Showing 114001 words to 117000 words out of 190771 words

Chapter 39 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1587

da har yanzun tana nan da cikakken darajarta matsayin cikakkiyar budurwa, sab'anin yanzun da dole sai an danganta da sunan bazawara, shiru tayi tana tuna irin yanda AK ya dunga tafiyar da ita cike da tsantsar kulawa kafin ya furta mata kalmar soyayya haka ma yanzun yanda baya iya boye adadin son da yake mata dan ma dai ita da take dan kakkaucewa shima da yake matsayin matashin saurayi,
Amma kuga Hashim please tsofai tsofai dashi shine zaizo ya fad'a mata magana son ranshi yana kaskantar da ita a gaban idonta, wallahi wannan ta tabbatar da cewa koda kaddara ta aure ta gifta a tsakanin su ba lallai ne ya iya riketa da kyau ba,

AK yazo kuma ta tabbatar da cewa yagan su shi yasa bai shigo falon ba ya koma,
Wama yasani ko ita yazo dubawa yaga kota dawo tunda jiya basu had'uba d'azun kuma dataje side din shi tayi ta nocking baya nan, gashi ya dawo da farin ciki yazo ya cimma bacin rai ta sani cewa dole zaiji ba dad'i,
Kafin ta ankara a zaman da tayi cikin d'aki sai kiran sallan k'arfe biyu ta jiyo daga masallaci dake k'ofar gidan,
Gabanta ne ya fad'i yanzun kuma saura Aliyu shi kuma yaxo taji shima me yake tafe dashi, Lallabawa tayi ta shige ban d'aki tayi tsarki kafin ta d'aura alwallah ta fito ta tada sallah,
Mintoci kad'an da idar da sallanta Hajiya da kanta ta leko cikin d'akin nata,

"Idan kin idar ki sauko k'asa kina da bak'o"

Yankewa gaban Meenal din yayi ya fad'i har saida taji marar ta ta cika da fitsarin tsoro, bata san tsoron ko na minene ba, shin tana jin tsoro ne kar AK ya k'ara zuwa ya ganta da wani? Ko kuma abunda shi Aliyun zai gabatar mata take tsoro?
Ya riga dai yazo babu kuma yanda za'ayi ta doje tace bazataje ba dan haka dole ta mik'e sai da ta koma tayi wani fitsarin dan mitsil kafin ta fito gaba d'aya jikin ta babu wani karsashi a tareda ita,

Ya Sa'eed ne yama Aliyun rakiya dan haka su biyun ta samu zaune suna hira a tsakanin su, bayan gaisuwa ta buk'aci data kawo musu ruwa shi Aliyun ne ya dakatar da ita da cewa ta barshi kawai,
Fita Ya Sa'eed yayi daga falon yana amsa waya wanda kuma yayi hakan ne dan yabasu daman tattaunawa a tsakanin su,

"Hajiya Meenal likita bokan turai, yau dai gani a gaban ki dafatan dai kinyi farin ciki da zuwan nawa?"
Murmushin yak'e tayi mishi,
"Ba dole inyi farin ciki ba tunda bawa zai kawo gaisuwa wajen uwar gijiyar shi, ko ka manta cewa nice dai Gimbiya Aminatu uwar d'akin ku kanawa?"

"Wane ke yarinya yita kanki maza ne a gaban ki"

"To yayi yanzun dai me matar ka ta bayar ka kawomin, kuma shine baka taho min da yarona ba"
Dariya yayi kasancewar shi mutum mai yawan fara'a,
"Saurin me kikeyi haka, indai yaronki kike son gani ai kamar yaune in kinso kina iya rik'eshi ma ya zauna a wajen ki nasan uwar shi bazata hanaki shiba niko dai dama kin san bani da tacewa kune iyayen d'anku"

Shiru tayi bata amsa ba tana d'an murmushi, hakan ne kuma ya bashi damar kiran sunan ta,

"Meenal gani nazo duk da cewa ni na nemi ki bani damar zuwan nasan zakiji mamakin dalilin zuwan nawa"

