Showing 165001 words to 168000 words out of 190771 words
yace shi bazai tara bidi'a da yawa ba in suna so su burgeshi To suyi ta sama auren albarkha kawai shine Abunda yake so.
To suma dai a gefen su basuja zaren da tsayiba Dan haka suka hada gaggarumar dinner acewar su baza'ayi bikin "Mai Jama'ai " lami ba mahadi ba,
Gaskiyar yan magana dake cewa masu layya nacin nama,
wallahi abokan shi gaba daya Kamar basu san zafin neman kudiba,
Tunda suka shiga gidan nan suke rabon kudade sun raba a cikin gidan wajen iyaye mata sannan bayan sun fito kai tsaye filin wasan da matasan gidan suka hada nasu casun Suka karasa nan ma dai haka suka dunga masu yayyafin nerori.
kowa yayi mamakin yanda mai jama'a da kanshi ya shige cikin su duk da ba wani rawa yayi ba,
Amma ya musu liki abokan shi dai kam su sukace in bakuyi bamu waje Dan sun warwasa abunsu, acewar su bikin daya rana in basu mishi karaba Ai sunci amanar zama.
Gaskiya dai sun burge dan sun bada Kala wallahi ,
Ana ta casu Amma shi dai Ango burin shi yaga ta ina gimbiyar shi zata fito,
Yasan dai duk inda take dole ta fito su gaisa da abokan shi, sauyin bugun da yaji zuciyar shi tayi shiya tabbatar mishi da cewa duk inda take tabbas tana kusa dashi.
***Dan haka tun kafin su karaso tsakiyar wajen ya kafe hanyar da mayatattun idanuwanshi, yana mai jiran yin tozali da muradin zuciyar shi.
Kam ya rike ta da kwayar idon shi ko son kiftawa bayayi, a wannan lokacin shi kadai yasan yanayin daya riski kanshi a ciki, wallahi badan su baba suna cikin harabar wajen ba,
Babu ubanda ya isa ya hanashi zuwa ya rungume matar shi a wannan lokacin da yakeji Kamar ya dauketa kawai su bace bat abinsu.
Shi wallahi da za'a kyauta mishi kawai a bashi matar shi yayi gaba da abunshi,
Dan allah in bama daukar alhakiba Ai kamata yayi daga daura aure kawai a mika amarya dakin ta.
Hummm ya sauke ajiyar zuciya a bayyane, dai² lokacin da suke karasowa cikin filin,
"Lallaima yarinyar nan, wato bama zata matso inda nike ba".ya fad'a kasa²
A wayen ce ya lelleka gefe da gefe saida ya tabbatar babu wani idon kunya daga cikin mutanen dake wajen zagaye dasu, sannan ya juya ya hango inda su baba suke Allah da ikonsa zuwa wannan lokacin babu su baban a wajen sai dai wasu daga cikin abokan su.
"Alhmadulillahi "ya fada yana mai karasawa wajen da Ameena take tsaye suna gaisawa da abokan shi sun sata tsakiya sun dage wai sai tayi rawa tunda Mai Jama'a shi Yakiya,
duk wannan wainar da ake toyawa har lokacin fuskanta rufe yake cikin gyale Kamar yanda ta fito,
jawo hannun ta yayi daga cikin su zuwa ainihin tsakiyar filin.
Wallahi tunda taga ya dososu gudun zuciyarta ya karu,
"ya allah kar kasa gayen nan ya bani kunya a wajen nan" kawai take fada a zuciyarta. Taushin hannun shi dagaji a cikin nata hannun shi yasa sakar zucinta yankewa
taso t doje a sanda ya jata amma ba hali karfin ba daya ba, baiyi magana ba da idon shi yaci gaba da kallonta kuma bawai murmushi yake ba,
Ita dai bata gane yanayin da yake cikiba,
Dan dago kaita tayi dan ta saci kallon shi kawai idota ya fada cikin nashi.
"Na miki kyaune? "Ya tambaya yana kashe mata ido,
Murmushi tayi ba tareda ta amsa ba,
"kinyi kyau" yace kasa².
Bata san ko dama can sun shirya hakan bane da abokan shi domin kamar hadin baki haka suka zagayesu suna musu likin fafare bugun fct Abuja kudaden nan kamshin su daban ne kun daisan yanda sabon kudin kamshi shi yake da dad'in shak'a balle kuma ya fito daga tsaftace cen aljihu, wato sabon Abu baka gajiya da kallon shi yasin sabon kudi akwai daukar hankali, Allah dai ya tsine tsiya ya mana katangar karfe tsakanin mu.
Wani abokin su mai suna Wazir ne yace wai sunyi likin ganin fuskan Amarya.
Dan haka Ango ya taimaka inba rowar ta yake ba ya bude musu fuskarta,
To shima dai dama a kagare yake Dan haka bai tsaya yanga ba ya fara kokarin dage lullubin fuskan.
