Showing 159001 words to 162000 words out of 241367 words

Chapter 54 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1572

ce masa bata da lafiya, sai dai tayi ta daurewa a haka, in ma ta gaya masa don ya zagi iyayenta ba komai bane a wajensa, in zazzaSin ya rufeta sai dai ta kwanta har sai sanda zata ji dama dama sannan ta daure ta tashi. Ranan Friday tana dakinta a kwance ko breakfast bata yi ba har kusan karfe sha biyu da rabi, zuwa yanxu ta gaji da cin indomie da ma tana da dakakken yaji sai ta dinga yin ko shinkafa da mai da yaji ne amma babu, indomie duk ya fita a kanta bata iya ci ko ta dafa, gashi haka take dafasa babu yaji balle albasa, bude kofar dakin nata yayi ta mike zaune da sauri tana kallonsa gabanta na faduwa, kamar zai fasa mata dodon kunne taji yace "Ina Cufflinks din da na bari a parlor shekaranjiya?" Sauka tayi daga kan gado, ita dai ta gyara parlon ta goge ko ina jiya da yau amma bata ga wani Cufflinks dinsa ba, a hankali tace "Toh bari in duba a parlon" Wani mugun kallo yake mata hakan yasa ta raSa tabi ta gefensa ta fita daga dakin zuciyarta na bugawa ta tafi parlor tana dudduba Cufflinks din, da alama masallaci zai je don yin sallan juma'a, babu ta yanda za ace iya Cufflinks din da yake tambayarta yake da shi a gidan, amma sbda neman hanyar da zai musguna mata yake shi yasa zai saka ta gaba ta fito da abinda bata gani ba, kuma rabonsa da gidan tun shekaranjiyan, tana cikin dube dube a parlon shi kuma yana tsaye fuskarsa a murtuke alamar he is loosing his patient aka bude kofar parlon, Momy ce ta shigo da Cousin sis din Alhaji Musa, warce suke kira da Ummu, Yau kwanan Ummu uku a Nigeria daga Dubai inda take aure da yaranta duk a can, kuma a yau zata koma Dubai shi ne ta sa a kawota ta ga matar Abdul kafin a kai ta airport, duk da Abdul yaje ya gaisheta san da ta zo, Khaleesat da duk a rude take ta kalli Abdul a hankali tace "Wallahi ban gansa ba da nake gyaran parlorn jiya da yau, kilan ka sha'afa ko a daki ka bar su ne ka manta" Bata rufe baki ba ya sauke mata wani gigitattcen mari yana huci ya fixgota yace "Ni zaki gaya ma a daki na bar su?" Ta dafe kuncinta hawaye cike idonta tana girgiza masa kai, nan da nan fuskarta yayi ja, ko minding uwar sa da Cousin sis din Babansa da suka shigo parlon bai yi ba, duk suka yi cirko cirko baki bude suna kallon ikon Allah, cikin tsawa yace "Baza ki fito min da shi ba sai na maki dukan tsiya a nan?" Tana shesshekan kuka tace "Nace maka ni ban ga wani links din ka ba wallahi...." Bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin, Momy da taji ranta yayi fari tass cikin kwantar da murya tace "Subhanallahi, Babana ka bi a hankali, hakuri ake Babana" Ummu ta jefar da handbag dinta kan kujera ta nufesa cikin bacin rai tace "Abdallah?? kana hauka ne kake marin mace haka don uban ka?" Momy ta wani hade rai tana kallon Ummu, Abdul yaki ko kallon Ummu dake masa magana, ya wani haure Khaleesat a mugun fusace har sai da ta fadi kasa, Wani Mari Ummu ta sauke masa a fuska, cikin fushi tace "Ashe kai jahili ne shashasha ban sani ba?" Juyowa yayi yana kallon Ummu da mamaki baya ko kiftawa, Momy ta dinga huci tana kallon Ummu ita ma, nan da nan idanuwanta suka kankance don bacin dai, tunda ta haifi Abdul bata taSa marinsa ba haka ma ubansa sai gashi yau an maresa a gabanta, Abdul dake kallon Ummu kamar me counting din words dinsa yace "Ummu akan wannan jakar yarinyar kika mareni??" Ummu tace "Na mare ka din, zaka rama ne? Wawa kawai mahaukaci ka saka yarinya karama haka a gaba kana duka? Tarbiyar da aka maka kenan? In na san abinda zan zo in tarar a gidan ka kenan uban me zai kawo ni?" Abdul da idanuwansa suka sauya launi ya kalli Khaleesat yace "Ki je... na sake ki" Yana fadin haka ya dau makullin motarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda yace ba, Momy ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "To Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Ummu tace "Ke kuma Muhusina kin ci darajar Musa banda haka da babu uban da zai hanani rama ma Wa na marin da kika masa don tunda na haifesa ban taSa marinsa ba haka ma ubansa, kuma Abdul yayi min dai dai hukuncin da ya dauka, dama me ake da auren er gidan talakawa er gidan matsiyata? Ai ba class din mu bace ita, kuma duk bama goyon bayan wannan tsinannen auren, kawai irin wannan rana muke ta jira gashi Allah ya kawo mu cikin ruwan sanyi, Alhamdulillah Allah na gode maka, Allah na gode maka, yau zan yi bacci cikin farin ciki da kwanciyar hankali burina ya cika, effort dina kuma bai tashi a banza ba" Momy na kai wa nan ta nufi kofa tana tafiya gansan gansan farin ciki fal a ranta mara misaltuwa tana murmushi ta bude kofar parlon, Khaleesat ta bi Momy da kallo with shock ko kwakkwaran motsi ta kasa tsabar mamaki, maganganun Momy suka dinga yawo a kanta kamar a mafarki, Ummu ta zauna gefen kujera ta dafe kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai a sannan Khaleesat taji hawaye masu zafi na silalowa fuskarta, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta har kasa ta fito.....