"Ah haba dai wani mamaki kuma dan kawai za'a sada zumunci, ai naji dadi sosai wallahi kaga tunda na dawo nan yanzun bana sanin wad'anda sukazo,
Kamar dai kai kaga da ace baka fad'amin ka shigo garin ba da har sai kayi kwana kinka ka koma bani da labari k'ila da sai dai daga baya ko zanji amma daka nemeni bagashi kazo mun sada zumunci ba"

"Eh kinyi gaskiya kam to Allah ya bamu ladan dake cikin sadar da zumuncin"

Ameen suka amsa baki d'aya,

"Meenal wannan zuwan da nayi wajenki zuwane na musamman domin ina so mu tattauna ne in gabatar miki da wani abunda nike ganin cewa ya shafi nidake, yarda da kuma amincewar ki nazo nema domin dai duk da kasancewar ki yar uwata bazan so hakan yasa a miki dole a kaina ba, ni ba kowa bane kamar dai yanda kika sani ne suna na ALiyu Jibril kuma ni d'in ma'aikacin banki ne ina zaune a garin yola nida matata da yarona d'aya, yau kuma nazo wajen kine dan in gabatar da kaina a matsayin saurayin da yake fatan samun amincewar ki kafin ya shiga cikin sahun manema auren ki,
Nidai na ganki ne zuciyata kuma ta gamsu da tarbiyya da tsarin ki, babu wanda yamin tallah ah ah nidai naga Abinda nike so shi yasa na biyo Meenal ina sonki ina kuma fatan idan akwai alhairi a tsakanin mu Allah ya shige mana gaba wajen tabbatuwar aure a tsakanin mu, ina fatan Allah yasa wani bai rigani ba, kamar kuma yanda na fad'a miki ne bazan miki dole ba inhar kinji bakya ra'ayina ki fad'amin duk da hakan bawai yana nufin zanyi saurin sarewa in jaye kai tsaye bane ah ah zanyi ta gwada sa'ata dan ban sani ba ko kila rabon samun naki yana nesa bane"

Shiru tayi yayinda a cikin zuciyar ta kuma take cewa,
"Shi wannan dan saukin kaine ba irin d'ayan ba amma duk da haka hakuri kaima zakayi dan gara inyima tufka hanci tun yanzun idan nayi sake zuwa anjima zaku iya zamar min kadangarun bakin tulu"

A fili ko sai ta amsa da cewa,
"Ya Aliyu naji dadi matuk'a ubangiji Allah yabar kauna, nagode da yanda ka nuna kulawar ka a kaina ta yanda har ka iya cireni a cikin jerin yan mata da zawarawan dake yawo a gari ka zab'eni in zamo maka matar ka ta biyu"

Washe baki yayi tun bata gama kai karshen kalaman taba ya fara furta, kalmar "masha Allah Β³, nima nagode sosai a yanda kika tarbeni"

"Ya Aliyu kayi hakuri nasan da gaske kake sona tunda har ka iya baro tarin aiyukan dake gabanka dan kawai kazo ka furtamin cewa kana sona, ka sani nima ina sonka sai dai kuma ni bawai so irin na aure nike maka ba, ah ah ina maka so ne irin na d'an uwa shak'ik'i wanda zai iya tsayawa ya goyama kanwar shi baya wajen ganin ta samu Abinda take so duk rintsi, kayi hakuri da ace kai ka fara zuwa ka gabatar da soyayyar ka kafin wanda zuciyata ta ansaw tabbas da taka soyayyar zan d'auka inbar nashi, dan haka nike mai baka hakuri domin zuciya ta tuni ta zab'i wanin ka Ina fatan hakan bazai tab'a zumuncin muba"
Tana kaiwa nan tayi shiru tana binshi da kallo k'asa k'asa,

"Amma Meenal ya kamata kije ki fara yin tunani kafin ki yanke hukunci ina ganin hakan zaifi"

"Kayi hakuri ya Aliyu gaskiyar kenan na fad'a maka,"

