Showing 105001 words to 108000 words out of 241367 words

Chapter 36 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1598

huta, kawai ranan juma'an nan da ta wuce sai ga kiran yayata wai an daura auren Khaleesat da Abdul, nace mata ban gane ba, Khaleesat din ta dawo ne? Sannan dama ana daura aure haka ba shiri? Nan take gaya min ai mahaifin Abdul din ne ya kira Baban Khaleesat da yamma likis yace ga bukatarsu gobe juma'a, babu bata lokaci kuma aka daura auren kamar yanda suka bukata washegarin, nace mata to shikenan Allah sa hakan shine mafi alkhairi, zuwa satin da za a shiga zan shigo kanon tunda tace Khaleesat din ma na Amurka bata dawo ba, ban kuma san komai dake faruwa ba sai ranan Lahadi da kirani, mun yi waya da kai babu dadewa sai ga yayata ma ta kirani tana kuka" Ajay ya sauke idonsa kasa, Calmly yace "Amma dai baki ce mata tana nan ba har yanxu ko?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai tunda muka yi waya kace kar in nuna ma kowa nasan inda take wallahi ban nuna ma yayata nasan komai ba, ita kanta har yanxu bata san inda Khaleesat take ba, Nasan Baaba Gaje bazata gaya mata ba ita ma" Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan, yanxun ma kar ki nuna tana wajenki, in sha Allah za mu ga yanda za ayi, in ma kudin baban nasa da abinda ya kashe mata na makaranta za a mayar masu wannan ba matsala bane in sha Allah" Aunty Farida ta gwalo ido jin abinda yace, ko dai bai ji amount din da ta kira bane da kyau, a hankali tace "Kudaden ne da yawa ai Junaid, miliyan dari fa banda abinda zai ce ya kashe mata na makaranta da bamu sani ba" Ajay yace "Bazai dai ce ya kashe mata sama da miliyan dari a makarantar ba, mu ma duk makarantar muke ai, in ma yace haka miliyan dari biyu ba abu bane da muke fatan zai gagara a mayar masu, so kawai kar ki ce ma kowa tana wajenki, we will see how things will go in sha Allah" Ita dai Aunty Farida tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, dama tun da ya sakko daga mota jiya taga kalansa take ta kallonsa tana mamakin inda Khaleesat ta samo shi, hatta wanda ya kira Wan uwansa bata ga yayi kalar tsiya ba shima, Shi dai Jay yayi shiru bai ce komai ba idonsa akan buhun shinkafa biyu da babban jarkan man gyada da carton din taliya dake parlon Aunty Farida, kana gani kasan food vendor ce, Ajay ya mike yana kallon Jay alamar ya tashi su tafi, Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Aunty Farida a hankali yace "Bacci take ne?" Ajay ya wani kallesa sai kuma yayi ficewarsa daga parlon, Aunty Farida ta mike tace "Bari in duba ta" Dakinta ta nufa Jay ya bi ta da kallo, after few seconds sai ga ta ta fito tana kallonsa tace "Ehh bacci take" Yace "Ohk, amma Drip din na raguwa kuwa?" Aunty Farida tace "Eh yana sauka" Mikewa yayi yace "Toh shikenan, sai anjima Aunty, kilan zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Aunty Farida ta Wan yi murmushi tace "Toh Allah ya kai mu Jawwad, mun gode sosai" Murmushin ya mayar mata ya nufi kofa, har ya fita ya sake juyowa yace "Amma Aunty ki Wan dinga duba drip din idan ya kare sai kiyi ma makociyar taki magana ta cire" Aunty Farida tace "Ina sha Allah, mun gode Jawwad" Daga haka ya fita daga parlon ya nufi kofar gida, cikin mota ya tadda Junaid har ya tada mota, ya karasa ya bude front seat ya shiga ya zauna ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido ya bude, saukansa kenan daga America ko hutawa bai yi ba balle ya ci abinci, yayi wanka kawai suka taho gidan Aunty Farida da Ajay, har suka isa gidan Cousin sister din parent dinsu dake Banana Island babu wanda yace komai a cikin