Showing 177001 words to 180000 words out of 241367 words

Chapter 60 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1612

suturu kam yayi mata ba iyaka, to wai ko monthly allowance da yake tura mata a kasar Amurka in kika ji sai hankalin ki ya tashi, uwa uba a zo kan kudin makarantar ta da House rent" Momy tayi mitsi mitsi da ido cikin bacin rai tace "Don Allah ki bar wannan maganar don raina baci yake Meemah, su je kawai Allah ya isa, ni da nake uwarsa ma sai ya ga dama yake siya min abu, to yanxu ko ce masu muka yi su biya a ina suka ga kudin biya Meemah? Ko gidan da suke ciki suka ce za su siyar wallahi karkari yayi dubu dari biyar, kai ni dubu dari biyar din ma bazan siya wannan kangon ba wallahi, kin ga kuwa gwara a bar zancen kawai, baki ji yanda raina ya baci ba wallahi, kawai Allah ya isa zan ta ja masu a kan uban kudin da Abdul ya kashe ma yarinyar kuma ba wai don bani da kudin maka su kotu ba...." Meemah tace "Ko kuma mu je duk mu kwaso kayan da ya dinga siya mata da jakunkuna masu tsada" Momy tace "Ki ci uwar me da su? Kema dai wallahi, shekara 38 ban san yaushe zaki yi hankali ba Meemah, Allah ya isan dai shi ne dai dai su, don babu abinda za mu ci da kayanta, tunda muka samu miliyan goman ma ai mun gode Allah" Meemah ta tabe baki ta koma ta kwanta tace "Kuma kin san wani abu Momy, da Abdul yana kasar nan har yanxu zai fa iya waiwayanta idan asirin ya sakesa, don wallahi masifaffen so yake ma shegiyar ke har yanxu baki gane ba, ji fa kafin su bar kasar yanda ko magana baya yi ma mutane a gidan nan, kullum zaka gansa babu walwala" Momy ta hade rai tace "Ni kuma ga er iska sai in sakankance har asiri ya sakesa ko? Ai da gangan na sa uban ya tafi da shi business trip din da za shi china, da biyu na takura uban su tafi tare don naga take takensa, ga sabon tijaran da na lura zai fara mana, kuma ko ba komai ai kinga za su dade a can kan su dawo, ni kuma kafin nan na sa anyi aiki sosai ya mance da wata shegiya wai ita Khaleesat a duniyar nan, sai kuma in tanadar masa mata er gidan mutunci, yana dawowa sai biki kawai" Meemah tace "Da dai yafi kam, yana dawowa yayi aure, ki sama masa yarinya dai dai class dinsa ba er talakawar da ya nace ma ba, ni wallahi ban zata talaucin iyayen yarinyar nan ya kai haka ba, har muka dawo gida na kasa cire view din gidan a idona, wannan ko karen gidanmu aka ajiye a gidan nan ai sai yayi rashin lafiya a bar mu da kashe makudan kudi zuwa veterinary balle ace mutum, to yanxu da bai rabu da ita ba haka wataran abu zai kama ki kwashi kawayenki da abokan business aje gidansu yarinyar? Misali ace ubanta ko uwarta wani ya mutu, haka za a kwasa aje masu gaisuwa wannan gidan?" Momy tace "Ai Abdul ya so ja min abun kunyan da bazai taSa goguwa ba, ya so tona min asiri a idon duniya amma Allah ya rufa min asiri ya takaita abun, da irin rainin da Abdul zai ja min sai Allah wallahi, to ni dai tunda na samu aka rabu lafiya ai sai su bi wani sarkin kuma" Meemah tayi dariya tace "Kuma da bai saketa ba fa sai ya iya canza masu wani gidan don ba hankali garesa ba, tunda don yayi ta ma shegiyar yarinyar bauta Allah ya halitto sa" Wani shegen kallo Momy tayi mata sannan ta juya ta fita daga dakin. Khaleesat na durkushe gaban Umma dake mata addu'an Allah ya kai ta lafiya, ya bata sa'an karatun ta, ita dai Khaleesat kanta na kasa duk jikinta a sanyaye, a hankali Umma tace "Ki kula da kanki don Allah, duk da na yarda dake Jiddah amma ki kara taka tsantsan, kar ki mance tarbiyar da muka maki, kuma ki rike addu'a da azkar, Allah ya kare min ke ya tsare ki duk inda zaki shiga..." Nenne ce ta bude labulen dakin a fusace tace "Yau naga jaraba wajen Zahra'u, sai me motar yayi zuciya ya ja motarsa ya wuce ne ko yaya? Duk daren jiya da wayewar garin yau baki sakata gaba da duk wani zancen da zaki mata ba sai yanxu da motar da zai kai ta iyapot ya iso, haba Zahra'u ya ki ke haka ne? Ko dai maidata ciki za kiyi?" Aunty Farida ta wani kalle Nenne tace "To kyauta zai kai ta airport din da bazai jira