"Ah ah ni bazan takura kiba zan baki isashen lokaci kiyi tunani zan k'ara tuntuban ka zuwa gaba, na kuma gode da kika tarbeni baki kuma boyemin Abinda yake cikin zuciyar kiba, ni zan tafi"

Mikewa yayi sai da ta raka shi har k'ofar gida inda suka faka motar su hango AK da tayi zaune a majalisar shine wanda tsautsayi yakai idonta wajen har suka had'a ido shi kuma ya jefeta da wata k'atuwar hararar datasa hantar cikinta kadawa ne kuma yasata juyawa ta koma gidan babu shiri, yau kam sai ta Allah,

Biyo bayan ta yayi tun kafin ta isa sashen Hajiya yasha gaban ta,

"Waye wancan kuma? Oh wato na d'azun yazo ya wuce bance miki komai ba shine yanzun ma Kika k'ara gayyato wani har cikin gidan nan dan ki wulakantani?,
Meenal idan baki sone basai kinyi hakan ne zaki tabbatar min da rashin son ba, idan kinayin haka kina wasa da lafiya ta ne ko so kike kiga bayana in yaso sai ki kawo wani ko kuma su a cikin su ki zab'i wanda zaki rayu dashi!"
Ya fad'a cikin d'aga murya, bai saurara ba ya d'aura da cewa,

"Dan kawai nace ina sonki shine kike ta faman wasa da zuciyata, minene laifina dan naso ki? Duba fa ki gani unin jiya gaba d'aya kin hanani ganin ki na kiraki waya baki d'auka ba na tura sako baki bani amsa ba, kin san yanda na damu kuwa?
Zuciya ta ciwo take min aduk sanda kikayi nisa dani amma haka nan na danne na miki uzuri tunda nasan kina cikin hidima, dazun na shigo gidan da burin inyi tozali dake haka nazo na iskeki da wani tsohon dake ko kunyar zaman yin zance dashi bakiji ba, kinsan halin dana kasance a ciki lokacin?
Wai anya Meenal kina jin tausayina kuwa?"

"Ina jin tausayin ka mana kuma dukan su su biyun daka gani ai ba samarina bane dukan su yan uwana ne"

"Ki rike jawaban ki domin dai ni ba yaro bane kuma shi wanda yaxo da farkon in baki sani ba duk tattaunawar ku a cikin kunnena naji komai, na kuma tabbatar kema kinji tsayuwata a kanku, Meenal fisabilillahi in so kike ki kasheni ai bakyaso inyi mutuwar kwaf d'aya ba"

"Nice zan kashe ka kuma?" Ta tambaya da karamar murya,

"To inba so kike kiga bayana ba fisabilillahi awa nawane da wancan ya wuce shine har wani yazo,
Badai ni kike so kiga bayana ba? To shikenan ni kuma insha Allah zan kauda kaina daga kanki zan baki dama kiyi iya abunda zuciyar ki keso kafin in waiwaye ki"
Yana gama fad'a mata hakan ya juya fuuu ya wuce kafin ta ankara harya shiga motar shi an bud'e mishi gate ya fice daga gidan.



*Ummiee ce*✍🏼
[9/29, 6:38 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 37*


Abun dai sai gashi kamar wasa amma kuma sai ya juye ya zama gaske domin dai tundaga ranar da AK yafice gidan a gaban ta bai k'ara yarda tayi tozali dashi ba domin gidan ya bari gaba d'aya yayi komawar shi Kaduna abinshi,
Ya zab'i yayi nesa da itane dan dukan su su sarara basai yana kusa da ita bane idan tayi wani abun zai gani har ranshi ya baci? To ya tafi ai sai taci Karen ta babu babbaka yanace itace a lokacin baya take tashin hankalin ta akan yan matan dake nuna cewa suna ra'ayin shi, wato ita harma ta samu damar kula wasu samarin harda basu damar zuwa har cikin gida su sameta alhalin shi ko ya nuna yana buk'atar keb'ewa da ita ta fito suyi hira a waje bata yarda shine zata zauna da wasu gardawa daga ita sai su a cikin falo wai sunan sunzo hira wajen ta, gaskiya dai yaji kishi matuk'a.
Dan haka tunda har ta b'ata mishi rai yayi rantsuwar bazai kulata ba har sai tayi biko dan yaji mai zafi ya daka domin ai ba mata kad'ai keyin yaji ba zai gani kwana nawa zai d'auketa ta sauke shegen girman kanta ta neme shi.

