Showing 132001 words to 135000 words out of 241367 words

Chapter 45 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1560

tayi a nata bayan ya lumshe idanuwansa, tsoron turje masa take yi don bata san me zai biyo baya ba idan tayi hakan, jikinta ya dinga rawa kamar me zazzabi hawaye na sauka idonta tana girgiza masa kai amma ta kasa cewa komai kar ya mareta kamar yanda ya saba, a haka ya ja ta zuwa saman gadon dakin yana sarrafata, he made sure he romanced her deeply to the extent that sai da ya birkice mata kamar ba shi ba, daga karshe kuma ya kyaleta kar ya kasa controlling kansa gashi tana period, amma fa sosai ya iya kai zuciyarsa nesa kafin ya kyaleta ya koma can edge din gadon yayi rub da ciki tare da lumshe idonsa, everything about Khaleesat is just perfect for a Man, laushin jikinta kadai ya isa ya kara gigita mutum, Khaleesat ta koma daya side din gadon a hankali take kukan takaici faduwar gabanta ya tsananta, juyawa yayi ya kalleta after some minutes yaga yanda dogon gashinta ya rufe duk fuskarta tana kuka, sai kuma ta zamo a hankali daga saman gadon ta kife kanta da jikin gadon tana shessheka, ji tayi ya dafata ta juyo a firgice tana komawa baya don bata san sanda ya zagayo ba, ya sa hannu biyu ya maida duk gashinta zuwa gefen fuskarta yana kallonta, tuni ta daina kukan da take saboda tsoro, ta sunkuyar da kanta kirjinta na heaving, jawota yayi jikinsa ya rungumeta ya lumshe ido, ita dai tayi tsit tsabar firgici, a haka ta dinga jin bugun zuciyarsa tana jikinsa, they were like that for 3 mins daga karshe taga ya mike a hankali ya fita daga dakin ta bi sa da kallo tana share sabbin hawayen dake sauko mata a fuska, throughout ranan haka Khaleesat tayi ta zama a daki sai dai ya kawo mata abinci, da ta tuno abubuwan da Abdul yayi mata daxu sai ta firgita, sai ya zama kamar tana hallucinating ne, hakan ya dinga sa mata ciwon kai taji kamar zazzabi zai rufeta, saura kadan panic attack ya kamata a dakin banda Allah ya takaita mata, gaba daya yanxu tunanin menene makomar rayuwarta take, shikenan haka zata hakura tayi zaman aure da Abdul ta ci gaba da shanye duk bakin cikin da zai kunsa mata a zaman aurensu bata da me tsaya mata tunda shi din mijinta ne? Did she even have a way out with the way things turn out to be all of a sudden? Is this going to be the beginning of a new era a rayuwarta? Shikenan irin rabuwar da zata yi da su Housemate dinta kenan? Kilan ma ba lallai ta sake ganinsu ba a rayuwarta? Shikenan haka Abdul zai ci gaba da caging dinta a gidansa ga threatening din kashe mata siblings da yayi idan taki zama da shi? Duk wa ennan tunanin suka sa ta dinga kuka tana tausayin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa, don tasan Abdul na gane ta gama period bazai daga mata kafa ba and that is the end of her, kuma shikenan dole ta zauna tayi zaman aure da shi ko da yankan naman jikinta zai dinga yi kuwa don azabtarwa, tunda Ummanta ta haifeta tana jin bata taSa shiga irin wannan tashin hankalin da take ciki ba a wannan lokacin, tana jin alamar zai shigo dakin take goge fuskarta ta langwabe a zuwan ciwon ciki take.... Cikin wannan yanayin Khaleesat tayi kwana uku a gidan tare da Abdul, a wannan kwanaki ukun kuwa duk da halin da take ciki a haka yake sakawa taje tayi masu girki a kitchen wai shi baya son abincin restaurant, Khaleesat bata taSa fatan kar period dinta ya dauke ba kamar irin wannan lokacin, she wish she will keep on flowing continuously like the woman with the issue of blood amma tasan dole ya dauke nan da kwana biyu don bata wuce 5 days in tana period, sosai hankalinta ke kara tashi idan ta tuna hakan, yau tunda gari ya waye tayi wanka