Showing 72001 words to 75000 words out of 241367 words

Chapter 25 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1578

bane jiya, frnds dinsa suka zo gidan yace masu ai ni yarinyar abokinsa ce na zo exam" Safiyyah ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa tace "To meye a ciki, in bai fadi haka ba so kike su yi zaton zaman kanki kike cikin maza? Ai nan kare maki mutunci yayi, kinga dai ai abokan za su yi tunanin baban naki ne da kansa ya kawo ki gidan abokansa ki zauna kiyi exams" Khaleesat ta wani kalleta tayi shigewarta bandaki, Safiyyah ta zauna gefen gado tana kyakyala dariya tace "To duka duka shekararki nawa da bazai ce ke 'yar su bace, ni dai ban ga laifinsa ba" Bayan duk sun yi sallah Safiyyah tace "Kin ga ki tashi mu je in taya ki girkin kafin mutumin can ya fara doka min kira yanzu kamar makaho" a hankali Khaleesat tace "Ni kamar ma kar inyi girkin, i don't want to go downstairs" Safiyyah tace "Amma ai ko don saboda Housemate dinki sai kiyi, tunda kika ga haka kilan shi ma yana son cin tuwon da vegetable soup ne" Khaleesat ta marairaice tace "To ai ni i am not comfortable ne, ban ma taba shiga kitchen din ba fa" Safiyya ta mike tace "Mu je, ai ni na taSa shiga har nayi girki" A haka ta ja Khaleesat suka sauka downstairs, da ba don Safiyyah tace kilan Housemate dinta na son cin abincin ba da babu abinda zai sa ma ta yarda tayi girkin, har sannan AJ na parlon amma babu karen a kusa da shi, shi dai wayarsa kawai yake dannawa bai kalli direction dinsu ba, a haka Safiyyah ta ja ta har zuwa kitchen din gidan, after a while suka gama girkin, Safiyyah tayi take away din wanda zata tafi da shi gida tana kallon Khaleesat tace "Ke ba yanzu zaki ci abincin bane naga baki zuba ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Sai anjima" Safiyyah ta tabe baki tace "To mu je, Allah dai ya sa Yaya Musty bai kirani ba" Suna fitowa main parlor suka tarar babu kowa a parlon, suka haura sama, kafin su karasa hanyar dakin da Khaleesat take aka bude kofar wani Bedroom din wata mace da bazata wuce 23 years ba ta fito, English dressing ne jikinta amma kana ganinta kaga Hausa Fulani, she is so beautiful, yarinyar ta bi su da kallo da mamaki, Safiyyah na murmushi tace "Hi dear" Yarinyar ta mayar mata murmushin tace "Hlo" Ita dai Khaleesat ta dauke kai tana biye da Safiyyah suka tafi dakin da take, Safiyyah ta kulle kofar ta dora hannu a ka tace "Na shiga uku, ke yanzu Khaleesat me yasa baza ki daina abu kamar warce bata waye ba? Mun ga yarinya ta fito daga daki kika san ko gidansu ne maimakon kice mata Hi kamar yanda kika ga nayi amma kika wani yi shiru kamar kurma kina bin ta da ido?" Innocently Khaleesat tace "To ai naga bamu santa bane" A fusace Safiyyah tace "Gaskiya na gaji da halin ki, ke ko ina sai kin sa an mana kallon en kauye? Ki ga yarinya er gayu wayayyiya abinda kema wayancewa zaki yi yanda nayi ki ce mata Hi, to meye amfanin ilimin in baka iya zaman duniya da kowa ba? Ko Wan uwan nan nasa da kike complain a kai kece baki iya siyasar zama da shi ba, ba gashi ni yana kulani ba har da tambayata ya exams, gaskiya ki canza hali Khaleesat, ya ci ace kin yi koyi da ni akan abubuwa da yawa" Khaleesat dai bata tanka ta ba, Safiyyah tace "Duk sai kika sa kunya ya kama ni tsamo tsamo, yanzu zata su kuma wa ennan en kauyen daga ina" Safiyyah ta dau jakarta tana ciro wayarta taga miss calls din Mustapha tace "Ahaf ai na sani" Tsaki ta ja ta fara kokarin order din ride din da zai maida ta gida. AJ ya bude kofar dakinsa jin ana knocking, tana kallonsa daga inda take tsaye ba tare da taje kusa kusa da kofar ba tana Wan kame kame tace "Ya Ajay, naga wasu mata ne a gidan, kun yi baki ne?" AJ ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, su nawa?" Ta Wan bude manyan idanuwanta tace "Su biyu" Ya gyada kai yace "Good, you saw the fair Slim one that is like yellow pawpaw?" Yarinyar tace "Sure" Yace "To sabuwar budurwar saurayinki ce, all of a sudden ya tattaro ta ya dawo da ita gidan nan suke zama tare, when i said i am reporting him back home he threatened me" The lady look totally speechless and confuse, a hankali tace "Budurwarsa kuma Ya Ajay?