Showing 99001 words to 102000 words out of 190771 words

Chapter 34 - Dangina Book 2 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1564

kuma yan gulma sun fara yad'a surutai akan zaman da takeyi har yanzun bata koma ba ko dai akwai wani abun a k'asa ne?
Shiru yayi bai iya bata amsa ba data matsa sai kawai yace mata zaiyi kokari ya shigo k'asar zuwa karshen wata, karshen watan nayi ya shiryo ya dawo gida sai dai kuma abinda ya tarar bayan dawowar nashi har sai yafi na baya tashin hankali domin dai ashe ita Ikram tun dawowar ta mutane da yawa sun ankare da cikin data dawo dashi wasu da yawa sunyi zaton ko rainon cikin nema ya dawo da ita tunda acan k'asar basu da kowa sai su biyu,
Sai dai duk wanda ya mata maganar cikin saita basar dan ta gaji dace musu bata da ciki ita a zaton ta hutun data samu a can kasar shi yasa mutane ke ganin kamar ko cikin take dashi,

Ranar da yaje gidan su ikram d'in saboda kafin yayi magana da kowa zaiso ya farajin ta bakin ta idan babu wanda yasan abinda ya faru kenan komai zaizo mishi da sauk'i zai tambayeta ne idan tana ra'ayin zama dashi in kuma tace tafi son su rabu zai saketa ne kawai batareda ya tona mata asiri ba,

Sai gashi daga zuwa uwarta ta tare da cewa ai tayi zaton ko sai watan haihuwar ikram din ya kama ne zai dawo,

Da fari yayi zaton zolaya ne kawai sai da ta k'ara mai maita mishi cewa,

"Ai tunda ta dawo nace to kunyi kyan kai dan dama rainon cikin fari ai sai gida, kodan saboda abubuwan kwadayi da ita zata buk'ata wadanda ba lallai ku same su a can k'asar ba,"

Yanke ta yayi a yayinda yake bin ikram din da kallo da cewa,

"Ai bata d'auke da komai"

Dariya tayi ita kuma a nata zaton tayi tsammanin ko kunya ne yasa shi fad'in hakan dan haka sai tace "to ai tunda gaka kazo sai ka d'auketa kuje asibiti dan a tabbatar mana da wata nawa ne cikin nata, dan gaskiya in cikin baiyi kwari ba bazan yarda ka d'auketa ku koma can wata k'asar ba dan ku yaran nan ba hakuri kuka cika ba kuna iya kuje can wajen rashin hakurin ku ku zunguro cikin ya fita"

Bashi da yake cikin kwankwanto ba ita Ikram da ake zancen ciki a jikin ta itace take cikin tashin hankali mad'aukaki,
Domin a iya sanin ta dai tasan cewa kafin ta fara yawace yawacen ta sai da tayi planing na shekaru uku saboda gudun b'acin rana,
To ta ina kuma zatayi ciki, kenan planning din ne baiyi ba ko kuma dai wannan bala'in ne daban ake kira mata, zufa ke shatata tako ina a jikin ta, ciki fa ake magana bayan kowa yasan tana da aure amma ai babu wanda yasan cewa cikin bana aure bane,
Yanzun idan shi kuma ya bud'e baki ya fad'ama duniya gaskiyar cewa bai tab'a kwanciya da ita ba da wani idon zata kalli iyayen ta bayan babu wanda yasan tana biye biye,
Ita dai ta shiga ukun ta ta lalace da ace tasan da batun cikin nan da tun dawowar ta zata zubar da shege ko kuma tabi malamai a kulle mata bakin shi ruf ta yanda bai isa ya musa cewa cikin ba nashi bane,

Ta ina ma zata yarda ta haifi cikin da uban nin shi suka kasu sama da biyar dan ita tsabar jarabarta bai barta ta rayu da namiji d'aya ba, indai kana da kud'i kana kuma sake mata su babu ruwan ta zata barka ne kayi ido iya iyawarka to yau ga ranar bacin rana,