motar, it's almost 7pm tsabar traffic din Lagos da ya rike su a hanya, bayan Ajay yayi parking Jay ya sauka daga motar ya nufi entrance din shiga gidan Ajay na biye da shi, a parlor suka tarar da Hajiya Fatima warce suke kira da Ummi, ta amsa gaisuwar da suka mata ta bi su da kallo, Ajay dai ya nufi sama, Tana kallon Jay tace "Baka ci abincin da aka ajiye maka ba Jawwad, ina ma ku ka je haka sai yanxu ku ke dawowa?" Jay ya shafa kansa a hankali yace "Wajen wani abokinmu" Daga haka shi ma ya wuce sama, ta bi sa da kallo. Wajen karfe tara na dare Ajay ya gama saka pajamas dinsa, Jay ya ajiye mug din tea dake hannunsa yana kallonsa Calmly yace "So now what is ur suggestion Ajay, gaba daya kai na ya kulle akan issue din nan, that guy have evil in mind shi yasa ya saka aka daura auren tun bata dawo ba, he have?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? a different plan, abinda kayi masa a USA na ransa har yanzu.... He married her immediately just to deal with her, I don't think he still loves her, he married her to take revenge" Ajay yace "Dama ai ba saboda Allah ya sa aka daura auren ba, akwai abinda yake nufi da hakan, ashe ma karamin Wan iska ne shi ban sani ba tun da bai yarda da kansa ba, da ya yarda da kansa bazai dinga kashe waya ba" Jay yace "Kamar ya?" Ajay yace "Na karbi numbersa na sa a duba min location dinsa, his location was showing Abuja on Sunday, tun sunday din har zuwa yau bai sake kunna wayarsa ba, kuma baya location din da aka gansa bayan na sa an je can" Jay ya bude baki yana kallonsa, can yace "Ban gane ka sa an je can ba, what are you trying to do? Plss ni bana son wannan dabancin naka Ajay, ni na zata fa ka shiryu, is that why u were busy shouting ku hadu a Nigeria on that very day? No pls ka girmi haka yanxu Prince, why spare ur precious time for a tout like him, don ni wallahi kallon tout nake ma gayen, sannan kar ka manta barrister ne shi kamar yanda kanwar mamarta ta gaya mana, definitely yasan plan dinka a kansa da yasa ka dage ku hadu a Naija, kaga bazai bar wayarsa a kunne ba kuwa" Ajay yace "Ai sai dai bai kunna wayarsa ba amma wallahi duk sai ya janye batancin da yayi min a parlon nan ranan, ya zata ana zagina a tafi scot free? I will so deal with him" Jay ya tabe baki yace "Yanxu dai that aside, meye abun yi" a takaice Ajay yace "Abun yi kawai a makasa a kotu ya fadi duk abinda ya kashe a biyasa ya saketa taje tayi rayuwarta, cause in har ta zauna zaman aure da mutumin nan zai iya kasheta har lahira, don prisoner zai mayar da ita kawai" Jay yayi shiru at first, can yace "But Ajay bamu san ko anyi a rubuce kan cewar an basa aurenta a madadin kudin da mahaifinta zai biya mahaifin Abdul din ba, sannan gayen nan Barrister ne, kana ganin zai bari ayi wannan yarjejeniyar babu sa hannu or anything of such ta bangaren shari'a?" Ajay yace "Su na ma iyayenta kallon talakawa marasu galihu da basu da wani say shine za su tsaya wani yarjejeniya? Ai masu arziki ke yarjejeniya, bayan sun san har a tashi duniya iyayen nata ba samun hanyar biyan miliyoyin kudin nan za su yi ba? Ai hankalinsu da tunani ma bazai je kan wata yarjejeniya ba cause they just assume sun samu yarinyar sun gama kuma ba wani abu da zai gifta ya hana hakan, so now we are taking this case to court, da bakinta zata ce ma alkali bata auren a kotu, iyaka ace ta biyasa abinda ya kashe mata na karatu sannan tayi masa wani auren ba shikenan ba" Jay yayi murmushi yace "Case din babanta da shi mahaifin Abdul din fa?" Ajay yace "We will reach der also" Jay yace "I just hope the agreement isn't in written form, but before mu