Showing 54001 words to 57000 words out of 190771 words

Chapter 19 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1546

taka k'afarta ba"
Bai sarara ba yana nuna Meenal da yatsa yaci gaba da cewa,

"Ke kuma saboda tsabar kin riga kin gama raina ni shine nake ta kiran wayar ki kika gagara d'auka saboda baki d'aukeni a bakin komai ba,
shin kin san irin tashin hankalin da kika nemi jefa zuciya ta a ciki kuwa?
In kuna son zaku fita mai yasa ba zaki nemi izini na ba? A ganin ki bazan iya barin duk uzurin dake gabana in dawo gida dan in kaiki inda kike buk'atar zuwa bane? Yanzun fisabilillahi ya kike zaton zanji inda ace wani abu ya sameku a fitar nan da kukayi, kun kama kun fice ni bana gida ita kuma Hajiya tana bacci hakan da kuka aikata dai daine kenan?"
Ya k'arasa jero tarin tambayoyin shi a kansu yana mai kai hannuwan shi duka biyun ya yamutsa gashin kanshi,

"Ya'ya!
Ya'ya please dan Allah ka tsaya kaji, muma fa Allah bamu san zamu dad'e haka ba, kuma ai ba b'ata mukayi ba,
Ba gashi mun dawo da kanmu gidan ba, kawai fa mun d'an fita zuwa wajen siyar da ice cream d'in daka siyo mana jiya ne, kuma ni ban san ranka zai b'aci ba amma kayi hak'uri kaji,
abunda ma duka duka daga gobe dai shi kenan zamuyi komawar mu muma, kuma ai mun so dawowa gida da wuri a hanya nefa muka lura da wata mota dake ta bin mu a baya shine mukayi ta yawo da kyar fa muka samu muka b'acema mai motar"

"Wata mota ta biyo ku a baya kuma?"

Meelat ce ta amsa mishi da cewa

"eh wallahi Ya'ya tun fa a wani shago da muka tsaya zan siya charger wayata dan na manta ban taho da nawa ba shine suka biyomu to mudai bamu kulasu ba, d'ayan yace wai yana son magana da Meenal ita kuma tak'i tsayawa ta saurare shi, kuma wallahi mu bamu hanata tsayawa dasu ba itace dai tak'i ko Sultana?"

"Eh wallahi Yaya sai da mukace mata ta tsaya taji me zaice mata amma tak'i nasan shi kuma yana ta bin mu ne dan yaga inda zamu shi yasa ya biyo mu a baya"
Cewar Sultana,

"Oh wato ma so kukayi ta tsaya ta saurare shi!
Ashe rashin wayan naku yakai har namiji ya tsare ku a titi ku tsaya dashi, ashe kenan data saurare shin kamar yanda kuka so da yanzun kuna can a titi su suna hira ku kuma kuna jiran su gama ku dawo gida, to ai ba laifi gobe ma in kun fita sai ku tsaya da duk wanda ya tare ku a titin tunda haka kuke so, ku shige kuje ku kwanta in kunga dama, in kuma baku tashi kwanciyar ba kuna iya kwana a nan ma in ya muku"

Girgiza kanshi kawai yayi, sai kuma yayi gaba ya shige cikin falon ya barsu nan a tsaye, dan in yaci gaba da tsayuwa a wajen to dukan su sai sunji ba dad'.

Kallon kallo suka farayi a tsakanin su bayan shigewar su ciki,

Kafin Maryam ta d'aura hannun ta d'aya a kirji bayan ta sauke doguwar ajiyar zuciya ne tace

"oh Allah mun sha da kyar, Allah nayi zaton zai d'an faffalla miki mari koda biyu ne a yanda naga ya d'aure fuskar nan, to dai anyi na farko anyi na k'arshe gobe kam ko ceton rai zakujeyi a wani wajen sai dai ince muku Allah ya bada sa'a a dawo lafiya"

"Ke wai kin tsorata da fad'an da yayi ne? Tab ai wallahi ko gobe sai mun fita koh Bebs?"
Ta fad'a tana mai da kallon ta kan Meelat,

