Showing 219001 words to 222000 words out of 241367 words

Chapter 74 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1621

window din parlon yana son tafiya amma bai tafi ba, kuma har lokacin ruwa ake, and before he know it 15 minutes into her sleep ta farka cikin firgici, Khaleesat ta dade bata ji irin wannan tsoron dake zuciyarta ba, yanxu idan ya ga Abdul a gidan nan me zata ce? Ko dai kawai ta gaya masa gaskiya, to amma idan ta gaya masa kuma ya kamasa da duka har ya aiwatar da abinda ta gani a mafarki ba, Da tunane tunanen nan wani baccin ya sake awon gaba da ita bata sani ba, cikin baccin taji an rufa mata duvet, ta bude ido da sauri sai kuma ta mike zaune tana kallon duvet din da ya rufa mata don parlon yayi sanyi sosai, tana zaro ido bata san sanda tace "A ina ka dauko?" Yace "Ban sani ba" Tsoronta kar yaje ya shiga dakin da Abdul yake, ta koma ta kwanta a hankali tayi lamo, Ajay ya tafi ya ci gaba da tsayuwarsa a jikin window din parlon yana duba wayarsa ganin Jay ke kiransa ya maida wayar aljihu. Karfe daya da rabi Khaleesat ta kara farkawa a bacci, ta cire duvet din jikinta tana kallon Ajay dake zaune kan one sitter ya jingina kansa da kujeran idonsa a lumshe, amma tana mikewa zaune ya bude ido, ta fara sosa kai taki barin su hada ido tace "Fitsari zan je in yi" Bai ce mata komai ba, ta mike tsaye tana tafiya a hankali ta wuce sama, waige waige ta dinga yi kamar munafuka a corridor din dakunan sannan ta bude one of the 3 rooms dake sama, taga Abdul baya ciki, ta dai san baya dakinta tunda har Ajay ya shiga dakin ya dauko mata duvet, dakin dake kallon nata ta bude a hankali, ta gansa kwance kan carpet at the far end of the room yana bacci, ta shiga uku ta lalace, how did she find her self in to this mess, duk don saboda tausayi, a hankali ta jawo kofar ta kulle har da makulli sannan ta cire makullin ta tafi dakint??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a da shi ta ajiye a handbag dinta, bayan kusan minti 7 Khaleesat ta sauko downstairs rike da darduma da Hijab don alwala tayi bayan ta tuna bata yi sallan isha'i ba, shi dai Ajay bin ta da kallo yake, ta shimfida darduman ta sa Hijab din sannan ta tada sallan, bayan ta idar tayi sallan Nafila, ta dade zaune kan darduma, lkci lkci take satan kallon Ajay don idonsa biyu har sannan, ganin ta fara jin bacci ta mike a hankali ta koma kan kujera ta kwanta ta rufa da duvet, a nan ne bacci ya dauketa wanda bata sake farkawa ba sai safe, don har gari ya fara wayewa, ta mike zaune da sauri don yaushe rabonta da makara haka, kalle kallen parlon ta dinga yi ganin Ajay baya parlon ta mike tsaye ta nufi window tana leka garage taga babu motarsa, ta fi minti biyu tsaye jikin window din sai kuma ta juya ta wuce sama bayan ta dau dardumanta da hijab, tana idar da sallah ta fito da makullin dakin da Abdul yake ta bude kofar dakin tana tsaye daga bakin kofa ta hade rai tana kallon cikin daki, yana zaune kan carpet, alamar tun bayan da yayi sallah yake zaune a haka, hade rai tayi tace "Ka zo ka fita don Allah" Mikewa yayi ya nufo kofar ta matsa ta basa hanya fuskarta daure, yana kallonta yace "Good morning Khaleesat" ?in amsawa tayi waiting for him to go downstairs, cikin sanyin murya yace "Nagode da rufa min asiri da kika yi" Yana fadin haka ya nufi downstairs, ita dai ta bi sa da kallo, sai kuma ta bi bayansa to be sure he is leaving, ko da ta sauka downstairs taga har ya bude kofar apartment din, tana tsaye tana kallonsa har ya fita ya kullo mata kofar, ta karasa ta saka ma kofar makulli, ta jingina da kofar letting out a sigh of relief.....



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H?


We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....
All at affordable prices

Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....



Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM



Wajen karfe tara Khaleesat ta sauko downstairs bayan tayi shirin tafiya makaranta, zaunawa tayi kan kujera ta jinginar da kanta jikin kujeran tana jin kanta na mata ciwo, banda suna da test da baza ma taje schl din ba don har a lkcn she was still stunned at what happen yesterday, gaba daya a dar dar take cikin gidan, ko appetite din yin breakfast bata da shi, ganin it's almost 10am ta ciro wayarta a jaka tayi ordering Uber da zai kai ta school din, bayan ya iso ta mike ta dau jakarta ta nufi kofa, tana isa school taga Safiyyah bata iso ba, kiranta ta fara yi a waya amma baya shiga, dab da za su fara test din sai ga Safiyyah, bayan sun fito Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Kawai daga na Wan sake ma yaro fuska uwarsa bata da lafiya shine ya kai ni ya baro Khaleesat" Khaleesat ta kalleta amma bata ce komai ba, Safiyyah ta gyara zama tace "Gaba daya ya lalata min jakunkuna da jambakin uwarsa, duk ya goggoga, daga in shiga wanka in fito, ai ko ni dai na dokesa in ma uban ya kullace ni shi ya jiyo, jakunkuna na masu shegun tsada sai kace uwarsa ce ta siya min" Khaleesat dai ta Wan yi murmushi kawai without saying anything, Safiyyah na kallonta da kyau tace "Me kuma ya faru na gan ki haka?" Khaleesat ta bude jakarta ta ciro zoben da Housemate ya bata ta mika mata, Safiyyah ta amshi box din ta bude, zaro ido tayi with awe tace "Oh my God, who got u this Khaleesat? diamond ne fa, don Allah wa ya baki, kamfanin Forevermark fa...." Ganin Khaleesat taki bata amsa Safiyyah ta hade rai tace "Don Allah ki min magana, where did u get this from?" A hankali Khaleesat tace "My Housemate gave me" Mikewa Safiyyah tayi baki bude tana zaro ido tace "Don't tell me he proposed to you?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ko ba propose ba, he just gave me as a gift Sophie" Safiyyah tayi wani ?ara tace "Omg, wallahi proposing yayi maki amma saboda sense is far from you kinga ai baki gane ba, ya salam luxury brand ne fa Forevermark, to da ya baki me kika ce masa? Kuma ta yaya ya baki, kuna zaune ne ko kuna tsaye sanda ya baki?" Safiyyah ta koma ta zauna kusa da Khaleesat looking so excited tace "Don Allah how did u react da ya baki?" Khaleesat tace "Bai ma jira nayi masa godiya ba kawai ya wuce" Safiyyah tace "A apartment din ki ya baki?" Khaleesat tace "A'a, he took me out for dinner yesternight, bayan da muka dawo shi ne ya bani a mota" Safiyyah ta kyalkyale da wani shegen dariya tace "Yanxu fa sai kice har yanzu baki gane Housemate dinki is in love with you ba ko? Duk sai kice he is just being kind ko?" Khaleesat ta wani kalleta, Safiyyah na dariya tace "Ae ba abun mamaki bane kice baki gane yana sonki ba har yanxu, amma wallahi Housemate dinki na bala'i son ki kawata, don wannan care din is extra ordinary, ko kanwarsa da suka fito ciki daya bazai dinga yi mata irin wannan hidimar da yake maki ba, kai budurwar da saurayinta zai mata haka ma ba karamin musulmin sonta yake ba, yan mata nawa ne yanxu ko Naira biyar baya hadasu da samarinsu kuma a haka wai aurensu za ayi, ke dai wallahi you are very lucky om earth, Allah ya kashe ya baki kawai, ni kuma zan baki shawara kar kiyi misusing privilege din nan, cause it's a privilege to you wallahi, bai duba wai kin taSa aure ba kawai shi tsakani da Allah yake son ki a zuciyarsa, come to think of who he is, daga gidan sarauta fa ya fito, in zaki ajiye kunya ki nuna masa kema kina sonsa to zai dai fi maki, you are not a kid Khaleesat, kinsan sonki Jawwad yake, so me tsanani kuwa" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Kinsan me Sophie?" Safiyyah na kallonta tana washe baki tace "Ina jin ki" After some seconds Khaleesat tace "Abdul came to my apartment yesterday night" Mikewa Safiyyah tayi ba tare da tasan ta yi hakan ba a tsorace, tana kallon Khaleesat with shock all over her face tace "Waye kuma Abdul? Did you have another frnd that is Abdul by name da ban sani ba?