je kotu nawa ne a account din ka Ajay?" Dariyar da Ajay bai yi niyya ba yayi yana shafa kansa, can ya kallesa yace "Why are you asking me that silly question Jay?" Jay yayi murmushi yace "Let me know first cause the money in my bank account isn't more than that amount" Ajay yace "200M?" Jay yace "Ban sani ba" Dariya sosai Ajay yayi yace "Na raina capacity dinka Bruh, meye kuma 200M a account dinka? Na zata account dinka ya doshi 1 Billion yanxu, Ohhh i remember baka wasa da investing fa, sannan kai Momy's boy ne har account din Momy ajiye kudi kake, Allah sa 200M din ma baya account dinta" Jay yaki tanka sa, Ajay yace "Kasan me, yanxu 600M or more ya kamata ace mun ajiye aside for this case cause I don't trust that stupid guy zai iya tripling kudin a kotu, i will get some more money from dad, Billah i am doing all this for the sake of humanity not because of that little brat, in don ta ita ne bazan yi ba, infact in don ta ita ne ba ruwana a case din ma" Jay dai danna wayarsa kawai yake bai ce komai ba don hankalinsa gaba daya yayi kan drip din da aka sa ma Khaleesat, yasan zuwa yanxu dai ya ci ya kare. Abdul na zaune gidan wani cin abinci tare da abokansa biyu da ke sauraronsa, Abdul yayi sipping energy drink din gabansa ya ajiye ya ci gaba da magana yace "I am still trying to gather more informations about the guy, kuma duk inda take yanxu da taimakon guy din taje can don bata da kowa a cikin garin kano or anywhere da zata je sai wajen sa, all of a sudden fa kawai naga yarinya ta canza attitude tana min wani sabon kalan raini, at first na zata naughty frnd din nan nata Safiyyah ce ke zugata duk da ita ma sai nayi maganinta don nasan da hadin bakinta a abubuwan nan da ke faruwa, i will fish her out too, ashe wai er ficiciyar yarinyar nan maza take kulawa a kasar suke bata liver take min raini, Billah sai na kauda gayen nan a doron kasa this is a promise i am making, sai dai uwarsa ta haifi wani, zai san gonata ya shiga sannan zai san bai daki banza ba, ba a dukana a ci gaba da rayuwa lafiya, he said we should meet in Nigeria ko? nasan yanxu shi ma yana bibiyan inda zai sameni, i don't want to be taken unaware shi yasa nake kashe wayata don nasan definitely zata basa lambata, idan na gama shirya masa tuggu zan bude wayar yayi tracking dina ya zo ya sameni inda nake, wallahil Azeem sai na kawar da shi kuma babu abinda zai faru, ita kuma duk inda take zata shigo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, sai dai in ban cika Abdallah Musa ba" Abokinsa Aminu yace "Toh kai baka ga fuskar guy din bane?" Abdul yayi wani murmushi yace "Ai ni yanxu ban damu da naga fuskarsa ko ban gani ba, burina in ga na aika sa barzahu, kun yankar mana ticket din da nace?" Aminu yace "But ta yaya zaka samu informations din wanda baka taba sani ba, baka da lambarsa ba, baka san komai kansa ba, baka san wanene shi ba, baka ma san inda yake a Nigeria ba ko kuma wanda ya san sa, How will that be possible Abdul?" Abdul yayi wani irin murmushi yana bubbuga kafarsa da kasa a hankali, sai kuma ya karyar da kai yace "Na zata you will be among people that will never underate my capacity and intelligence Aminu, ai ina da lambar wayarta ko? Kuma ni nayi mata registering sim card din, toh abokina dake aiki a kamfanin network din sim da take amfani na ba phone number dinta ya duba min duk calls dinta ya kuma turo min numbers din da take waya da su frequently a America, he just sent them to me few minutes ago" Yana kai wa nan ya mike yana wani murmushi yace "Let go" Dariya kawai abokan nasa ke yi, suka tashi duk suka fita daga eatry din.