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da ke ne balle in maki karya?" Shiru tayi bata ce komai ba ta sauke idonta kasa, yace "She's been in this house for 3 weeks now, ya kai ta school ya dawo da ita" Yarinyar ta sake daga ido ta kallesa, AJ ya daga kafada ya kulle kofarsa, juyawa tayi tana tafiya a hankali ta bar wajen. Har waje Khaleesat ta raka Safiyyah bayan ta takurata ta rakata, sai ma da suka jira Lyft din ya karaso sannan Safiyyah ta shiga ta mata sallama, Khaleesat ta daga mata hannu sannan ta juya ta koma cikin gidan, zaune ta ga yarinyar daxu a parlor, suna hada ido Khaleesat ta sauke kanta sai ta kasa wuce sai da tace mata "Hi, i am Khaleesat" Ido kawai yarinyar ta zuba mata tana kallonta babu yabo babu fallasa kuma babu alamar zata amsa mata, hakan yasa Khaleesat ta fara tafiya ta wuce sama, lkci daya jikinta yayi sanyi ta shiga dakin da take ciki ta kulle. AJ ya fito dakinsa zai sauka downstairs kenan sai ga Jay ya hauro sama fixgosa yayi a fusace yace "Are you out of ur senses Junaid, what did u just do?" AJ yace "Ban gane what did i just do ba, Hadeeyah came, she requested to know the lady she saw in this house, kai kuma baka isa inyi karya saboda kare ka ba tunda ba tsoronka nake ji ba, when i told u to look for another alternative for the brat ai mayar dani mahaukaci kayi" Bude kofar wani daki aka yi sai ga Hadeeyar ta fito da Handbag dinta, Jay ya sake AJ, ya bi ta da kallo yace "Hadeeyah" ko juyawa bata yi ba ta ci gaba da sauka downstairs, ita dai tasan AJ ba wasa yake yi da ita ba balle yayi mata karya, yaushe ma ya sake maka fuska balle ya maka karya, Jay yace "Look Hadeeyah, ko da wasa kika ce zaki ma people back home wannan magana i won't take it likely with you, and that will be the end between me and you, cause u never gave me a listening ear" Sai a sannan ta juyo tace "And so effing what? Wannan ne dalilin da yasa all this days baka da lokacina dama ko Ya Jawwad? I am not surprise" Tana kai wa nan ta sauka ta nufi hanyar fita gidan, Jay ya kalli AJ da ya daga kafada shima yana kallonsa. Jay wasn't even that bordered kamar babu abinda ya faru, amma gaba daya ya fita harkan AJ a gidan, ko kallon inda yake baya yi, ya canza code din kofar dakinsa ta yanda ma bazai shigo masa daki ba, yasan ba lallai ma Hadeeyah ta gaya ma yan gida komai ba, she won't even dare try that, amma still yaki ko da kiranta a waya, dama ita ce me kiran nasa, daga Oxford University take kuma bata ma ce masa zata shigo Maryland ba she just came without notice, ita ko Khaleesat bata ma san abinda ke faruwa a gidan ba amma abinda Hadeeyah ta mata ya tsaya mata a rai. Ranan friday Khaleesat suka yi second to the last exam dinsu, na karshen kuma za su yi ranan talata, gaba daya ta kagu su gama ta bar kasar zuwa sannan hankalinta yayi gida, she just want to go home, duk da tasan Housemate dinta zai ce zai siya mata flight ticket amma gani take she is just a burden to him, for weeks now hidima kawai yake da ita, ya kai ta schl, at times ya jira ta gama jarabawa ya maidota gida, wani lkcn dab da sanda yasan zata fito exam zai koma schl din don daukota, he really tried for her during this period and he is always making sure that she is fine, bata ma san ta inda zata fara appreciating din shi da Safiyyah ba, they where by her side all through, ba don su ba da bazata iya jarabawan ba ma, yau kam tunda ta tashi take jin ta wani iri tana dai kwance da tunani iri iri a ranta, ji take kamar ta jawo monday. AJ na zaune reading nook din dake parlor yana kokarin hada references dinsa a laptop