Showing 39001 words to 42000 words out of 241367 words

Chapter 14 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1577

jiran Lyft din da tayi ordering sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tun daxu ta kirata bata daga ba sai yanzu ta biyo ta, Khaleesat ta daga ta kai kunne tana jin muryar Safiyyah tace "Baki da lafiya ne?" Da kyar Safiyyah tace "Tun jiya da daddare, na ma zata rasuwa zan yi kawata" Khaleesat ta Wan bude ido tace "Me ya sameki?" Safiyyah tace "To ina ma na sani Khaleesat, Allah sa ba poison dina matar nan tayi ba don tun jiya sai yanzu nasan mutanen dake kaina" Khaleesat tace "Subhanallah, kina gida ne yanzu?" Safiyyah tace "Har da karin ruwa kuwa" Khaleesat tace "To bari in taho gidan yanzu" Khaleesat na maida wayarta jaka ta nufi gidansu Safiyyah, bayan tayi knocking kofar Surayya ta bude mata, Khaleesat ta sauke ido ta gaisheta, in ba kasa kunne sosai ba ma baza kasan Surayya ta amsa ba, Khaleesat taji muryar Mustapha na tambayar matar tasa wanene, ji tayi kamar ta juya ta fasa shiga cikin gidan, amma kasancewar a bude Surayya ta bar kofar yasa ta karasa ciki walking slowly, without looking at Mustapha dake parlor ta gaishesa, ya amsa yace "Ya karatun Khaleesat?" Khaleesat tace "Alhamdulillah, ya jikin Safiyyah?" Yace "Alhamdulillah, she is inside her room" Khaleesat ta juya ta nufi dakin Safiyyah, da gasken ruwa ta tarar ake kara mata don ta zata kawai tace mata haka ne don ta zo, Khaleesat ta zauna gefenta da damuwa tace "Sannu Sophie, ya jikin?" Safiyyah tace "Ba sauki Khaleesat, wallahi kilan abu matar nan ta saka min a abinci" Khaleesat tace "Don Allah ki dena cewa hka, kin ga yayanki ai bazai ji dadi ba in kina wnn magana" Safiyyah tace "Wallahi ita ce don lafiya na dawo gida jiya, ni na zata ma na rasu, sai da na farfado naga ba haka ba" Khaleesat tace "Allah dai ya baki lafiya, kin ci abinci?" Safiyyah tace "Ni bazan ci abincinta ba gaskiya tun daxu sai fruit kawai nake ta sha da lemon kwali" Khaleesat tace "Ko in je gida in maki girki? Me kike son ci?" Safiyyah tace "Ko tuwo da miyar kuka ne ki min in kina da ingredient, kawai shi naji nake so wallahi" Khaleesat tace "To ba damuwa, bari inyi sallah sai in tafi in maki girkin" A haka Khaleesat tayi sallahn azahar ta bar gidan bayan tayi ma Surayya da mijinta sallama, Mustapha ne ma ya tambayeta har zata tafi, Shine tace masa zata dawo anjima, Khaleesat na isa gida taga motar Housemate dinta a Garage, tana bude kofar ta shiga parlor ta gansa kwance kan 3 seater yana bacci, har ta kulle kofar bata ga ya bude ido ba, ta nufi dakinta ta shiga ciki ta canza kaya sannan ta fito ta shiga kitchen, tuwon ta dora har zata fara hada ingredient na miyar kukan sai kuma ta fasa taji gwara tayi vegetable soup kawai, ita kanta bata san menene yasa take son yin vegetable soup din ba duk da bata wani son cin miyar ganye she prefer slimy soup, sai da ta gama tuwon sannan tayi ordering lyft da zai kai ta nearest African store da zata iya siyan ingredients din miyan Vegetable.


*Make ur payment before the end of free pages*

_Halysaah is just 500 naira_

07087865788
' [5/10, 10:07 AM] khaleesat Haiydar =???
'?: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6




('(' HALYSAAH('('





By _Khaleesat Haiydar_
'




13....

