Showing 81001 words to 84000 words out of 190771 words
lafiya?"
"Lafiya lau Mama ya lafiyan jiki?"
"Alhamdulillah d'an nan ya rayuwa? Sannu kaji naji dad'i sosai wallahi Allah dai ya maka albarka yasa ka gama da iyayen ka lafiya, Allah yayo jagora kaji, nagode kwarai da gaske"
Shi kuma acan gefen shi amsa addu'ar nata yake tayi da "Ameen Ameen Mama nagode, ina dai ta rok'enta akan ta bani dama inzo gida in gabatar da kaina shi yasa nace ta baki wayar muyi magana ko zaki sa min baki ta amince"
"Ayah ayyah indai wannan ne ai karka wani damu kanka,
Tunda har ta had'ani da kai nasan ba k'aramin so take maka ba dan haka ka kwantar da hankalin ka abi komai a sannu dan nidai ka riga ka samu goyon baya daga gareni ban ganka ba amma sosai na yaba da hankalin ka"
Hira sosai Sultana tayi da shi a matsayin itace uwar Meenal kuma tayi na'am da soyayyar da yake ma yarta kafin su kayi sallama sai da ya fad'a mata cewa zai tura ma Meenal din sak'o yanzun sai ta siya mata goro,
Ita ko harda wani cewa "ayi haka d'an nan daga gaisuwa kuma sai ka fara dawainiya tun yanzun, to andai gode Allah ya k'ara bud'i"
Sosai ta dunga kwarara add'u'a shiko sai dadi yakeji irin a dole ya samu k'arbuwa a wajen uwar budurwa,
Bayan wayar ya koma hannun Meenal ne kuma ya k'ara tabbatar mata da cewa zai turo da sak'o dan Allah tayi k'ok'ari ta fita ta siyo ma Mommyn abunda tasan tana so wanda zai faranta mata rai,
Shi baya gari yanzun haka amma yana fatan idan ya dawo zaici arzikin da zata bari yazo ya kawo gaisuwar shi na musamman a wajen Mommy,
Lafiya lau sukayi sallama tana mishi godiya, suna yanke wayar ita da Sultana suka fara dariya kamar wasu tab'abb'u,
"Ke tashi fa muje in tayaki ki had'a kayan ki dan Wallahi yau ban k'ara kwana a gidan nan kafin wancan mahaukacin Salman d'in anjima ya k'ara dawowa,
"Ah zauna tukun muyi magana inji nawane nawa kason idan kud'in suka shigo mana"
"Dallah can ai dai kya bari harya turo kafin muyi kasafi"
Sultana ta bud'e baki zatayi magana kenan idonta ya hango mata Sheikh dake tsaye daga bakin kofa hankalin shi kachokam yana kansu,
Fuskewa tayi kamar bata ganshi ba ta d'auki wayar Meenal ta shiga da sauri ta goge number din mutumin daga jerin kira ta shiga cikin message ma ta goge message din da suka tura mishi na account number sai zufa take had'awa dan tasan yau su kuma sai ta Allah fatan ta dai allah yasa Sheikh baiji hirar su ba Allah yasa yanzun ne ya iso wajen bawai tun d'azun ba,
Ta yunkura zata bar wajen shi kuma ya k'araso fuskar nan kadaran kadahan bazaka iya tantance halin da yake ciki ba,
"Koma ki zauna"
Ya fad'a kai tsaye,
Sai lokacin Meenal ta d'aga kai ta kalle shi,
Zaman Sultana tayi kamar yanda ya buk'ata tana mik'a mishi gaisuwa bayan tayi kokarin boye tsoron dake cikin zuciyar ta,
Gaishe shi itama Meenal ta mik'a hannu zata d'auki wayar ta da Sultana ta turo mata yakai nashi hannun ya d'auki wayar kafin ya samu waje ya zauna,
Wayar bata da matakan tsaro dan haka kai tsaye call long ya fara dubawa sai dai ga mamaki babu wata number wanda akayi kira da ita yanzun dan number din dake wajen duka wad'anda aka amsa kira dasu ne tun na jiya ya gane hakan ne a sanda ya duba lokacin kiran,
"Dawa kuka gama magana a waya yanzun?"