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta, cikin sanyin murya tace "Abdul dai guda da kika sani" Safiyyah tace "Na shiga uku na lalace, Abdul tsohon mijin ki wai kike nufi?" Khaleesat ta kasa ce mata komai, Safiyyah ta koma ta zauna tana kallonta da wani expression tace "Ta yaya yasan apartment din ki Khaleesat? Kuma me yaje yi maki a apartment? Don Allah ki min bayani yanda zan gane, i am lost...." Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Wallahi ban san ta yaya yasan apartment dina ba Sophie, ni kaina i am still shock up till now, ko breakfast na kasa yi saboda tsoro, yanda kika san an jefo sa" Safiyyah ta maida jakarta gefe tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ji min shege Wan iska, to wai uban me yaje maki a apartment din, tell me what happen da yaje, ke kuma da yaje kofa kika bude masa ya shigo?" Khaleesat tace "Bayan Housemate dina yayi dropping dina a gida ya tafi ana ruwa, after like 10 mins sai aka danna bell, to na mance jakana a motar Housemate i was thinking shi ne ya dawo ya kawo min jakar, da na sauka downstairs sai na bude kofa kawai, ashe Abdul ne" Safiyyah da tayi mitsi mitsi da ido tana sauraron Khaleesat tace "Go on, ina jin ki, sai aka yi yaya?" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "I was very shock and afraid bayan na bude kofan ya shigo, shi ne na shiga kitchen da gudu dama wayata na hannuna nayi dialing number Ya Junaid, sai gashi ya biyoni kitchen din ya karbe wayar" Buda baki Safiyyah tayi tana kallonta da firgici a fuskarta, cikin sanyin murya Khaleesat ta gaya mata duk abubuwan da Abdul yace mata a kitchen din bayan da ya sameta a ciki, da kuma yanda Ajay ya zo gidan duk bata boye mata komai ba.... Safiyyah na girgiza kai tace "Amma kin bani mamaki Khaleesat, yanxu shi Abdul har wani abun tausayi ne shi da zaki boyesa a apartment dinki? Abdul fa???" A hankali Khaleesat tace "Ce min fa yayi in tuna alkhairansa gare ni Sophie, kuma he look afraid also baya son Ajay ya gansa, shi ne yace in rufa masa asiri" A fusace Safiyyah tace "Wani shegen alkhairin yayi maki da zaki tuna? Harrassing dinki da ya dinga yi ko kuma gorin da yake lafta maki da walakanta ki da yake yi? Nan nan ranan kika bani labarin zaman ukuban da kika yi a gidansa kafin ya sake ki, da yanda ya bar ki da kwalin indomie ko albasa babu balle tarugu, marukan da ya dinga maki da zagin cin mutunci ne alkhairin da zaki tuna game da shi? Mutumin da ya ci mutuncinki ya sake ki bayan ya samu abinda yake so a wajenki har shi ne abun tausayi Khaleesat? Yanxu kina nufin kika boye Abdul har washegari a apartment din ki kika bar Ajay da gadin ku? Ikon Allah, Gaskiya baki taSa bani tsoro irin yau ba Khaleesat, i fear who no fear you, me yake damun ki ne haka?" Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi tana kallon Safiyyah tace "Safiyyah kar ki manta this is America, we are not in Nigeria, Ya Junaid na lura temper dinsa a kusa yake, yana da zuciya sosai, what if yaje ya masa wani illa wajen dukansa don nasan definitely bazai kyalesa ba idan ya gansa a gidan, kina tunanin idan yayi masa wani abu za a kyalesa ne a kasar nan? dole doka zai yi aiki a kansa, kuma duk saboda ni sai haka ya faru Sophie??" Safiyyah ta wani kalleta tace "Sannu me hangen nesa, da duk baki san da hakan ba kika doka masa kira? Why did you call him at the first place idan ba don ya zo ya fitar maki da Abdul ba?" Hawaye ya cika idon Khaleesat tace "Ai a sannan ban san da wani Intention ya zo min gida ba, kinga if he just came to harm me wannan daban ne, amma he meant no harm he was even afraid, banda haka ai bazai rokeni kar in gaya masu ya zo gidan ba" Safiyyah tayi wani murmushi tace "Maa sha Allah, kinga shawara daya kawai Abdul ya koma Nigeria ya bada sabon sadaki a kara daura maku aure kije can ku karata, tunda yanxu kam ya tuba kuma har kin yarda da tubansa kina mugun tausayinsa a