Showing 42001 words to 45000 words out of 241367 words

Chapter 15 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1575

zata tafi, sannan ga kuma domestic flight ticket from lagos to kano, and from kano to Abuja, bata mance irin hotel din da ta zauna na few hours a garin Lagos ba, sauke idonta kasa tayi bata sake cewa komai ba, Safiyyah ta ja tsaki tace "Wallahi ki ajiye wnn kauyancin naki ki zama wayayyiya ki dinga yin abun da ya dace, komai a rayuwar nan kamawa yake Khaleesat, to wai ku ka zauna apartment daya ba ace rashin kamun kai ba sai don zaki je dubasa bai da lafiya? ni abinda ke daure min kai kenan" Khaleesat dai taki cewa komai with many thoughts running her mind, a haka dai suka rabu kowa ya tafi gida... The next day sai da Safiyyah tasan duk yanda tayi convincing din Khaleesat da dadin baki da masifa da bacin rai, daga karshe Khaleesat ta yarda su je can inda Housemate dinta yace gidansu ne su dubosa amma fa don babu yanda ta iya da Safiyyah ne don har cikin ranta tsoron zuwa anguwan take don unguwa ce na masu kudi a kasar, to in ma sun je su ce me ya kai su? What if iyayensa ko wasu yan uwansa mata na gidan sai su yi yaya kenan? Kasa hakura tayi har sai da tayi ma Safiyyah wannan tambayar, Safiyyah tace "Dai dai kenan in ma iyayensa na gidan, ai ba Nigeria bane nan USA ne, kuma tsaf za su amshe mu hannu bibbiyu su yi farin ciki da zuwan mu don duba Wan su muka je yi bai da lafiya" Khaleesat ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, Safiyya tace "Amma ni har raina ina son sanin dalilinsa na dawowa apartment dinki ya zauna bayan ga nasu gidan can, nace da wani abu a kasa kince min ba haka ba, wallahi kilan ya san ki from somewhere Khaleesat" Khaleesat tace "Sai kuma kiyi ai, nace maki bamu taSa sanin juna da shi ba" Safiyyah tace "Ma ji ma gani dai" Sai da Safiyyah ta fara jan Khaleesat zuwa inda za su siya kayan ciye ciye sannan suka yi ordering Uber da zai kai su unguwan, tun da suka shigo Safiyyah ke kallon manyan Gidaje with fascination, Khaleesat kuwa gabanta sai faduwa yake sai addu'a take a ranta, ita banda Safiyyah tayi insisting da babu abinda zai kawota wai duba Housemate dinta, dai dai kusa da gidan Uber din ya tsaya duk suka sauka, Safiyyah dake zaro ido tana kare ma Glass house din kallo tace "Ke kin tabbata nan ne kar mu shiga gidan mutane a kira mana 911 mu shiga uku Khaleesat" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba amma bata tanka ma Safiyyah ba, Khaleesat ta ciro wayarta tayi dialing number Salem ita kanta zuciyarta bugawa yake gaba daya she is afraid, sai da kiran ya kusa yankewa ya daga, sai gashi a mota zai fito daga cikin gidan, sauka yayi daga motar ganinsu, yana kallon Khaleesat da mamaki yace "Ohh you are here, sannu da zuwa...." Gaishesa tayi ta sauke idonta kasa kamar munafuka, ya amsa da fara'a, Safiyyah ma ta gaishesa sannan tace "Dama ta zo duba jikin Housemate dinta ne shi ne na rakota" Yana gyada kai yace "Ohh that's so thoughtful of her, mu je ciki to...." Suna biye da shi suka shiga cikin katon gidan, Safiyyah dai sai gwale ido take tana bin gidan da kallo ta gefen ido, ita dai Khaleesat gabanta sai faduwa yake sosai ko daga kai ta kasa, after walking briefly sai gasu sun iso entrance din shiga parlon gidan, kofar shiga parlon ma kadai sai ka kalla ka sake kalla, Safiyyah ta saci kallon motoci uku dake compound din kuma masu tsada, suna shiga parlon gidan Khaleesat ta hada ido da Ajay dake zaune kan kujera ga different fruits daga gefensa yana kallon abu a wayarsa at the same time yana cin apple dake hannunsa, 3 quarter ne ba?i a jikinsa with gray polo, tuni ta dauke idonta tsabar yanda ta rikice bata ma san sanda ta bude baki ta gaishesa ba tana makale bakin kofa, hade rai yayi ya dauke kai ya ci gaba da kallon abinda yake a wayarsa.