Bai k'ara kiran wayarta ba haka kuma ya soke aika mata sakon nin soyayyar daya saba tura mata sau uku a rana ma'ana safe rana dare,
Ku gane horon iyafa iya ita yake son horawa dan kuwa shidai yana da Sultana a gefe ita ke sanar dashi duk wani halin da Meenal din take ciki tun daga ranar daya d'auke mata wuta, idan yaso jin muryarta zai kira wayar Sultana idan kuma yana son ganin ta zai kira Sultana video call ita kuma sai tayi amfani da back camera ta hasko mishi sahibar nashi,

Ita ko Meenal Allah kad'ai yasan halin da take ciki domin dai duk yanda takai ga dannewa tana ta boyewa saida abin ya nuna a jikinta karsashin ta da walwalanta duk sai ya ragu laifin kanta kawai take gani da ace bata basu daman zuwa gidan ba da bazai gansu ba balle yayi fushi, gashi a banza ta b'ata mishi rai ta dalilin su alhalin shi kullum burin shi shine yaga ya faranta mata saboda dai kar tayi fushi, a d'an lokacin nan ba k'aramin sanya shi tayi a cikin ranta ba matsayi mafi kololuwa ta kaishi ta yanda batajin zata iya had'ashi da kowa gashi tun tafiya batayi nisa ba ita ta fara b'ata mishi rai dan haka duk sai tabi ta tsanagwami kanta,
So take ta kira shi taji yana ina wani hali yake ciki? Yana lafiya ko a'ah duk bata sani ba ashe ji da ganin shi da takeyi a kusa da itama rahma ne?
Yanzun da yayi nesa sai takejin kamar bata da lafiya duk ta rasa kuzari da kwanciyar hankalin ta,
To wai shi me yasa ma zaiyi fushi har haka ne?, inhar da gaske ya saurari hirar ta da ya Hashim kamar yanda yace ai ya kamata ya fahimci cewa su d'in dukan su basa gaban ta shi dai shi ta zab'a, wato shine yama tattara yabar mata gidan to ai shi kenan tunda haka ya zab'a yama dad'e bai tafi ba yafi ruwa gudu in yaso badai dan yaga
tana son shine yasa yake son ya jata a k'asa ba? To soyayyar taci uwata kuma kewa ai bata kisa dan haka can da yawar shi,
A wannan halin da take ciki haka ta dunga daurewa tana cigaba da nuna bata damuba suka cigaba da gudanar da sha'anin bikin su a unguwar malamai take uni saboda gyaran jikin da suma sukeyi dan yanzun basa zuwa yawo,su kuma su Maryam ganin shirun ta yayi yawa ne kuma basa ganin tana yawan amsa kira daga wajen AK kamar yanda suka saba sai ranar maryam ta gaji take tambayar ta ko sun samu matsala ne ita da mutumin nata?
Bata boye musu komai ba kaf abunda ya faru ta kwashe ta fad'a musu,

Ajiyar zuciya Maryam ta sauke bayan ta gama jin jawabin Meenal din,

"Bebs me yasa to baki kirashi kin bashi hak'uri tun ranar ba? Kema dai kinsan cewa ko waye dole zaiji babu dad'i"

"To me zance mishi idan na kira shi?" Ta tambaya da karyayyar murya dan Wallahi a dame take kwarai,

"In ma kina jin shakkun karki bashi hakuri ajin ki ya zube ne to ki kirashi idan ya d'auka sai ki basar kawai kice kin kirane kiji ya yake"
Meelat ce tayi magana wannan karan dan tasan tsabar jin kaine ya hana Meenal d'in kiran shi tun tuni,

