kamani? To wallahi shine ya faru yau, haka kawai mutumin nan zai wani ce wai zasu bimu a baya suga gida kamar wani body guide dina" ta fad'a ta tareda ta dena dariyar da takeyi ba
"Kai Beb wallahi baki da kyau, yanzun yanzun kin wanki mutanen nan kusan dubu d'ari biyu fa, wallahi shi yasa nike son fita dake zuwa waje irin wannan dan zuwan ki alkhairi ne, wai haka dama yace zasu bimu tab lallai ma?"
Jakarta dake gefe ta d'auka ta mik'ama Meelat
din
"duba cikin Jakar zakiga katin daya bani fito dashi kimin gutsi gutsi dashi ki watsa shi ta window"
"Ah haba dai kina nufin ko sau d'aya bazaki kirashi ba?"
Cewar Maryam itama tana dariya.
"Wai hala dai idanuwan ku sun samu matsalar da basa gani da kyau ne? Ku daganin wannan mutumin ai kun san mijin wasu ne wallahi dan tabbas da ganin idon shi bazai yarda ya zauna da mace d'aya a gidan shiba to niko inba bakin iyaye ke bina ba uban me zanyi dashi, mtwss dallah ni karku bani haushi ma"
"Eh ai baki da uban