Showing 138001 words to 141000 words out of 241367 words

Chapter 47 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1556

ta ajiye plate din, cikin ladabi tace "Ga kazar ta kammala Hajiya" Momy tace "Kalan Hijabin nan naki na daga min hankali a gidan nan, kar ki sake saka min shi, in yar wa zaki yi to ki yar bana son shi kwata kwata yayi kalar talauci" Mai aikin ta dukar da kai tace "Toh Hajiya in sha Allah bazan sake sa shi ba, kiyi hakuri" Fita tayi daga parlon da sauri, Momy ta dau plate din tulin kazar da aka ajiye mata ta fara ci tana cewa "Ai dama tunda aka ce min zai taho da ita hankali na ya kwanta, don dama taho da ita shi ne me wuyan...." Meemah tayi murmushi ita ma ta dau yankan kaza daya tana ci tace "I trust you Momy" Khaleesat ta saka Hijab dinta har kasa tana harhada wasu daga kananun kayan dake cikin closet din dakin kamar yanda Abdul ya umarceta tayi, absentmindedly take aikin don tayi nisa a tunanin da take, bude kofar dakin yayi ya shigo, ita dai bata juya ba tana ci gaba da abinda ya sakata, ya karasa har bayanta ya tsaya, taki juyowa gabanta na faduwa, juyo da ita yayi yana kallonta ta sunkuyar da kanta, yace "Me ya sa baki son ki saki ranki har yanxu? Always looking worried" A hankali ta daga kanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Kin gama hada kayan ne?" Girgiza masa kai tayi, yace "To gama" ta juya ta ci gaba da abinda take, shi dai yana tsaye yana kallonta, pad ta dauko a karshe zata saka cikin karamin trolley din yace "What are you using that for? Ba yau zaki gama ba?" Taki kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Amma ban gama ba ai" Bata jira me zai ce ba ta saka a akwatin sannan ta kulle ta mike tsaye, kamo hannunta biyu yayi yana kallon cikin idonta, speaking slowly yace "Promise me you won't act silly har mu isa kano Khaleesat" Ta rasa dalilin da hawaye ya cika idonta, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds yace "If you try anything silly, zaki yi matukar mamakin abinda zan yi, i promise you" Da kyar tace "Toh, amma plss ina son inyi waya da Safiyyah, i am missing her" Yace "Baza ki yi waya da Safiyyah ba, amma idan muka isa kano zan fara kai ki gidanku ki gaishesu sannan mu tafi gidanmu" Ita dai bata ce komai ba hawaye na zuba idonta, a haka suka bar gidan zuwa airport tunda yana da hoton National ID dinta a wayarsa. Da yamma suka sauka garin kano, driver din gidansu har ya iso airport din yana jiransa, Drivern ya bude ma Khaleesat back seat bayan ya gaisheta, kanta a kasa ta shiga motar, kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai gashi ta kara zagbewa gaba daya, Abdul ya shiga ta daya side din, sannan drivern ya shiga motar ya tada suka bar airport din, sai bayan da suka fita daga cikin airport Abdul ya gaya ma drivern inda zai fara kai su, sun yi nisa sosai da tafiyar Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa cikin tunanin da take, hannunta ya saka cikin nasa wanda hakan ya dawo da ita reality, ta Wan kallesa, yayi kasa da murya yace "Are you hungry?" Girgiza masa kai tayi, ya jawota zuwa jikinsa yana kallonta, ita dai bata ce masa komai ba zuciyarta na bugawa, a haka suka isa Mariri wajen karfe biyar da rabi na yamma, Drivern na parking daga opposite din gidansu Khaleesat Abdul ya bude motar ya sauka, jiki a sanyaye Khaleesat ta sauka daga motar, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko akasin haka ganinta a kofar gidansu, Abdul ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan sai a sannan hawaye suka cicciko mata ido, Noor ce ta fara hangota tana hura gawayi ta taso da gudu ta rungumeta, sai a sannan sauran en gidan duk suka juya suna kallon Khaleesat, Umma dake zaune bakin kofar dakinta ita ma ta dinga kallonta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka taSe baki suna kallon juna, Aunty Farida dake gyara dakin Umma ta fito da sauri jin sunan wanda Noor ta kira, Khaleesat ta tafi ta rungumeta ta fashe da matsanancin kuka, Farin ciki wajen Aunty Farida ba a cewa komai