Showing 69001 words to 72000 words out of 241367 words

Chapter 24 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1548

sai yau a bakin Sophie, Safiyyah tace "Ga dai katon daki an baki, kiyi karatun exams dinki cikin kwanciyar hankali, nima in abun duniya ya isheni in taho nan in sameki kafin dare yayi in koma den dina, don ko da wasa bazan ce ki dawo gidanmu ba ni kaina ban tsira gun tsinanniyar matar Yaya Musty ba kuma yaki kwatar min en ci, da zai bar ni ba nima sai in dawo nan kusa dake ba tunda ba rasa abincin da za su bamu mu ci za su yi ba, wannan dakin ai ya ishemu rayuwar America, bari kiji Khaleesat dama Allah ya riga ya rubuta Abdul ne silan zuwan ki Amurka ki hadu da mutanen arzikin ki, babu me canza haka ko yaki ko ya so dole sai ya kawoki ya hadaki da mutanen arzikin ki tunda Allah ya rubuta haka, iya role dinsa kenan a rayuwarki, kuma Allah ne zai basa ladan hakan bamu ba, ba shikenan ba?" Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza mata kai tace "Ni bazan zauna gidan nan ba Sophie" Safiyyah na mata wani kallo tace "Ohk, Apartment din naki zaki koma ki kai ma Abdul din kanki kenan?" Khaleesat ta sauke idonta kasa muryarta na rawa tace "Bazan iya jarabawan ba Sophie, gwara kawai in koma gida, i want to go home, i want to go to my mother" Safiyyah zata yi magana aka yi knocking kofar dakin, Safiyyah ta amsa aka bude kofar Jay ya shigo, kallon Khaleesat yake yace "Kin sha maganin Housemate?" Ta gyada masa kai without looking at him, Safiyyah ta kallesa cike da damuwa tace "Ashe kuma iftila'in da ya faru kenan jiya Yaya Housemate? To Allah Ubangiji ya tsare na gaba, ku kuma Allah ya saka maku da alkhairi ya baku ladan hidimar da ku ke yi da kawata don bata da kowa a garin nan sai Allah sai ni da ku, kuma she is not longer safe in this state don Abdul can be cunning, azzalumi ne mugu, nasan har yanzu yana labe garin nan bai tafi ba, kuma ba imani ne da shi ba ina jin tsoron next move dinsa, Allah kadai yasan sau nawa ya koma apartment din nan yaga babu kowa ciki" Jay dai ya Wan yi murmushi yace "She will remain here har ta gama exams dinta in sha Allah" Khaleesat ta kallesa ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Bazan iya exam din ba, Nigeria nake son tafiya" Safiyyah ta mata wani kallo kamar zata ce in tana da kudin jirgi ta tafi sai dai kuma kawai tayi shiru tana hararanta, Jay ya kwantar da murya yace "Saboda me baza ki iya exam ba Khaleesat, stop saying that pls, in sha Allah zaki yi jarabawan ki lafiya, in kun gama sai ki koma Nigeria" Safiyyah tace "Atoh shi dai na gani, kan wani tantirin Wan iska take son lalata future dinta, duka duka fa shekarar karshe za mu shiga yanzu a makarantar" Khaleesat ta sauke idonta hawaye na sauka idonta don tasan baza su gane abinda take nufi ba, Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Try calming her down Safiyyah, and naga tun jiya bata wani ci abinci ba ban san ko tafi son abincin Nigeria ne ba, nasa cook din gidan yayi ordering ingredient din har an kawo, i don't know ko zaki girka mata a kitchen tunda kina nan" Safiyyah tace "To ba damuwa, let me cook for her" Yace "Alright" a tare suka bar dakin Khaleesat ta bi su da kallo hawaye na bin fuskarta. Tunda suka shigo kitchen din Safiyyah ke bin ko ina da kallo don the kitchen is so big and well equipped, irin modernize kitchen din nan, bayan Jay ya fita cook din gidan ya nuna mata ingredients din shinkafa da miya sannan shi ma ya fita, tuni ta hau girkin a kitchen din. Wajen karfe biyar Safiyyah na daki tare da Khaleesat hira kawai take mata kamar ba abinda ya faru, ita dai Khaleesat tayi shiru tana kallonta amma gaba daya hankalinta baya kan hiran, wayar Safiyyah ya fara ring ta jawo jakarta ta ciro wayar ganin Mustapha ke kiranta ta wani turo baki sannan tayi pick ta sa handsfree tace "Ina wuni yaya" Ko amsa gaisuwar bai yi ba yace "Waye ya zo ya daukeki a mota Safiyyah?" Safiyyah ta bude baki tace "Ohh