"Eh kekam zaki fita amma wallahi nidai babu ruwa na, dan nasan yanzun haka sai ya fad'ama mijina cewa munje yawo kina ganin saboda kar ya kira wayata yaji a alamar muna wani wajen ne ba gida ba shi yasa na kashe wayar gaba d'aya, to tsakani da Allah muna shiga ki k'ara bashi hakuri a toh"

"Ai kuma sai kuyi"
Cewar Meenal

"Amma Sister mai yasa kikayi mishi k'aryar cewa wani ne ya biyo mu? kunga duk yanda ya damu kuwa😕?"
Cewar Sultana,

"Zauna a wajen to yasin da bamu ce mishi haka ba da har yanzun muna nan muna jero mishi dalilan da yasa mukayi daren, amma ba gashi yanzun harya gama fadar nashi ya wuce ciki ya barmu ba ku muje ciki please kafin mu k'arayin wani laifin kuma,"

"Tsaya Sister wai wannan d'in shima yayanki ne? Gaskiya dai yana da kulawa wallahi duba kuga duk ya damu kar wani abu ya same mu" Sultana ta k'ara tambaya.

"Yayana kuma?😒" Itama Meenal ta tambaya,

"To ba gashi naga kuna kama dashi ba, ai naga sauran Yayyinki da Baba Adamu ya nuna min d'azun bakya wani kama dasu sosai amma shi da ganin shi an san d'an uwan kine"

"Ke bafa yayan ta wanda suka fito ciki d'aya bane taubashin tane! ba d'azun kinji muna maganar mota ba, to shine wanda yayi kyautar motar da muke magana ai"
Maryam taba Sultana amsa tana dariya,

"Miye *taubashi* kuma?"
Sultana ta k'ara tambaya.

"Cousin dinta ko ince miki abokin wasa kamar yanda kuke keda ita, kinga kamar yanda Maman ki take dasu Baba Auta haka shima baban shi yake da Mommy Hauwa shi yasa kikaga suna kama in kin lura ai zakiga dukan su fuskar kakar su Hajiya suka d'auko wacce muka dawo da ita d'azun kinga kuma ai ko ita Maman Meenal din da Hajiya take kama itama"

"Wai dan Allah da gaske shine kuke hirar shi d'azun wanda ya bata wannan motar yau d'in nan?"

"Shifa! Kin ganshi zazzafa koh,Mai Jama'a ake ce mishi saboda tsabar farin jinin da Allah ya mishi sai ma kinga yanda yan mata ke suma a kanshi kuma wai a hakan yar uwar ki ke kushe shi, kema da kikazo yau kika fara ganin dramar su tsakanin ki da Allah zaki cemin baki fahimci komai ba🤔 tsakani da Allah ko abun da ya aikata yanzun ai ya tona asirin abinda ke cikin zuciyar shi amma ita yar uwar ki babu abunda take ganewa sai karatun likitanci🤨" Meelat ta fad'a tana matsawa gefe, dan a kusa da Meenal take ta kuma san halin mutuniyar,

"La'ilah ha'ilallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun nan Meenal wai dama duk zakalkalewar da kikayi d'azun wannan kyakyawan halittar kike kushewa? Kai amma dai da badun kar kiga zakewa taba da nace rashin rabo ne ke bibiyar ki, ina laifin wannan yace ma mace yana son ta ai da gudu zaki amsa shine ke kike wani jan aji! Zo Abuja kiga yanda yan mata ke neman irin su da kud'in su da kyau da ilimi ga kuma gata amma basa samu,"

Tunda Meelat ta fara soki burutsun zancen ta dama Meenal tayi gaba, bayan ta suka bi bayan su kwaso ledojin da suka bari a cikin Motar,

Itace ta fara shiga falon, dan haka tana shiga sai ta nemi waje ta zauna a gefen kujerar da yake zaune,
D'aya d'aya suka shigo duk wacce ta shigo kuma sai ta mishi gaisuwar da basu samu damar yi mishi ita a d'azun ba,
Shiko a takaice yake amsa musu da cewa "lafiya lau,"

Sad'af sad'af suka sulale suka wuce ciki suka barta dashi a falon,

Tunda ta zauna ko gefen da take zaune bai yarda ya kalla ba, hannu wanshi dai duka biyun suna saman kanshi wanda ya duk'ar yana kallon k'asa,

"Ya'ya dan Allah kayi hakuri, kaga dai d'azun nace ma Hajiya mun dena fad'a yanzun kuma in taji ai dariya zata mana wallahi, nidai tunda kace baka son muna fitan ma to gobe zamu jira har sai ka dawo sai mu fita tare kaji?"