dinsa, ga textbooks kaca kaca a gabansa, gaba daya Jay ya bi ya goge duk wanda ya tura masa ta WhatsApp, infact duk wani abu da Jay yasan AJ zai karu da shi na bangaren PhD da suke sai da yabi ya goge tas, shi da AJ bai nuna masa ma yasan abinda yayi ba, shi yasa ya dukufa tun asuba yake reading nook, Waga kai yayi bayan yayi perceiving din wani turare da ya gauraye ko ina na parlon, he was a bit shock ganin wanda ya shigo parlon tare da wasu mutane biyu suna biye da shi, ya sauke idonsa, he was surprise and shock, sai kuma ya mike ya dawo cikin parlon, ya Wan dukar da kansa yace "Sannu da zuwa Abba" Wanda ya kira da Abba yace "Ya karatun? Ina Ahmad?" AJ yace "He is upstairs, Abba surprise visit ka mana" Zaunawa Abban yayi saman kujera yana amsa gaisuwan da ma'aikatan gidan ke masa cike da ladabi sannan ya kalli AJ yace "I just branched to check on u both, daga England mu ke munje wani taro" AJ dai ya sunkuyar da kansa, sai kuma ga wata mata da bazata wuce 50 ba cikin shiga ta alfarma ta shigo parlon da wata yarinya that is 16 years old, AJ dai ya shafa kansa don shi abun ma dariya ya fara basa, ya dai gaisheta ta amsa, yarinyar ta tafi ta rungumesa tace "Ya AJ naga ka zama kato, are you going to the Gym?" Matar da suka shigo tare ta nemi waje ta zauna tace "Allah sa karatun yake" Wani kallo ya mata ta gefen ido ya wuce sama su kuma masu aikin gidan suka tafi dauko bottle water da lemo, direct dakin Jay ya nufa a dai lkcn da Jay ya bude kofar dakinsa ya fito, AJ yayi wata dariyar bosawa yace "Wallahi ga Abba da Aunty a parlor" Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, can yace "Abba da Aunty kuma?" AJ couldn't stop laughing, Jay ya Wan leka downstairs yaga da gaske ne, buda baki yayi yana kallon AJ da ya kasa daina dariya, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya jawosa yace "Look, let's talk pls Ajay...." Ajay yace "Talk about what? Ba dai baka jin maganata ba, zaka san yanda zaka yi da yarinyar nan yau, kaga ban ma kai report ba sun zo da kansu za su gane ma idonsu rayuwar da ka jefa kanka a Maryland" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ ya daga kafada irin ko a jikinsa din nan ya sauka downstairs yana murmushi, Jay ya fi minti biyu tsaye thinking of what yo do, daga karshe dai ya nufi bangaren AJ, yana tura kofar dakinsa yaji dakin a bude, juyawa yayi ya tafi dakin da Khaleesat take yayi knocking, duk da ba bacci take ba amma idonta a kulle, ta bude idonta ta mike zaune sai gashi ya shigo dakin, Calmly yace "Bacci kike ne Halysaah?" Ta girgiza masa kai tace "A'a" yana kallonta yace "Ya na ganki haka ko baki da lafiya ne?" Nan ma ta girgiza masa kai tayi shiru, ya kwantar da murya yace "Gaya min gaskiya, ko dai tunani kike Housemate?" Calmly yake mata maganar kamar ba komai, ta Wan yi murmushi cikin sanyin murya tace "A'a" Yace "Good, i think we have visitors a gidan nan yau, i will change you to another room wanda babu wanda yake shiga zuwa har sanda za su tafi, nasan baza su wuce kwana biyu ba bakin za su tafi in sha Allah" Ita dai tayi shiru tana kallonsa, ya sakar mata murmushi, ta sunkuyar da kanta, yace "Alright, ta so mu je ko?" Sauka tayi daga kan gadon ta dau gyalenta, yace "I will bring you all u need to the room afterward" daga haka ya nufi kofa tana biye da shi, direct ya nufi bangaren AJ da ita, ya bude kofar dakin yana kallonta yace "Here" ta sauke idonta tana kallon cikin dakin dake wani kamshi na musamman sannan ta shiga, ko da wasa bata san dakin AJ bane, Jay yace "I will be back soon Halysaah" Ta gyada masa kai, ya jawo kofar sai dai bai kulle ba tunda bai san code dinsa ba yanzu, sai bayan da ya bar wajen yaji dariya ya taho masa, to yanzu ta ina ma zai fara lallaba AJ, kawai yasan ya ma gama kashe AJ, to in ba haka ba bai san way out ba don bangaren AJ ne kadai Halysaah zata tsaya da babu wanda zai san tana