[6/26, 9:27 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat na fitowa parlor suka hada ido da Ummu dake kokarin kiran Alhaji Musa da wayarta cikin bacin rai, sunkuyar da kai Khaleesat tayi tana goge hawayen dake ta zuba idonta, Ummu tace "Zo ki zauna tukunna diyata" Khaleesat tayi shiru bata ce mata komai ba don har cikin ranta bata ji zata iya zama a parlon ba kamar yanda Ummu ta umarceta, amma kar tayi disrespecting matar duba da tsaya mata da tayi sanda Abdul ke ci mata mutunci yasa kawai ta duka kasan carpet kanta a kasa, Sau uku Ummu na kiran wayar Dad din Abdul, daga karshe ya daga kiran, cikin fushi ta fara koro masa abubuwan da ta zo gidan Abdul ta tarar da kuma abinda Abdul ya aikata daga karshe, Alhaji Musa dake ta sauraronta ya jira har ta gama, sannan yayi gyaran murya yace "Ai ina ganin Muhusina wannan ba issue bane da zaki shigar da kanki farat daya, ke da ba ma a kasar kike ba zuwa kawai kika yi, i don't think it's proper kiyi involving kanki sama ta ka, it's not done that way, alright? kuma tunda kika ga ya saketa definitely yana ganin hakan shi ne dai dai so meye zaki damu kanki, ko mu iyayensa we are not in the rightful place to question his act, okay? decision dinsa ne, so just stay out of what u know nothing about Muhusina, ba naji kin ce flight din karfe biyu gare ki ba? Ko kin daga tafiyar taki ne?" Kasa cewa komai Ummu tayi tsabar mamaki, kana ganinta kasan she is speechless, ita dai Khaleesat kanta na kasa don ba handsfree Ummu ta saka wayar ba balle ta san abinda Dad din Abdul ke cewa, a hankali Ummu tayi ending call din ta ajiye wayar a gefen kujera don ba ma ta da amsan da zata ba Wan uwan nata, sosai jikinta yayi sanyi, yanxu dama Family din Alhaji Musa basu canza ba daga yanda ta san su tun tale tale, don ita sai tayi shekara aru aru ba a ganta a Nigeria ba in ba muhimmin abu bane ya kawo ta, Momy ce ta bude kofar parlon fuskarta a murtuke, ashe all this while tana kofar gida tana jiran ganin Khaleesat ta fito ta bar gidan amma shiru shiru bata ga ta fito ba, Momy na kallon Khaleesat tace "In dai ba gidan ubanki bane ko na uwarki nan din tunda har ya furta ya sake ki ai kya fito ki kama gabanki, ko zaman ubanki kike yi har yanxu? Da wani abinda kika zo gidan da shi ne kika yi waya a zo da mota a kwashe maki ko yaya?" Ummu ta kalli Momy tana girgiza kai cike da takaici tace "Ki ji tsoron Allah Hajiya, ki ji tsoron haduwar ki da Allah, ke ma fa kina da yaran nan mata...." A mugun fusace Momy ta karaso cikin parlon ta dakatar da ita tana nunata da Wan yatsa tace "Kin ga wannan family issue ne ki cire bakin ki a abinda bai shafeki ba Muhusina don ke bare ce a wannan Sangaren, kuma ba ke kika haifar min Abdul din ba da kike neman cusa kai abinda ya shafi rayuwarsa, who are you to even interfere? Ko Musa kin zata ya isa ya hana Abdul abinda yayi niyyar zai yi ne? To wallahi ki cire bakin ki da idonki akan abinda ya shafi zuri'ata, 'ya ya mata kuma dama ko wani shege ya haifa ai, meye a ciki" Momy na kai wa nan ta kalli Khaleesat cikin daga murya tace "Baza ki tashi ki san inda dare yayi maki ba ko sai na kira su Meemah sun fitar min da ke daga gidan nan??" Mikewa Khaleesat tayi bata bari sun hada ido da Momy ba ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ummu ta kasa cewa komai tana kallon Momy tana girgiza kai, sai da Khaleesat ta fita daga compound din gidan gaba daya sannan ta fara share hawayen dake sauka idonta, tunanin yanda zata koma gida bata da ko sisi ta fara yi, tafiya me nisa tayi har ta iso titin da zata samu abun hawa, daga karshe bayan jiran kusan minti sha