Dukan su haka suka fidda wayoyin su masu daukar hoto nayi masu video suma haka,
Ita dai wallahi gaba daya kunyar da bata san yaushe ta fara jinta ba ita ta kamata gashi ba wajen buya dan su Maryam ma gefe suka koma suna kallon ikon mai sama.
Da sauri ta runtse idonta a sanda ya maida gyalen zuwa kan kafadunta,
shiko kyar haka yake binta da wani mayataccen kallon shi mai kara sata tanaji gabban jikinta suna macewa,
"Bude idon!"
Ya fada a hankali yana sauko da tashi fuskar dai dai tata bayan yadan rankwafa ya dai²ta tsayinta da nashi,
Kara nokewa tayi tana neman hanyan guduwa kafin ta ankara saijinta tayi gaba dayanta ta shige cikin jikin shi tayi kane²,
shiko Dama Abunda yake muradi Kenan dan haka baiyi kasa a gwuiwa ba wajen riketa gam a cikin jikin shi baifa tsaya a iya rungumar ba itadai taji abokan shi suna fadin
"YOU MAY KISS THE BRIDE, halal kiss and hug" kujimin wani salon rashin dajara wani irin kissing kuma Ana zaune kalau Kamar wasu masu auren coci gidan Malam nefa ....
Zaro ido tayi
"Dan allah kar kayi! Karkayi kissing dina a cikin mutanen nan please 🙏 kagafa wallahi duk kallon mu akeyi kuma su Baba suna nan, Kai Dan allah wani irin kissing kuma a gaban jama'a muke fa"
Take fada tana kokarin kwace jikinta kara kankameta mugun yayi yana dariya,
"Kunyar su kikejine bayan sun riga sun aura min ke?"
"Eh mana kannen mune fa a wajen kuma kaima ai dai baka yarda kayi faduwar bak'ar tasa a gidan sirikai ba"
Wallahi AK mugune, kugafa tun dazun ko murmushin shi bai bari ta gani ba,
Amma yanzun daya shirya bata kunya a cikin mutane shine da dariya harda kyakyatawa.
Kasa yayo da bakin shi duk wasu alamu sun nuna sumbatata zaiyi amma ga mamaki na sai naji saukar bakin shi a goshina,
Kai wallahi ta tsorata allah kadai yasan dalilin da yasa ya fasa abunda yayi niyya,
Waiyo Allah kuzo kuga ruwan flashers na masu daukar hoto, kafin ta ankara shi uban gayyar da kanshi wannan karan ya fara mata liki,
Aifa Kamar jira saiga matan cikin gida suna bulbulowa suma dai gaskiya sunyi kara kwarai, sunyi rawa a cewar su wanda bai takaba da bakin ciki zai mace, gaskiya dangi da dadi suke wallahi duk wanda ya rasa ahali tabbas yaci a tayashi kuka dan ban san waye ya kira yayyenta maza su Ya Farouq ba haka suka zo suka shiga cikin mu akayi ta hotuna dasu kuma suma sunyi liki,
kallon mutanen da suka cika wajen ta dungayi a cikin zuciyata kuma tana kiyasta yanzun duk yawan su badan kowa suka hallara ba sai sabida su,
Dan da yawa daga cikin su batagan su a lokacin aurenta na farko ba Amma wannan karan duk da yanda auren yazo dangi na nesa dana kusa kowa ya hallara, lallai Yan magana sunyi gaskiya da sukace (dakan d'aka, shik'an d'aka, tankaden bakin gado)
wallahi hakan nan sai taji wani farin ciki ya kamata yanda Yan uwa takowani gefen suka sasu a tsakiya duk dakewar mai jama'a saida suka sashi rawa gaskiya dai wajen nan duk wanda ka gani fuskar shi cike take da farin ciki idan ma akwai masu bakin ciki to sunyi kokari kwarai wajen adana hakan a cikin zukatan su,
gaskiya anyi nishadi kwarai a wajen Dan musamman ma yayen mu maza masu forming cewa su ustazai ne su kansu yau saida suka Dan tattaka kuma naji dadi Dan nasan Dan ni sukayi iyayen mu mata ma sun nuna nasu farin cikin Dan sun shigo filin suma anyi dasu Amma dai Mommy taki fitowa tace bada ita ba a shiga ruwa lafiya, a takaice dai anyi buduri sosai a wajen ana ta abubuwa banga Fauxieyerh ba Sultana ke cemin ai an wuce da ita Abuja tuni kuma shima Ya Sheikh ya bisu ,
sai anan na gane cewa wato yan gidan saboda babu Shehi shi yasa suka rak'ashe abinsu,
Duk likin da akayi a wajen kuma su firdausi kannena sune kwamitin kwashe kudi ban san ya zasuyi da shiba,dan haka na jawo ta na rad'a mata a kunne cewa 50/50 zamuyi idan sun gama k'irga su kawo min kasona wallahi.