ta saka pad take kwance kan gado saboda azababben ciwon kan da take, all these pass days bata wani samun baccin kirki da daddare tsabar damuwar da ta saka ma kanta da tunane tunane, daga karshe dai haka ta daure ta fita zuwa kitchen da kyar don dora breakfast kafin ya fito daga dakinsa kamar yanda yayi mata umarni 2 days back, tana fita parlor ta leka compound din gidan taga babu motarsa alamar ya fita, ta murda kofar parlon taji a kulle kamar yanda tayi tunani, Zaunawa tayi kan kujera ta dafe kanta hawaye masu zafi na zuba idonta, after a while ta mike tana shesshekan kuka ta wuce kitchen din, tana cikin hada breakfast taji alamar shigowar motarsa gidan, after a while aka bude kofar parlon, ?asa kunne tayi jin kamar muryar mace take ji a parlor, can kuma taji tsit, ita dai ta ci gaba da abinda take yi jiki babu kuzari har ta gama ta tsaftace kitchen din sannan ta juya zata fito ta kusa cin karo da wata mace in her late 30's zata shigo kitchen din, daga sama har kasa matar dake tsaye kofar kitchen din take mata wani irin kallo da za a iya kira da kallon kaskanci, ita dai Khaleesat tunda ta kalleta sau daya ta sunkuyar da kanta ita kanta bata san sanda ta gaisheta ba don duk ta rude gashi kuma taga suna kama da Abdul duk da bai taSa nuna mata wani nasa ko da a hoto ba, a walakance matar tace "Da ban kwana ba zaki gan ni munafukar Allah, Er gidan matsiyata ma ci amana.... A gidan ubanki kika san ni da zaki gaisheni?" Sai a sannan Khaleesat ta sake daga kai tana kallonta da mamaki cause kalmomin matar kawai a bazata suka zo mata, bata san sanda tace "Ki zageni amma banda iyayena...." Bude baki Meema tayi da mamaki tana kallonta ganin guts dinta, kafin tace komai Khaleesat ta bi gefenta zata fice daga kitchen din wanda saura kiris ta bangajeta wajen fitan, cikin zafin nama da bacin rai Meema ta fincikota ta dawo da ita gabanta sannan ta sauke mata wani wawan mari ta shakota tana kokarin kai ta kasa ta nakadi banza, Khaleesat ta kwala wani kara, dai dai isowan Abdul wajen, lkci daya yanayinsa ya canza don a kan idonsa yayar tasa ta sauke ma Khaleesat mari sannan ta shakota tana kokarin dukanta, cikin daga murya yace "Zo ki fita ki bar min gidana Amina, how dare you? Me tayi maki zaki mareta haka? Baki da hankali ne? Get out of my house pls, fita ki bani waje" Sake baki Meema tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin zafin nama ya tafi ya bude kofar parlon kirjinsa na sama da kasa yace "Ki fita nace Amina kar in rama mata" Cikin karfin hali Meema ta dafe kirjinta da hannu daya tace "Abdallah ni kake cewa in fita a gidanka?" Ya jefar da wayar hannunsa yana huci ya nufeta kamar zai kai mata duka cikin daga murya yace "Na ce ki fita din ko gidanki ne? Get out of this house before i loose my control Amina, gerrout" Ita dai Khaleesat makalewa tayi jikin kofa jikinta na rawa, sum sum sum Meemah ta karasa ta dau handbag da karamin travelling bag dinta don dama daga airport yaje ya daukota saukanta garin kenan, ta nufi kofar fita parlon sannan ta juya tana kallonsa da mamaki tace "Abdallah ni kake daga ma murya kake cewa in fita in bar gidanka akan wancan matsiyaciyar? Har kake ikirarin zaka kai min hannu? Ni din Abdallah?" Da karfi yace "Duk nayi, fitaa ki bar min gidana malama" Fita tayi daga parlon ya bi bayanta kamar zai tashi sama ya tafi ya bude mata gate din gidan, ta fita yayi banging gate dinsa ya kulle, har ya dawo parlon Khaleesat na makale jikin kofa ita tsabar yanda ta tsorata ma ko digon hawayen marin da Meemah tayi mata babu a idonta, ya karasa kitchen din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, sai a sannan taji hawaye ya fara zuba idonta.
