Showing 12001 words to 15000 words out of 241367 words

Chapter 5 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1592

tace "Ban gane zaki tafi gida ba daga na kawo maki maganar arziki" Khaleesat tace "Wallahi da na sani babu abinda zai sa in bi ki gida jiya Safiyyah, haba fisabilillah, put ur self in the wife's shoe in kece aka ma haka zaki ji dadi?" Safiyyah tace "Godforbid, her shoes will never size me sef kafin in sa kafata ciki Khaleesat, ai ni bani da mugun hali kamar ta, kina ga fa ko tsayawa ta amsa gaisuwarki bata yi ba ta wani ?ara waya a kunne t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a wuce daki ita er iska, sannan bari kiji jiya iya cikina ta ajiye abinci a kitchen bayan nace mata nan zaki kwana kuma ta sani, ni dai wallahi in kika ce baki son yayana nice kawai baki so, Ya Musty bai da wani aibu wallahi, ga arziki ga Ilimi ga kyau, baza ma ki ce ya taSa auren wata er iska ba wai ita Surayya, Wan saurayi da shi" Khaleesat tace "In matarsa kike son tura ma haushi ai kema zaki iya aurensa tunda he is ur cousin brother kuma da aure tsakanin ku" Daga haka Khaleesat ta bar wajen tayi wucewarta, Safiyyah tace "Oho dai wallahi ce masa zan yi kin amince sai dai ki mutu, haka kawai kin makala ma kanki Wan daba kina kiransa da wanda zaki aura, ki auresa ki ci uwar me da shi, wannan har duka sai ya dinga nakada maki babu me kwatarki in ku ka yi aure" Khaleesat na isa gida taga babu motar Housemate dinta a parking space, jingina tayi jikin entrance din apartment din nasu, gashi ta gaji sosai ga yunwar da take ji, babu wanda ta saba da shi a Neighborhood din balle ta shiga gidansa, balle su turawa basu yarda da hakan ba ma, ta kusa twenty minute a tsaye sai ga motarsa ta hango, sunkuyar da kanta tayi har yayi parking ya karaso kofar entrance din, gefe ta koma without looking at him, tun kan ya karaso kofar apartment din ya sa hannu a aljihunsa yaji babu makullin, ya Wan bude ido still yana laluba duk aljihunsa, sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, juyawa yayi ya koma motarsa ta bi sa da ido, ya gama dube dubensa a motar bai ga makullin ba, ai tana ganin yanda yake dube dube tasan kilan ya yar da makullin, shikenan ta shiga uku, she is soo tired, har wani jiri take ji a tsayen da take, dawowa yayi yana kallonta yace "Look Halysaah, i think i left the key at where i am coming from" Ita dai bata ce komai ba kuma bata bari ta hada ido da shi ba, yace "Ko zaki shiga apartment din Neighbor dinmu kafin in dawo" Sunkuyar da kanta tayi still keeping mute, yace "Or ain't you familiar with them?" A takaice tace "Eh" Yace "Ok i will be back as soon as possible" Juyawa yayi ya koma gun motarsa ta bi sa da wani kallo.... Khaleesat na ta tsaye har bayan wani minti sha biyar sai gashi ya dawo, yana kallonta yace "Allah ya taimake ki na gani" Wani kallo tayi masa wato ita Allah ya taimaka ma, yana bude kofar tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta ba tare da ta juya ba, sai da ta kwanta na kusan minti sha biyar sannan ta mike a hankali ta shiga bandakinta, bayan Khaleesat tayi wanka tayi sallah tana zaune kan darduma taji yayi knocking kofar dakinta, kallon kofar take bata ce komai ba kuma bata amsa ba balle ta tashi, taji yace "Halysaah" Bluntly tace "Me ya faru?" Jin ya murda kofar dakin ta zaro ido ta mike tsaye da sauri tace "What?" Tuni ta isa gun kofar ta bude tana masa kallon tuhuma, ledan hannunsa ya ajiye mata yace "I got you food, naga kin yi laushi" Ta kalli ledan, ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya koma parlor, sauke idonta tayi, bayan few seconds ta duka ta dau ledan ta juya ta koma dakin. Khaleesat ta bude abincin da ya kawo mata ta fara ci kenan wayarta ya fara vibrate, mikewa tayi ta bude handbag dinta ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ke kiran ta, zaunawa tayi gefen gado tana kallon screen din wayar har sannan gabanta na bugawa, kafin kiran ya katse tayi karfin halin dagawa ta sa handsfree sannan tayi sallama cikin sanyin murya, maimakon ya