rai, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a masu yawa" Khaleesat ta hade rai tace "Come off it Safiyyah, ni nace maki i am ready to accept his repentance? Ko sake daura min aure aka yi da shi ba sai dai a kai gawata gidan ba, how will I forget what i went through so soon Safiyyah, wallahi kawai kalman alkhairi da ya furta ne da kuma irin sigar da naga ya zo min yasa na rufa masa asiri, ni ba butulu bace bazan ce Abdul bai min abubuwan Alkhairi ba a rayuwata, in ba don shi ba yaushe har ma zan zo kasar nan in hadu da su Housemate dina? I lacked nothing tun da Abdul ya kawo ni kasar nan karatu, don har nafi wasu da iyayen nasu ke daukar nauyinsu, kinga bazan ce Abdul bai min wani abun alkhairi ba, kuma bazan taSa iya biyansa abinda yayi min ba, ki fahimce ni plss Sophie, ba wai nace ya kamata in sake kulasa bane, don wallahi ko ganinsa bana son yi don hakan na fama min ciwon dake zuciyata..." Safiyyah ta tabe baki tace "Tun da kin rufa masa asiri kin ga yau ma nasan yana can bakin apartment din naki yana jiran ki, hauka ake zan rufa ma Abdul asiri idan ni ne a shoe din ki? Abdul fa? Ai ko duk alkhairan duniya yayi min wallahi bazan rufa masa asiri ba sai dai Allah ya yafe min kawai, Monster in form of human ne fa Abdul, gaskiya kin ci amanar Junaid, kin cuce sa, kuma da ya kuskura yasan abinda kike boyewa a gidan nasan ko ciki daya ku ka fito da shi bazai sake barin wata ala?a ta hada ku ba har abada, kuma bazai taSa yafe maki ba, in kina tsoron kar Ajay ya masa illa me ya hanaki kiran 911?" Khaleesat dai tayi shiru tana bin inda suke zaune da ido, Kawai ganinsa suka yi a gabansu, ta rike numfashi tsabar yanda tayi shock tana kallonsa babu ko kiftawa, Safiyyah da ita ma ta gwalo ido tana kallonsa da mugun mamaki ta mike tana huci tace "Kai bawan Allah lafiya muna zaune zaka tsaya mana a kai, ko dai batan hanya kayi ne?" Sau daya ya kalli Safiyyah sannan ya mika ma Khaleesat wayoyin dake hannunsa guda biyu yana kallonta, daya na Jay daya na Ajay, Khaleesat ta wani hade rai tace "Abdul kaga bana son muyi creating scene a nan, kindly stay away from me, are you even okay? Meye zaka dinga bibiyata?" Safiyyah ta figi jakarta tana kokarin ciro wayarta tace "Idan ban kira maka 911 ba Allah ya tsine min albarka...." Tana ciro wayar ya fixge daga hannunta yana kallonta da kyau yace "Wajen ki na zo da zaki kira min 911 Malama?" Safiyyah ta kundumo wani zagi tana kallon Khaleesat tace "Kin dai ga crook din da kika ji tausayi har kika boye a apartment din ki kar Ajay ya gansa ya jibgesa ko, kin taSa ganin inda shedan ya tuba dama? Shey u can see the useless monster you are pitying har da boyesa kar a dokesa?" Abdul na mata wani kallo yace "Hey watch your tongue, idan ba haka ba i will teach you a bitter lesson Billah, Ajay kika kirasa ko? To ya zo ya dokeni tunda ni statue ne, ina ga shi ko gidan dambe bai taSa zuwa ba, ki je ki tambayi wanene ni a Lagos..." Khaleesat ta maida box din zobenta cikin jaka sannan ta mike ta amshe wayar Safiyyah dake hannunsa, ta dau jakar Safiyyah da nata ta fara janta su bar wajen, banda zagi babu abinda Safiyyah ke kunduma ma Abdul idonta rufe tana cewa "Munafuki kawai algungumi, wato saboda ka san tana da tausayi shi ne ka dawo sumui sumui da kai kamar na Allah zaka kara yaudaranta ka cuceta, har kana cewa ta rufa maka asiri, to kuwa sai na tona asirin nan naka wallahi, shegen duka za ayi maka da zai sumar da kai, in ka farfado ka siya ticket ko koma gida kayi jinya, tsabar baka samu daman ci gaba da musguna ma kawata ba har da rama sai da kayi kamar me ciwon Aids, to wallahi in baka fita harkar Khaleesat ba sai nayi maka abinda har ka koma ga Allah bazaka manta ba, mugu azzalumi kawai" Gaba daya attention din mutane ya dawo kansu a wajen, Abdul yayi wani murmushi yace "Sai kinyi regretting duk kalaman nan naki wallahi, sai na sa an lalata maki rayuwa i promise you this...." Khaleesat dai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login