Dauriya sosai Bash ya aro ma ranshi koda Maman ikram din tace suje asibiti baiyi musu ba dan shima yana so a tantance din domin dai yanzun kam an yanka ta tashi,
Allah ya gani yaso ya rufama ikram asiri kodan saboda kasancewar ta yar uwar shi amma hakan zai yuwune kawai in babu cikin a jikin ta idan kuma akwai to babu ubanda zaisa shi amsar cikin da bai san inda ta samo shiba wallahi,
Uwar da kanta taja ikram din d'aki ta shirya badan taso ba haka ta fito ta same shi a mota suka wuce asibitin,

Wani private hospital sukaje inda acan ne aka k'ara tabbatar musu da batun cikin,

Tunda suka fito a asibitin ikram ke kuka shi dai bai kulata ba, to me zaice mata bayan inda yana da hali shima kamata yayi ya daura hannu akai yayi ta kwarara ihun har sai ya gamsu dan kanshi,

Gajiya da kukan tayi dan kanta ta nemi ya faka dan tana son su nemi mafita tun yanzun,
Bai musa ba haka ya faka motar a gefen titi yana binta da kallo da son jin abinda zatace,

"Yaya ni dakai dukan mu munsan cikin nan ba naka bane,
Kayi hakuri bansan da wani idon zan kalleka ba shi yasa na dawo gida, saboda in baka sararin da zaka yanke hukunci ba a cikin fushi ba,
Wallahi tunda Nazo ban iya fadama kowa laifin dana aikata maka ba saboda bansan da wani idon zan kalli iyayena ba, Yaya ka yafe min nasan na cutar dakai wajen cin amanar auren ka gashi kuma tun ba'aje ko ina ba Allah ya saka maka nayo cikin daba na aure ba, nayi laifi kana da damar da zaka hukunta ni nasan ban cancanci cigaba da zama a matsayin matar kaba, sai dai kuma ina so in rok'eka alfarma d'aya dan Allah ka rufa min asiri kamar yanda baka fadama kowa dalilin dawowa na gida ba bana son iyayen mu su san abunda na aikata maka ka rufamin asiri dan Allah, ko baka fadaba nasan cewa ni yanzun ba matar auren ka bane sai dai kuma duk da haka zanso ka rubuta min takardar saki wanda zai zama shaidar dazan gabatar bayan ka koma a matsayin ka sakeni,"

Katseta yayi da cewa shi kuma cikin jikin naki ya zakiyi dashi?

Zan zubar dashi saboda idan na haifeshi duk daren dadewa dole wata rana asirina zai tonu duniya zata gane cewa dan dana haifa da auren ka ba naka bane ni kuma bani da amsar da zan bashi idan ya tambayeni wanene uban shi, dan haka gara in zubar dashi tun cikin bai gama yin kwari ba,"

"Bakyajin tsoron wani abu ya sameki a yayin cire cikin? Ko baki san cewa har mutuwa anayi ba"

"Na sani amma hakan shi yafi min,"

"Ok tunda hakan kika zab'a ni bazan tilasta kiba rayuwar kine sai dai ina fatan hakan daya faru ya zama silar da zaki canza rayuwar ki"

A takaice dai a wannan ranar ikram bata yarda ta koma gida ba dan a hanya tasa ya sauketa bayan ya rubuta mata takardar saki d'aya ya damka mata ita kuma tayi cikin sabon gari ba ita ta koma gida ba saida aka kwalkwale cikin nan tsaf ta tabbatar da cewa ta rabu dashi koda ta koma gida kuma dauri ya ta aro sai ta sheda ma Mahaifiyar nata cewa ba ciki bane al'adarta ne yayi gardama amma an bata magani tayi amfani dashi har period din nata yazo,

Shiko daya tashi komawa koda iyayen sukayi magana ce musu yayi ba can Malesia zai koma ba South Africa zashi ta zauna har sai ya koma kafin ta dawo,

