Showing 123001 words to 126000 words out of 241367 words

Chapter 42 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1606

komai ya lafa, mu ma hankalinmu zai fi kwanciya da hakan don Alhaji Musa da tsinannen Wan sa ba barin mu za su yi mu zauna lafiya ba, duk da kotu ta wanke Ali amma Allah kadai yasan wani sharrin za su billo da shi don mutane ne wa enda babu Allah a ransu, wallahi sai su iya sa wa duk a kona mu cikin dare muna bacci, kunga ance zaman lafiya yafi zama Wan sarki shi sa cikin rufin asiri mu tattara komatsanmu ko zuwa gobe da magariba ne Ali ya mana shatan katuwar tirela mu koma kauyen mu" Mama Zubaida da Mama Shatu da suka saki baki suna kallon Nenne kusan a tare suka ce "Kauye kuma Nenne?" Nenne na kallonsu da kyau tace "Kwarai kuwa kauye, don dama can ne asalinmu, na gaji da tsallaka kogi cikin kwale kwale zuwa neman ma Ali taimako wataran inje in kife, gwara tun da sauran mutuncinmu mu bar garin nan" Mama Zubaida na girgiza kai tace "Inaaa, ai bazata saSu ba gaskiya, sai dai ni a bar ni a nan in ci gaba da kasuwancina ina rufa ma kaina da 'ya ya na asiri, akan matsalar da buzuwar matarsa da er ta suka jawo baza a cucemu a mayar da mu riga ba, bazai ma taSa yiwuwa bane gaskiya" Mama Shatu ta cafke tace "Sai dai ya tattara matarsa da 'ya yanta su kuma kauye Nenne, amma mu kam muna nan tunda ba mu ko 'ya yanmu muka jawo magana ba, dama mu ke ciyar da kan mu balle mu ji tsoron zamu rasa abinci" A fusace Nenne tace "A yaushe ku ka fara ciyar da kan naku munafukan Allah? ba sai bayan da ku ka tsiyace sa da fararen kafafuwan ku ba tukun? Ai ko Alhamdulillah kowa zai ma Ali shaidan kula da iyalinsa banda jarabawan shegun mata da Allah ya hadasa da, ku ne nan ku ka ja masa karayar arziki, dama ance min dukkanin ku babu alkhairi a tare da shi gwara ma Zahra'u, wallahi ce min aka yi in dai zai rabu da ke da Zubaida to arzikinsa zai dawo kaca kaca har fin na Wa, Zahra'u ce kadai matarsa ta arziki aka ce min, da zai ji ta nawa ma duk ya sallameku in ga inda za ku koma idan ba kauyen ba, ke Zubaida kin manta kauyen da uwarki da ubanki suke sai sati sati ake kawo ruwan pampo? Kin manta ko wutar lantarki ba a ja maku har yau a kauyen ba? Kauyen da muka je na dawo ina ta amai da gudawa watana daya a asibiti amma har kina da bakin kushe namu kauyen da babu abinda babu? To wani Wan iskan ne ma yace Rano kauye ce tukunna? Sannan ke shatu baza ma a kira garin iyayenki da kauye ba sai dai ace daji, haka nan muka dawo kano maguzawan mayu suka kamani da kyar aka samo kaina ba don Allah yayi da sauran shan ruwana a duniya ba da tuni na rasu wallahi" Shi dai Malam Ali yayi tagumi yayi shiru bai ce komai ba don tun kan Nenne ta kawo wnn shawara dama yake jin gwara ya koma garinsu don bai san da me Alhaji Musa da Wan sa za su billo ba kuma, shi dai bai yarda kotu zata wankesa akan kudaden nan masu yawa ba gani kawai yake dadin baki su Ajay suke masa, Nenne tace "Yau ga samun waje kai, ita Zahra'u me yasa bata kushe shawarata ba sai ku masu fararen kafa, ko da yake ita ta guduwan er ta da ta shiga duniya ma take, mu bar ta taji da wannan ma" Mama Shatu tace "Wace er ta? Ai wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Zahra'u tasan inda er ta take, mu dai ne kawai aka rena ma wayo aka raina mana hankali" Mama Zubaida tace "To ai ba ma sai kin rantse ba Shatu, kwarai kuwa Zahra'u tasan inda Khaleesat take" Nenne dai sai kallon Umma da ko kallon kishiyoyin nata bata yi ba take, a hankali Nenne tace "Lallai biri yayi kama da mutum, na kuma yarda da maganarku don Zahra'u da na sani da har yanzu tana nan kan darduma sanye da dogon hijabi tana rike da carbi tana kuka ba dare