Ya tambaya yana tsatstsare su da ido,
Shiru sukayi kafin Meenal ta d'ago kanta suka had'a ido da Sultana kafin ta maida duban ta kanshi ita din shima yake kallo.
"Uhumm ku nike saurara kuma karku sake kumin k'arya inba haka ba saina b'ata muku rai"
Yana rufe baki ko numfashin kirki bata bari ya sauke ba ta amsa mishi da cewa,
"Bazawari nane ya kira, ya buk'aci in had'ashi da Mommy ni kuma ban shirya gabatar dashi ma kowa ba shi yasa na had'ashi da sultana"
Ta fad'a irin ko a jikin ta, tunda yace kartayi mishi karya ai dama ko baice ba gaskiyar zata fad'a tunda dai tasan bashi da wuta ko aljannar da zai saka ta,
In ya iya takura ita tayi zama ma da wanda magana d'aya biyu zakiji yace "sai na zane miki jiki, saina mareki, sai na karya k'afarki"
Kuma har yanzun ya kasa aikata ko d'aya balle kuma shi Sheikh d'in.
Babu editing
*UMMIEE CE*βπΌ
[9/13, 10:40 PM] zainabusmanummiee584: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 27*
Yanzun ke tsakanin ki da Allah hakan da kikayi kina ganin kin kyauta kenan?
Wannan ai tsabar yaudara ne da cin amana, idan bakya son shi mai yasa zaki yarda ki bashi number dinki, ina amfanin k'arya a cikin zaman takewa, ai gara ki fito ki shaida mishi cewa bakya ra'ayin shi a maimakon wannan k'aryar da yaudarar shi da kikeyi da girman ki da komai,
baku kyauta ba gaskiya"
Da yatsar shi manuniya yake nuna Sultana kafin yaci gaba da cewa,
"Kema ashe haka kike?
Wato k'ananan yara daku kunsan yanda zaku had'a kai ku cuci wani, ke kece mai gyara murya kika amshi waya kikayi magana dashi a maimakon Mahaifiyar ta daya buk'ata, kun manta ne da cewa koda shi baya ganin ku Ubangijin al'arshi yana ji da ganin duk abinda kuke aikatawa a sarari ko a cikin duhu?"
Katse shi Meenal tayi da cewa,
(Shehi ko kuma Ustaz)sune sunan da take kiran shi dashi mai makon ta kira shi da (Ya Sheikh ko Ya Naseer da wasu ke kiran shi dashi a gidan,
"Shehi kaga dagani har Sultana fa duka ba laifin mu bane,
Shi dai mutumin nan tun ranar farko na nuna mishi cewa yayi hak'uri bana ra'ayin tarayya a tsakanin mu amma ya nace ya tasani a gaba da rok'o Allah Annabi akan dai in bashi number na,
Ni kuma girman Allah daya had'ani dashi shi yasa na bashi number d'in,
To fisabilillahi tunda ni nasan ba son shi nikeyi ba ina zan yarda in had'ashi da uwata, kawai dan kar yaji ba dad'i a matsayin shi na Babban mutum shi yasa yau na had'ashi da Sultana kaga idan hankalin shi ya dawo jikin shi a hankali ni kuma zan san yanda zan fahimtar dashi ya gane bana ra'ayin shi amma kafin nan ai kasan sai nabi dashi a sannu tunda ban sani ba ko mugu ne kar inyi gaggawa in b'ata mishi rai ya kullaceni a banza dan Wallahi ance wasu mazan da asiri suke shawo kan mata"
"Koma dai menene bai dace ku yaudare shiba, kuma ma kud'in minene naji yana batun zai tura?"
Zaro idonta Meenal tayi wai mutumin nan lab'e ya musu ne da yazo ya titsiyeta a gaban shi yana musu wa'azi da tambayoyi ko ya abun yake ne? Wai dama suma maza sun iya lab'e ashe, to andai fad'i ba nauyi wallahi ustazu da sauraron hirar mataπ
"Kud'i kumaπ³? Wani kud'in?"