[6/14, 9:16 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Juyawa Abdul yayi ya fice daga kitchen din ba tare da yace mata komai ba ya dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake zuba idonta har ta dena hango sa, jingina tayi da kofar kitchen din ta kai hannunta fuskarta dai dai inda Meemah ta mareta don sai a sannan ta fara jin zafin marin, fashewa tayi da kuka tayi me isarta kafin ta fito daga kitchen din tana tafiya a hankali ta tafi ta zauna kan 1 seater dake parlorn tana share hawayen da yaki tsaya mata, abubuwan da Abdul yayi ma Meemah ne suka dinga dawo mata a kai don hakan yayi mugun shock dinta, but she just don't want to believe senior sister dinsa yayi harrassing haka har da koranta, to ko dai ita ce Aunty Aminan da suke ce ma Meemah don taga sosai suke kama da ita, tana ta zaune parlon bayan wani lokaci sai gashi ya fito daga dakinsa, sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers dinta, ya karaso cikin parlon yace "Kin yi breakfast din ne?" Da Authoritative voice yayi tambayar yana kallonta, hakan yasa ta Wan rikice kamar mara gaskiya ta girgiza masa kai with fear all over her face, sai kuma ta mike da sauri ta nufi kitchen ya bi ta da kallo har ta shiga ciki, shayi rabin cup ta hada sannan debi Irish kadan a plate don tension yasa ta rasa appetite dinta gaba daya , sai kuma ta tuna shi ma bata basa breakfast din ba, tunanin ko ta kai masa parlor ta fara yi don a kwanaki ukun nan Bedroom dinsa take kai masa breakfast din kamar yanda ya umarce ta, kamar munafuka ta makale jikin kofar kitchen din tana kallonsa tana son tambayarsa ko ta kawo masa breakfast din nasa parlorn amma ta kasa don bata san me zai ce ba kar yayi mata masifa, wayarsa kawai yake dannawa bai ma san tana wajen ba, juyawa tayi a hankali ta koma kitchen din a sanyaye ta hada masa breakfast din ta fito da shi parlor, jikin kujera ta tsaya a hankali tace "Ga breakfast din nan" Daga kai yayi ya kalleta, gabanta ya dinga faduwa ta sauke idonta daga kallonsa, jin bai ce komai ba yasa ta karasa har gabansa ta duka ta ajiye masa breakfast din, yace "Ke ina naki?" Taki barin su hada ido tace "Yana kitchen" Yace "Dauko" Mikewa tayi ta tafi ta dauko nata ta dawo tana kallonsa, yace "Ajiye ki ci a nan" Bata masa musu ba kanta a kasa ta zauna gefensa da ya nuna mata ta fara tuttura irish din kamar dole tana satan kallonsa ta gefen idonta, a hankali taga ya jawota jikinsa taji gabanta yayi mugun faduwa, calmly yace "I am a monster to you right?" Da sauri ta girgiza masa kai zuciyarta na bugawa, yace "Gashi nan, kin maida ni dodonki" Ita kanta bata san sanda hawaye ya cika idonta ba, yayi kasa da murya yana zame hulan kanta yace "Now tell me what u want from me, tell me what's on ur mind.... amma before then ki sani bazan taSa rabuwa da ke ba saboda ina son ki Khaleesat, rabuwa dake will be the last thing i will do on earth no matter what, You know i love you genuinely from onset, i loved you wholeheartedly and i gave u the best of everything I could, i loved you even before you become the woman you are today, i love you since when u were just a 15 year old teenager tun baki girma ba, yea i know about my flaws but loving you is all that matters, not in the sense that abubuwan da nake yi are right, i am obsessed with you Baby, may be you can change me in ur own way...." Khaleesat ta rufe idonta tana jin kamar ta fashe da kuka, jin kalamansa take kamar ana soka mata mashi a kirji, Ya dora forehead dinsa a nata murya can kasa yace "Why not give me a chance and forgive my flaws Khaleesat?" Bude idonta tayi hawaye suka hau zarya a idonta, har cikin ranta taji bata son jin maganganun da yake mata, a hankali yace "Forgive me, i know i wronged you in all ways, but don't forget ina sonki, ina kuma sonki ne saboda Allah, they are many beautiful ladies out der buh i chose you Khaleesat" Lokaci daya gaba daya tunaninta ya tafi kan Housemate dinta, kasa daurewa tayi ta fashe da matsanancin kuka, ya daura kanta a saman shoulder dinsa patting her softly, ta dinga kuka kamar an aikota, shi dai bai ce mata komai ba, sai da tayi kukan me isarta sannan ta hakura don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya daga kanta yana kallonta taki yarda su hada ido, breakfast dinta ya ajiye mata a kusa da ita, ba musu ta fara ci a hankali da tunani iri iri a ranta, muryarsa taji