Har Khaleesat ta fita daga gidan zuwa Supermarket Housemate dinta bai tashi ba, bayan ta dawo sai bata gansa a parlor ba alamar ya shiga dakinsa, kafin karfe hudu da rabi na yamma Khaleesat ta gama miyan da take, tayi dishing ma Safiyyah abincin a warmer din da zata kai mata, kan kace me aroma din girkin ya cika gidan, ko tuwon bata ci ba ta tafi dakinta tayi wanka tayi alwala tayi sallan la'asar sannan ta shirya, fitowa parlor tayi ta nufi kitchen, tsaye ta ga Housemate dinta ya jingina da cabinet din kitchen din idonsa a lumshe, ya dora lipton a gas, tace "Bacci kake a kitchen din?" Bude ido yayi ya juya ya kalleta yace "Not at all" Tace "To me kake yi?" Ya dan shafa kansa yace "I am having a terrible headache" Tayi kasa da murya tana kallonsa tace "Ka sha magani?" Ya kashe gas din yace "Zan sha" Tace "To in sa maka abinci?" Yace "What did you cook?" Tace "Tuwo...." Bai jira ta karasa ba da sauri yace "A'a, Alhamdulillah, am full" Murmushi tayi tace "To ai ba miyar kuka bane, vegetable soup ne" Tana fadin haka ta bude masa tukunyar miyar tana kallonsa, bayan ya ga miyar a hankali yace "Ohk, but let me dish the food my self" Ita dai bata ce masa komai ba ya dau plate ta nuna masa inda tuwon yake, kallon dan tuwon da ya zuba ta dinga yi, sai kuma tace "Wannan dan kadan din?" Without looking at her yace "Zai isheni" bata sake cewa komai ba ya zuba miyar a gefe with just one protein ya saka spoon a gefe, sannan ya dau mug ya debi lipton da ya dafa ya dau plate din tuwon yace "Thank you" Bin sa tayi da kallo har ya fita daga kitchen din. Ko da ta fito parlor da abincin Safiyyah ta samesa zaune kan kujera bai fara cin abincin ba, ya daga kai ya kalleta, ta dau handbag dinta dake saman kujera, yace "Are you going out with food?" Tace "Yea, kawata zan kai ma abinci she is sick" Yace "Ohk Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" Daga haka ta fita daga gidan. Har kusan Magrib Khaleesat na tare da Safiyya, sosai jikin Safiyyah yayi sauki sai labari take ma Khaleesat da tayi shiru hankalinta baya kan hirar, da ta tuna maganar da Ummanta tayi mata jiya da kuma abinda Abdul yace mata da ta kirasa daxu sai taji duk duniyar tayi mata zafi babu abinda ke mata dadi a rai, Safiyyah da ta kula da yanayin Khaleesat tace "Wai me ke damun ki ne kawata?" Khaleesat ta kalleta, sai kuma ta dan yi murmushi tace "Bakomai Sophie, kawai na gaji ne sosai har na fara jin bacci" Ba don khaleesat bata son gaya mata damuwarta bane yasa tace mata haka sai don bata son fadin damuwar tata a wnn lkcn, but tasan dole zata gaya ma Safiyyah abinda ke faruwa, Safiyyah tace "To ki kwana a nan mana tunda bamu da lectures gobe, it's already pass 7 yanzu" Khaleesat ta dan bude ido tace "In kwana a ina? A'a ni dai kin ga tafiyata" duk yanda Safiyyah ta so convincing Khaleesat ta kwana gidan, khaleesat ta ki sauraronta tayi sllhn magariba ta kama hanyar gida, dama tun da ta kawo tuwon da tayi ma Safiyyah daxu Mustapha ya shigo har dakin ya diba ta zama uncomfortable zama a gidan, matarsa kuwa ta kasa ta tsare a parlon gidan, ko da ta fito parlorn ita kadai ta samu zaune fuska a murtuke, Khaleesat tayi mata sallama ita dai har ta fita daga gidan bata ji ta amsa mata ba. Khaleesat na isa gida ta kulle kofar parlon ta karasa ciki tana kallon plate din dake saman kujera da yayi covering with another plate, mug din shayin ma na ajiye bai sha ba, ta tafi ta bude plate din tuwon taga bai ci ba, abinda ya fada mata a kitchen ne daxu ya fado mata that he is having headache, ta juya tana kallon kofar dakinsa, tana tafiya a hankali ta nufi dakin tayi knocking gently, sai da ta sake knocking jin bai amsa ba ta Wan bude kofar slightly, bacci ta gansa yake yi saman gado, ta sauke idonta kasa, lkci daya ya bude ido yana kallonta, ta Wan koma baya kamar mara gaskiya tana kame kame tace "Are you okay?" Kansa kawai ya nuna mata ta karasa cikin dakin ta duka ta side dinsa da damuwa tace "Baka sha maganin bane?" Bai yi responding ba hakan yasa ta kai hannu kusa da forehead dinsa sai dai bata taSa sa ba, amma she could feel he is running temperature, a hankali tace "Should i order an Uber ride sae kaje asibiti?" Ya girgiza mata kai idonsa a lumshe, rasa abinda zata yi tayi, lkci