"Ke karki mai dani karamin yaro mana bayan duk abunda kuka tattauna naji ko kin manta a loud speaker kika sa wayar ne?
To kud'in da kuke son yin kasafi akan shi nike magana ki kirashi yanzun nan ki fad'a mishi cewa bakya buk'ata, kinji na fad'a miki dan banga dalilin da zaisa ku amsar mishi kudi bayan kince bakya son shiba"
"To amma shehi nifa ban rok'e shi kudin nan ba ra'ayin kanshi ne yasa yace zai tura kud'in, kaga kuma ai dai babu kyau maida hannun agogo baya koh? Wanda kuma yayi niyyar yin aikin alkhairi ai bai dace a dakushe mishi niyyar shiba sai yaga kamar ana mishi bak'in ciki da ladan dake ciki ne"
Ta fada tana tura baki to waima akan me zai wani ce ta kira tace karya turo kud'in bayan ita harta fara kasafin abinda zatayi da su tun kafin su shigo, Akwai friends event da suke so su had'ama Meelat ita da Maryam da sauran friends dinsu a school,
surprise suke so suma Meelat d'in shi suke ta yima shirye shirye ita dasu Moon kunga ko ai dole ta buk'aci kud'ad'e masu d'an tsoka to tana murna ta kamo jibgegen zakara kuma shine shi wannan ustazun zai wani zo ya nemi yi mata karan tsaye,
Kara wayarta yayi alamun shigowar sak'o,
Yana dubawa ko yaga daga bankin da take amfani dashi ne First Bank,
Budewa yayi yaga Alert ne na zunzurutun kud'i har naira dubu d'ari biyu,
Mamaki da tsoron Allah ne suka cika shi ya kasa cewa komai sai mik'a ma Meenal wayar da yayi yana cewa,
"Duba kiga asarar dukiyar da kukaja mishi,
Shin fashi kuka farayi ma maza ne babu wanda yake da labari ko a ina ma kuka samu fasahar aikata hakan?
Kai shima dai duk yanda akayi b'arawo ne inba haka ba taya zaka d'auki kud'i zunzurutu har naira dubu dari biyu ka turama budurwar dako gidan su baka sani ba kawai daga kayi magana da Maman ta,
Ki kiramin shi yanzun nan ya turo da account number din shi ku maida mishi da kud'in shi ki kuma fad'a mishi gaskiyar cewa ba son shi kikeyi ba dan haka gara ya dena wahalda kanshi"
Kan kame wayar tayi tana tura baki, da ido tama Sultana signal akan ta tashi ta fita daga falon,
Dan haka simi simi Sultanar ta tashi Allah yasa dama akwai Hijjabi a gefen ta dan tun d'azun sukaso zuwa gidan su Meelat sai zuwan Salman ya tsaidasu,
Ficewa tayi daga falon tana fita batayi sallama da kowa ba ta shiga motar Meenal ta tuk'a ta fice daga gidan dan hakan shine matakin farko na tsira daga wa'azin Sheikh dan tasan shi kenan kuma sun shiga uku tunda har ya kamasu kirikiri wa'azine zasu sha har su gaji amma in bai gansu a gidan ba sai dai yayi jininin shi kada'i,
"Yanzun nan shehi fisabilillahi da gaske kakeyi lallai sai na kira shi ya turo account number din na maida mishi kud'in? , kyauta fa ya bani ba tareda na rok'a ba taya zan maida kyauta bayan kaima kasan hakan babu kyau"
"Kyauta daban Meenal wannan daban"
"Babu ban banci tunda bamu rok'e shiba"
"Ok kenan dai kina so kice bazaki kirashi ya turo account number din ki maida mishi ba? To in kinci kin san kudin me kika ci?"
"Nidai koma dai menene kayi hakuri dan gaskiya ina jin kunyar yanda zan kirashi ai sai yaga kamar wulakanta shi kawai nake son yi"
"Meenal!....