07087865788
' [5/11, 5:06 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: ('('HALYSAAH('('





By _Khaleesat Haiydar_
'




14....

Safiyyah ma dake kallonsa kamar munafuka tana in-ina tace "Good... good evening sir" Without looking at Safiyyah ya amsa yana cin apple dinsa, Salem na kallonsa speaking calmly yace "Ajay sun zo duba jikin Jay ne" Ajay ya ajiye apple din hannunsa, sai kuma ya kai wayarsa kunne alamar bashi da lkcn basa amsa, ganin haka Salem ya juya ya kalli su Khaleesat yace "Bari in masa magana a sama, za ku iya zama ku jira ni, have a sit pls" Daga haka ya nufi stairs, ko haurawa saman bai yi ba Khaleesat ta zaro ido tace "Innalillahi" da sauri ta koma bayan Safiyyah ganin wani jibgegen kare ya nufo su yana haushi, Safiyyah ta dinga buga ma karen jakar hannunta tana koransa ita ma a tsorace, Salem ya dawo parlon da sauri ganin haushin da karen ke yi zai yi attacking dinsu, Ajay ya mike ya nufi karen yana kiransa yace "C'mon Legend" Karen ya juyo da gudu ya dawo gun Ajay da yayi patting din kansa, Salem ya dawo kusa da su yana murmushi yace "Mu je saman kawai tunda tsoron kare ku ke, ai ba abinda zai maku kawai yaga ba?in fuskoki ne shi yasa" Khaleesat da jikinta ke rawa ta bi bayan Salem da sauri Safiyyah na biye da ita, a haka Salem yayi leading dinsu har sama zuwa Bedroom din Jay, knocking yayi yana tsaye bakin kofar, Khaleesat sai waige waige take tana ganin kamar karen zai sake biyo su saman, sai da Jay ya amsa ma Salem knocking din da yayi sannan ya kallesu yace "Bari in sanar masa yana da ba?i" Daga haka ya bude kofar dakin ya shiga ciki ya kullo, Safiyyah ta rike haSa ta kalli Khaleesat murya can kasa tace "Ke wani tantirin Wan iska ne wannan muka gaida a kasa ya mana walakanci haka?" Khaleesat bata tanka ta ba, har sannan kuma bata daina waige waigen da take ba don gani take ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fa karen nan zai iya biyo su har sama, sai ga Salem ya fito daga dakin yana kallonsu yace "Za ku iya shiga, ni zan Wan fita sai na dawo" a hankali Khaleesat tace "Ohk mun gode" Bude kofar dakin tayi still gabanta na faduwa ta shiga cikin massive room din da sallama Safiyyah dake gwale ido na biye da ita a baya, wani Waddadan kamshi hade da sanyin Ac ne yayi welcoming dinsu a cikin babban dakin, Housemate din nata na zaune saman makeken gadonsa alamar Salem just woke him up, his room was just something else wajen tsaruwa da haduwa, Khaleesat taki yarda ta hada ido da shi zuciyarta na bugawa ta zauna nan ?asan lallausan carpet din dakin, a hankali yace "C'mon Halysaah, ga gefen gado ku zauna, ko ku zauna kan kujera" Khaleesat bata dago kanta ba tace "I am comfortable here" Ya lura kamar she is frightened, ya kalli Safiyyah dake kallonsa bayan ita ma ta zauna, dan murmushi yayi mata yace "Hello...." Kana jin muryarsa kasan he is still recovering, Safiyyah ta gaishesa da fara'a tana tambayarsa jikinsa, yace "Alhamdulillah, ya karatu?" Tace "Alhamdulillah" Ya kalli Khaleesat yace "Ya kwana biyu Housemate? Hope you are doing good?