Dago kanshi dake duk'e yayi yana binta da kallo idanuwan shi a k'an k'ance,

"Oh kun ma shirya wani fitan a gobe kenan?"

"Eh mana amma ai bazamu wani dad'e sosai ba zamu dawo da wuri I promise"

"Meenal "
Ya kira sunan ta,

"Na'am" ta amsa dashi tana wasa da zoben dake yatsar ta,

"Meenal kina jin tausayina kuwa?"

"Eh wallahi sosai ma nikejin tausayin ka"

"Karya kikeyi!"

"Allah kuwa da gaske"

"To me yasa kika fita bayan kin san dole zan dawo da wuri saboda ke?, amma kuka fita harma wani sakarai ke bin ku"

"To aini ban san zaka dawo ba, kuma mu bamu san cewa dare yayi haka ba"

"Meenal"

"Uhumm" ta k'ara amsawa,

"Meenal Zuciyata zafi take mun"ya fad'a bayan yakai hannun shi saitin da zuciyar take ya danneta da d'an karfi,

"Baka da lafiya ne dama?"

"Nima ban san ko wani irin ciwon ke damuna ba amma dai naji ba dad'i da naji cewa wani yaso tsaidake dan yayi magana dake, bai hak'ura ba kuma shine har saida ya k'ara bin bayan ku, to idan da mugune ya samu damar da zai cutar dake kuma fa ya kike tunanin zanji,"

Shek'ek'e take binshi da kallo dan ba wani gane abunda yake cewa takeyi ba,

Rik'o hannun ta suna kallon juna ido cikin ido, kafin dakyar ya fizgo maganar dake cikin bakin shi,

"Meenal ban san me yake faruwa dani ba, amma tabbas inajin babu dad'i aduk sanda na nesan ta kaina dake,
Zuciyata takan kasance a kuntace idan na ganki a cikin damuwa komai k'ank'an tanta kuwa,
Ina jin matsanan cin farin ciki aduk sanda naga murmushi kwance akan wannan kyakyawar fuskar taki, ki fad'amin me yake faruwa dani Meena.



*Ummiee ce*✍🏼
[9/4, 6:16 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️
*BOOK 2*

*PAGE 20*


Cigaba da kallon shi tayi ba tareda tace komai ba,

"Tashi kije ki kwanta dare yayi!"
Ya fad'a hakan a yayinda ya saki hannun ta daya rik'e tun d'azun,
Mik'ewa yayi ya wuce wajen kofar falon ya rufe da makulli ya kuma kashe TV dake aiki dama sauran kayan wutan dake falon,
Bai yarda ya kalli inda take ba ya wuce d'akin shi yana shiga ya kullo kofar,
Ita ko da kallo kawai taci gaba da binshi tun tashin shi a wajen har saida ya k'ule ma ganin ta sannan ta d'age kafad'un ta, alamun ko a jikin ta itama ta tashi ta nufi d'akin dasu Meelat ke ciki, a zuciyar ta take cewa k'ila da gaske dai Hajiya keyi da tace yana da aljanu wallahi🤔.