Sai da ya tafi da kusan wata biyu ita kuma lokacin tana da kusan wata HUDU kenan a gida kafin ta gabatar da takardar daya bar mata,

Ganin abin yana shirin tab'a zumunci ne kuma yasa ta fadama iyayen nasu cewa suyi hakuri itace ta mishi laifi kuma itace ta nemi Sakin,
Sunyi sunyi da ita ta fada musu maiya faru amma tak'i, shima kuma da aka tambaye shi sai cewa yayi su tambayeta,
A haka dai maganar saki ya tabbata aure ya lalace ba tareda kowa yasan mai ya faru ba,

Tun wancan lokacin kuma bai dawo k'asar ba sai wannan dawowar da yayi ya had'u da Maryam a k'ofar doka gashi kuma yau ya had'u da Meenal,

Meenal din da rashin ta ne duk yayi sanadiyar fadawar halin daya tsinci kanshi a ciki tsayin shekarun nan,
Taya kuma yanzun data dawo wata zatace mishi wai wani auren zata karayi, kenan suna nufin cewa zai kara rasata a karo na biyu?

Koda ya isa unguwar malamai so yayi ya wuce gidan su meenal din kai tsaye sai kuma wata zuciyar ta hana shi dan haka sai yaci burki a k'ofar gidan su Meelat kasancewar shi zaka fara isa kafin gidan Malam,

Cikin masu gadin gidan yayi magana da wani akan yayi mishi kiran Meelat d'in babu dadewa ko sai gata ta fito saboda basu dad'e da magana da musty ba yace mata zai bada sak'o a kawo mata amma sai gashi bayan fitar ta taci karo da bash,

Bash dai tsohon saurayin Meenal wanda yayi d'awainiya dasu a shekarun baya,
Lallai Maryam batayi karya ba da tace ya canza domin kuwa da gaske ne ya canza din ya k'ara girma da cikar kamala ga kuma arzikin da yaci uwar na baya,

Fara'ar dole ta aro ta yafa ma fuskarta a sanda ta k'arasa inda yake,

"Wa nake gani yau a k'ofar gidan mu kamar Bash din mu?"

"Ni ne dai Bash din Meenal ba gizo idanuwan ki sukai miki ba, Jamila ya gida ya kwana da yawa?"

"Ah ah aini bai kamata ma in tsaya ko gaisuwa muyi ba ace kana raye sai yau zaka nemeni tsayin shekarun nan ina ka shige Bash?"

"Kiyi hakuri nayi laifi amma bana k'asar ne shi yasa ban neme kuba, nabar k'asar ba'a cikin hayyacina ba a sanda abubuwa suka dai daita kuma bani da kwarin zuciyar da zan iya zuwa unguwar nan shi yasa ban neme kiba sai yau ina fatan za'amin afuwa?"

"Ah haba dai ba komai wallahi komai ya wuce ai, to ya bayan rabuwa ya rayuwa? Duk da dai Alhamdulillah yanda na ganka nasan an samu cigaba sosai, ya madam da yara to dan nasan kila baza'a rasa ba duba da shekarun da aka d'auka"

Guntuwar murmushi yayi kafin ya amsa mata da cewa,
"Alhamdulillah sai dai iyalin da kika tambaya ne har yanzun babu, sai dai muna fatan wannan karan a dace tunda shekarun baya dai an kasani"
Ya karasa fad'a idanuwan shi a kanta,

Murmushi itama tayi bata bashi amsa ba,
Sai ya daura da cewa,

"Dazun naga Meenal tareda wannan yayan nata na tudun wada, mun kuma hadu da maryam da wata kawarta dukan su a cikin ABU,
Sai dai ita k'awar tayi wasu magan ganu wanda ban gane ba shi yasa nazo nan,
Naso in wuce gidan su Meenal ne sai kuma naga ya dace in farajin ta bakin ki duk da ban sani ba ko kina gida ko allah yasa kinyi aure sai da na zo ne mai gadin ku yace min kina gida.