Bata barshi ya furta komai ba ta mik'e tsaye tana cewa,
"Bari inje in tambayo idan Baba Malam yace in mayar mishi sai in maida"
Tana kaiwa tsakiyar falon ta kwasa da gudu ta fice sai da ta tabbatar ta yi nisa da falon sannan ta tsaya ta waigo sai suka had'a ido yana kallon ta tana kallon shi kafin ta mishi gwalo harda kashe idon ta guda d'ayaπ ta kuma murgud'a mishi baki ta juya da gudu ta fice daga gidan,
Tunda ya fara had'uwa da yarinyar nan abubuwan ta yake bashi matuk'ar mamaki ya lura da cewa kwata kwata Meenal bata da tsoro ko shayin da zata kasa aikata abunda tayi niyya a gaban shi,
Duk yaran gidan ya lura idan yana waje suna kama kansu suna shayin aikata ba dai daiba amma ita,
Ita kam kanta tsaye takeyin abubuwan ta ko a jikin ta kai shifa yama lura da cewa wani abun idan tanayi ganin idon shi yake sawa takeyin su,
Amma yau dai abunda suka aikata ita da Sultana yasa ya fara jin tsoron mata, idan har su da ba wani hankalin kirki suke dashi ba suka iya aikata haka to sauran matan da suka fisu girma wayau da kuma shekaru su kuma ya suke tafiyar da maza kenan?
Dama kenan haka mata suke tafiyar da namijin da basa so musamman idan suka had'u da sakaran namiji, kuga fa wannan shashashan daya tashi ya tura mata zunzurtun kudin daya isa ya cida marayu na tsayin wata d'aya a k'arance,
"Allah ya yafe muku kuma ya shirye ku"
Ya fad'a yana girgiza kai bayan Meenal din ta wuce,
Shifa mamaki yakeyi ma da akace mishi wai likitanci Meenal din ke karantawa, dan shi a haka yanda yake kallon ta gani yake kamar rashin d'aukar abubuwa da mahimmanci da takeyi bazasu barta tayi karatu mai wahala kamar karatun likita ba.
Suko tunda sun san abunda suka aikata kuma a yanda ta lura tsaf Shehin nan yana iya kai zancen nan gaban Malam dan haka kawai ya bud'e mata aiki, dan haka daga gidan su Meelat Tudun wada suka wuce a ranar babu wanda suka sallama sai da dare yayi nema da Mommy Hauwa taga shiru basu dawo ba ta kira Meenal din dan taji ko a gidan su Meelat zasu kwana shine Meenal din ke shaida mata cewa sun koma Tudun wada zatayi magana da Fauxieyerh ta had'o kayan Sultana gobe ta biyosu dashi can gidan,
Hatta Malam a waya ta kirashi ta shaida mishi cewa suna Tudun wada,
Baiyi fad'aba duk da cewa bai so hakan ba sai ma cewa da yayi ta gaishe mishi da Hajiya,
Shiko Salman a ranar ma sai da ya k'ara komawa gidan Malam din da dare sai kuma ya samu labarin bata gida,
Har gidan su Meelat yaje aka shaida mishi cewa basa nan,
Kwana biyu ya jera yana jelan zuwa gida Hajiya amma Meenal bata bashi daman da zai gana da ita ba daga karshe ma masu gadin ta fad'ama cewa duk ranar da yazo karsu k'ara bud'e mishi gate suce mishi bata nan,
Abun duniya duk yabi ya dame shi dan haka ya yanke hukuncin gara ya sami Uwar gida da maganar kawai,
Baiyi k'asa a gwuiwa ba haka yaje mata da zance a wani zuwa da yayi gidan Hajiya masu gadin suka hana shi shiga,
Dan haka bayan ya koma gida ne ya iske Uwar gida da malam Sulaiman a falon na Malam Sulaiman,
Bayan sun gama gaisawa ne Malam Sulaiman din ke tambayan shi ya aikin gyaran gidan Sarki wanda ya siya a Kaduna yake tafiya,
Shi kuma ya shaida musu da cewa komai ya kammala yanzun gida masu shi kawai yake jira su shiga cikin su,
Ya dade a zaune ganin bashi da niyyar tafiya ne hakan yasa Baban nashi tambayan shi da cewa,
"Salmanu lafiya kuwa ko akwai wani abu ne?"