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa tace "Ya jiki?" Yana murmushi yace "Da sauki, Alhamdulillah" A hankali tace "To Allah Ubangiji ya sauwake ya kara lafiya" Yace "Ameen ya Allah" Safiyyah ta ajiye ledan hannunta kusa da gadon dakin tace "She got you this" Khaleesat ta kalleta, godiya yayi masu gaba daya, sai kuma ya fara kokarin sauka daga saman gadon yace "Bari in kawo maku ruwa" Edge din gadon ya zauna kamar bazai iya tashi ba, Khaleesat tace "Aa mun gode, we are okay" Ya kalleta a hankali yace "To ai ba ke kadai nayi offering ba Housemate" After some seconds ya tashi ya bude portable Fridge din dake dakin ya dauko masu ruwa da tsadaddun lemuka duk ya ajiye masu sannan ya fita daga dakin walking slowly, exactly irin kayan jikin Ajay ne a jikinsa shi ma, Safiyyah ta rike haba tana kallon Khaleesat bayan ya fita, sai kuma tayi kasa da murya tace "Khaleesat kin dai ga arziki ko? Gidansu kenan fa a Amurka ina ga Nigeria kuma?" Khaleesat ta hade rai tace "Pls stop this Safiyyah" Safiyyah ta rufe baki da sauri, sai kuma tayi kasa sosai da murya tace "Kuma haka fa, kar ace da Cctv a dakin mu ji kunya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ki ji kunya dai, tun da mun gaishesa ki tashi mu tafi kawai" a hankali Safiyyah tace "Gaskiya Housemate din nan naki is more than nice and calm, ni har naji yana burgeni wallahi, look how he welcomed us warmly duk da bashi da lafiya" Khaleesat ta daga ido ta kalleta sai dai bata ce komai ba, ita dai Safiyyah sai bin katon dakin take da kallo with fascination, tayi kasa da murya tace "In na samu irin wannan dakin ai mance me ya kawo ni kasar ma zan yi gaba daya, anya ma kuwa student ne Housemate din nan naki" Khaleesat ta hade rai tace "Tashi mu tafi tunda mun dubasa Safiyyah" Safiyyah tace "Amma ai kya jira ya shigo mu yi masa sallama ko, dadina dake a ko ina sai kin nuna halin ki, kamar ana koranmu daga shigowa gida kice mu tashi mu tafi" Budewar kofar dakin ya sa duk suka yi shiru, Housemate dinta ya shigo da sallama ya zauna kan kujeran dakin ya jinginar da kansa da kujeran, sai ga wani chef din gidan ya shigo da wasu tsadaddun cookies ya ajiye masu kusa da su, sannan ya juya ya fita, Jay na kallon Khaleesat yace "Naga kina son cookies sosai Housemate, here are some for you and ur frnd" Bata yarda ta kallesa ba tana wasa da gyalenta tace "I am okay, tafiya ma za mu yi" a hankali yace "So soon? Amma sai kun ci cookies tukun" Khaleesat ta Wan kallesa suka hada ido a karo na farko tun shigowarsu dakin, sosai taji gabanta ya fadi tayi saurin sauke idonta, ya kalli Safiyyah yace "In bazata ci ba ke ki ci abunki... Amma ban san sunanki ba kawar Housemate" Safiyya tayi murmushi tana bude cookies din ta dau guda daya tace "Sunana Safiyyah Adam" Yace "Maa sha Allah, it's nice meeting you Safiyyah, i am Jawwad Ahmad, or you call me Jay" Safiyyah tace "Nice meeting you too Jay" ita dai Khaleesat wasa da gefen veil dinta kawai take kanta a kasa, Safiyyah ta bude handbag dinta saboda kiran wayarta da ake yi, tana dubawa taga Cousin brother dinta ne, ta mike tace "Let me pick a call pls" Jay yace "Alright Safiyyah" Kofa ta nufa ta bude ta fita sannan ta kullo masu kofar, ledan da suka shigo dakin dashi ya Wan bude yace "You got me all this Halysaah" Khaleesat ta Wan kallesa tace "Um" Yace "Ohk thank you so much i really appreciate" Tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin?" Yace "I am getting better gradually, daxu sai naji ina sha'awar wannan tuwon da kika yi some days back" Tana kallonsa tace "Na vegetable soup?" Yace "No, wannan da na kasa ci, the dark soup, I can't remember the name" Bata san sanda tayi murmushi ba tace "Ok miyan kuka?" Yace "Shi... kawai naji shi nake son ci sincerely" a hankali tace "Ohk zaka je can gida anytime soon ne?" A hankali yace "Idan na samu lafiya in sha Allah" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam idonsa na gun different direction, Ajay ne ya bude kofar dakin, kai tsaye ya shigo ya nufi Jay yana mika masa wayar hannunsa yana kallonsa, ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata kalli inda yake ba, Jay ya amshi wayar yana duba screen din, sauke ?afafuwansa yayi daga kan kujeran da yake zaune ganin wanda ke kan layi, ya kai wayar kunne da ladabi yayi sallama hade da gaisuwa, sai kuma yace "Alhamdulillah Abba da sauki, wayar a silent yake ne shi yasa" Sai kuma ya daga kai ya kalli Ajay jin abinda Abban ke ce masa, a hankali yace "A'a ba haka bane Abba, i do eat... but not much, ba gaskiya ya fada ba" Daga haka yayi shiru bai sake cewa komai ba, after a minute yace "To in sha Allah Abba, Allah ya kara girma" Sai da ya jira Abba ya katse wayar sannan yayi wurgi da wayar saman gadonsa yana kallon Ajay, wani kallo Ajay yayi masa ta gefen ido ya juya ya tafi ya dau wayarsa a kan gadon sannan ya fice daga dakin, Khaleesat ta gama tura ma Safiyyah text din da take na cewa tayi masu ordering Lyft su tafi gida, sai kuma ta daga kai ta kalli Jay, ganin mood dinsa ya canza, a hankali tace "Baka cin abincin ne ko?" Yace "Ki kyalesa mana, i took cereal daxu da safe kuma a gabansa, shi in bai bata min rai ba baya jin dadi a rayuwarsa" Khaleesat tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can dai tace "To ai Cereal ba abinci bane, ka dai dinga ci ko kadan ne" ?an murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace "Shikenan, za mu koma, Allah Ubangiji ya baka lafiya" Yace "Baza ki bari Salem ya dawo yayi dropping din ku ba?" Tace "Aa, Safiyyah nasan brother dinta ne ke kiranta a waya, kaga tun daxu muka gama lectures bata koma gida ba" Yace "Ohk ni bari in ajiye ku" Khaleesat ta zaro ido tace "Aa kai da baka da lafiya, za mu yi ordering Uber do not worry about us pls" Khaleesat ta mike, yana ganin haka shi ma ya tashi, amma sai da ya dafa kujera for sometime saboda juya masa da kansa ya fara yi, A hankali Khaleesat tace "Pls kar kayi stressing kanka, just lie down and rest" Ya dago kansa yace "No, let me see you downstairs" Juyawa tayi ta nufi kofa, ya bi bayanta, ga mamakinta sai ta ga Safiyyah tsabar samun waje tana zaune parlon dake upstairs tana kallo tana cin cookies ga lemo a gabanta, to a ina ta samo lemun da cookies, Safiyyah ta washe baki ganin Khaleesat sannan ta mike tace "Shikenan mu tafi?" Jay da ta hango ne yasa tayi tsit, Khaleesat ta nufeta suka fara sauka downstairs a tare amma gabanta faduwa yake kar su kara ganin karen daxu, hakan yasa ta bari Safiyyah ta shiga gaba, Jay na biye da su a