Showing 183001 words to 186000 words out of 241367 words

Chapter 62 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1616

kamata yayi move on, amma ke kiyi ta kuka kamar me takaba, i understand you are lost of words amma kiyi composing kanki kiyi appreciating dinsa plss, wallahi ban taSa ganin mutum with kind heart like Jawwad ba, kuma shi tsakani da Allah yake abun sa ba don komai ba" Khaleesat ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "I don't know where to begin Safiyyah, ban san ta inda zan fara masa godiya ba, i am just confuse" Safiyyah ta rungumeta tana patting bayanta a hankali tace "I understand Khaleesat, i understand you, nasan you are confuse, but just start from anywhere, tell him anything that means appreciation zai fahimce ki" Khaleesat ta gyada mata kai hawaye masu zafi na sauka idonta, a haka Lyft din Safiyyah ya karaso, Khaleesat ta kamo hannunta da kyar tace "Thank you for everything Safiyyah, thank you for always being by my side through thick and thin, thank you for being supportive, nagode Allah ya saka da alkhairi" Tana magana hawaye na zuba idonta, Safiyyah ta hade rai tace "C'mon Khaleesat, ni kar ki sake min godiya, don na dauke ki tamkar sister din da bani da ita ne, i care so much about you" Safiyyah ta zame hannunta ta bude bayan motar ta shiga ta kulle kofar sannan ta daga ma Khaleesat hannu, kai kawai Khaleesat ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata sannan ta juya tana tafiya a hankali ta koma Apartment din, tana bude kofar parlon Jay ya juya ya kalleta sai kuma ya ci gaba da danna wayarsa, walking slowly ta nufesa har inda yake zaune ta durkusa kasa tana kallonsa, Kafin tace komai ya dakatar da ita ba tare da ya kalleta ba yana magana softly yace "I don't want ur thanks Khaleesat, bana bukata, ba don ki gode min nayi duk abinda nayi ba, nayi ne saboda Allah, nayi ne saboda kinyi deserving in yi maki, so bana bukatar godiyan ki pls, instead ki gode ma Allah" Khaleesat ta kasa cewa komai kanta a kasa hawaye na zuba idonta daurewa kawai take kar ta fashe masa da kuka, ya mike yace "Let me show you round the house before i leave" Tana goge fuskarta ta mike ta fara bin sa tana tafiya a hankali, kitchen ya fara kai ta, ita dai tana tsaye daga bakin kofa take bin kitchen din da kallo, hatta foodstuff duk ya siya mata, fridge din kitchen din ma was fully stocked up, ga cookies kala kala a kitchen din saboda yasan tana son cookies, ta kasa daurewa bata san sanda ta kamo hannunsa ba muryarta na rawa tace "Ban san ta inda zan fara maka godiya ba...." Ya Wan bude ido cause he never saw that coming, lkci daya yayi saurin janye hannunsa daga nata, yana murmushin karfin hali yana komawa baya ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "Nace maki bana bukatar godiyan ki, let me show you other places" Daga haka ya fita daga kitchen din, ta jingina da kofar kitchen din bayan ya fita tana kuka a hankali, sai da tayi me isarta sannan ta fito daga kitchen din tana jan kafa da kyar, tsaye ta gansa dai dai staircase yana danna wayarsa alamar ita yake jira, yana ganin ta fito daga kitchen din ya mayar da wayar aljihunsa ba tare da ya kalleta ba yace "The rooms are upstairs" Sai da ta karaso har inda yake sannan ya fara haura stairs din ta bi bayansa, ya fara nuna mata spare rooms guda biyu, sannan ya bude kofar nata dakin, calmly yace "Ur room" Ita dai tana tsaye bakin kofa tana kallon dakin babu ko kiftawa, ba abinda babu cikin dakin nan na comfortability, duvets ma manya hudu duk sababbi cikin case dinsu ta gani a dakin, the room look so beautiful sai wani sparkling yake, a hankali ta juya ta kallesa ya sauke idonsa bai dai ce mata komai ba, sai kuma ya juya ya bar bakin kofar dakin ya sauka downstairs ta bi sa da kallo, jingina tayi da kofar dakin for almost 5 mins tana kallon cikin dakin, a hankali ta juya ta bar bakin kofar dakin ta fara sauka downstairs cikin rashin kuzari, tsaye ta gansa bakin kofar fita daga parlon, yana ganin ta sauko yace "I will take my leave now Halysaah, amma dai sai jibi zaki shiga school, cause i see you look stressed" Ta gyada masa kai a hankali, yace "Ohk, here are the apartment key" Ta karasa ta karbi bunch din makullan da yake mika mata, sai kuma ta kallesa tace "Baka cire spare key ba?" Yace "A'a ki ajiye su kawai a wajen ki" Ta gyada masa kai kawai bata ce komai ba, ya bude kofar parlon without looking at yace "Text me ur Skin care set via WhatsApp" Yana fadin haka ya fita daga parlon yace "Good night Halysaah" Tana kallo ya kulle kofar parlon, after some minutes ta ji alamar tafiyar motarsa.