don duk tunanin su Ajay ne suka dawo da ita gida, sallaman Abdul yasa duk suka juya suna kallon hanyar shigowa gidan da mamaki, nan da nan fara'ar Aunty Farida ya bace, su Mama Shatu ne kawai suka amsa masa sallaman, ya karaso cikin compound din, Aunty Farida ta saki Khaleesat ta tafi ta zauna kusa da Umma fuskarta babu yabo babu fallasa, Mama Zubaida ta mike da sauri ta shimfida masa tabarma ita da Mama Shatu na masa sannu da zuwa, ya zauna kan tabarman yana kallon Umma ya gaisheta, Umma ta amsa tace "Sannu da zuwa" Aunty Farida ta mike ta shige dakin Umma, Abdul ya gaida su Mama Zubaida dake ta washe baki, duk suka amsa da fara'a, Ita dai Khaleesat na durkushe kusa da Ummanta kanta a kasa, Abdul ya kalli Umma yace "Baba baya nan ne" Umma tayi karfin halin cewa "Eh bai dawo ba" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Malam Ali ya shigo gidan da rabin buhun dankalin Hausa a hannunsa, ajiyewa yayi ganin Abdul da Khaleesat, yace "A'aa, ikon Allah, baki mu ka yi yau a gidan" Abdul ya tashi ya tafi har inda Malam Ali ke tsaye ya gaishesa, Malam Ali ya amsa yana kame kame, ya tafi da sauri ya dauko tabarma ya kara shimfida ma Abdul yace "Yi zaman ka a nan, bari in zubo mana ruwa a buta lokacin Magariba yayi" Da sauri ya tafi ya dauko butoci biyu ya tafi zai debo ruwan, Umma ta mike ta shige dakinta, Khaleesat ta bi bayanta, Nenne ce ta shigo gidan da sallama tace "Allah me hikima, sannunku da zuwa Awdul" Abdul ya gaisheta, ta jawo kujera ta zauna tana facing dinsa tace "Lafiya lau wallahi, ya iyayen naka, ina kokarin daura sanwa kenan sai ga wani almajiri da gudu ya zo ya sanar min ai kun zo, kasan Wan albarka ne almajirin nan duk wani abu da ke faruwa a gidan Ali kamar kiftawan ido yake rugowa ya sanar min, ni kuma in ina da er dabino kwara uku in basa la'ada, nayi farin cikin ganin ka wallahi, ina matar taka, in ji tare ku ke?" Yace "Tare mu ke" Sai ga Malam Ali da ruwa a butoci yace "Ai ina jin tana dakin uwarta" Nenne tace "Kai kuma lafiya? ina zaka da butocin ruwa ko karfe shidda bai yi ba?" Malam Ali yace "Au? To to bari a ajiye, na zata magariba ta yi" Da sauri ya koma ya ajiye butocin ya dawo, Nenne tayi kasa da murya tana kallon Abdul tace "To Awdallah, ka dubi girman Allah ka rike amanar da muka baka, yanxu kai ne uwarta kai ne ubanta, duk ta kuskure maka ka kawota wajena ni zan san yanda zan yi da ita, kuma albarkacin auren da ya shiga tsakaninka da jikata ka kara ba Mahaifinka hakuri ya yafe ma Malam Ali komai ya wuce a wajensa don girman Allah, don yanxu kam duk mun zama daya tunda ga aure har ya shiga tsakani, Allah Ubangijin ya baku zaman lafiya ya kauda duk wata fitina ya kawo zuri'a dayyaba" Abdul yace "In sha Allah Kaka" Nenne na murmushi tace "To madallah, gashi ko tuwon dare ban yi ba balle in zubo maka" Yace "Ba komai, can gidanmu za mu wuce yanxu yamma tayi" Nenne tace "Gaskiya kam, bari in fito maka da ita ku tafi, go slown hanyar nan bata da kyau" Tashi Nenne tayi ta nufi dakin Umma, kuka kawai Khaleesat take Umma tayi tagumi tana kallonta ta ma rasa abun cewa amma daurewa kawai take ita ma hawayen bai zubo mata ba, don bakin ciki Aunty Farida na jingine jikin bangon dakin ita ma ta kasa cewa komai, a haka Nenne ta shigo dakin ta same su, taSe baki tayi tace "Ta so ki fita mijinki na waje na jiranki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana kuka kamar ranta zai fita, Nenne tayi kasa da murya tace "Wato a yanda kanwar uwarki ke zube ba mashinshini shekara da shekaru haka kema kike son ki zauna mana tunda kyau kawai gare ku amma babu farin jini, banda samun waje ki samu miji zankadede kamar Awdul amma son zuci irin taki da na uwarki da kanwarta bazai sa ku yi farin ciki da hakan ba, in a baya Awdul Wan iska ne dama Allah ya taSa halittar da bai shiryar ba in yayi niyya? Daga yanda Awdul ke magana a kintse na gane ya shiryu wallahi, to ko kawota da yayi ta gaishemu kadai ya isa mu shaida shiriyarsa, wallahi ku dinga jin tsoron Allahn da ya halicce ku, duk wanda burinsa ya