*UMMIEE CE*
[10/11, 9:19 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA*👨👩👧👦🔱⚜️
*BOOK 2*
*PAGE 48*
Karku manta fa duk wannan budurin da ake uban gayyar fa yana gefen ta dan koda yace ya gaji da rawar da aka sashi na dole bai yarda yaje ya zauna shi d'aya ba saida ya jata zuwa kujerar da aka tanada dan Ango da amarya saboda tsabar kishin ganin ta tsamo² cikin yayyen ta da kannin ta maza da yaji yana neman tafiyar mishi da numfashi,
Haba suma dai abu babu kara ba komai a gaban shi matsayin shi na mijinta zasu wani dunga kakkama mishi mata suna sata rawar dole kawai dan dai suna takamar cewa su yayyen ta, ya take kan yayyen yawuce😠
koda suka zauna kuma koda wasa yaki ya raba hannu ta da nashi a hakan kuma su Sa'eed din basu hak'ura ba haka suka dunga biyo su ana musu hotuna Baba Adamu da Baba Auta suma sunzo har wajen anyi hotunan dasu amma Malam baizo ba dan baya cikin gidan a lokacin.
"Wana Kama?"Yake tambayar ta bayan sun zauna,
"waka kama kuwa?" Ta bashi amsa,
"Ok ba laifi,
yarinya kina duba lokaci kuwa?"Ya fad'a yana kara yin kasa da muryar shi,
" saura dan k'ank'anin lokaci kibar gidan nan keda shi kuma sai dai ziyara,"
matse hannu ta dake cikin nashi yayi,
"da zafi fa!"
Tace mishi, shi kuma sai ya amsa mata
"Eh Ai nasan zakiji zafin shi yasa na matse,"
"Ai dama kai muguntar ka bata sauka akan kowa saini marainiyar wayon ka,"
" eh to ya zakiyi dani? Amma ga shawara, mai zai hana anjima in an kaimin ke gida ki rufe kofa dani a ciki kinga saiki hukunta ni ba wanda yaji koya gani, koya kikace? Shawara ce kyauta ki hukunta ni kawai ki huce haushi dan nasan kina da fushina dama"
Gyara zama tayi ta fuskance shi,
"Wai wa za'a kai maka yau? "
Bata tsaya saurarar amsa daga gareshi ba ta daura da cewa,
"kamanta abunda na fada maka dazun ne? Ni ban shirya tarewa yanzun ba,
Kamar yanda ban shirya aure yanzun ba kukamin dole to sai ku Bari in shirya tarewa da kaina.........."
Hannun shi guda dayan dake free yayi amfani dashi wajen tab'a mata gefen wuyarta,
da ido ta bishi da kallo.
"Baki da lafiya koh? Amma kuma jikin ki ba zafi,"
"Ni lafiya ta kalau,"ta amsa tuna tura baki,
"Masha allah to albishirin ki!
Wallahi yau kam insha Allah ko suma kike kina farfadowa bazaki kara kwana a gidan nan ba kinjima na rantse mai kankat Kenan kuma ke
Kin san halina" ya fada yana d'age mata kafadun shi,
Shi Kenan ta faru ta kare dan wallahi tasan tunda har ya rantse to magana ta zaunu.
Basu tashi daga wajen ba sai gabanin magrib abokan shine sukama jama'a magana akan su shirya idan an idar da sallah ne za'a wuce wajen dinner,
Su kuma mazan fita sukayi zuwa masallaci matan kuma suka shige ciki dan ita dama tun kafin su an kara aka shige da ita cikin gida bayan dawowar Malam.
Takardar gidan da Hajiya ta bata ta d'auko ta wuce d'akin Baba Auta, da sallama ta shiga Mommy ce da Baba Autan zaune da alama wani abun suke tattaunawa,
"Amarya Meenal taho nan kusa dani ki zauna" cewar Baba Auta yana yafito ta da hannu,
"Me kike nema anan kuma keda ya dace ace kina can ana shirya ki ko baki san ana idar da sallah za'a wuce dake bane?" Inji Mommy
Tura baki Meenal din taci cikin kunkuni take cewa,
"Ai dama ni tuntuni nasan bakya wani sona kuma nima ai ba wajen ki nazo ba wajen Babana nazo"
"Ina fa zan soki tunda Allah yasa bake kad'ai na haifa ba, keda hankalin dukan dangi yake kanki ne zan wani damu kaina saboda ke,
Idan nasoki ke kad'ai su sauran yaran nawa wazai so mun su tunda a fili ake wareki a barmin su, ke mai uba komai aka rarumo sai a juye kanki dan haka kije can ki k'arata"
"Ah ah Jidda me yasa zakice haka,
Taho nan kinji uwar masu gida ki fad'amin abinda kike so"
Karasowa tayi ta zauna a gefen shi, bata ce komai ba illah takardar data mik'a mishi,
Amsa yayi saida ya gama duba takardar kafin ya mik'ama Jidda itama,
"Takardar minene?"