gidan tunda babu me zuwa ko kusa da bangaren nasa sanin halinsa, amma kaf din gidan yasan Aunty sai ta bude ta shiga banda part din AJ, downstairs ya sauka da sauri don zuwa gaida su Abba, Khaleesat dai ta kasa daina bin dakin da kallo, komai na cikin dakin fari ne kal har wani kyalli yake tsabar neatness, ita abun yana mata kamar dakin wani important person ne a gidan Jay ya kawota, ta karasa ta zauna gefen gadon a hankali, she just don't know why she is not comfortable with the room. Jay dai na zaune parlor ne amma gaba daya hankalinsa na kan AJ dake ta shan fruit din da aka kawo ma Abba hankali kwance kamar shi aka kawo ma, Aunty kuwa tana dakin Abba dake nan downstairs tana gyara masa, AJ ya mike zai tafi sama, Jay na ganin haka ya mike ya bi bayansa da sauri, bayan sun haura sama Jay yace "H???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ey let's talk AJ" AJ ya wani kallesa, sai kuma yayi wani dariyar shakiyanci yace "Talk about what? Pls sort ur self out, ka daina ma involving dina a crime din nan da ka aikata, kar a zata tare muka aikata" Jay dai ya fara kokarin danne dariyar da ya taho masa don bai ma san ta inda zai fara masa bayani ba.



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H? [5/22, 6:50 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Parlon dake sama Jay ya ja AJ zuwa can yace "Ohk now, let me explain Bruh" AJ na girgiza kai yace "I am not interested pls Jay, ni fa bana son ma kana min magana a gidan nan kar ayi zaton tare mu ka kawota" Jay yace "Naji.... bayan yanzu bazan sake maka magana ba, kawai dai na duba naga duk gidan nan dakin ka ne kadai yake da wahalan shiga..." Nan da nan AJ ya hade girar sama da ta kasa yana kallonsa yace "I don't understand, me yasa kake using dakina kake misali? What are you insinuating? What is ur point??" Jay ya shafa sumar kansa a hankali yace "My point is, na kai Housemate dita dakin ka for the meantime before i find a way out, nasan can ne kadai su Aunty baza su ganta ba, tunda dakin ka out of bound ne" Haka AJ yayi dropping jaw yana kallon Jay baya ko kiftawa with shock written all over his face, Jay ya sosa kansa zai yi magana suka ji muryar Hajiya Rukayya warce suke kira da Aunty, ta karaso parlon tace "Jay ka je Abbanku na magana a parlor" Jay yace "To gani nan zuwa Aunty" Ta Wan kalli AJ sannan ta juya ta bar parlon, Jay ya sauke ajiyar zuciya yana kallon AJ that was still looking at him ko kwakkwaran motsi baya yi, da alama ya ma kasa cewa komai, Jay yayi patting Win shoulder dinsa yace "I know u gat my back Bruh, you won't love seeing Abba Mad at me" Yana fadin haka ya juya ya bi bayan Aunty yana sauke wani ajiyar zuciya, after almost 15 mins Jay ya dawo sama, zaune ya tarda AJ a parlon dake sama ya tallabi chin dinsa da duk hannunsa biyu yana girgiza kafa, he looks restless, Jay dai ya danne dariyar da ya taho masa da kamar zai juya ya koma downstairs, AJ na ganinsa ya mike ya nufesa a fusace ya fixgosa yace "What offense have i done to you Jawwad? Why my room? Why will u take her to my privacy, my own comfort zone, what sort of nonsense is this plss? Dakina fa? Meye hadina da ita zaka kai ta har Bedroom dina?" AJ was so mad at him, nan da nan idonsa suka sauya launi, Jay yace "To Abba dai na kiran ka, je ka dawo sai ka ci gaba" AJ dai sai kallonsa yake yana huci, can ya turasa ya bar parlon kamar zai tashi sama, Jay ya wara ido yana shafa kansa yana Wan murmushi, karkari dai iya abinda zai yi kenan bazai wuce haka ba, kuma ba wani kiransa da Abba yake yi kawai wahala ne bai so yasa yace masa ana kiransa downstairs, dakin Khaleesat ya koma ya dauko mata box dinta da abubuwan da yasan zata yi needing ya kai dakin AJ, Khaleesat ta mike da sauri ganinsa, a hankali tace "But Housemate i am not comfortable in this room" ya Wan bude ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login