biyar ta samu wani adaidaita sahun da zai kai ta Mariri a dubu biyu da dari biyar, in taje gida sai ta basa kudinsa, har Khaleesat ta isa gida hawaye ya ki tsaya mata a ido, ita kanta bata san yanda take ji a ranta ba game da abinda Abdul yayi mata, farin ciki take ko akasin haka har sannan ta kasa ganewa a zuciyarta, but she was deeply hurt and pained, daurewa kawai take kar ta fashe da kuka a adaidaita sahun, bayan ya tsaya dai dai kofar gidansu ta sauka tace "Za a kawo maka kudin yanxu, nagode" Daga haka ta shiga cikin gidansu, a tsakar gida ta tarar da kishiyoyin Ummanta sun gama abincin siyarwansu na yamma yara za su fita da shi talla, ta gaishesu ba tare da ta bari sun hada ido da su ba direct ta nufi dakin Ummanta, duk suka bi ta da kallo, Aunty Farida da fitowar ta daga bandaki kenan zata yi alwala don lokacin sallan La'asar yayi ta ajiye butan hannunta ta bi Khaleesat da kallo ita ma duk da Khaleesat bata ganta ba, Khaleesat na shiga dakin Ummanta ta fada jikinta ta fashe da kuka a hankali, Kasa cewa komai Umma tayi tana kallonta da mamaki, sai ga Aunty Farida ta shigo dakin ita ma, sosai gabanta ya fadi ta tsaya nan bakin kofa tana kallon Khaleesat, da kyar Umma ta dago kanta cike da karfin hali tace "Me ya faru?" Khaleesat ta kasa cewa komai tana kuka sosai, Umma da nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta ta rungumeta bata sake ce mata komai ba ta bar ta tayi kukan me isarta, cikin sanyin jiki Aunty Farida ta karasa cikin dakin ta zauna gefen katifa tayi shiru, Umma ta goge idonta tana patting Khaleesat a baya a hankali trying to calm her amma bata hanata kukan da take ba, sun fi minti biyar a haka sai ga Mama Zubaida ta dage labulen dakin tace "To Wan sahu dai na ta jira a mika masa kudinsa a kofar gida" Magana take amma idonta na kan Khaleesat da Umma, tsabar gulma yaron makota me adaidaita sahun ya aiko cikin gidan amma tayi karaf ta mike bayan yaron ya sanar masu ta nufo dakin Umma taki barin yaron ya karasa, don tun shigowar Khaleesat suka baza kunnuwa ko za su ji wata magana amma shiruu basu ji ko tari ba a dakin Umma, Aunty Farida ta dau handbag dinta ta fita daga dakin ta sake labulen daga hannun Mama Zubaida dake rike da shi, sannan ta fita zuwa gun mai adaidaita sahun, sai a sannan Umma ta iya daga kan Khaleesat, suna hada ido Khaleesat ta sauke jajayen idanuwanta, Umma tayi karfin halin cewa "Me ya faru Jiddah?" Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na zuba idonta tace "Yace ya sakeni" Hawayen dake makale idon Umma ya zubo tana kallon Khaleesat babu ko kiftawa, Khaleesat ta rufe fuskarta jikin Umma ta fara wani sabon kukan, Umma ta rungumeta sosai, cikin rawan murya tace "Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ki, kiyi hakuri kin ji?" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata tana shesshekan kuka, a haka Aunty Farida ta dawo dakin ta same su, Aunty Farida ta zauna gefen Umma tana kallonsu, Da kyar Umma ta kalleta tace "Wai sakin ta yayi" ?asa cewa komai Aunty Farida tayi tsabar yanda ta girgiza, ta dinga kallon Umma babu ko kiftawa, nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, after a while ta goge hawayen dake zuba idonta ta fita ta dau buta tayi alwalanta ta dawo ta tada sallah, Umma ta dago Khaleesat da tayi shiru a jikinta, sai taga bacci take, Khaleesat ta bude ido a hankali, Umma tace "Kin yi sallah ne?" Girgiza mata kai Khaleesat tayi, Umma tace "Ki je kiyi alwala kiyi sallah" Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin. Khaleesat na idar da sallah Aunty Farida na kallonta tace "A zubo maki abinci?" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Na koshi" Daga haka ta mike ta hau saman gadon Ummanta ta kwanta, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya iya cewa komai a dakin, suna ta zaune har kusan karfe shidda, ita dai Aunty Farida tana rike da Al-qur'ani tana karatu silently a ranta, su Islam suka dawo hadda wanda suke zuwa har ranan friday, Umma ta sa su je su hura gawayi su dora girki, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana cewa "To Zubaida sai ki dau na annabawa don kin tafka asara lafiyayye yau, almajirai na mugun wasa suka hamSare Suwaiba tallan da kika dora mata ya kife a kasa, su kuma suka tsere, sanin azaban da zaki mata ta taho ta sameni tana kuka kamar ranta zai fita, yanzu haka tana can gidana nace tayi zamanta, ga robobin tallan da faranti nasa an kwaso maki kayanki, ko roba daya bata siyar ba suka hambare farantin" Mama Shatu ta saki salati tana kallon Mama Zubaida da ta nemi waje ta zauna jin abinda Nenne ke cewa, Nenne ta kwashe da dariya har da kyakyatawa tace "Yaran layi kuwa duk suka wawushe abincin da ya zube a kasa suka loda ma cikin su" Daga haka ta nufi dakin Umma ta dage labulen tace "Zahra'u kina da er kuka ko kubewa ki tsam inje in ?ada miya" Umma bata yarda sun hada ido da Nenne ba tace "To bari in duba maki, Ina wuni" Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace "Wacece wancan kuma a kwance kan katifarki?" Umma dai bata ce komai ba ta tashi zata dauko ma Nenne kubewa busasshe, Aunty Farida ta gaida Nenne ba tare da ta kalleta ba, Nenne na kallon Khaleesat tace "Wai wa nake gani kamar Khaleesah a kwance?" Aunty Farida ta ajiye Qur'anin hannunta still bata kalli Nenne ba tace "Ita ce" Nenne ta shigo dakin tace "Wato ni dai shikenan kun nuna mata banda matsayi da har zata shigo unguwan nan ta karasa gidana ta gaisheni ko? In ma bata je ta gaisheni don Allah ba ai sai tayi don ubanta Ali tunda ni na haifesa har ya haifeta" Daga Umma har Aunty Farida babu wanda yace ma Nenne komai, Nenne tace "Mijin ne ya kawota? Shi ma ai shegen ne tunda ba karasawa yake yi gidana ya gaisheni ba, banda kaddara a ina za mu san sa har mu aura masa Khaleesat mutumin da baya ganin mutuncin mu, kana masa magana yana amsa maka cikin gadara da yanga wai shi Wan Alhaji Musa, waye bai san satan da ubansa ya zabga a gwamnati ba kafin ya koma kasuwanci, ko don muna kauda kai?" A takaice Aunty Farida tace "To sakin ta yayi..." Nenne ta juya ta kalli Aunty Farida na en sakwanni, can tace "Ban ji me kika ce ba Parida?" Aunty Farida da har hawaye ya kawo idonta tace "Sakinta Abdul din yayi" Nenne ta kasa motsi a inda take tsaye, a hankali tace "Sakin aure ko sakin me?" Aunty Farida dai bata tanka ta ba, ita dai Khaleesat na kwance tayi backing din Nenne bayan surutunta ya tasheta daga baccin da take, Nenne ta saki wani salati muryarta na rawa tace "Wato dai Wan nawa ne ba a son a ga ya zauna lafiya a gidan duniya kamar yanda kowa yake zaune" Fita tayi ta koma tsakar gida ta rushe da kuka sosai tace "Allah ya isa tsakanina da Zahra'u da er ta, babban burin su a duniya su ga Ali ya tagayyara, babban burinsu su ga Ali cikin mawuyacin hali cikin tashin hankali, banda haka ko dukanta da zaginta Awdul ke yi a gidan bazata hakura ta zauna ba albarkacin ubanta? Shi ne har zata amshi sakin da yayi mata hannu bibbiyu ta dawo mana gidan nan domin shari'arsu da Ali ya dawo sabo?" Mama Zubaida da Mama Shatu tuni suka mike tsaye jin abinda Nenne ke cewa, cikin kuka Nenne tace "Ban taSa ganin er da burinta taga ubanta a walakance ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login