Ta tambaya,
"Ki duba mana"maida kanshi yayi kan Meenal
"Nayi miki murna kwarai uwata ubangiji Allah ya sanya alkhairi"
Ameen Meenal ta amsa ita kuma Mommy cewa tayi,
"Ina kika samu gida kuma Meenal mu bamu da labari?"
"Gidan Babana Malam ne ba nawa ba na fara nuna muku ne kusa albarka kafin in kai mishi takardar kuma kudin kayan dakina da Hajiya ta siyar ne na had'a da nawa kudin ita kuma tayi min ciko aka siya gidan"
"Masha Allah lallai ina alfahari da uwata allah ya miki albarka yasa ki gama lafiya kinji, maza jeki yanzun ki kai mishi nasan zaiyi farin ciki matuk'a Allah yayi miki albarka ya baku zuria d'ayyaba"
"Allah yayi albarka"itama Jidda tace a yayinda take maida mata da takardar,
Tana amsa ta fice daga cikin d'akin a harabar gidan suka had'e da ya Farouq da Ya Abdul,
"Ina zaki kuma?" Suka tambaya,
"Ya dan Allah muje ku rakani wajen Baba Malam"
"Ke fad'an ne bazaki bari akai ki ya miki ba shine ke zaki kai kanki saboda kin k'osa kibar gidan?" Cewar Abdul yana dariya,
"Allah ya kyauta"tace kafin ta wuce a fusace su kuma suka rufa mata baya,
"Ke ki tsaya mu jera mana ko bakyason rakiyar ne kuma?"
"Eh bana so"
A natse ta shiga falon babu wasu mutane a ciki Innar yara ce kawai sai Maman kano da kuma shi Malam d'in,
Sai da ta gaishe su kafin ta k'arasa ta zauna a k'asa dai dai k'afar Malam wanda yake ta washe baki yana binta da kallo cike da so,
"Kinci abinci yau kuwa Mamana? Ameena zuba mata abinci taci"
"Ai bana jin yunwa Baba"
"Ba'ayi haka ba uwata gara dai kici ko babu yawa ne babu kyau zama da yunwa kuma kin fini sanin hakan a matsayin ki na likita"
Koda su Ya Abdul suka shigo suma waje suka nema suka zauna bayan sun gaishe dasu,
"Ya akayi ne?" Maman kano ta tambaya Farouq ne ya amsa mata da cewa rakiya mukayo ma Amarya,
Takardar Meenal ta mika ma Malam,
"Takardar micece kuma wannan uwata bayan kin san nidai banyi boko ba balle in gane me aka rubuta,
Kai Baba zoka dubamin takardar nan"
Tasowa Farouq yayi ya amshi takardar a ladafce ya duka anan kusa da Meenal saida ya gama duba takardar kafin ya dago yana kallon Meenal fuskar shi cike da fara'a yace,
"Baba takardar gida ce, kuma sunan Meenal aka rubuta a jikin takardar"
"Gida kuma uwata waya baki kyautar gida sukutum haka?"
Malam ya tambaya yana tsare Meenal da ido,
"Gidan kane ba nawa ba,
Gidan kane na siya maka ina so ka koma can da zama nan gidan hayaniya yayi yawa dan Allah baba karkace min bazaka amsa ba ko kuma kace bazaka koma ba dan gidan bashi da nisa nan k'asan layi ne"
Ta fad'a a marairaice,
"Mamana wayace miki ni ina da burin barin gidan nan inje inyi rayuwa a wani wajen ne?"
"Nasan baka da burin barin nan Baba amma nidai ina son ka koma can ka zauna Baba shi yasa na nemi gidan dake kusa da nan kaga ko a k'afa ne kullum zaka tako kazo nan"
To dai bayan jani inja din da akayi tsakanin Malam da Meenal mutanen gidan suma sun sa baki dan haka Malam ya amshi gida kuma kowa sai albarka yake sama Meenal din,
Yayin da wasu suke ganin cewa kamar ita tafi kowacce mace sa'a a cikin dangi kiran Sallan ne ya watse zaman falon na Malam,
Bayan sun shige kowa haramar sallah yayi ana saukowa daga sallah kuwa aka fara kwasar mutane ana wucewa dasu wajen dinner wadanda sukace bazasuje dinner ba kuma gidan Hajiya aka dunga wucewa dasu ganin d'akin Meenal din,
bayan masu wucewa sun wuce su Aunty fati da Aunty Sas da wasu daga cikin Yaran Malam mata