Showing 102001 words to 105000 words out of 241367 words

Chapter 35 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1569

apartment uku self contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa, ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace "Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai" AJ ya daga kansa ya kalleta yace "Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?" Aunty Farida tace "Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da barina wancan Unguwan na dawo nan" Ajay dai yayi shiru idonsa a kasa, Aunty Farida tace "Kuma ba unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo" Ajay yace "Toh shikenan, jikinta da zafi ne?" Aunty Farida tace "Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta min magunguna in siyo mata" Ajay yace "Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip ayi mata karin ruwa" Aunty Farida tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid" Ajay ya Wan yi murmushi yace "Bari in je in dawo dai" A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya harhado mata magunguna da drip da allurai. Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar kafafuwanta, cikin fada take cewa "Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata? Er talakawa? Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na'am bane kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka? In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya? Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane" Wata matashiya ce er shekara 39 dake zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace "Momy ban gane abinda kike nufi ba? Wai nufinki ya saketa kenan?" A fusace Momyn tace "Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema? Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?" Warce ta kira da Meema ta girgiza kai tace "A'a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy? Ae wallahi bata isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci da tijara haka?" Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace "In har aka ga na saketa to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan ne zata gwammaci bata taSa sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her" Momy ta tabe baki tace "Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar yarinyar nan" Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace "Ai ki ma dena maganar asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji" Momy dai ta tabe baki tana kallon me aikinta tace "Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min naman yatsu" Hakuri mai aikin ta hau bata. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta Wan kishingida a 3 seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya taSa biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta kalli Khaleesat tace "Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?" Khaleesat ta girgiza mata kai, dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace "Tare da brother dina muke" Aunty Farida tace "To ku shigo mana" a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara'a, sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace "Are you feeling better now Housemate?" Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace "Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha Allah, i promise you" Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl din hannunta Softly yace "Take ur soup" Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali, Aunty Farida ta kalli Ajay tace "Baka zauna ba Junaid" Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna, Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace "Mu ma duk ba da son ran mu bane abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za su dau er su su ba Abdul aure"


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H?


Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG s Beauty Lounge zai buWe a ranar Litinin, 2nd June 2025  daidai lokacin Sallah!=?
?

 Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG s Beauty Lounge ya buWe da kwalliya, tsafta da ?amshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai Waukar ido

Wanke ?afafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ?amshi masu daWi

Shirin amare da na musamman


Ba kawai gyara muke ba  kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daWin wanke ?afa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ?amshi  komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki  ki ji daWin sauyin MG s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
[5/30, 8:55 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: *Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga me kasuwar garin Dutse Hajiya Aunty Zahrah da Hajjaju Sadiya Chamo Ex in-law, Hajiya Nafeesah Mom twins da Ummu Zainab Maman Ramla, Aunty Maryam Dan Ladi nasidi kema na gaisheki da katon murya, Hajiya Jumare da Hajiya Asmy me kayan amare, Oum Nabeelah, Mardiyyah, Uwar Janan, Halysah Garba=?? i hail you all with respect yan Palace*

Manyan Membobin _d'
>?y?Khaleesat's Citadel_d'
>?y?
*Su Meenah parrot=??, Oum Noor, Nafeesah Jawwad, Rukayya, Fidomashi, Siyam, M manal, Mrs Barrister, Shanono Esq, Ummilos, Na'imatu, Zulaiha, Ummu Abdrhm, Khaleesat Haiydar is saying a big thank you to you all for ur support always, Allah ya bar min ku*>?p?


