Showing 99001 words to 102000 words out of 241367 words

Chapter 34 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1609

taimaka ma aka rasa wanda zai bi yaga inda ma aka kai sa, ashe daga kano Abuja aka nufa da shi, bayan dogon binkice aka gano trailern an yasar a wani gari an kuma juye duk kayan cikin trailern, dama me trailer daban, me kaya daban, adadin kayan cikin trailern kuma zai yi na miliyan dari, to ba kowa bane me kayan cikin trailern nan illa mahaifin Abdul, sam ba a yarda babu sa hannun Mahaifin Khaleesat a juye kayan cikin trailern ba, dama kuma yan unguwa na jin haushin ya samu lodi me yawa haka ya tafi kai kayan shi kadai ko yaron mota bai dauka ba, kuma ko wani dreba an san sa da yaron mota daya ko biyu, nan aka yi ta zuga baban Abdul akan kar ya yarda wai dama planning Baban Khaleesat yayi don ya taSa yi ma wani mutum haka da dadewa yace barayi sun kwace kaya a hanya sai yafewa mutumin yayi, kuma wai don yaga Alhaji Musa wato mahaifin Abdul me kudi ne sosai shi yasa zai cucesa yace an sace kaya tunda yanxu ta kare masa bai da komai, kuma wallahi sharri ne ba haka Baban Khaleesat yake ba, bai cin kayan wani baya taSa abu in ba nasa bane, beside bai taSa sanin Baban Abdul ke da kayan ba sai da iftila'in ya faru sannan yaga me kayan, shi dai kawai ance masa ga Lodi zai kai lagos ya kuma amince tunda sana'ar sa kenan kuma kullum fatan samun Lodi yake, ko da babu zugin yan anguwa baban Abdul bai yi kama da mutumin da zai iya yafe kudinsa ba don kana ganinsa kasan bashi da mutunci bashi da kirki, sai da Mahaifin Khaleesat yayi wata uku bamu sa shi a idonmu ba kafin aka dawo da shi kano duk ya rame yayi baki ya dawo kamar ba shi ba, da kyar aka bari muka gansa a fursin da aka ajiyesa na nan kano, ranan duk bamu yi bacci ba bayan mun dawo gida, yayata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa don tun dauke mahaifin Khaleesat dama ta fara alalan siyarwa don mu rufa ma kanmu asiri saboda Wan jarin da nake da shi nima duk ya karye bani da komai, kafin ma a dawo da mahaifin Khaleesat kano sau uku muna zuwa gidan Alhaji Musa a Nassarawa GRA domin mu basa hakuri ko zai dubi halin da muke ciki ya taimaka a sake mana Baban Khaleesat amma duk aka mana koran kare, na farko masu gadi ne suka kore mu, na biyu Matarsa ranan ta rako ba?inta ta gan mu tayi mana cin mutunci ni da yayata da Baaba Gaje ta sa aka kore mu, na uku kuma Wan cikinsa Abdul wanda dama shi kadai ne namiji a 'ya yansa, ana haka aka shiga kotu ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka kawo Malam Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan, to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai na ganesa da na gansa a kotun don ranan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara tunda Malam Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?haka aka dage shari'ar zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa, Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotun tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama'an wajen kallonta suke, Alhaji Musa babban mutum ne kuma me kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani Wan jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke ?ara ce Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda bakin jama'a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abinda za ayi akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar kotu ranan rai babu dadi muka koma gida, bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake 'ya yan su maza kanana suna fita almajiranci suna ciyar da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna sana'a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shigo gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari, Baban Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa don shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat"
[5/30, 7:48 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka, gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah, Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace "Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta Wan yi murmushi ta koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace "Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau" Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar Inteesar taji a hankali tace "You are Beautiful Khaleesat" Khaleesat ta Wan kalleta sai kuma ta mayar mata da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace "Sosai fa" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "And you too Inteesar" Inteesar tayi dariya tace "A'a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba" Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace "Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa" Inteesar tace "Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a lagos ne in kin je?" Khaleesat tace "Zan Wan yi kwana biyu a can in sha Allah" Inteesar tace "Akwai sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will meet with you there" Murmushi Khaleesat tayi tace "Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya" Inteesar ta tashi ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado tace "You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later" Khaleesat tace "Alright, thank you so much" Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo dakin, Inteesar ta wara ido tace "Waow is all that ur hair Khaleesat?" Khaleesat dai ta mata murmushin karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace "Bari in baki Hair net" Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace "Nagode sosai" Washegari karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau, Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar's care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge. Karfe sha biyu saura suka sauka garin Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Ina wayar da na baki?" Jakar hannunta ta nuna masa tace "Yana ciki, na sa silent ne" Driver seat ya bude ya shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba, ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata ?aso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta, bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat, yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace "Ya ake ciki?" Daga daya bangaren mutumin yace "Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja yanxu haka" AJ yayi shiru kafin yace "Ohk, i will get back to you nagode" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi ?asa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace "Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login