*UMMIEE ce*✍🏼
[9/21, 8:22 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 33*


To mu shiga daga ciki mana nasan bakasan ansa ranar aure na ba wannan satin mai kamawa zanyi aure kaga ba dad'i mutane su ganni tsaye da kai a nan dan haka bismillah mu shiga daga ciki ina ganin hakan zaifi "

Cikin suka wuce suka nemi waje a farfajiyar gidan suka zauna,

"Bari in shiga ciki in kawo maka ruwa,"

"Ba bukata ki barshi kawai nagode"

"Ok tunda kace haka yanzun me kake son ji daga gareni?"
Ta tambaya tana binshi da kallo, tunda har ya wanko kafafun shi yazo har nan tasan gaskiyar yake son ji daga bakin ta dan haka babu amfani ta boye mishi.

"Ina son insan komai, idan nace komai Meelat ina nufin komai karki boyemin akan Meenal ,"

Gyara zama tayi da kyau kafin ta fara da cewa,

"Kamar yanda ka sani a shekarun baya da suka wuce kaida Meenal duka mun shaida kuna son junan ku, nasan kayi bakin k'okarin ka wajen ganin ka shawo kanta akan ta baka daman gabatar da kanka a gaban iyayen ta amma hakan bai faru ba har zuwa sanda komai ya faru,
tasha fad'ama na yanda kukayi da ita akan hakan,nasan a lokacin zakayi zaton ko bata sonka ne shi yasa amma kuma ita a gefen ta ba hakan bane, tak'i yarda ka gabatar da kanka din ne saboda tasan da zarar ka kai maganar ka gidan su to zancen aure za'ayi saboda kaima kasan yaran gidan su ba'a barin sukai har matakin da ita takai a lokacin ba tareda an aurar dasu ba,
WallahiΒ³ Meenal bataci amanar kaba ta kuma soka da dukkan zuciyar ta a wancan lokacin,
In baka sani ba bari in fad'a maka idan kuma ka sani hakan zai zama maimaici ne a gareka, ita kanta bata san cewa itama tana cikin wadanda za'a d'aurama aure a wannan lokacin ba har sai ana gobe daurin auren nata, tayi kuka tayi kuka babu kalar borin da batayi ba akan bata son auren amma kuma bata isa ta canza abinda Allah ya riga ya kaddara zai faru a lokacin ba sai dai kuma duk halin da take ciki bata manta da kaiba, ina da labarin kiran da Aunty Hassana tayi maka domin a wajen Meenal ta amshi number dinka,
Kayi hakuri a lokacin nida Maryam mun kasa zuwa asibitin da aka kwantar da kai duba Kane saboda bamu sanda wani idon zamu kalle ka ba, munyi zaton cewa zuwan namu zai iya zama k'arin tsanani a gareka.... "

Katseta yayi saboda shi ba wancan labarin daya riga ya sani yake son jiba, ah ah halin da Meenal take ciki a yanzun shine damuwar shi,

"Yanzun Meenal tana ina?"

"Tana Tudun wada gidan Hajiya, auren ta da Sarki ya mutu a watannin baya hakan ne yasa ta koma can da zama"

"Me yasa bayan auren ya mutu daga ita har ku babu wanda yayi tunanin nema na?"

"Saboda a iya sanin mu baka k'asar, kuma ko kana k'asar ma ai hakan bai dace ba tunda nidai nasan kayi aure, yanzun da allah yasa kayi katarin ganin ta ba gashi ka biyo sahu ba "

"Eh bana k'asar kuma nayi auren kamar yanda kikaji, sai dai kuma nima mun rabu da matar"

"Ayya to Allah yayi zab'i da mafi alkhairi"
Cewar Meelat,

"Ameen!
Meelat meke tsakanin AK da Meenal domin a yanda na gansu yau jikina yana bani cewa akwai wani abu a tsakanin su kuma ita waccan yarinyar dana ganni tareda Maryam tace min wai shine mijin da Meenal din zata aura shi yasa Nazo nan dan ina son inji gaskiyar komai daga bakin ki dan nasan bazakiyi min karya ba"