Aunty Farida ta numfasa a hankali tace "Da yake Abdul shi kadai ne namiji gun mahaifinsa, mahaifin ya dauki son duniya ya dora masa kuma bai jin maganar kowa sai nasa, duk abinda Abdul yake so shi mahaifinsa ke so, bayan yaga Khaleesat a kotu babu tantama zuwa yayi ya samu uban ya nuna yana sonta zai kuma aureta, wannan dalili yasa babu bata lokaci suka janye kara a kotu suka bar maganar miliyan dari da sharadin Malam Ali zai ba Abdul auren er sa Khaleesat, mu dai har yau bamu san ko da wata yarjejeniya da aka yi a kotun ba ko babu, mun dai san an janye kara kawai kuma duk muka yi farin ciki sosai da hakan, burin mu kawai Malam Ali ya dawo gare mu ko da bazai tsinana mu da komai ba amma mu dinga ganinsa a tare da mu a matsayin kantangar gida, balle duk mun san yayi ma iyalansa hidima dai dai gwargwado ya kuma kyautata masu yanda ya kamata, jarabawa ce kawai ta fada masa, bana mantawa Khaleesat ta shiga damuwa sosai a lkcn tana ta koke koke wai ita bata son Abdul tun ma bata san kalansa ba bata gansa ba tace bata sonsa bazata iya aurensa ba, mu kam idonmu duk ya rufe da son ganin an wanke Malam Ali daga laifin da ake zarginsa da shi, ni da uwarta muka yi ta bata baki muna kwantar mata da hankali muka ce ko tafi son a maida mahaifinta prison ne, ko don mahaifinta bazata hakura ba ta amince da bukatar Abdul na son aurenta don case din ya mutu gaba daya, gashi tun bayan dawowar Malam Ali yayi ta rashin lafiya ko kudin kai sa asibiti babu, duba da hakan ne ma yasa muka yi ta karfafa ma Khaleesat gwiwa muna bata baki, a haka dai muka samu muka lallabata ta fara hakura, nan kishiyoyin Ummanta suka fito da ba?in cikinsu da hassada a fili tunda su ma ai suna da 'ya ya mata sa'annin Khaleesat da ma wa enda suka girmeta amma shine Abdul zai ce sai Khaleesat, nan fa duk suka hau gaba sosai da yayata saboda Wan mai kudi ya ga Khaleesat yace yana so, ranan farko da Abdul ya fara zuwa unguwan cewa yayi shi bazai shigo da motarsa layin ba ta fito bakin titi ta samesa, gashi daga gidan zuwa bakin titi akwai tafiya sosai, haka nan uwar ta lallabata ta shirya ta saka nikab dinta kannenta biyu suka rakata har bakin titin ta samesa, a ranan kuma ya bata babban waya ya kuma hadata da dubu hamsin, ba ma ita ta amsa ba don nuna masa tayi bata so shine ya ba kannenta yayi tafiyarsa, da kudin aka samu aka biya mata waec dinta tunda ba mu da yanda za mu yi, a kaf tarihi ban taSa jin wanda yake neman yarinya da isa da gadara da walakanci kamar Abdul ba, for almost 2 months in Abdul zai zo unguwan mu sai dai dole ta fito titi ta samesa shi bazai shiga layin da motarsa ba, watarana ne ya kira bata da lafiya shine da ya tashi zuwa dubata da yamma ya shigo layin a karo na farko tunda ya fara zuwa gurin ta, daga nan kuma ya dena cewa ta fito bakin titi in ya zo sai dai ya karasa ciki da motarsa, ya kai ya kawo har cikin gida yana shigowa, tun a wannan lokacin Abdul baya raga ma Khaleesat, fadan yau daban na gobe daban, bashi da fahimta bashi da uxuri, ga nuna isa da gadara abinda yace yake so dole shi zata yi, haka nan yarinyar nan ke hakuri da halinsa duk don saboda mahaifinta, rana daddaya ne baya sa ta kuka, sai dai ni da uwarta mu yi ta bata hakuri muna ganin duk me sauki ne tunda har yana sonta kuma yaji zai aureta ya zauna