ba, naga dai kudi zata basa Nenne" Nenne tace "Ai ba motar ubanta bane da zata shanya sa a rana don zata basa kudi, kuma shi ba boyi boyinta bane da zai ta tsayuwa yana jiranta a rana kamar Wan iska, tunanin ku kenan 'yan Adam, don zaka ba mutum kudi sai aka ce ka walakantasa? Ka ki darajasa?" Aunty Farida taki tanka Nenne, Umma na kallon Khaleesat tace "Tashi ki je Jiddah, Allah ya tsare ya kai ku lafiya" A hankali Khaleesat tace "Ameen Umma" Daga haka ta mike ta dau handbag dinta don duk an fitar da akwatunan ta kofar gida, Nenne na kallon Umma tace "In ji dai duk an saka mata doya da dankalin da na kawo mata a akwatin nata?" Da sauri Aunty Farida tace "An saka komai" Nenne tace "Wake da su albasa da garin masara da na alkama fa?" Aunty Farida tace "Har su an sa" Nenne tace "To mu je" Khaleesat ta bi bayan Nenne suka fita daga dakin, Aunty Farida ta kara tura doya da dankalin da Nenne ta kawo da su garin alkama da Masara a bayan kyaure ta boye yanda Nenne bazata gani ba ko ta dawo dakin, daga nan ta bi bayan su, kasa daurewa Umma tayi ta mike ita ma ta fita, su Mama Zubaida da Mama Shatu na tsaye tsakar gida duk suka bi Khaleesat da kallo, Kana ganin fuskokinsu kasan babu farin cikin komawa Amurka da Khaleesat zata yi, Yaron Mama Zubaida ya nufo Khaleesat da gudu yana mika mata kudin hannunsa yace "Wai gashi inji Ummanmu da Mama Shatu ki sha ruwa a hanya" Nenne ta karbe kudin a hannun yaron ta kirga taga dubu biyu ne, sokesa tayi jikin haSar zaninta tace "Ta gode" Daga haka ta kalli Khaleesat tace "Mu je" Khaleesat tayi ma kishiyoyin ummanta sallama sannan ta bi bayan Nenne suka fita daga gidan Aunty Farida na biye da su, a kofar gidan Khaleesat ta kara sallama da Babanta don bai fita kasuwa ba ranan yana jiran tafiyarta, kasa hada ido tayi da shi yana mata addu'a da fatan alkhairi, Nenne ta bude mata bayan motar tace "Ni dai shiga don Allah, tun jiya basu san da addu'an su ba sai yau da kike sauri salon jirgi ya tafi ya bar ki" Khaleesat ta shiga motar Nenne ta kulle, haka kawai Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, ta daga masu hannu kawai sannan drivern ya ja motar suka bar kofar gidan. Ko da Khaleesat ta isa airport ta tarar Safiyyah na ta jiranta don tun daxu ta iso airport din, Khaleesat ta amshi boarding pass dinta suka nufi Departure Lounge, bayan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin Abuja, inda a nan za su hau jirgin da zai kai su kasar America.
[7/3, 9:23 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Tun da suka sauka Amurka wajen karfe hudu na asuba gaba daya walwalar Khaleesat ya bace, ta dawo so silent kamar mara lafiya, cikin rashin kuzari ta dinga yin komai har suka gama da custom da Immigration, Safiyyah na kallonta tace "Wai duk sanyin ne yasa kika dawo haka? Naga mood din ki ya canza all of a sudden, are you okay?" Khaleesat tayi murmushin karfin hali ta girgiza mata kai kawai tana gyara Jacket din jikinta don tun a kasar da suka yi transit duk suka saka Jacket din su saboda sanyi, Safiyyah na kallon wayar hannunta ganin kiran Mustapha for the 4th time tace "Shi kuma wannan daga sauka ko kashe jirgin ba ayi ba ya fara doka min kira kamar jira yake, kilan kewan fadan da muke yi da matarsa kullum yake yi, bai san i came fully ready for her ba, don this time around bazan sake tolerating nonsense dinta ba wallahi" Khaleesat dai murmushi kawai tayi bata ce mata komai ba har suka fita daga Arrivals, Safiyyah tace "I don't want us to stress ur Housemate, naga message dinsa tun muna Abuja yana tambayar karfe nawa za mu taso kuma a ina za mu yi transit, kilan da na gaya masa zai iya estimating time din da za mu iso ya zo yayi picking din mu daga airport cikin azababben sanyin nan da ake, shi yasa kawai ban masa reply ba kar muyi inconveniencing dinsa" Khaleesat ce ta fara hango Ya Mustapha tsaye jikin motarsa kafin Safiyyah ma ta gansa tayi kasa da murya tace "Sai kin ga yanda ya addabi Dad din mu wai an koma makaranta naki dawowa, sai kace zaman jin dadi nake yi a gidansa da shegiyar matar nan tasa" Khaleesat ce ta fara gaida Mustapha bayan ya iso inda suke tsaye, ya amsa da fara'a yace "Ya hanya Khaleesah?