haka matar taka tace maka? to ta manta a jirgi aka zo aka daukeni ba a mota ba, kuma munafurcinta zai kare mata wallahi" Tsawa ya daka mata yace "Ina maki magana kina min maganar banza? Are you okay?" Ta wani murguda baki tace "Toh ba ina hanya bane wai, haka kawai dai babu dalili bazan kama hanya in fito cikin sanyin nan ba yaya, ko ka manta jibi za mu fara exams ne?" Kashe wayarsa yayi, Safiyyah tace "Allah dai ya tsine ma Surayya albarka, kuma wallahi kafin mu gama exam mu bar kasar nan sai na mata abinda bazata taSa mantawa ba a rayuwarta, ko da wasa kuma bazan ma gaya masa abinda ya faru dake ba kar yayi burgan cewa ki dawo gidansa ya kara ma matarsa extra nama" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta mike ta dau jakarta da gyale tace "Sai na zo gobe in sha Allahu, saura kar ki karasa cinye abincin ki zauna kina asaran hawayenki akan Wan daba, ga lambata na sa maki a waya in da wani abu ko kuma kina bukatar komai kawai ki kirani" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat ta sauke idonta kasa, Downstairs Safiyyah ta hadu da AJ wanda shigowarsa gidan kenan tana Wan murmushi ta gaishesa ya tsaya ya amsa yana danna wayarsa yace "How are you doing" Tace "Alhmdlh ya karatu" Yace "Fine, ya naki" Tace "Muna ta fafatawa dai, to fa mun gode da hidima yaya, Allah ya saka da alkhairi da abinda ku ka ma kawata, Allah ya biya ku" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta jin wai tana masa godiya, ita dai ta ci gaba da godiyar ta ba kakkautawa, Yace "Ameen" Tace "Yaya Housemate din ya fita ne, ni zan koma gida ne yanxu" Sai ga Jay ya shigo parlon from outside, ganinta yace "Ohk zaki koma Safiyyah?" Tace "Eh wallahi yamma tayi amma in sha Allahu zan shigo gobe da safe" Yace "To Allah ya kai mu, mu je inyi dropping dinki" Tuni AJ yayi wucewarsa sama, Safiyyah ta bi bayan Jay suka fita daga parlon tana mamakin inda karen gidan yake bata gansa ba tun daxu, sai bayan da suka dau hanya tace "Yaya Housemate...." Dariya ta ba Jay bai jira me zata ce ba yace "I am Jawwad Safiyyah" Tace "To ni dai don Allah kayi dubara ka amshe wayar da ka ba Khaleesat kar taje ta kira yan gidansu su gigita ta, kaga bamu san ko Abdul din na kasar nan ba ko ya koma Nigeria, in ta kira suka gaya mata wani maganar da kyar ta iya abun arziki a jarabawan nan" Jay yayi shiru cause he reason with what Safiyyah is saying, can yace "Haka ne kuma, i will tell her not to speak to anyone for now, amma bazan iya amsan wayar ba naga kamar it's whiling away her time" Safiyyah tace "To in da kati a wayar don Allah ka kone sa, in da WhatsApp kayi uninstalling dinsa kaga ta haka babu wanda zata ma magana, the exams is just for a few weeks, kamar gobe ne za mu gama" Yace "Sure i will do so Safiyyah" A haka suka isa gidansu ta sauka daga motar ta masa godiya yace "Ki gaida mutanen gidan" Tace "To za su ji" Yayi reverse ya dau hanyar gida hoping Khaleesat bata riga ta ma kowa magana back in Nigeria ba. Washegari da safe Jay yayi booking appointment na ganin likita saboda daren ranan ma Khaleesat dai bata yi bacci ba, yasan dai ba lallai su samu ganin likitan a ranan ba, so he was just helping her to manage her self with the drugs available, da Safiyyah kuma ta zo sai taji ta nemi zazzabin ta rasa dama kadaici ne da damuwa suka mata yawa. Ranan monday da safe Jay yayi dropping din Khaleesat school for her first exam, and he stayed behind har zuwa sanda za su gama don su koma gida tare, kawai shi dai baya son barin ta ita kadai, Jay is trying his very best na ganin Khaleesat ta sake ranta domin tayi karatun jarabawanta da kyau kar ta samu matsala, ga kuma Safiyyah dake encouraging dinta a gefe ita ma, kuma hakan yayi tasiri sosai don ta Wan sake ranta tana karatun, AJ dai tun ranan da ya shigo ya ganta zaune a daki har bayan da suka yi Exams uku bata sake saka shi a ido ba, bata san ko yana gidan ba ma ko baya gidan, ita dai 24/7 tana daki, hatta abinci cook din gidan