ya daki dodon kunnenta "Yaushe zaki gama period?" Gabanta yayi mugun faduwa, ta ajiye cup din shayin dake hannunta ba tare da ta kallesa ba, a hankali tace "Ai ban dade da farawa ba" Yace "Yau kwana hudu da farawan ki" Da kyar ta dake tace "A'a, uku ne.... first day din ai bana yi sosai..." Yace "Saura kwana nawa ki gama kenan?" Sosai gabanta ke bugawa, ta sunkuyar da kanta cike da karfin hali tace "Kilan nan da kwana uku ko hudu" Jin bai ce komai ba ta daga kai a Wan tsorace ta kallesa, taga kallonta yake without blinking, sauke idonta tayi tana wasa da karamin cokalin dake cikin mug din shayinta, ya dauke shayin ya mayar gefe, taga ya kai hannu shoulder dinta zai sauke siririn hannun rigar dake jikinta, sosai hankalinta ya tashi amma bata ce masa komai ba gabanta na ci gaba da faduwa, ya sauke rigan gaba daya yana kallon bare chest dinta, hawaye ne ya cika idonta taki yarda su hada ido, can dai tayi karfin hali muryarta na rawa tace "Toh baka sha shayin ka ba zai huce" Yayi kasa da murya yace "Wa ennan zan sha... " Momy ce tsaye parlor tana kallon Meemah dake rusa kukan bakin ciki uwa er yarinya, ga trolley dinta a gefenta, bacin rai ne karara kwance fuskar Momy da idanuwanta suka ?ankance tana huci, mai aikin gidan ce ta shigo parlon rike da bowl din pepper soup din da tayi ma Momy, cikin ladabi ta risina tace "Hajiya ga farfesun nan ya kammala" a fusace Momy ta figi throw pillow ta jefa mata tace "Don ubanki wuce ki ban waje ke da farfesun, baki ga magana nake bane zaki shigo min parlor kai tsaye, yau ga jahilar mata kai" a tsorace mai aikin ta juya da sauri ta bar parlon ta koma kitchen ta kullo kofar, Momy tace "Na kusa daina daukan tsinannun masu aikin nan don sun isheni haka kuma, na kori wancan shegiyar da ta shigo min parlor da yan uwan Alhaji da suka zo daga kauye babu izinina yanxu kuma an kawo min wannan jakar da ko kwana biyu bata yi ba ta fara nuna halayyan dabbobi" Ita dai Meemah kuka kawai take tana fyace hancinta da handkerchief, tsabar kuka idonta har sun suntume, Momy ta kara kankance idanuwanta tana kallon Meemah tace "Shi Abdallahn ne yayi maki haka Meemah?" Meemah ta hadiye wani abu da ya tokare mata wuya don bakin ciki tace "Momy da kin ga tijaran da Abdallah yayi min akan yarinyar nan ko, hmmm, ki bari kawai Momy, Momy kare bazai ci abinda Abdul yayi min ba, bayan zagi da cin mutunci wai ni ya kora a gidansa, kora irin ta walakanci" Momy ta zauna kan kujera with disbelief, duk da AC dake aiki a parlorn sai zufa take yi dama ga ta narkekiya, tana gyara zama tace "Ko dai ya sha wani abu ne Meemah??" Cikin rawan murya Meemah tace "Babu abinda ya sha wallahi Momy don lafiyan Allah ya dauko ni a airport muna ta hira, tare fa da ni duk aka yi tracking yarinyar nan tunda akwai wani tsohon saurayina wanda aikinsa kenan, amma wai yau akanta Abdallah zai min irin wannan tijara haka tun ba aje ko ina ba, duka duka fa kwananta yau hudu da shiga hannunsa, amma ya rufe ido ya zazzageni ya ci min mutunci ya koreni" Momy tayi wani murmushin takaici tana girgiza kafa tace "Kin ga abinda nake ta gudu kika kasa ganewa kenan ai ko? Dama ance duk abinda babba ya hango yaro ko uban me zai hau bazai taSa hangowa ba wallahi, ba ya kwana da ita ba dole ki ga abinda yafi haka ai, babu yanda banyi in lalata batun auren nan ya hakura ba amma sam Meemah kika ki bani hadin kai ki ka koma bayan Abdallah, har da bin wasu malamanki da basu taka kara sun karya ba duk don yarinyar ta shigo hannunsa, to ai ta shigo kuma kin ga abinda ya biyo baya daga shigowarta, to wallahi zai kai ya kawo wataran Abdallah yace bai san mu ba akan yarinyar nan, ni na haifesa ba wani ya haifar min shi ba sarai nasan abinda zai iya aikatawa" Meemah ta dinga kallon Momy babu ko kiftawa don ita sai yanxu ta kara fahimtar dalilin Abdul nayi mata irin wannan mugun tijara kan yarinyar da yake ta ikirarin zai koya ma lesson idan ta shigo hannunsa, sarai kuwa ya kwana da ita dole ya birkice haka ya haukace kanta, dama buzaye da aka sani da mugayen asiri, Meemah tayi wani murmushin takaici tace "To kuwa yanda nayi ruwa nayi tsaki har sai da yarinyar nan ta shiga hannunsa to haka zan yi har sai ya rabu da ita a kwanan kuwa ba da jimawa ba" Momy ta kwado ma sabuwar me aikinta kira, matar ta taho a guje har sai da tsantsin tiles ya kwasheta sbda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login