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah ma ta gaishesa ya amsa sannan suka nufi motar sa gaba daya, ya amshi trolley dinsu ya saka a booth din motar yace "Kun ji sanyin America ko, don ma yau babu snow" Khaleesat dai tayi murmushi, Safiyyah ta bude mata back seat tana kallonta, Khaleesat ta shiga sannan Safiyyah ta zaga ta bude gaban motar ta shiga ita ma, Mustapha ya tada motar bayan sun bar Airport din ya kalli Safiyyah yace "Amma dai Khaleesat won't be going to her apartment now, zai fi kyau mu je can gidana idan ta huta sai ta koma Apartment dinta anytime she is ready" Safiyyah tace "Dama gidan ka zaka kai mu gaba daya mana, cikin sanyin nan ta ina zata je ta fara gyaran apartment dinta ga gajiyar hanya" Ko da wasa Safiyyah bata ba Mustapha labarin abinda ya faru da Khaleesat ba, ita dai Khaleesat tayi shiru a bayan motar tana tunanin another new life that she is going to begin in America with her burden on people's shoulder, shikenan ita kuma daga wannan ya dau responsibility dinta sai wannan ya dauka, sosai tunanin nan ke kara kashe mata jiki, gashi rayuwar America ba dai tsada ba, kawai tasan takura Housemate dinta zata yi da burden dinta, a haka suka isa gidan Mustapha da tunani iri iri a ranta, bin unguwan ta dinga yi da kallo don bata san unguwan ba, sati biyu da fara exams dinsu Last semester Safiyyah ke gaya mata Mustapha ya amshi wani apartment da ya fi wanda suke ciki girma za su tashi a gidan da suke, ita dai har suka bar America bata san gidan da suka koma ba, bayan Mustapha yayi parking suka sauka a motar Safiyyah ta bar sa da shigo masu da kayansu ta kama hannun Khaleesat zuwa cikin gidan, ita dai Khaleesat bin ta kawai take, upon yanda ta tsani duk abinda zai hadata da gidan Mustapha saboda matarsa sai gashi yau saboda rashin option da choice ya sa ta amince da zuwa gidansa babu ko musu, zaune suka tarar da matarsa a parlor ta sha uban rigan sanyi ga daurin dankwalin ture kaga tsiya da tayi da zaninta, sosai jikin Khaleesat yayi sanyi ta rakube jikin kujera tana kallonta ta gaisheta, amma matar nan ta dinga kallon TV tana cin popcorn kamar bata ji Khaleesat ba, Safiyyah dama ko kallonta bata yi ba ta nufi hanyar dakinta ta murda taji a kulle kuma babu makulli a jikin kofar, tsaye tayi fuskarta babu yabo babu fallasa tana jiran Mustapha ya shigo gidan, bayan yan sakwanni sai gashi ya shigo parlon da akwatuna biyu, Safiyyah tace "Yaya ina makullin dakina?" Ya karasa ya murda kofar yaji a kulle, ya dawo parlor yana kallon Surayya yace "Surayya ina makullin dakin can yake?" Sai a sannan Surayya ta juya ta wani kallesa tana ci gaba da cin popcorn din hannunta tace "Makullin daki? Ban gane Makullin daki ba, Ajiyar makulli aka bani da za a tambayeni?" Safiyyah dake ta kallon Ya Mustapha tana huci tace "Kai dama yaya da ka wani ishi Daddy da kira cewar mun koma makaranta in dawo a saman roofing din gidan nan kake da niyyar ajiyeni tunda gashi an dauke makullin dakin an boye? Wannan ai iskanci ne da walakanci, mutum yayi dogon tafiya haka ya dawo kuma yaga an dauke masa makullin daki?" Mustapha ya karasa kusa da Surayya da sauri yace "Ke Surayya ko dai Aslam yana wasa ya cire Makullin dakin ne a jikin kofar?" Surayya taki ko kallonsa, Safiyyah ta wani tsuke fuska tace "Aslam ne tsayinsa zai kai har ya cire makulli a kofar daki? Ai sai dai Uwar Aslam, kuma Allah ya so ban bar komai da za a sace min a dakin ba sai takardu, tunda an saba min satan dama" Mikewa Surayya tayi tana mata wani tsinannen kallo tace "Keeee, in kina cin kasa ki kiyayi ta shuri, wallahi ki iya bakin ki don ni ba sa'ar ki bace ki kiyaye ni, in kika yi wasa za ki sha mamakina yanxun nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Osheyy ancient of days, ashe dai ke ba sa'a ta bace, ai sai yau kike gaya min nake ji, kuma in kin fasa bani mamaki sunanki ba Surayya