raba aure to tsinuwar Allah ne zai tabbata a garesa, kuma in sha Allahu Khaleesat tayi aure kenan mutuwa kadai ne zai rabata da mijinta tunda duk mun san yana sonta, tashi ki fita gun mijinki ku tafi munafuka kawai, duk da can baki san baki son shi ba sai da ya aika ki kasar turawa idonki ya bude a can" Cikin kuka Khaleesat tace "Ni wallahi bana son sa, bana son sa, bazan iya zama da shi ba" Nenne tace "Aikin banza, to uban me ya rage kuma bayan ya kwana da ke? Ai duk rashin son da kike masa dole ki zauna da shi tunda ya kwana dake yau kusan satin ki daya a gidansa ba kuma ajiye ki zai yi yana kallo kamar hoto ba tunda shi ba Wan iska bane, kuma gidan Ali ba Obalande bane da za a tara masa fararen zawara har biyu a gida, Farida ma kadai ta ishemu, tashi ki fita ki bani waje ko in tafi in kira maki Ali yanxun nan ya fitar min da ke, tun da uwata ta haifeni ban taSa ganin er da bata son kwanciyar hankalin ubanta ba sai ke" Umma ta share hawayen dake zuba idonta tana kallon Khaleesat tace "Ta shi ki je Khaleesah, Allah ya maki albarka, Allah kuma ya baku zaman lafiya" Mikewa Khaleesat tayi tana kuka sosai ta fita daga dakin Ummanta, Nenne tace "Atoh dai, iya addu'ar da za mu yi mata kenan a matsayin mu na rikakkun musulmai, tun da muka ga haka to Allah ne kadai ya san hikimarsa nayin hakan, kuma dama an gaya min aurenta da Awdul aure ne me kyan gaske in har zata kwantar da hankalinta, gashi mun shaida yana son ta, kuma ta dalilinta arzikin ubanta duk zai dawo har ma ya fi na da, wallahi haka aka ce min, kawai dai babba ba a son yayi ta surutu ne shi sa nake jan bakina nayi shiru" Har suka bar gidan da Abdul hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat, dubu talatin ya ba kishiyoyin ummanta ko wacce 15k, ya ba Islam 50k, Nenne ya bata 20k, Malam Ali kuwa bai amsa kudinsa ba sai ajiye masa Abdul yayi kan tabarman dake bakin kofar dakinsa, babban tashin hankalin Khaleesat yanxu period dinta da ya dauke, don kafin su taho kano a dari dari tayi sallahn Azahar kar ya shigo ya ganta, tasan yau dai ?aryar ta ya kare kawai, a haka suka iso gidansu Abdul bayan sallan magrib, Driver na shiga babban compound din da mota Khaleesat taji gabanta ya tsananta faduwa, bayan yayi parking a space din parking Abdul ya sauko daga motar yana kallonta, da kyar ta iya saukowa daga motar zuciyarta na bugawa sosai wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba all of a sudden, ya fara tafiya tana bin sa har suka isa entrance din shiga parlorn gidan....
[6/18, 7:34 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat na tafiya a hankali ta shiga parlon tana karanto addu'o'i a ranta don irin faduwar da gabanta yake yi isn't normal, ga tsikar jikinta sai tashi yake, she was so uncomfortable and restless at the same time, Abdul ya kulle kofar parlon ya kalli mahaifiyarsa dake zaune cikin parlor ita da kanwarta Aunty karima da Meemah, ko wannensu da bowl cike da farfesun kayan ciki a hannu, Khaleesat ta sunkuyar da kanta ganin gaba dayansu zubo mata ido suka yi suna kallonta fuskarsu babu yabo babu fallasa, amma kana kallon kwayar idanuwansa babu abinda zaka gani sai tsantsan kiyayyarta, da kyar ta karasa tsakar parlon kamar zata harde ta fadi, ta duka kasa cikin sanyin murya ta gaishesu gaba daya, instead Momy sai ta dauke kai tana kallon Abdul tace "Flight din sai na dare ka samu kenan Babana, bayan tun sassafe Meemah tayi maka text" Aunty Karima ta hau kwalo ma mai aiki kira ta zo ta karo mata farfesu, Abdul bai ce ma Momy komai ba ganin babu wanda ya amsa gaisuwar Khaleesat cikinsu ya kalleta yace "Ta shi mu je" Khaleesat ta Waga kai ta kallesa amma bata tashi ba ga zuciyarta sai bugawa yake, Momy tace "Ta tashi ku je ina? Wacece ita din tukunna?" A takaice yace "Matata ce" Aunty Karima ta gyara zama da mamaki tace "Ikon Allah, ita ce er gidan barawon da yayi ma Alhaji sata har na miliyan dari kenan?" Meemah tace "Kwarai kuwa gashi kin gane ma idonki, ita ce dai er matsiyatan da Abdul ya makale ma saboda rashin sanin