ba rana duk ta fita hayyacin ta, kawarta Uwar Salame da makociyarku sha'awa me daddawa su yi ta shigowa suna dannarta su zazzauna kusa da ita kamar me takaba, amma ina lura da ita yau kusan sati uku kenan tana ta harkar gabanta kamar babu abinda ya faru, nima dai ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba tasan inda Khaleesah take" Malam Ali ya gyara zama yana kallon Umma cikin lallami yace "Kiyi ma girman Allah Zahra'u ke da er ki ku rufa min asiri yanda Allah ya rufa maku, duk inda er nan ta tafi kiyi masu waya ta dawo ta amshi auren mijinta hannu bibbiyu, dama Allah ya riga ya kaddara Abdul ne mijinta mu din banza ne za mu canza hakan? don girman Allah ta rufa min asiri, ina cikin tashin hankali har yanxu wallahi don ban san kuma da me Alhaji Musa da Wan sa za su dawo min ba, rufin asirina shi ne na damka masu Khaleesah kawai, in har suka kasheni wallahi banza kawai za su kashe tunda ba galihu ne da ni ba, tunda aka maida ni furson din nan nake rashin lafiya me tsanani, yanzu haka maganar da nake yi kirjina kamar an aza min katuwar dutse, ku yi min rai ke da er ki" Kamar zai yi kuka ya kare maganar, Nenne na matsar kwallan da babu tace "In wani abu ya same ka dama da Zahra'u da er ta zan yi kuka wallahi, don su ke kokarin salwantar min da kai ta karfi da yaji" Umma da hawaye ya cika idonta tace "To wai ta yaya zan san inda Khaleesah take ni ba waya ba balle ku yi tunanin tana kirana? Ko kun ga ina zuwa wani waje daga cikin dakina ne?" Mama Zubaida tace "Na rantse da wanda raina ke hannunsa Zahra'u kinsan inda makirar er ki take, don haka sai dai ki rena ma wani hankali amma ba mu ba, duk abinda ya samu mijinmu dama har karshen duniya mun yi ta ja ma ke da 'ya yanki Allah ya isa kenan, banda samun waje ita Khaleesah har tana da ta cewa da har zata bude baki tace bazata zauna da Abdul ba? Da me tafi Abdul din banda rufa mata asiri da yayi zai aureta? Mutumin da ya maida ta fess ya maida ta mutum ya kashe mata dukiya babu adadi don butulci da samun waje tace ita bata son sa kuma a ina aka taSa tafka wannan iskancin? Wallahi ba a samu wanda zai ci ubanta bane shi yasa ta samu waje da yawa" Umma tace "Tun da har kuke tunanin nasan inda take kuma baza ku rasa sanin inda take ba ai, kilan ma za ku fi ni sani, don haka sai ku je ku fito da ita ku kai ta gidan Abdul din" Umma na kai wa nan ta mike ta shige dakinta, Mama Shatu tayi kasa da murya tace "Al-qur'an tasan inda take, da bata san inda take ba wallahi da har yau bata dena koke koke ba kilan har sai tayi rashin lafiya, kuma ni na ma fi zargin tana wajen kanwarta ne a garin Legas wallahi, in da ba haka ba ai da tuni mun ga Farida a gidan nan kamar an jefota amma gashi kusan sati uku har yau shiru Farida bata zo ba" Mama Zubaida tace "Ahaf ai mu ba yara bane" shi dai Malam Ali sai zazzare ido yake, Nenne tayi kasa da murya tace "Gaskiya na yarda da maganarku, don nima ina ta mamakin me yasa har yau farida bata zo ba, ita da ko tari yayarta tayi zata hawo mota ta kamo hanyar kano, amma ace an rasa Khaleesah yau sati uku shiru bata kamo hanya ba, ai da alamar tambaya" Malam Ali ya share zufar goshinsa duk da sanyin da ake shi ma yayi kasa da murya yace "To yanxu meye shawara? Ko ni zan shirya in tafi Lagos din ne?" Sosai hankalin Umma dake tsaye bakin kofarta daga cikin daki ya tashi don duk tana jin abinda suke cewa, Mama Zubaida tayi kasa da murya tace "Ai ban ma yarda da shiga dakin da tayi ba kilan er uwar zata kira, ko da yake bata da waya, kawai ina ga a gaya ma...." Mama Shatu ta Wan tsunguli Mama Zubaida alamar tayi shiru, lkci daya Mama Zubaida tayi tsit, Nenne ta mike tana kallon Malam Ali tace "Mu je