amsa sai ji tayi yace "Wato all this While ni kike jira in kiraki ko Khaleesat?" Ta sauke idonta a hankali tace "To ai cewa kayi duk sanda kake son magana da ni zaka kirani amma kar in sake in kira ka" Yace "Don nace kar ki kirani sai ki ki kiran nawa? Me yasa baki reason ne?" A sanyaye tace "Kayi hakuri" Yace "In ban hakura ba ya zan yi da ke? Ai saboda baki damu da ni bane yasa kika zama comfortable without calling me all this while, ko da bazan daga ba ai kamata yayi ki kira" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" Yace "Yaushe za ku fara jarabawa?" Tace "Probably nan da 6 to 7 weeks" Yace "I can't wait har zuwa nan da sati bakwai ban gan ki ba Khaleesat, idan na samu lokaci zan shigo anytime from now in sha Allah" Shiru Khaleesat tayi as if trying to process what he just said, yace "Hello" Da sauri ta kifta ido tace "Na'am ina ji" Yace "Me yasa kika yi shiru? Ko baki son in zo ne?" Tayi yake tace "Aa ban yi shiru ba network ne, ban ji me kace ba" Yace "Ohk, nace you should expect me any moment from now" A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, me kike yi yanzu?" Tace "Abinci nake ci" Yace "Ohk switch to video call" A hankali tace "Toh" Mayafinta ta jawo sannan tayi yanda yace mata.


07087865788 for more info
' [5/2, 5:50 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: ('(' HALYSAAH ('('





By _Khaleesat Haiydar_
'



5......

Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta fito parlor daga dakinta, window ta nufa tana leka garage ta ga motar Housemate dinta alamar yana gidan, juyawa tayi ta tafi kitchen zata yi disposing takeaway din da yayi mata daxu, ta window din kitchen din ta hangosa zaune a Lawn din dake bayan kitchen din waya ?are a kunnensa alamar he is making a phone call, komawa baya tayi don kar ya hangota ta window din kitchen din, ta ajiye ledan hannunta a hankali ta juya ta fita daga kitchen din ta dawo parlor, tsaye tayi tana kallon handle na kofar living room din, sai kuma ta tafi gun da ya ajiye takardun karatunsa ta hau bincika Books din da sauri, har ta gama dube dubenta bata ga abinda take nema ba, ta koma kitchen din tana kara lekansa, seeing he is still on call ta dawo da sauri ta tafi corridor din dakunansu, tsaye tayi gabanta na faduwa as if contemplating on whether to do what is on her mind or just forget it, ganin she is just wasting time ta runtse idonta ta bude, sai kuma ta kai hannu handle din kofar dakinsa a hankali ta bude ta shiga ciki zuciyarta na bugawa, bin dakin that was neat and tidy ta fara yi da kallo kafin ta karasa can ciki da sauri, har sannan tana kallon ko ina na dakin, ta ma rasa daga inda zata fara duba abinda ta shigo nema, zagaye dakin ta fara yi tana dube dube with confusion, daya wayarsa dake gefen gado yayi haske alamar shigowar sako, kallon screen din wayar take yi ganin wani matashi kamarsa a shekaru ne a fuskar wayar, ta juya ta kalli Trouser dinsa, gabanta na faduwa ta dauka ta kai hannu aljihun wandon, Dollar ta ciro masu yawa tayi saurin ajiyesu gefen gado, sannan ta duba daya aljihun, zaro ido tayi jin makulli da Counter a ciki, ta ciro da sauri tana kallon makullin taga makullin kofar parlor ne, bata san sanda tayi murmushi ba ta ajiye wandon a inda ta dauka sannan ta juya da sauri, ?amewa tayi a spot din da take ganinsa tsaye bakin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta daga sama har kasa, kawai ta juya masa baya zuciyarta na bugawa taji kamar ?asa ya bude ta shige ta huta, after some seconds taji yace "Sannu da aiki" Ita dai ta kasa juyowa, she felt so ashame at that moment, she wish this never happened, sai juya makullin hannunta take with shame, Calmly yace "Give me the key" Ta wani turo baki taki juyowa tace "To ba amfani zan yi da shi ba" Yace "Dama in bana nan bincike kike shigowa ki min a daki?" Bata san sanda ta juyo tana kallonsa babu ko kiftawa ba jin abinda yace, sai kuma ta ajiye makullin a gefen gado ta nufi kofa ta bi gefensa ta fice daga dakin ta shiga nata ta tura kofar, nan da nan taji