Ajiyar zuciya ta sauke tana kauda kanta gefe dan yanda ya tsareta da ido tasan gaskiyar maganar yake son sani,

Kai Sultana dai bata ji
sam wallahi,inba shegen surutun taba meye ya kaita wani ce mishi AK ne mijin da Meenal din zata aura bayan sun shaida mata komai dake tsakanin Bash din da Meenal, ai da tayi shiru da bakin ta ba lallai yasan cewa auren ya mutu ba,

saida tayi gyaran murya kafin ta amsa mishi da cewa,

"Itafa yarinyar nan daka gani shegen iyayine da ita, ko kuma dai kayi wani abunda ka b'ata mata rai shi yasa ta fad'a maka hakan, nidai nasan akwai kyakyawar alaqa a tsakanin su kamar yanda kaima kasan shi din d'an uwanta ne bayan hakan kuma ban san wani abun ba zaifi dacewa ka tun kare Meenal d'in kuyi magana kai tsaye ta yanda zakaji komai a bakinta"

Sun danyi hira kad'an kafin ta rakoshi k'ofar gida sukayi Sallama shi ya shiga motar shi ya tafi ita kuma ta dawo gida,

Tana shiga gidan Maryam ta fara kira ta fad'a mata cewa suzo ita da Sultana su sameta tana jiran su, a wannan ranar kuma Sultana bata dawo gidan Hajiya ba a Unguwar malamai tayi zaman ta saboda su sunyi zaton cewa tunda Bash yasan inda Meenal take zaije can ya neme ta.

*washe gari*

Hajiya, AK da Meenal ne zaune akan dinning suna karin kumallon safe,

Wato dai Hajiya bata k'ara tabbatar da cewa soyayya yana sa mutum ya zama wani abun daban ba sai yanzun da so ya damk'e mata wuyan D'an mai k'arfi, gayen nan fa gaba d'aya ya fitsare kafafuwan shi yayi fatali da wani abu da akeji in ana gaban sirikai mai suna kunya,
Dan dai Hajiya ko tana waje ko bata babu abinda ya dame shi zai aiwatar da abunda yayi niyya ne kawai abinshi,

Domin dai tunda ya dawo masallaci yana komawa d'akin shi kayan shi ya tattaro shida su (Kabir wani yaron shine dake mishi aikaceΒ² idan yana gari) ya dawo dasu sashen Hajiya a cikin d'aya daga cikin d'akunan kasa ya zuba kayan, duk wani abu na bukata nashi sai da yasa su kabir din suka kwaso mishi,
Tunda farar safiya masu aiki sukazo suka fara aikin yima gidan kwas kwarima, inda duk yake da buk'atar gyara an gyara sauran kuma ko ina aka bishi da sabon fenti gyara sosai akema gidan wanda badan komai ake yin shiba sai dan shirin bikin Musty,

Hajiya tayi mamakin ganin AK ya kawo kayan shi sashen ta dan haka gaza yin shiru tayi saida ta magantu,

"Kai wai nace wannan kayan naka da naga ka kwaso ka kawo nan badai kana nufin k'aura kayi daga can sashen ka ka dawo nan bako?"

"Kema dai Hajiya kin san bana son kamshin sabon fenti kawai zan zauna anan ne na yan kwanaki kafin ranar bikin zan koma sashe na"

"Ah ah Abdul wannan batu dai duk wanda yaji yasan gulma ne dajin baki, tsakani da Allah tun tuni kasan zakasa ayi aikin fentin gidan nan baka sa anyi tun kafin ka dawo ba sai yanzun daka dawo ne zaka wani tattaro min kayan ka kayo sashena wato dai shi kenan ni bani da sirri, duk wanda ya kwaso gyayyar shi wajena zai sauka,
To ta ina ma zan yarda niko inyi rayuwa hankali kwance da kai sankacecen k'ato a sashe guda bayan nasan ina da budurwar daka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login