[7/6, 5:55 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat ta dade rabon da tayi bacci peacefully babu abinda ke damunta a rai kamar yanda tayi daren jiya, bayan tayi sallan asuba ta sake komawa baccin don garin akwai sanyi sosai, karfe takwas da yan mintuna na safe vibration din wayarta ya tasheta daga baccin da take, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta duk da tasan bazai wuce Safiyyah ba, ai ko taga ita ce, picking din kiran tayi ta kai kunne murya can kasa tace "Sophie" Safiyyah tace "Nasan kina nan kina bacci ko?" Khaleesat tace "Um, Good morning" Safiyyah tace "Morning, amma baza ki shigo school ba yau?" A hankali Khaleesat tace "Sai gobe in sha Allah" Safiyyah tace "To Allah ya kai mu, ni dai gani har na shigo school din, amma fa gobe akwai get together da za mu yi na manta ban gaya maki ba, just few of us, ba mu wuce mu sha biyar ba duka, the time is 5pm prompt" Khaleesat tace "Cikin sanyin nan za ku yi get together Sophie?" Safiyyah tace "So? Kin ga alamar sanyi na hindering daily activities din mutane a kasar nan ne in dai ba snow bane yayi mugun yawa? Beside ai ba a open space za ayi get together din ba, it will take place at one of our Course mate House" Khaleesat tace "Toh ai shikenan" Safiyyah tace "Ban gane ai shikenan ba, banda ke za ayi get together din kenan kike nufi?" Khaleesat tace "Kema kin san bana son gathering ko ya yake Sophie, me yasa kika yi tunanin har da ni za ayi bayan kinsan bazan je ba" Safiyyah tace "Plss for once ki zama Social or should i even say Civilised Khaleesat, ko ba komai idan kika zo za kiyi nishadi ki mance duk wani damuwar ki na Nigeria kiyi freshen up din ?wa?walwar ki for this semester, amma kawai kiyi ta zaman gida ke kadai kullum kamar me wani cuta, kin ga wannan shekara dayan da ya rage mana so nake ki waye ki fara yin abubuwa irin na wayayyu ta yanda babu wanda zai raina ki babu wanda zai san daga wani irin background kika fito, yanxu fa ba da bane a gareki Khaleesat don ke kin ma tsallake matsayin da mu bamu zo ba ma, don haka use this last opportunity in USA ki zama wise ta yanda babu shegen da zai raina ki" Khaleesat dai idonta a lumshe yake don har ta ci gaba da baccin ta, Safiyyah tace "Hello" Khaleesat ta bude ido da kyar tace "We will talk later Sophie" Safiyyah tace "Tun da ina gaya maki gaskiya ba dole kice we will talk later ba, kuma ko kin ki ko kin so sai mun je get together din nan da ke don yanxu ba da bane" Daga haka ta katse wayar ta, Khaleesat ta gyara kwanciyarta ta rufa da duvet zata ci gaba da bacci, ita kanta tasan bashin baccin da bata yi a Nigeria ne take biya.... Sai kusan karfe uku na rana Khaleesat ta tashi daga bacci, bayan tayi wanka tayi sallan azahar ta sauka parlor don yunwa take ji sosai, kunna heater din parlon tayi don parlon yayi sanyi kamar fridge, ta karasa ta tsaya jikin window din parlon ta daga labule tana kallon beautiful Neighborhood din ta, ko ina fari tas saboda snow din da aka yi sosai daren jiya da bai gama narkewa ba, after some minutes ta sake drape din windan a hankali ta nufi kitchen, shayi ta hada ta debi cookies ta dawo parlorn ta zauna, bayan ta gama ta kai plate din da cup kitchen ta wanke sannan ta koma sama don harhada textbooks dinta da reading materials, gaba daya sauran kayanta na tsohon Apartment dinta duk ta gansu a dakin alamar Jay ne ya kwaso mata su daga old apartment din nata, ta gama hada kan reading materials dinta, ta fara gyara kayan sawanta a press din dakin kenan taji an danna bell din gidan, ta Wan yi jim to be sure a apartment din take jin karan bell din, after some seconds ta fita daga dakinta ta sauka downstairs bayan an sake danna bell din, ta karasa har bakin kofar ta bude a hankali tana duba waye a bakin kofar, yana kallonta calmly yace "Good evening Halysaah" ?an murmushi tayi ta koma gefe don basa hanyar shigowa, yace "A'a kawai ki shirya, za mu je kiyi shopping abubuwan da kike bukata, i will wait for you inside in the car" Shiru Khaleesat tayi tana kallonsa, ganin zai koma motarsa tace "Amma ai ba abinda zan bukata yanxu, don naga akwai komai a gidan" Yace "For ur personal use Halysaah, beside ai babu cleaning agents a gidan, i forgot to get them..." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, yace "I am waiting at the garage" Daga haka ya juya ya koma garage ta bi sa da kallo kafin ta rufe kofar ta juya ta nufi sama a sanyaye, bayan minti sha biyar ta sake saukowa downstairs tana sanye da jacket dinta, tana fita waje taji wani azababben sanyi duk da Jacket din jikinta, ta kulle gidan tana rike da makullin ta nufi motarsa, bude front seat din tayi ta shiga ta kulle, yace "Akwai sanyi ko?" Tana kara takurewa waje daya tace "Sosai, ni ban ma san akwai sanyi haka ba" Yayi murmushi ya kara dumin motarsa yace "Kina cikin gida da room heater ya za ayi ki san akwai sanyi" Murmushi tayi tana juya makullin hannunta ta Wan kallesa a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya Halysaah, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Hope you are comfortable in the new house?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace "Good to hear that..." Tada motar yayi suka bar garage din, bayan sun dan yi nisa da tafiyar a hankali tace "Yaya Junaid fa?" Sai a sannan ya kalleta yace "Ajay yana gida, he is under the weather, baya son irin season din nan" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Ya kika baro su Umma and Aunty Farida?" Tace "Mun yi chatting dasu jiya da daddare, Umma tace tana son ta maka magana if you are around" Yace "Ohk to idan mun koma gida sai in kira ta" Khaleesat bata sake cewa komai ba, jifa jifa dai take kallonsa, shi kam ya maida hankalinsa kan driving din da yake, Wani babban Shopping mall ya kai su, bayan yayi parking sun shiga ciki ya dau shopping cart yana turawa, zata amsa cart din a hannunsa yayi murmushi yace "No, don't worry Halysaah, i will do the wheeling and u do the shopping" Ta sauke idonta bata ce komai ba, gun cosmetics ya fara kai su yace "Ki dauki duk abinda kika san za ki bukata a nan Housemate..." Ta Waga kai ta kallesa, ya Wan bude ido yace "Look Halysaah, i want you to be free and open with me, kar ki saka komai a ranki ko kiji nauyin tambayar wani abu da kika san kina da bukata, assuming i don't have the means ai bazan ce zan yi ba Halysaah, so feel free plss Housemate, haka jiya nace ki turo min Skin care set din ki ba ki turo ba, ni ina maki duk abinda nasan zan ma kanwata ne ko er uwa ta, so ki dau duk abinda kika san kina da bukata yanxu" Ita dai idonta na kasa bata ce komai ba, ya mika mata katin kudinsa yace "Ko in baki katin in jira ki a mota?" Ta Wan kallesa sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tana murmushin karfin hali tace "A'a" yace "Then shop all you need Housemate" Cikin sanyin murya tace "Ohk, Thank you so much" Shi dai murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba, few abubuwan da tasan zata yi needing take dauka a wajen cosmetics din tana ajiyewa a cart din da yake tura mata, amma idan ta dau abu daya sai ya kara mata biyu a kan wanda ta dauka, ita dai sai dai ta kallesa, ta dau set din Cream din shafawanta da shower gel, nan ma yayi doubling mata su ya zuba a cart, a hankali tace "Ina da saura fa" Bai ce mata komai ba, ta ci gaba da tafiya, tana kallon pad amma ta kasa dauka kawai ta wuce, shi ma kuma bai ce mata komai ba yana wheeling cart din har dai suka gama da bangaren cosmetics, ya nufi gun cleaning agents tana biye da shi abaya, duk shi ya dinga daukan abubuwan da yasan zata bukata a gida, sai bayan minti talatin suka fito daga shopping mall din ya zuba duk abubuwan da