ne ke kai mata sama yayi knocking ta fito ta amsa, in ta gama still shi yake zuwa ya amshi tray din, bayan sati biyu da fara exam dinsu ranan suna da interval Safiyyah ta zo gidan da yamma, abinci ta kawo ma Khaleesat, Khaleesat taji dadi sosai ganin tuwo ne don dama tun jiya take sha'awan tuwon, Safiyyah tace "Kinga ba dadewa zan yi ba yanzu zan tafi kafin mutumin can ya fara kirana kamar Surayya ce ta bar gida" A hankali Khaleesat tace "Baza ki bari anjima kadan ba pls" Safiyyah tace "Wallahi yanzu Ya Mustapha zai fara kirana, bai ma san na fito ba, kuma nayi order din Lyft ma da zai maidani gashi nan ya kusa karasowa nan, tashi ki rakani kofar gida" Khaleesat ta girgiza kai tace "Kawai ki tafi za mu hadu schl tomorrow in sha Allah" Safiyyah tace "Wai ke baki gajiya da zama ke kadai a daki, don Allah ni dai tashi ki rakani kema ki Wan yi strolling kafafuwanki" a hankali Khaleesat tace "Baza ki gane ba Sophie, wallahi i am not comfortable staying in this house, na kagu mu gama jarabawan nan in koma Nigeria" Safiyyah tace "Ae ranan Housemate dinki ya gaya min wai kince masa zaki koma apartment dinki nace lallai baki da hankali, Allah ma yasa Abdul bai sake gidan ba" Tana dariya ta kare maganar, sai kuma ta kwantar da murya tace "Kiyi hakuri kawata, nan da sati kadan zaki ga mun gama exams din in sha Allah, ki kwantar da hankalinki pls, yanzu dai tashi ki rakani" a hankali Khaleesat ta sauko daga kan gadon ta dau gyalenta suka fita dakin tare da Safiyyah, suna saukowa downstairs suka tarar da AJ a parlor da Jay, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta don sai yau taga AJ for almost 2 weeks, ita ta zata ma baya gidan ne, Jay na kallon Safiyyah yace "Are you going soon Safiyyah?" Safiyyah tace "Eh wallahi Yaya Jawwad Lyft dina yana hanya ya kusa" Yace "Alright, ki gaida mutanen gidan" Tace "In sha Allah za su ji" Sallama tayi ma AJ ya amsa mata, sannan ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna tsaye waje suna jiran karasowar Lyft wata mota ta shiga gidan bayan matukin motar ya fito daga cikin motar ya bude gate, Safiyyah tayi kasa da murya bayan sun shiga ciki tace "Ke kinga wani Ride me suna ride Khaleesat? Su dai da masu kudi kawai suke harkar su a kasar nan, in kin bibiya abokansu ne 'ya yan masu kudi irinsu" Khaleesat dai bata ce komai ba, bayan kusan minti uku sai ga Lyft din Safiyyah ya iso, Safiyyah ta bude bayan motar ta shiga, Khaleesat ta daga mata hannu, Safiyyah na mata murmushi tace "Sai mun hadu a schl kawata, kiyi karatu da kyau fa" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata sannan ta koma cikin gidan, duk a dar dar take tafiya a babban compound din gidan, har yau ita dai ta kasa sakin jiki a gidan nan gani take kamar a kaya ma take she is so very uncomfortable, a haka ta isa parlon gidan ganin baki biyu dake parlon tare da su Jay wanda da alama abokansu ne Khaleesat ta sauke kai ta gaishesu, suka amsa da fara'a, ita dai ta nufi stairs, daya daga frnds din nasu taji yace "Bakuwa ku ka yi a gidan" AJ dake shan fruit salad yace "Eh, yarinyar wani abokinmu ne a Nigeria ta zo jarabawa" Jay ya saki baki yana kallon AJ da ke ta shan fruit salad dinsa ko ajikinsa, Ita kanta Khaleesat sai da ta Wan juya ta kallesa sannan ta wuce sama, abokin na gyara zama yace "Waow, amma da gani da wuri abokin nan naku yayi aure, ya huta abunsa gashi mu duk mun kasa har yanzu" AJ dai ya ci gaba da shan fruit salad dinsa yace "Ai kam ya huta, mu ma da munyi auren da wuri duk da mun haifi kamarta ai"