"Sister don't call him just send him a short text message,"cewar Sultana,

"Me yasa bazata kira shiba bayan kuma tsakani da Allah ita ce bata kyauta mishi ba ai kamata yayi ta kira ta bashi hak'uri tun sanda Abinda ya faru shine zakice ta tura mishi sak'o" Maryam ta fad'a tana jiran jin dalilin da yasa ita Sultanan tace kar Meenal ta kira shi,

"Will You please let me explain my self ko in barku da iyawar ku?" Sultanan ta fad'a tana wani shan kamshi, irin ita a dole tana nemar musu mafita,

"Ok muna jinki"suka fad'a a tare harda Moon wacce tunda suka fara hirar bata sa baki ba saboda ita damuwar da take ciki yaci uwar na Meenal ya shanye domin ita meenal ai tasan matsayin ta a wajen nata masoyin ko yau taso gabatar dashi a gaban iyayen ta kuma tasan da gudu zasu amince amma ita fa???

Gaba d'aya tun zuwanta komai yake shirin zama tarihi a tsakanin ta da Sarki, alaqar da taso ya yanke a tsakanin su tun tuni shine bai yanke ba sai yanzun da yasan cewa ya riga ya mata dashen son shi a cikin nata zuciyar!
Me yasa wai maza basa da adalci ne? Wannan abun shita gudarma kanta tun farko shine kuma yasa tun farko tak'i sakin jiki dashi tayi ta d'ariΒ² tana kakkaucewa dan dai ya rabu da ita amma yak'iya,
Bai barta ta huta ba har saida ya riga ya gama siye zuciyar ta, bikin Meelat yau saura kwana biyu sannan ita kuma kwana 7 din da Baba Usman ya bata tuni ta cinye shi, jiya da dare kuma shida kanshi ya d'auki waya ya kirata yana k'arayi mata tuni akan maganar su cewa karta manta dai ta fad'ama duk wanda ta tsayar cewa ya shirya turo iyayen shi cikin satin nan suzo su gabatar da kansu,
Ta tabbatar da cewa duk wani bak'on da zaizo ma Hajiya biki tabbas jibi idan Allah ya kaimu kowa zai halarto nan Zaria to wani amsa zata ba iyayen ta a sa'ilin da suka zaunar da ita danjin wata tsayar a matsayin mijin auren ta?
Wallahi tana son Sarki bata tabbatar da cewa ta kamu da mugun son shiba sai bayan zuwan ta garin nan da shi kuma yayi dif ya d'auke mata wuta ba kira ba sak'o,
To wanda ya wofantar da ita irin haka taya zata gabatar dashi ma iyayen ta? Idan suka kirashi shi kuma yanuna musu cewa baya ra'ayin ta ya zatayi kenan,
Me yasa rayuwarta ya juye upside down cikin kankanin lokaci haka?,
Tayi shiru tana sauraron shawarar su Sultana zuwa ga Meenal ne dan tasan ba iya Meenal dince kad'ai zata amfanu ba itama tana buk'atar shawarar sai dai kuma ta yanda zata bud'e baki ta shaida ma Aminan nata halin da take cikina ta gagara yin hakan duk da cewa ita Meenal din bata boye mata komai na alaqar ta da AK ba ta kuma tayata murna domin duk wanda yaga masoyan biyu yasan sun dace da juna kwarai, sai dai ita kuma ga abin yana matukar damunta a cikin zuciya amma ta kasa sharing din shi ma kowa a cikin su, to mema zatace musu bayan shi dayace yana son nata yanzun kuma ya juya mata baya,

***
Daurawa Sultana tayi da cewa,
"Tsaya kiji sister kin san dai ba kece budurwa ta farko da ta fara muna mishi soyayya ba, dan haka na tabbata yasha jin kalaman ban hakuri a wajen yan mata daban daban tunda ya saba kullum suke neman shi dan haka komai yayi gani zaiyi akan dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login