suka siya a booth din motarsa, maimakon su nufi gida sai taga ya kai ta wani babban store din Africa yace "I didn't get much cooking ingredients for you cause i am not good at that, so mu shiga sai ki dau duk me zaki bukata na girki...." Ta kallesa tace "To ai ko fara amfani da wanda ka siya ban yi ba" Yace "I know, zan Wan yi tafiya ne Housemate, so i want to be sure you have enough of everything" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, yace "Mu je" Daga haka ya sauka daga motar, jiki a sanyaye ita ma ta sauka ta bi sa zuwa cikin store din, Spices din girki da su seasoning, albasa, irish, dankalin hausa, doya, eggs, all kind of peppers, tomatoes, da dai duk wani mahadin girki suka siya a store din, sannan ya kara mata frozen chicken da turkey, sai beef, bayan ya biya kudaden suka bar store din, yana driving Khaleesat ta kallesa cikin sanyin murya tace "Thank you so much, Allah ya sa kafi haka" Yayi murmushi kawai, sai kuma ya dau wayarsa dake vibrate yana dubawa, ganin Ajay ne ke kiransa yayi picking ya kai kunne yace "How are you feeling?" After some seconds ya ajiye wayar, Khaleesat tace "Is he sick?" Yace "Yeah, i told you he is under the weather" Khaleesat ta yi shiru, Jay ya kalleta yace "Ko mu je gidan ki dubasa?" Ta Wan buda ido, sai kuma tayi murmushi a sanyaye tace "Bazai kulani ba ai" Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace "Saboda me bazai kula ki ba?" Ta sauke idonta tace "Jiya ma da ka je dauko makulli ai yayi kamar bai gan mu ba a mota" Jay yace "Jiyan nan ma da ku ka gansa ba shi da lafiya, sai da nace kar ya fita yaki saurarana, bayan ya fita kuma aka fara snow" A hankali Khaleesat tace "To Allah ya basa lafiya" Jay yace "Mu je can gidan za ki gaishesa?" Tayi shiru don har zuciyarta tana fargaban kar ya shareta, Jay yace "A bari next time ko?" Ta sauke idonta a hankali tace "To mu je, amma idan bai kulani ba ai shikenan" Jay yayi murmushi yace "Idan bai kulaki ba kema sai ki sharesa" Khaleesat ta Wan kallesa suka hada ido, murmushi tayi har sai da dimple dinta ya lotsa tana kallonsa, ya dauke idonsa ya maida dubansa kan titi yana ci gaba da driving dinsa gently. Kusan karfe biyar da rabi suka isa gidan, Jay yayi parking a compound ya kashe motarsa ya Wan kalleta yace "I can see you are tensed?" ?an murmushi tayi tana wasa da fingers dinta bata ce komai ba, ya bude motar yace "To mu shiga" A hankali ta bude motar ita ma ta sauka, ta bi Jay da kallo har ya dau hanyar entrance din babban gidan nasu, ta bi bayansa tana tafiya slowly, bayan ya bude kofar parlon sai da ya jira har ta iso, ta sunkuyar da kanta ta shiga parlon sannan shi ma ya shiga, sosai gabanta ya fadi bayan wasu memory sun dawo mata, memory that is so disturbing to her, tana tafiya a hankali ta karasa har cikin parlon ta zauna kan kujeran da ta zauna ranan da Jay ya kawota gidan da daddare, ta daga kai ta kalli Reading Nook din da Ajay ya zauna a ranan da daddare, sauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, Jay ya karaso cikin parlon yana kallonta yace "Give me some minutes" Ta gyada masa kai ya nufi stairs ta bi sa da kallo har ya haura sama, Jay na tafiya sama ya karasa bangaren Ajay ya bude kofar gently yana kallon cikin dakin nasa wanda babu haske sosai don Drape din dakin very thick one ne saboda sanyi, Jay ya shiga ciki ya kunna dim light din dakin yana kallon Ajay, kwance yake saman gado yayi rub da ciki yana bacci, har wani hucin zafi dakin yake tsabar yanda ya kure room heater, Jay ya karasa kusa da gadon yana kallonsa, lallai yanxu ya kara tabbatar da bai da lafiya, Ajay ne har za a bude masa daki a kunna wuta a shigo bai sani ba, ai duk baccin da yake kana taSa kofar dakinsa yake tashi tun kafin ka shigo masa, Jay ya juya ya fita daga dakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login