hawaye ya cika idonta ta zauna gefen gado, sai kuma ta Wora kanta saman pillow hawaye na sauka idonta har da shessheka. Karfe bakwai da few minutes Khaleesat na zaune kan darduma, tun da ta idar da sallah take zaune wajen, da ta tuna abinda Housemate din nata yace mata sai taji hawaye ya cika idonta, gaba daya taji ta tsani zaman gidan, kuma bata jin zata iya ci gaba da zama as far as he is here, ta yanke shawaran kawai zata gaya ma Abdul ya canza mata gida kamar yanda Safiyyah ta bata shawara tun farko taki dauka, wayarta dake gefen gado ta dauka jin ana kira, tana dubawa taga Mustapha ne ke kiranta, ajiye wayar tayi gefenta taki dauka har ya katse, ya sake kira nan ma taki dagawa, bayan Wan lokaci aka sake kiranta kallon wayar tayi a bit fed up thinking it's still Mustapha sai taga Abdul ne ke kiranta this time around, ta jawo wayar a hankali tayi picking ta kai kunne, sallama tayi masa sannan ta gaishesa, yace "Ya naji muryarki haka?" Tayi shiru tana tunanin ta inda zata fara sanar masa the situation at hand, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, a Wan tsawace yace "Ke, baki ji na ne zaki min shiru?" Kasa gaya masa tayi don bata ma san yanda zai fara daukar lamarin ba barin yanda taki gaya masa tun farko, Ta Wan yi yake tace "Ina jin ka, kawai muna da wani jarabawa ne gobe, kuma ina jin ciwon kai, and I haven't covered up, shi yasa nake damuwa" Yace "Na ce ki dena stressing kanki da karatu, u are not dull to be studying as if ur life depends on it, read a little and get enough rest, nasan za ki yi passing ko ma me za kuyi gobe" Tana murmushin karfin hali a hankali tace "To" Yace "Kin ci abinci ne?" Ta girgiza kai tace "Ban ci ba" yace "Ohk get something to eat, idan kin gama sai ki kirani ina jiran ki" Tace "Toh" Katse wayar yayi, ta bude WhatsApp dinta tana duba ko Neighbor dinsu ta mata reply taga ta hau WhatsApp din amma still bata yi reply ba, yau kwana uku kenan basu yi magana da Ummanta ba, Dialing din Number Sha'awa tayi ta direct call, har ya katse ba a daga ba, sai da ta sake kira aka daga, sallama Khaleesat tayi mata sannan ta gaisheta, Sha'awa ta amsa tace "Lafiya lau Khaleesah, ya karatu?" Khaleesat tace "Alhamdulillah ya gida ya su Kamilu?" Sha'awa tace "Duu lafiyansu lau wallahi" Khaleesat tace "Su Ummanmu suna lafiya..." Sha'awa tace "Kwana biyu kinyi magana ta wassap kinji shiru ko, to Ummanku dai bata da lafiya amma da sauki yanzu" Nan da nan Khaleesat taji hankalinta ya tashi don dama tun da taji shiru for days tasan ba lafiya ba, don ko bata yi ma Ummanta magana ba ita zata mata ta wayar Sha'awa taji ko tana lafiya, Hankalinta a tashe tace "Aunty Sha'awa tun yaushe?" Sha'awa tace "Ina jin yau kwana uku, ai an ma ce kar a gaya maki, shi yasa ko mayar maki da sakon da kika yi ta wassap din ma ban yi ba, yanzun ma kar ki wani ce zaki kira kowa kiyi ta mata addu'a kawai Allah ya bata lafiya" Khaleesat taji hawaye na sakko mata ta kasa cewa komai, Sha'awa tace "Wai daga ta tashi zata fito daki tayi alwalan magariba shi ne fa ta yanke jiki ta fadi a bakin kofar dakin, duk kwanan nan ina rabata da saka ma kanta damuwa tunda tasan matsalarta na hawan jini, to kinga ai irin haka ake gudu gashi kuma ya faru, Farida ma ta taho daga legas tun jiya ta iso, kar ki wani tada hankalinki don jikin da sauki" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Suna asibiti ne yanzu?" Sha'awa tace "Wani asibiti? To har sai da Farida ta zo sannan ta kai ta asibiti jiya in gaya maki, amma duk kwanakin nan tana gida gashi ko taSata kika yi a daya barin jikinta bata ji wai, ko magana ma in tayi sai kin sa kunne sosai zaki ji, ke abun fa ba kyau, har yanzu hankalinmu a tashe yake, an dai ce kar a gaya maki kar hankalinki ya tashi...." Khaleesat in hankalinta yayi dubu ya tashi a lkcn, ta kalli Screen din wayarta jin kiran ya katse alamar katin ta ya kare, ajiye wayar tayi ta fara rera kuka kamar an sanar mata da mutuwa... Har karfe goma na dare Khaleesat ta kasa tashi daga kan darduman da take, sosai ta shiga damuwa ba