Suko iyayen gulma tun bayan barin su falon suna shiga cikin d'akin ledojin hannun su kawai suka ajiye suka dawo bakin k'ofar suke jeru uwa kujerar roba da ake d'aurawa d'aya dan d'aya domin duka ukun haka suka jera Maryam ce a k'asa ta lek'o kai sai Meelat sai Sultana a saman su sun kasa kunne da zuba idanuwa suna kallon abunda ke faruwa a cikin falon duk da ba wani jin abunda shi AK yake cewa sukeyi ba,

Suna ganin shi ya shige itama kuma ta nufo d'akin sai sukayi hanzarin barin bakin k'ofar kowaccen su ta samu waje ta zauna suka kama bud'e ledojin da suka shigo dashi suka wani basar kamar basu ne suka gama lek'e yanzun ba,

Da Sallama Meenal ta shigo itama ta nemi waje ta zauna,
Maryam ce ta mik'a mata leda guda d'aya.

"Ga nashi ki mik'a mishi waya sani ma ko k'ila baici komai ba tunda ya dawo yana gadin dawowar mu"

Babu musu Meenal ta amshi ledar ta juya ta fice daga d'akin,
Kofar d'akin shi ta tsaya sai da takai hannun ta tayi nocking kafin ta had'a da sallama tana jiran ya bata izinin shiga,

"Bud'e ki shigo!"
Ya fad'a bayan ya amsa Sallamar nata yana daga zaune a gefen gadon shi dan tun bayan shigowar shi d'akin bai iya tab'uka komai ba zama kawai yayi ya rasa ina zaisa kanshi,

Shi baima san meya hau kanshi d'azun ya zaunar da yarinyar nan yana neman tona ma kanshi asiri a gabanta,
Yanzun nan dan Allah daya fad'a mata gaskiyar abunda yajeki akanta kamar yanda kullum su Yusuf ke zugashi akan ya bayyana mata Soyayyar da yake mata ai yasan wani fassarar daban zata mashi,
Wallahi tanama iya cewa dan ya mata kyautar mota ne ko kuma tace dama ba dan Allah ko da zuciya d'aya ya bata motar ba,
dan haka zai jira lokacin daya dace sai ya fitar mata da abunda yake cikin zuciyar shi amma ba dai yauba.

Sai da ta k'arayin wani sabon sallaman bayan ta shigo,

"Ameen Alaikis Salam"
Ya amsa kafin ya d'ago kai yana k'are mata kallo,
"Ya akayi? Ba cewa nayi kije ki kwanta ba me kike nema anan kuma? Wato kin dai rantse sai kin shigo min d'aki sannan hankalin ki zai kwanta, to sai ki d'auki abinda kike buk'ata ki wuce ki bani waje bacci zanyi"

"Ummh Ummh ba komai fa dama abinci na kawo maka dan Allah kaci kasha magani kuma kafin ka kwanta kaji!"

"Kinga alamun yunwa a tareda nine? da zaki kawo min abinci ? Inda da gaske kin damu dani har haka ai da bazaki kwashi kawayen ki ku fice yawo ba, waye ma ya siya muku abincin?"

"Allah kuwa babu wanda ya siya mana da kud'in mu muka siya, kuma kaga ai su bak'i nane kuma idan mutum yayi bak'i kamata yayi ya karrama su shi yasa nima na fita tare dasu muka d'anyo siyayya,
kuma ai na duba kan dinning table banga alaman kaci komai ba, nidai kaci dan Allah kaji, ai dai na baka hak'uri nace maka bazan k'ara zuwa ko ina ba sai da izinin ka"
Ajiye ledar tayi da sauri ta juya ta fice daga cikin d'akin kamar wacce tayi mantuwa, bai motsa daga inda yake ba harta k'ara dawowa d'akin hannun ta d'auke da wani wani faranti madai daici wanda ta d'auro kwalin 5alive sai gorar ruwa mara sanyi sosai da kofi guda d'aya akai,

wani stool d'in data gani a gefen gadon shita jawo ta d'aura farantin akai sannan ta fidda abubuwan dake cikin ledan suma ta jera su a gefe,

"Wai Ya'ya kai baka shan ko wani drink ne sai na yayan itatuwa? Babu coca cola ba fanta ko maltina babu a cikin pridge din gidan nan sai su 5 alive exotic da wadansu daban"

shi dai da kallo kawai yaci gaba da binta ba tareda ya bata amsar tambayar taba,
harta gama ta juya da niyyar barin d'akin ya ruk'o hannun ta,

"Ni dawa zamuci wannan abincin da kika jera ne wai?"