daga gefe mu yi shawara Ali" Mikewa Malam Ali yayi ya nufi can hanyar fita daga compound din Nenne na biye da shi, Mama Shatu ta mike tayi ma Mama Zubaida alamar su shiga ciki, suna shiga daki Mama Shatu tace "Ke ya muna neman maganar auren nan ya rushe gaba daya ko zai hakura yace a basa Labeebah ko Lamisah amma kike basu shawaran su je Lagos?" Mama Zubaida tace "Wallahi gaba daya na sha'afa kinsan kwakwalwar tawa, kuma kece kika kawo maganar Khaleesah, tun asali ma bai kamata mu ce komai ba gashi yanxu mun karkato da hankalinsu zuwa Lagos, sai fa Malam ya iya shiryawa ya kama hanyar Lagos wallahi" Mama Shatu tayi shiru, can tace "Ai ko in yaje lagos din nan shikenan tsarinmu ya lalace don taso keyarta zai yi su dawo kano ya mika ma Abdul ita, kinga shikenan mun tashi a tutar babu mun kai ba malamai kudadenmu a banza, tunda duk mun san Abdul din na sonta kuma hannu bibbiyu zai amsheta su fara rayuwar aure" Mama Zubaida tace "Toh kuwa ina ga da kaina zan kira Farida ince mata in har tasan Khaleesah na wajenta to tayi maza maza su bar gidan don Malam zai kama hanyar lagos tare da Abdul" Mama Shatu tace "A'a bari in shiga dakin Zahra'u in gaya mata hakan, tunda ga Nenne da Malam can sun kebe bamu san maganar da suke ba" Bata jira cewar Mama Zubaida ba ta fita zuwa dakin Umma, Zaune ta tarar da Umma bakin katifarta abun duniya ya isheta gashi babu waya hannunta, kuma in tace ta fita daga gidan ta amshi waya a makota tasan dole za a zargeta, kuma daxu da safe suka yi waya da farida ta wayar Mama Salame take sanar mata jibi za su Nijar da Khaleesat, Mama Shatu na kallon Umma tayi kasa da murya tace "Zahra'u, ga can Nenne da Malam suna shirya yanda za a tafi legas wajen Farida gobe da asubar fari, in dai kinsan Khaleesah na wajenta wallahi kiyi maza ki buga mata waya su bar gidan su tafi wani wajen, a ajiye batun kishi a gefe abinda baza ka so ma danka ba kar ka so ma Wan wani, don duk mun san Abdul ba mutumin kwarai bane, kuma a zamanin nan an dena auren dole, mu ma ba a mana dole ba don haka baza mu yi ma 'ya yan mu ba" Mama Shatu na kai wa nan ta juya ta fice daga dakin, Umma ta mike gabanta na faduwa ta Wan leka tsakar gidan taga Nenne da Malam Ali tsaye a can lokon tsakar gidan suna magana kasa kasa.... Jay ya fito daga kitchen hannunsa rike da mug din shayi yana juyawa a hankali, Step Mom din Ajay ce zaune parlon cikin shiga ta alfarma, a ranan ta sauka gidan tare da jakadiyarta sun dawo daga kaduna, Jakadiyarta na dinning area tana yanka mata fruit, Jay ya tsaya dai dai inda yake don bata san ya fito daga kitchen din ba, da wani kallon tsana kawai yaga take bin Ajay dake haurawa sama hannunsa rike da laptop dinsa, after few seconds Jay ya ci gaba da juya shayin hannunsa yana kallonta, tana jin sound din cokali ta juya da sauri tana Wan murmushi ta hau canza channel din TV, shi dai Jay ya karasa cikin parlon bai sake kallonta ba, Jakadiyarta ta taho ta ajiye mata fr????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
uit din da ta gama yankawa cikin ladabi take sanar mata ga kayan marmarin, Cike da isa Aunty ta dau Apple ta fara ci, ta Wan kalli Jay ganin sama zai wuce shi ma tace "Gobe Abbanku zai shigo wani taro" Jay yace "Mun yi waya da shi" Daga haka shi ma ya wuce sama, ta wani taSe baki ta bi sa da kallo, Jakadiyar da ta zube gefenta cikin girmamawa tayi kasa da murya tace "Ranki shi dade, Allah ya ja zamaninki, daxu na jiyo mana wani labari Allah ya sa zaki yi maraba da wannan labarin" A takaice Aunty tace "Labari akan me?" Jakadiyar ta gyara zama tace "Akan Yarima" Aunty ta ajiye Apple din hannunta ta ba jakadiyar gaba daya attention dinta tace "Me kika jiyo?"