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H? [5/21, 6:02 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat na zaune da daddare tana duba course din da za su yi washegari a laptop dinta, sosai take kewan Ummanta tasan kilan tana ta mata magana ta WhatsApp taji shiru, she just pray everything is alright back home in Nigeria, duk in wannan tunanin ya fado mata sai taji ta kasa karatu, haka nan dai ta tsura ma laptop dinta ido, knocking din kofar dakin aka yi ta mike a hankali ta karasa gun kofar ta bude don tasan Jay ne, sau da yawa sai dai yayi mata knocking bai fiye shigowa dakin ba, daga nan bakin kofa yake tsayawa yayi mata duk maganar da zai mata, yana kallonta bayan ta bude kofar yace "Are you sure u are studying for ur next course Halysaah?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, ya Wan jingina da bangon wajen yace "Erm, sorry about what you overheard AJ saying few hours ago Halysaah, kinga dalilin da yasa nake barin masa gidan shi kadai ya karata kenan, he is a serious nuisance... Kiyi hakuri da abinda yace kin ji Housemate?" Khaleesat ta Wan yi murmushi tana wasa da gefen gyalenta kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Ai ni ban ma san tsoho bane sai yau" Jay couldn't help it but laugh out loud, Khaleesat ta daga idanuwanta tace "Allah kuwa ban san shi tsoho bane, don wanda ya isa haifata ai tsoho ne" akan kunne AJ da ya fito daga parlon dake sama, tsaye yayi yana kallonta, tana hada ido da shi ta kulle kofar dakin gbamm, AJ ya kalli Jay dake ta dariya, can ya juya fuuu ya bar wajen, Jay dai ya bi sa da kallo still laughing, har ransa yaji dadin abinda Khaleesat tace akan kunne Ajayn. Jay na dakinsa wajen karfe goma da rabi yana duba laptop dinsa AJ ya shigo dakin, sau daya ya kallesa ya ci gaba da abinda yake, AJ yace "That brat will not continue staying in this house anymore, ka samar mata wani alternative kawai in ba haka ba in kira gida in fada masu ka kawo mana yarinya tana rayuwa cikin gidan nan" Jay ya daga kai ya kallesa yace "Ni ai na zata har ka kira ka gaya masu, kuma tunda ba gidanka bane baka isa kace bazata zauna ta gama exams dinta ba" AJ yace "Ohk zaka sha mamaki" Daga haka ya fice daga dakin, Jay ya ja tsaki ya ci gaba da abinda yake. Washegari tare Jay ya dauko Khaleesat da Safiyyah ya kawo su nan gida bayan sun gama exams din ranan, bai shiga compound din ba ya tsaya a waje yace "I will be going out now, sai na dawo later" Khaleesat ta sauka daga motar tana kallonsa, a duk sanda baya gidan sai taji gidan duk babu dadi, duk da ko yana nan yawanci yana dakinsa sai in da wani abu ne yake zuwa kofar dakinta ya mata magana, but she prefer him to be at home always ko da baza su ga juna ba, duk sanda ya fita sai ta shiga kadaici wani lkcn har da damuwa, kuma in dai zai fita din sai ya gaya mata zai fita, yau kam she felt relieved tunda tare suka dawo gidan da Safiyyah, yana kallonta yace "Zan kiyi girkin yau tunda ga kawarki sai ta taya ki?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Ohk" Yace "Alright take care" ta gyada masa kai ya ja motarsa ya wuce, ita da Safiyyah suka shiga gidan, Safiyyah tace "Kai na dade banga mutumin me kirki irin bawan Allahn nan ba, he is just extra nice, ni dai Allah ya sa it's what i am thinking" Khaleesat ta kalleta, Safiyyah ta washe maki tana wani murmushi, Khaleesat taki tanka ta, Safiyyah tace "Kinga kamar jiya muka fara exams gashi saura mana course biyu mu gama, baki ga farin cikin da nake ba za mu koma gida" Suna shiga parlon gidan suka ga AJ a zaune da kare a gefensa, sosai gaban Khaleesat ya fadi don tun da ta zo gidan ita dai bata ga karen da idonta ba sai da taji haushinsa wani lkcn, karen ya mike tsaye yana kallonsu AJ ya masa umarnin ya koma ya zauna, tuni Khaleesat tayi wucewarta sama, Safiyyah ta tsaya ta gaida AJ da fara'arta, ya amsa yace "How was ur exam?" Tace "Alhamdulillah, sauran mu kwara biyu, kawai intervals din ne ke da tsayi" AJ yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Daga haka ta wuce sama, dakin da Khaleesat take ta shiga, ta rike haSa tana kallonta tace "Ni fa karfin halinki mamaki yake ban Khaleesat, ya kina gidan mutane zaki zo ki wani wucesa babu gaisuwa? Me yasa kike yin haka ne?" Khaleesat ta cire mayafinta without looking at her tace "Don baki ji abinda yayi min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login