da ita wataran zata canza sa da kanta, ni dai a sanda na fara sarewa da lamarin Abdul jikina yayi sanyi shine watarana da ya daga hannu ya mareta har sai da shatin yatsunsa ya kwanta fuskarta, mu dai har yau bata gaya mana me tayi masa da yayi mata haka ba don a cikin motarsa hakan ya faru, nan jikin uwarta ma ya fara sanyi kan lamarin har ta samu Mai gidanta ta gaya masa amma Malam Ali yayi ta kakkarewa har da cewa duk wanda ma ya kara tada maganar Allah ya isa, ana haka har ya biya mata jamb ya kai ta da kansa ta zana don fara jami'a tunda waec dinta ya fito kuma sakamakonta yayi kyau sosai, kawai rana daya kwatsam ubansa ya kira mahaifinta wai ga abinda Abdul yace yake so, wato zai tura Khaleesat Amurka tayi karatu a can, duk kawaicin da yayata take wannan karan sai da ta nuna bata amince da hakan ba, don ana ta bin su a yanda suke so ba hakan ke nufin bamu da ta cewa akan lamarin Khaleesat ba, ba Yayata ba har kakar Khaleesat Nenne ta nuna rashin amincewarta a wannan bukatar tasu, babu ta yanda za a dau yarinya karama haka da ko mallakan hankalinta bata gama yi ba ace za a tura ta har Amurka da sunan karatu, in haka ne kawai a daura auren mana sai ya kai ta duk inda ma zai kai ta tayi karatu, in ko ba haka ba babu inda er ta zata je da sunan karatu sai dai duk abinda zai faru ya faru, a nan dai laifin Mahaifin Khaleesat ne da ya dau tsoron duniya ya dora ma Abdul da mahaifinsa ba kuma tsoron komai ba sai tsoron kar su sake maidasa inda ya baro wato prison, dama tunda ya baro can ya dawo gashi nan gashin nan dai kamar ya Wan samu matsala a kwakwalwarsa, yau lafiya gobe akasin haka, ya dawo kamar ba Malam Ali ba, a lokacin duk ya gigice yayi ta bala'i wai ina ne ba a tura yaro karatu a zamanin yanxu, yarinya me shekara sha bakwai ce za ace ma yarinya, inda yake shiga ba nan yake fita ba, hakan ya zame masu bacin rai sosai da mahaifiyar Khaleesat har sai da ta bar gidan ta koma gidan Mahaifiyarsa warce ita ma yaki sauraronta, haka nan Malam Ali ya dau Khaleesat ya damka ma Abdul ba tare da amincewar uwarta ba ya kai ta karatu Amurka, Shiru Aunty Farida tayi tana kallon su Ajay dake kallonta duk suna sauraronta, a hankali tace "Tun daga sannan shi yake sponsoring komai nata a Amurka, cin ta da shan ta, da suturanta komai dai shi ne, sai san da ya ga dama ne yake bari ta zo hutu Nigeria, mu tsakaninmu da ita dama sai sanda muka ganta ko kuma muyi magana ta WhatsApp, gashi yaki a daura auren nasu wai sai ta gama karatun wanda wnn ne ke kara daga mana hankali, a haka ake ta rayuwar bamu da kwanciyar hankali, a ko da yaushe fatanmu shine ayi ayi auren don duk wasu iyaye nagari baza a same su da kwanciyar hankali ba ace yau er su budurwa bata gabansu, kusan kullum sai uwarta ta zubda hawaye kan wannan lamari sanadiyar hakan har sai da hawan jini ya kamata, ace bata da iko da er ta sai dai abinda Abdul da ubansa suka tsara gashi mai gidanta ya dau tsoron duniya ya dora masu sai jan sa suke kamar rakumi da akala.... ko wata biyu ba ayi ba ranan yayata ta kirani take sanar min sun kawo kudin auren Khaleesat, duk muka yi farin ciki sosai da hakan, muka yi fatan Allah ya sa hakan alkhairi ne a rayuwar Khaleesat tunda mu ma mun fi son ayi auren kowa ma ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login