[6/11, 8:28 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Har mahaifin Abdul ya gama bambamin da yake yi a parlon Momy kamar zai ari baki bata ce masa komai ba illa rungume hannu da ta yi tana zaune kan kujera tana girgiza kafa fuskarta babu fara'a, Meemah dake zaune parlon ita ma dai bata ce komai ba fuska a murtuke, Alhaji Musa yayi bala'in sa me isarsa sannan ya juya zai bar parlon a fusace, sai kuma ya sake dawowa yana huci yace "Ina wawan Abdallan yake? Ina yake yaga abinda rashin tunaninsa da rashin daukan shawarar sa ya ja min" Momy ta tabe baki ita ma cike da takaici tace "Ai Alhaji yau kwana uku curr rabonsa ma da gidan gaba daya, kuma ba a samun sa a waya, ya kashe wayar" Rai bace Alhaji Musa yace "Duk shi ya ja min wannan bala'i ina zamana, wa yace masa dama ana harkar arziki da talaka? Sam ai ba a shige ma talaka duk yanda yake kuwa, tun asali zuri'ar da yake son in hada da wancan barawon mutumi ba wai nayi na'am da hakan bane, kawai bani da yanda zan yi da Abdallah ne" Momy ta gyara zama zuciyarta na tafarfasa tace "Atoh dai, har na gaji da nanata wannan sentence din da kayi Alhaji, ai ba a abun arziki da talaka don tun asali dama a tsiyace ya zo duniya kuma a tsiyace zai koma, kana zaman zaman ka gashi Abdullah ya ja maka asaran makudan kudi har da su taran kotu, wai kai da aka zalunta kai ne kuma da biyan tara saboda rashin adalci, ai Abdul bai kyauta mana bai duba mana ba, ace shi bazai dau maganata a matsayina na uwarsa ba? Babu yanda banyi discouraging dinsa kan tsinanniyar yarinyar nan ba na nuna masa ba ajinsa bace yaki saurarata wallahi, kyanta ne kawai ya rudesa wato kyan Wan maciji, har tayin er aminiyata nayi masa amma firr yaron nan yaki, to ga dai abinda ya ja mana" Meemah tace "Ni duk ba wannan ba Momy, kawai so nake in san wasu 'ya yan shegun ne suka tsaya mata haka har suka maida case din kotu? Sannan ga auren ma suna kokarin kotu ta rabasa ta karfi da yaji, kun ga kenan mun tashi a tutar babu, kuma babu tantama duk yanda aka yi ma su suka boye yarinyar, su waye en iskan nan ne?" Alhaji Musa na safa da marwa a parlon yace "Don kotu ta kori karar nan ba shi ke nufin na bar wannan mutumi da ya salwantar min da dukiya ba, mu zuba mu gani da shi, sai na lahira ya fi sa jin dadi wallahi" Daga haka ya bar parlon kamar zai tashi sama, Momy ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tana girgiza kai tace "Abdallah bai duba mana ba wallahi, ya kaskantar da mu a idon duniya kawai, wai yau talaka ne ya ci nasara a kan mu a kotu, this is a big slap to us, kuma ko uban menene dalilinsa na dinga kashe waya ba a samun sa oho? Ni taran da aka ci Alhaji ne ma yafi ?ona min rai wallahi, ga mari ga tsinka jaka, ki sake kiran wayarsa kiji ko zai shiga" Meemah tace "Baza fa a samesa a waya ba Momy, mu da ganin Abdallah sai ya cika burin dake ransa kema ai kin san halinsa, gwara ma ki saka ma ranki salama mu bi sa da addu'a kawai" Momy ta kalleta tace "Wato kin san inda yake kenan?" Meemah tace "Ke dai kawai ki bi sa da addu'a Allah ya basa nasaran abinda ya saka a gaba Momy, amma shegiyar yarinyar nan ai kamar ta shigo gidan nan ne babu me hana hakan, don baza mu yi biyu babu ba" Momy ta tabe baki tace "Har ga Allah ni so nayi kawai ya hakura da er matsiyatan nan Meemah, kada tsautsayi ma yasa a hada iri da ita mu shiga uku, hada iri da talaka ai ci baya ne Meemah, don ni har cikin raina naki jinin talaka wallahi balle in hada zuri'a da su" Meemah tace "To ai dama bama fatan a hada iri da ita Momy, personally bazan ma bar hakan ya faru ba trust me, kawai ta shigo gidan ta gane Allah daya ne, ke kuma ki fara masa fafutukar wani auren da wuri wuri" Momy dai tayi shiru, can ta tabe baki tace "Allah ya sa ya saurareni to" Meemah tace "Haba dai zai saurareki, da kaina zan masa magana, a samar masa yarinya dai dai class dinsa" Momy tace "To ai shikenan, yanxu tracing din matsiyaciyar yarinyar ya sa a masa kenan?" Meemah tace "Ko ma dai menene mu dai mu zuba ido mu bi sa da addu'a kawai Momy" Mikewa Momy tayi tace "Bari in je in lallaba babanku, na dade ban ga ransa ya baci irin haka ba, haba ai abun da bacin rai, wai ace talaka yayi nasara akan ka a kotu bayan kai ne me gaskiya ai abun da ciwo" Daga haka ta wuce sama, Meemah ta dau wayarta tayi dailing number da take samun Abdul da shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login