darajan mahaifinsa bai dubi rashin kirkin da aka yi ma Daddy a kotu akan hakkinsa ba ya koma ma yarinyar, dama yawon ta zube uwarta ta shigo yi Nigeria shi ne ta hadu da ubanta bayan sun yi watsewarsu ya aureta...." Katse ta Abdul yayi a fusace yace "Idan kika ci gaba da voicing gibberish zaki sha mamakin abinda zan maki a nan Amina, bridle ur tongue" Aunty Karima ta bude baki da mamaki tace "Amina kai tsaye? Ko ka fara shaye shaye ne Abdul? Akan shegiyar yarinyar nan kake nema kayi ma yayarka rashin kunya?" Abdul ya kalleta yace "Kar ki sake sako min baki tunda ba dake nake ba, stay out of anything that concerns me, Momy ce dolen ki ba ni ba" Momy tayi wani murmushi tace "Rabu da su Babana, take her inside ta huta, sannunku da zuwa" Tana fadin haka ta tashi ta taho kusa da Khaleesat ta dafa ta tace "Welcome my daughter, ku je sama kin ji" Da kyar Khaleesat ta mike tsaye duk jikinta a sanyaye ta bi bayan Abdul, Momy ta koma ta zauna ta bi ta da kallon gefen ido, har ta ga sun haura sama sannan ta kalli su Meemah tayi kasa da murya tace "Sam baku da hankali baku da tunani, haka muka yi da ku daxu?" Meemah da ke huci tace "Ni matsala ta kinsan ban iya pretending bane Momy, wallahi ban iya ba ko nace zan yi" A fusace Momy tace "To in kin san ruguza min plan za ki yi ki ja min asara to tun wuri ki tattara ki tafi gidan Suwaiba bana son hauka, duk ba ke kika ja mana wannan bala'i ba? da sa hannun ki fa abubuwan nan suka faru, ai wallahi sati daya yayi ma yarinyar nan yawa a gidan nan in dai ni na haifi Abdallah, don haka duk wanda bazai iya abinda nace yayi ba to ya bar gidan nan kawai kar ya ja min asara" Aunty Karima tace "Toh Momy kar kuma fa yace zai koma can gidansa da ita, kin san babu me sa shi babu me hanasa idan yayi niyyar yin abu" Momy tace "Ku dai ku zuba min ido kawai ku ga ikon Allah, ance maku ni mahaukaciya ce warce bata san abinda take yi ba irin ku? Ai ni ba yarinya bace nasan me nake yi" Mikewa Momy tayi tana tafiya gansan gansan ta nufi staircase, Meemah ta kyabe baki tace "Wallahi ji naki zuciyata bazata iya wani pretending ba akan shegiyar yarinyar nan me kamar sadaka yalla, ban taSa jin tsanar mutum a duniya irin yanda na tsaneta ba, Abdul bai taSa min kalan tijaran da yayi min akan ta ba, kuma fa a gabanta yayi min haka tana ji tana kallo" Aunty Karima ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima ba gashi yayi min ba Meemah, fatan mu kawai komai ya zo karshe cikin gaggawa, mu yi yanda Momy tace kawai" Khaleesat ta dinga bin dakin da Abdul ya kawota da kallo wanda babu tantama dakinsa ne, a hankali ta zauna saman kujeran dakin tana kallonsa yana cire agogon wrist dinsa alamar zai shiga bandaki yayi alwala, abinda aka yi mata a parlor ne kawai ke yawo a kanta, tayi nisa tunanin da take yi sai gashi ya fito daga bandakin yana kallonta yace "Shiga kiyi alwala" Sosai gabanta ya fadi ta daga kai tana kallonsa, ta dake tace "Ai ban gama ba" Wani tsawan da ya gigitata ya daka mata, yana mata wani mugun kallo yace "Kar ki raina min hankali, is it going to take u forever to finish ur period? Karya kike yi kin gama" Tsabar yanda ta tsorata jikinta har bari yake ta ma rasa me zata ce masa, yace "Idan na dawo masallaci i will check for my self" Daga haka ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, hawaye ya fara zarya a idonta, wannan moment din take ta tsoro gashi ya zo kuma babu yanda ta iya, shesshekan kuka ta fara yi cikin tashin hankali, bayan ya fita da kamar minti biyu taji an bude kofar dakin, ta juya da sauri gabanta na faduwa, Momy ce ta shigo dakin ta sakar mata murmushi ta nufota tace "Ya sunanki daughter? Mu sai yace mana Khaleesat, ni dai nace Khaleesat ai ba sunan yanka bane" Khaleesat ta sauke idonta zuciyarta na bugawa a hankali tace "Sunana Hauwa" Momy tace "Maa sha Allah, ashe uwata ce, welcome to the family my dear, taso mu je kiyi sallah" Khaleesat felt a bit relieve da gesture din Momy toward her, ta mike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login