Kanshi a duk'e ya amsa da cewa,
"Eh to dama dai wani magana ne nake so in fad'a muku"
Yakai karshen zancen yana sosa keya irin yanda maza keyi in suna jin kunya,
"To bismillah yi bayanin ka muna sauraron ka ai"
"Uh uhm uhmm dama... Dama... dama ina so ince muku na samu matar da nike son,
Umm nike son aure... Aure ne, to. To. Tooo shine dama.. Dama nace bari infad'a muku saboda ina son a shige gaba wajen yimin tambaya"
Ya kai karshen zancen da kyar yana jin zufa yana d'an karyo mishi dan bai san yanda suma zasu kalli zancen ba,
"Ah to masha Allah, shine tun d'azun ka kasa magana sai faman kame kame kakeyi"
Cewar uwar gida cike da farin ciki mad'aukaki a fuskarta,
"Bakiji d'an naki yau har da in ina ya fara ba"
Shima Malam Sulaiman ya furta yana ma Salman din dariyar in inan daya dungayi akan maganar da batafi wasu yan takaitattun harafi ba,
"A ina ka samo matar? Ina nufin yar wani gari ne kuma su waye iyayen ta?"
Malam Sulaiman ya tambaya.
Duk'ar da kanshi k'asa yayi sosai ba tareda ya iya kallon d'aya daga ciki su biyun ba ya amsa da cewa,
"Ameenatu Meenal nike so, har cikin zuciyata nike son kasancewa da ita a matsayin matar aurena dan Allah kusa baki ku nema min auren ta"
"Wai naji kamar ka kira sunan Meenal ko tsufane yasa banji sunan da kyau ba Baban su?"
Uwar gida ta fad'i hakan tana kallon malam Sulaiman wanda shima Salman din yake kallo cike da mamaki mad'aukaki,
"Ah ah ya kuma zaki maido tambayar ki kaina bayan ga wanda yayi maganar nan zaune a gaban ki,
Nima dai ban fahimci mai yace ba,
Kai wata Ameenatu Meenal din kake magana ne wai,
Ina fatan dai ba matar da d'an uwan ka ya saka kake so bakoh? dan nidai nasan ita kad'aice Ameenatun da muke kira da Meenal kaf a cikin Dangi?"
Malam Sulaiman ya tambaya yana jiran amsar da Salman d'in zai bashi,
"Ana magana dakai kayi ma mutane banza,
Ko bakaji tambayar da akayi maka bane?" Cewar uwar gida.
Da kyar Salman din ya bude baki ya amsa musu da cewa
"Eh ita nike nufi Aminatun Baba Malam kuma ai aurena da ita bai haramta ba tunda shi yaya bata mishi ba ni tayi min ina son ta zan aureta in zauna da ita"
"Da kata Malam"
Uwar gida ta fad'a a fusace tana d'aga mishi hannu alamun dakatarwa,
"Kai baka da hankali dama ashe ban sani ba?
Matar da d'an uwan ka ya aura ya sakice kake tunanin zamu sa baki a aura maka ita?
Saboda ka mai damu mahaukata,
To baka isa ba kayi kad'an dan haka karma ka sake in k'arajin maganar nan ta fito daga bakin ka koda wasa balle kuma har zancen ya fita ya zaga cikin dangi,
Kajini da kyau na kashe zancen nan bakai ba auren Meenal in auren kake so ka duba a cikin Dangi ko a waje zamu aura maka ko wacece"
Tana gama fad'in hakan ta mik'e fuuuu ta fice bata k'ara sauren mai zaice ba,
Hannuwan shi ya hada alamun roko da jan gwuiwa ya k'ara gaban Malam Sulaiman,
"Abba dan Allah kasa baki wallahi ina son ta please π "
"Salman kana magana ne akan abunda kasan