ba, shege ka fasa tsakanin ni da ke" Fada Mustapha ya fara yi yana cewa "Meye haka? Ko kuna hauka ne? Wannan wani irin iskanci ne? A gaban nawa ku ke wannan rashin hankalin?" Magana yake yi at the same time yana kai kawo yana dube duben makullin dakin Safiyyah a parlon, Ita dai Khaleesat na rakube jikin kujera taji kanta har ya fara mata wani azababben ciwo, banda rashin option me zai kawota gidan nan ita kam, tunanin hakan yasa ta ji hawaye ya cika idonta, Safiyyah sai girgiza kafa take tana hararan Surayyah da ta koma ta zauna tana cin Popcorn dinta tana gyara daurin ture kaga tsiyan dake kanta tana kara cokarosa gaba, Mustapha ya karasa inda Aslam ke kwance yana bacci a parlon ya fara tashinsa yana tambayarsa makullin dakin Safiyyah, yaron da ko shekara biyu bai karasa ba, a fusace Surayya tace "Wallahi kar ka tada min yarona Mustapha, shi yasan maka wani makulli da zaka tashesa yana bacci" Mustapha ya juya ya kalleta yace "Surayya in ke kika dauke makullin nan ki fito da shi bana son rainin hankali" Surayya ta wani hararesa tace "Kar ka bata min rai this early morning, in dau makulli inyi uwar me da shi? Plss do not provoke me Mustapha" Tana kai wa nan ta mike ta figi yaronta dake bacci ta nufi dakin ta da shi, Mustapha ya kasa cewa komai ya bi ta da kallo yana rike da waist dinsa, can ya juya ya kalli Safiyyah dake masa wani mugun harara kamar zata kwadesa, karasawa yayi kusa da ita yace "Look Safiyyah...." Katse sa tayi a fusace tace "Babu abinda zaka gaya min Yaya, Don't tell me anything, dama don matarka ta min wannan walakancin ya sa ka dage sai na dawo an koma makaranta, wallahi ni dai Daddy zan kira a samar min wani gidan da zan zauna in karasa final year dina kawai in peace, don bazan iya zama da wannan devil wife dinka a gida daya ba" Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Mustapha bai iya yace mata komai ba, can dai ya nufi hanyar dakinsa don daki uku ne a gidan, yana shiga dakin ya dau duk abinda zai bukata ya fito da shi parlor ya ajiye yana kallon Safiyyah yace "Ga bedroom dina can ku shiga" Safiyyah na jin haka ta figi hannun Khaleesat zuwa dakin nasa, da sauri Surayya ta fito daga dakinta don bata kulle kofar dakin ba saboda ta dinga jin abinda za ace a parlon, tana kallonsa da wani irin mamaki tace "Ban gane ga Bedroom dinka can su shiga ba Mustapha, turakar namu za su shiga kake nufi ko me?" Safiyyah ta kwashe da wani dariya har da kyakyatawa ta ja Khaleesat suka shiga dakin sannan tayi banging kofar ta kulle, Surayyah zata yi magana Mustapha ya Waga mata hannu fuska a murtuke alamar baya son jin komai sannan ya fice daga parlon zai shigo da sauran akwatunan su Safiyyah, Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ta dinga kallon Safiyyah tace "Haba Sophie, this isn't proper mana, why not mu zauna a parlor har san da za a ga makullin dakin naki, dakinsu ne wannan fa" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ai ba kowa ne Wan iska mara zuciya kamar ki ba Khaleesat, kuma wallahi ina dakin nan babu inda zan je har sai ranan da ta fito min da makullin dakina...." Khaleesat ta kasa cewa komai don da gaske she is shock, sai ga Mustapha yayi knocking kofar dakin sannan ya ajiye masu hand luggage dinsu yace "Me za ku ci yanxu?" Safiyyah na zaune gefen gadonsa fuskarta babu walwala irin ita an bata mata din nan tace "Kawai shayi da cookies kafin gari ya waye" Yace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo masu kofa, har sannan Surayyah na tsaye inda take a parlor ta kasa motsin kirki, ta bi sa da kallo har ya shiga kitchen zai hado masu shayin, bata san sanda ta fashe da kuka ba tana rufe bakinta ta nufi dakinta da sauri, Mustapha ya dawo dakin nasa da Cup din shayi biyu da cookies ya ajiye masu ya fita.... Khaleesat na idar da sallan Asuba ta kwanta kasan carpet din dakin Mustapha don dakin da dumi saboda room heater dake kunne, amma hakan bai hanata dinga jin sanyi ba saboda wankan da tayi, babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login