daya taji hankalinta ya tashi, mikewa tayi ta fita zuwa dakinta ta dau karamin towel tayi soaking dinsa da ruwa bayan tayi squeezing ta dawo dakin, ta nufi inda yake kwance ta duka kusa da shi ta dora karamin towel din da ta linke saman forehead dinsa, ya bude idonsa, cikin sanyin murya tana kallonsa tace "In yi ordering ride din?" Ya dafe towel din da ta dora masa a forehead yace "Don't worry Halysaah" ita dai kallonsa kawai take, can ta tuna tana da pain reliever a daki, mikewa tayi dai dai nan taji kamar ana kwankwasa kofa a parlor, ta juya ta nufi kofar ta fita zuwa parlorn, tsaye tayi bakin kofar parlon tana tambayar waye at the same time tana bude kofar, ta Wan koma baya tana kallonsa with surprise, shi ma daga sama har kasa yake kallonta hannunsa rike da wayarsa, su biyu ne tsaye bakin kofar, lkci daya ta hade rai tace "How may i help you?" Kai tsaye shi wanda yake mata kallon sama da kasa ya shigo parlon har sai da ta matsa gefe da sauri kar ya bangajeta, shi dayan mutumin dake tsaye bakin kofar calmly yace "Hello, plss is Jay in here? Ahmad Jay...." Mutumin da ya shiga parlon ya juya yana masa wani kallo yace "Kaii wajenta ka zo halan?" Shi wanda ke waje ya Wan yi murmushi ya shiga parlon ya sauke kai kasa, amma sai ya tsaya daga bakin kofar bai karasa can cikin parlon ba, shi ko wanda ya fara shigowa har ya nufi hanyar dakunan dake apartment din, da sauri Khaleesat ta nufesa a fusace tace "How will you just barge into someone's apartment without excuse or an explanation?" Juyawa yayi ya kalleta from head to toes, ita kanta bata san me yasa ta tsaya Wan nesa da shi ba taki ci gaba da bin sa ba amma bata fasa masa kallon da take masa ba fuska a daure, ya gyada kai ya ci gaba da tafiyarsa kamar yasan dakin, kawai taga ya bude ya shiga ciki, ta juya ta kalli mutumin dake tsaye har sannan a parlor tace "Ku haka ake yi daga inda ku ka fito?" Cikin nutsuwa mutumin yace "We are sorry Madam, location shi Jay din ya tura masa wai bashi da lafiya and here is the location sannan mun ga motarsa a garage din apartment din nan, hope we are in the right place?" Khaleesat tace "Sai bayan kun shigo za ka tambayeni ko kuna right place din?? Where Is it done this way?" Mutumin ya hade hannunsa biyu alamar bada hakuri yace "Kiyi hakuri dai" Yana fadin haka ya bi bayansa ya shiga har cikin dakin shi ma, bin su tayi amma ta tsaya a corridor, ji tayi wanda ya fara shiga dakin da farko na cewa "Jay me kake yi a gidan nan da wannan karamar yarinyar da bata da manners? Is this the reason why ka dena zama 24/7 a gida yanzu? When did u start this useless life? First of all who is the little brat i want to know?" Da wani expression yake kallon Jay dake fama da kansa a kwance yaki basa amsa, shi dai mutumin da ya shigo a karshe na tsaye daga daya gefen Jay yana masa sannu, sai kuma ya kalli Ajay calmy yace "Kaga dai bashi da lafiya yanzu Ajay, all this question isn't necessary now" Da kyar Jay yace "Ka kyale Wan iska mana, laifina ne da na tura masa location" Ajay dai sai bin dakin da kallon mamaki yake yi ganin property din Jay duk a dakin, can ya kallesa yace "To ma menene yasa za ka kirani? in baka da lafiya ita yarinyar ta kai ka hospital mana, ba tare ku ke zama a gidan ba" Mikewa zaune Jay yayi yace "Kai wai did you know how i am feeling? Ka wani zo nan ka isheni da unnecessary surutu, pls get out Ajay, gerrout pls" Khaleesat dake sauraron conversation dinsu ta wani taSe baki ta juya ta koma parlor ta zauna wani mugun haushin mutumin da taji ana kira da Ajay take ji a ranta, taga Abdul ma balle shi, Salem ya mika ma Jay hannu zae taimaka masa ya tashi, Jay yace "Pls kace mata ta kawo min bottle water, or you check the kitchen ka dauko min" Salem ya juya ya fita, Ajay dake taSe baki ya juya ya fice daga dakin shi ma, direct ya nufi kofar fita daga apartment din yayi ficewarsa ya koma can waje ya tsaya jikin motarsa, Salem dai ya bi sa da kallo ya sauke ajiyar zuciya ganin fita yayi, sannan ya kalli Khaleesat ya gaya mata ta dauko ma Jay ruwa, ta mike ta tafi kitchen ta dauko ruwan ta basa, ba a dau lokaci ba sai ga shi sun fito tare da Jay, mikewa tsaye tayi tana kallonsa, Jay ya zame hannunsa a na Salem ya zauna saman kujera ya jinginar