[6/2, 1:05 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Wajen karfe goma na dare Khaleesat na zaune dakin Aunty Farida da fruits a gabanta ta kasa sha, ita dai Aunty Farida na zaune opposite dinta ta zuba mata ido don har ta gaji da ce mata ta sha fruit din, ga abinci ma taki ci, tun tuni makociyar Aunty Farida ta shigo ta cire mata drip din bayan ya kare, ta daga kai ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty su Housemate dina sun tafi ne?" Aunty Farida tace "Waye kuma Housemate din ki?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, Aunty Farida tace "Junaid din ne Housemate din ki?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Wanda suka zo tare" Aunty Farida tace "Ohk, tun daxu ai suka tafi kina bacci, ta yaya ya zama Housemate din ki?" Khaleesat na juya fruits din gabanta a hankali da fork tace "Gida daya muke da shi a America" Aunty Farida ta Wan buda ido da confusion tace "Gida daya kuma? Kamar yaya? Amma ba kin ce makociyarki mace bace?" Khaleesat tace "Eh daga baya ta tashi daga apartment din, shi ne shi ya dawo gidan" Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi kuma Junaid din a ina kika san shi?" Khaleesat tace "Cousin brothers ne ai, dalilin Housemate dina na san shi" Aunty Farida ta kafe ta da ido, Khaleesat ta sauke kanta bata boye ma Aunty Farida duk abun da ya faru tun daga dawowar Housemate apartment dinta, yanda ya biya mata kudin jirgi to and fro ta dawo Nigeria ta duba Umma, irin zaman da suka yi da shi da kirkin da yayi ta mata, har zuwa lkcn da Abdul ya zo kasar a karo na biyu da kuma abinda ya faru tsakaninsa da Ajay, da yanda suka maidata gidansu har ta gama Exams, babu abinda ta boye ma Aunty Farida hawaye na zuba idonta, Aunty Farida ta kasa cewa komai sai kallonta kawai take jiki a sanyaye, after almost a minute Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tayi tagumi don she is just speechless bata san ma me zata ce ba, amma ta fahimci wani abu a labarin da Khaleesat ta bata..... Washegari wajen karfe goma na safe Jay ya bude kofar dakin Ajay ya samesa tsaye yana buttoning din shirt dinsa ya gama shiryawa, Jay ya jingina da jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonsa calmly yace "You know what Ajay?" Ajay ya dau face cap dinsa ya saka, yana kokarin daura agogonsa a hannu yace "All ears" Jay yace "I think we shouldn't say anything to Abba akan kudin da muka yi magana jiya" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "Why?" Jay yace "Kasan zai yi querying dinmu about what we are using that huge amount of money for, i think gwara in amshi kudi wajen Mamina kawai, cause you know i can't lie to Abba idan yayi insisting akan abinda za mu yi da kudi haka, zan iya gaya masa me za muyi da kudin if he insist" Ajay ya masa wani kallo daga sama har kasa yace "Sannu saint, ita Mamin ce bazata yi querying dinka akan me zaka yi da huge sum of money din ba?" Jay yace "Yeah, but i know how to convince her" Ajay yayi wani murmushi yace "Mamin ce zaka yi convincing, i see" Bai jira amsar da Jay zai basa ba ya dau makullin mota da wayar sa ya bi gefensa ya fice daga dakin ya sauka downstairs, Jay ya bi sa da kallo, after a while ya jawo kofar dakin ya kulle sannan ya bi bayansa, Ummi dake zaune parlor ta bi su da kallo ganin alamar fita za su yi tace "Ina kuma za ku da safen nan?" Without looking at her a takaice Ajay yace "Bar beach" Ummi tace "Dama ana zuwa Bar beach da safe?" Ajay yace "Eh" daga haka ya fice daga parlon, Ummi ta kalli Jay tace "Wai Beach za ku?" Jay ya Wan sosa kansa yace "A'a sai da yamma, yanxu dai kawai yawo za mu yi a gari" Ummi ta tabe baki tace "Ai shikenan, traffic ma kadai ya isheku, Mami ma suna hanya yau in sha Allah, sun ma kusa sauka" Jay ya sauke kansa yace "Eh haka tace min" Ummi tace "To sai kun dawo" Jay yace "Allah ya sa" Daga haka ya fita daga parlon, ya tarar da Ajay a mota yana jiransa, yana shiga motar Ajay yace "Ko ina ruwanta da inda za mu, ni bana son sa ido a rayuwata, shi yasa bana sauka gidanta a garin nan, i hate what i don't like" Jay yace "Ikon Allah, what's wrong with her asking us where we are going?" Ajay yace "That's very wrong, we are not kids da zata dinga tambayar mu inda za mu idan za mu fita, ko Abba baya controlling din mu yanda matar nan take yi, i don't think i am going back to that house zan je in kama hotel kawai" Jay ya girgiza kai yace "Kai fa matsala ne da kai kamar gidan haya, ni ban ga wani abu ba don ta tambayemu inda za mu da safe, it's normal ai" Ajay ya kallesa yace "To ni ba kai bane da ake controlling yanda aka ga dama a family, kai da kaga za ka iya sai ayi ta controlling dinka Jawwad" Jay bai sake ce masa komai ba, Ajay ya ja motar suka fice daga gidan. Da sallama Safiyyah ta daga buhun dake makale kofar shiga compound din gidansu Khaleesat, Mama Shatu da Mama Zubaida ne tsakar gida ko wacce na zaune bakin murhunta ana girka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login