baya har suka sauko downstairs, ai ko karen na ganinsu ya nufo su da gudu yana haushi, Khaleesat ta juya a tsorace zata koma sama ta ci karo da Housemate dinta dake bayanta, ya rikota da sauri yace "C'mon, are you afraid of dog Halysaah?" Bayansa ta koma zuciyarta na bugawa, Safiyyah kuwa sai kora karen take da jakar hannunta fuska daure, shi dai Ajay na zaune parlor tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai ya ci gaba da kallon Football da yake, sai da Jay ya kori karen sannan ya juya da gudu ya koma gun Ajay ya zauna saman kujeran kusa da shi, Jay ya juya ya kalli Khaleesat da ta marairaice ita ma tana kallonsa, ya Wan yi murmushi yace "Ba abinda zai maku ai, bai san ku bane shi yasa...." ita dai bata ce komai ba, Jay ya jufi Ajay yace "Ajay ina makullin motana?" Ajay yace "Me zaka yi da makullin mota?" Khaleesat dai tuni ta nufi kofar fita parlon da sauri don ko kallon Ajay bata son yi, Safiyyah kam tana kallon Ajay tace "To sai anjima, Nagode sosai" Yace "Allah ya tsare" sallama tayi ma Jay shima sannan ta bi bayan Khaleesat, Jay yasan bazai basa makullin ba, hakan yasa ya duba aljihun Ajayn ya zaro few dollars sannan ya juya ya bi bayan Safiyyah, duk yanda yayi da Safiyyah ta amshi kudin taki amsa, Khaleesat tuni ta kusa fita daga gidan gaba daya, a haka Safiyyah ta bi bayanta. Safiyyah na kallon Khaleesat bayan sun shiga Lyft har sun fara tafiya ta rike haSa tace "Ke ashe wannan gayen da muka yi misunderstanding da farko da muka shigo gidan yana da kirki sosai, in gaya maki da na zauna parlon nan na sama ni kadai ya zo wucewa ya ganni sai ya tsaya yayi powering min TV, har da kunna min wutan parlon, ya kuma nuna min fridge in dau lemo in sha, wallahi i never expect such kind gesture from him duba da yanda ya amsa mana gaisuwanmu da muka shigo parlon da farko, ashe mun yi misperceiving dinsa ne" Khaleesat tayi kamar ma bata ji abinda Safiyyah ke cewa ba.


07087865788
' [5/12, 6:46 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6


('('HALYSAAH('('





By _Khaleesat Haiydar_
'




15.....

Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune parlor tana duba wani reading material dinta wayarta ya fara vibrate, daukan wayar tayi taga number Salem, ita dai kallon screen din kawai take at first, after some seconds ta daga ta sa Hands-free tayi shiru tana saurare, daga daya bangaren aka mata sallama, muryar Housemate dinta ta ji, ta amsa sallamar tare da gaishesa, yace "Ya kika je gida Halysaah?" Tace "Lafiya lau" Yace "How about Safiyyah?" Tace "Tana can gidansu" Yace "Good, thank you so much for the visit" a hankali tace "Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen Housemate" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayar, bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa ta ga Abdul ne, sai a sannan ta tuna damuwar da take ciki for days now, nan da nan mood dinta ya canza, tayi picking call din ta saka hands free sannan ta ajiye a gefenta tana ci gaba da duba reading material dinta a hankali ta gaishesa, yace "Didn't you see the money i sent to you?" Ta girgiza kai tace "Ban kula ba" yace "To ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login