"Kai kadai zakaci shi mana nima zanje muci tareda su Meelat a d'akine"

"Kwashe su ki wuce dasu ku k'ara a naku kuci ni ban saba cin abinci ni kad'aiba, ba kuma zan fara yau ba shi yasa ma jiya na zauna naci tare dake shine zaki kawo ki wani jeramin su a gabana kiyi tafiyar ki"

Da mamaki take kallon shi,
Dan Allah jama'a ina laifin wanda ya kula dakai ya kawo maka abunci kaci? Ita da tayi mishi abun arziki mai makon ya gode mata shine yake kok'arin kushewa! Ita fa duk tana mishi ne saboda ganin da tayi ranshi ya baci da fitar da sukayi inba haka ba fisabilillahi miye had'in ta dashi da zata wani biyoshi da abinci har d'aki tana lallab'a shi kamar wani yaron goye,
Daurewa tayi tana cigaba da kallon shi take cewa.

"To da kafin muzo nan kai dawa kake cin abincin ba kai kad'ai kake ciba?"
Ta tambaya tana tura baki, dan itafa a k'age take tayi tabar d'akin ta koma wajen su Meelat dan fitan da tayi d'auko mishi ruwa sai da ta lek'a tace musu su jirata ta dawo sai suci abincin tare shine shi kuma yake wani son ya hanata komawa,

"Da baki zoba a restaurant nike cin abincina ko kuma in siyo inzo muci da Mansoor in kuma d'aya daga cikin su Musty na nan tare muke ci yanzun kuma da kike nan jiya munci tare kinga kenan yau da gobe ma duk tare ya dace muci kafin ki koma koh? "
Ya k'arasa fad'a yana d'age mata girar shi guda d'aya.

"To amma Yaya nace masu Maryam fa su jirani har in dawo sai muci tare dasu😒" ta furta hakan a shagwabe,

Jawota yayi ya zaunar a kasan carpet d'in dake d'akin bayan ya mik'e tsaye,
sauke abincin data jera akan stool d'in yayi ya mai dasu kasa kan carpet ,

"Bismillah kici abincin nan inhar kina son barin d'akin nan in kuma ba haka ba tsareki zanyi wallahi"
Ya furta yana kallon ta fuskar shi a daure babu alamun wasa,

Badan taso ba haka tasa cokali da dunga diba tana cusama cikin ta,dan tasan tunda ya fad'a tofa tsaf zai aikata dan haka gara su rabu lafiya, gobe ma ai rana ne da bata d'auko abincin ta biyoshi dashi har cikin dakin ba ai da bazai samu damar yin mata wannan mulkin mallakan ba.

shima gyara zama yayi yaci gaba dacin abincin da kyau yanajin nishad'in hakan a cikin zuciyar shi, ita ta fara tsame hannun ta daga abincin alamun ta k'oshi amma duk da haka bai bata damar tashi ba har saida ya kammala tsaf tukun,

"Muje in rakaki kikai kayan kitchen sai kije ki kwanta"

"Zan iya kaiwa ni d'aya fa!"

"Ai nasan zaki iya din amma kuma na buk'aci yi miki rakiyar"
Shi ya tattara inda sukaci abincin ya rik'o farantin a hannun shi duk da taso ta amsa ya hanata, bai damu da samun su Meelat da yayi zauna a falon sun kunna Tv suma suna cin abincin ba, illah ma d'auke kai da yayi sai da ya rakata har kitchen d'in suka wanko hannu, sannan ya fito ya barta a kitchen din ya koma d'akin shi, yana shiga wanka ya farayi yayi ya kuma d'auro alwallah yana fitowa ko mai bai shafama jikin shiba turare kawai ya d'an feffesa sai kuma ya Sanya kayan bacci ya gabatar da shafa'i da wuturi yana idarwa ya kashe wutar d'akin yabi lafiyar gado,
Asuba ta gari jikar Hajjaju🥰.

Ita ko kasa fitowa da wuri tayi daga kitchen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login