kadan ba, a inda take zaune Abdul ya kirata sau biyu amma ta kasa picking call din nasa, karfe goma da rabi taji anyi knocking kofar dakinta, ta juya ta kalli kofar tana share hawayen dake idonta amma bata tashi ba sai ma hade rai da tayi, after a while ya sake knocking still dai bata tanka ba, sai kuma taji yace "Assalamu alaikum" kawai ji tayi ya bude kofar dakin ta juya da sauri daga inda take zaune suka hada ido, daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta, ita dai taki yarda ta sake hada ido da shi, ya karasa ciki ya tsaya still leaving enough distance between them, calmly yace "Maganar da na maki yasa kike kuka? But i was only pulling ur legs Halysaah, i am sorry about that, was just joking" Wasu hawaye suka cika idonta sai kuma ta fara kuka, bude ido yayi alamar mamaki sosai yana kallonta, can dai ya kwantar da murya yace "Look, do not take my words serious Halysaah ni wasa nake maki wallahi" Ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka a hankali, dukawa yayi da mamaki sosai yana kallonta ya ma kasa cewa komai, after few seconds da taji shiru ta Wan bude fuskarta don tunaninta ya fita daga dakin, suna hada ido ta daure fuska tace "Ni saboda kai nace nake kuka?" Yace "Toh why are you crying?" Shiru tayi bata ce komai ba wasu sabbin hawayen na cika idonta, Yace "Tell me Halysaah, what is making you cry?" Kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "My mother is sick" Yace "Hasbunallah, what's wrong with her?" bata sake ce masa komai ba tana goge idonta, After few seconds ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma ai ba kuka zaki zauna kina yi ba, addu'a zaki mata Allah ya bata lafiya" Nan ma dai bata ce komai ba, ya mike yace "Allah ya bata lafiya" Sai a sannan tace "Ameen" Yace "Are you going back home to check on her?" Ta daga kai ta kallesa amma bata ce masa komai ba, yayi shiru shima, can yace "Are you from kano?" Ta gyada masa kai, Yace "Allah Ubangiji ya bata lafiya, and try getting something to eat for Dinner" Ta sunkuyar da kanta kawai, ya juya ya fita daga dakin ya kullo mata kofar gently. Wajen karfe sha biyu na dare Khaleesat na kwance taji ya sake knocking kofar dakinta, juyawa tayi ta kalli kofar, bayan wasu yan sakwanni ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake knocking sannan ta sauka daga saman gadon ta dau hijab dinta ta saka ta nufi kofar ta bude, yace "Are you still crying?" Ta hade rai ta girgiza kai without looking at him, yace "Ok naga baki fito kinyi dinner ba and it's past 12, ki nemi abinda za ki ci kar ki kwanta haka" Ita dai bata ce komai ba, yace "Hello" Daga kai tayi ta kallesa tace "Naji" Yace "Good" Kullo kofar dakin nata tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, sai da yaga ta shiga kitchen din sannan ya shiga dakinta yana bin ko ina da kallo, after a while Khaleesat ta fito daga kitchen din with a cup of tea and some cookies, tsaye ta gansa corridor, bayan ta karaso yace "Kin ga nima Ummi na bata da lafiya amma ban zauna ina kuka ba kamar yanda kika yi" Khaleesat bata kallesa ba ta shige dakinta ta kulle kofa, tana gama shan shayin ta koma saman gado ta kwanta, tasan yau da kyar ta iya bacci, she wish she can just see herself in Nigeria, but how?? Wasu hawaye ne suka zubo idonta ta lumshe ido, after a while ta jawo wayarta a hankali tayi dialing number Abdul bayan ta tuna ya kirata har sau biyu daxu bata iya tayi picking ba, har kiran ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, tasan as usual yayi fushi kenan, ko uxuri bazai mata ba, ajiye wayar tayi ta juya zuwa daya side din gadon. Washegari da safe Khaleesat na zaune daki tana ta kokarin kiran Aunty Farida amma baya shiga, har Sha'awa sai da ta kira ita ma wayarta baya shiga, ta rasa wa kuma zata kira, ta kalli agogon wayarta dake nuna karfe goma sha daya ta ajiye wayar tayi tagumi, tun daga daren jiya har yau bata da sukuni, ko schl din ma yau tasan bazata iya zuwa ba, juyawa tayi jin knocking a kofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login