da kansa da kujeran ya lumshe ido, a hankali Khaleesat tace "Amma hospital zaku je ko?" Da kyar yace "No, gida za mu je ya min treatment" Khaleesat tace "To Allah ya sauwake, Allah ya baka lafiya" Ya gyada mata kai sannan ya mika ma Salem hannu ya mike tsaye, Khaleesat na son tambayarsa abu amma ta kasa, ganin za su fita daga parlon ta dake tace "Can i get ur digit so i can be checking up on you?" Salem dai ya juya ya kalleta da Wan mamaki jin tambayar da tayi, does this mean basu san juna ba kenan tunda har bata da lambarsa, Housemate din nata ya juya ya kalleta yace "Ai zaki gane gidan da muka je ranan da na mance makulli da daddare bayan kin dawo Nigeria, that's our home, zaki iya zuwa at anytime...." Khaleesat dai ta dinga kallonsa, sai kuma yace "Salem give her my digit, ko kuma ka bata nata kar ta kira bata sameni ba" Salem yace "Ohk bari in bata nawa" Khaleesat ta dauko wayarta sannan ta amshi number Salem, bayan ya gama bata suka fita daga parlon tare da housemate din nata, tana tafiya a sanyaye ta karasa gun window ta bude labule tana kallonsu, sae da suka fito Ajay ya shiga motarsa, bayan sun shiga yayi zoom off. Khaleesat ta sauke idonta sannan ta juya a hankali ta koma cikin parlon. Bayan kwana uku Khaleesat sun fito daga aji tare da Safiyyah dake waya, ita dai Khaleesat na tafiya ne amma gaba daya hankalinta na wani gun daban, Safiyyah tace "Wai ya jikin Housemate din naki yanzu? Ko ya dawo ne baki gaya min ba?" Khaleesat ta kalleta tace "Har yanzu ai bamu yi magana da shi ba" Safiyyah tace "To wanda ya baki number sa fa ko har yanzu bai daga kiran naki ba?" Khaleesat tace "Aa ya daga jiya, amma sai yace min he is much better, da na tambayesa ko yana kusa sae yace min a'a yana bacci, kawai ni dai i hope da gasken jikin nasa da sauki..." Safiyyah tace "Shegen mutumi in ba kinibibi ba me yasa zai wani ?i baki lambar Housemate din naki sai na shi, me za kiyi da lambarsa when u have no business with him, in ni ce ke cewa zanyi a'a ba nasa zai ban ba gaskiya, amma fa har yanzu abun na ban mamaki ace duk mutuncin Housemate din nan naki bai taSa requesting phone number din ki ba ko sau daya, ji ma sanda kika je Nigeria, to ko me yasa oho" Ita dai Khaleesat kallonta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah tace "To wai ma ba kince har cewa yayi ki je gidan nasu ba, tun jiya nake ce maki mu shirya mu je kin ki, in baki je kin dubasa ba ta yaya zai san kema kin damu da halin da yake ciki, ai ance gaida me gaisheka, beside da bakinsa ya maki kwatancen gidan nasu ai, to me yasa baza ki je ba, da Nigeria muke sai mu ce ai bai kamata ba saboda yan sa ido da yan fassara lamari but this is USA Khaleesat, kuma abu ai kamawa yake for 3 days baki san halin da mutumin nan yake ciki ba gashi ke kanki kina testifying kyawawan halayyarsa, wallahi ki shirya in rakaki mu je ki dubasa da jiki, kuma kafin nan mu fara biyawa ta shopping mall kiyi masa shopping da zaki kai masa, shi ma sae yaji dadi wallahi" Khaleesat tace "Kawai sai in kama tafiya har gidan nasu duba shi? Ai bai ma dace ba sai kace wasu marasa kamun kai Safiyyah, be it in USA still bai dace ba, mu mata ne fa" Safiyyah ta mata wani kallo, can tace "Ai da naki matsalar ya taso haka ya cire kudadensa sama da miliyan goma sha biyar ko fin haka if i am not mistaken yayi solving maki matsalar ki, shi kuma bai da lafiya rai kwakwai mutu kwakwai kince zuwa dubasa rashin kamun kai ne, to rashin dacewa ya wuce zaman da ku ke yi gida daya? Shi wannan me za ki ce masa? Wani lokacin baki ma nazarin maganar dake fitowa bakin ki Khaleesat, in zuwa dubasa bai dace ba to zamanku gida daya ma ai bai dace ba be it in USA" Khaleesat dai sai kallonta take ta kasa cewa komai, can dai tace "Ban gane ba, Miliyan goma sha biyar for what??" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ohh for what ko? da yake business class ticket din da ya siya maki an gaya maki na wasan yara ne ai, to bari ki ji Business class ticket kusan 5000 dollars ne base on Airline, ki lissafa 5000 ko 4000 dollars kudin Nigeria kiga nawa zai baki" Khaleesat was speechless after realizing Safiyyah is saying the truth, banda dala dubu dayan da ya bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login