Showing 111001 words to 114000 words out of 241367 words

Chapter 38 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1552

Ya Jawwad, i now have rest of mind knowing my frnd is safe" Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar, Khaleesat ta ajiye plate din abincin hannunta don ta kasa ci, iya spoon uku kawai ta iya yi, tuni Aunty Farida har ta ajiye ma Jay abincin da ta zubo ta nemi waje ta zauna, sai da ta jira suka gama waya da Safiyyah sannan ta kallesa tace "Ina Junaid din ga abincin na zuba maku" Jay yace "Aunty bamu dade da cin abinci ba da gaske" Aunty Farida tace "Ai ko in baku ci ba bazan ji dadi ba, haka jiya ku ka bar min abincin ku ka ki ci, yanxu fa karfe biyu da rabi ake nema kuma breakfast kace kawai ku ka yi" Jay dai murmushi kawai yake, can yace "Toh zan ci Aunty" Tace "To ko kai fa, ina Junaid din kayi masa magana ya shigo ku ci" Jay na shafa kansa yace "Ai shi ya ci snacks a mota bazai ci abincin ba na sani, bai fiye cin abinci da rana ba" Aunty Farida tace "Ikon Allah to saboda me?" Jay yace "Haka yake, iya breakfast da Dinner kawai yake yi" Aunty Farida tace "Iko sai Allah" Jay na kallon abincin da Khaleesat ta rage ya mike ya dauko yace "Zan ci wannan kar mu bata abincin Aunty" Aunty Farida tace "Don Allah ka ajiye ka debi abinci ga plate nan Jawwad" Yace "Aunty wannan fa ya isheni ba iya cinyewa zan yi ba ma" Spoon din ya dauka ya fara cin abincin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, Aunty Farida tace "Ai shikenan" Karfe uku da yan mintuna Ajay da Jay suka bar gidan, Jay ne ke driving din idonsa akan titi yace "To ya ku ka yi da Lauyan?" Ajay yace "He said we should meet in kano" Jay ya Wan kallesa yace "Zuwa gobe kenan?" Ajay yace "Sure, tomorrow in the morning za mu tafi kano" Jay bai sake cewa komai ba har suka isa gida, yau dai traffic din da Wan sauki, bayan Jay yayi parking ya juya yana kallon Ajay yace "Please since gobe za mu tafi kano ka bar maganar hotel da kace zaka koma" Ajay yace "Ai matar ne ta fiye takura da sa ido" Jay yayi dariya bai dai ce masa komai ba suka sauka zuwa cikin gidan, Ummi na zaune parlon Hadeeyah na kwance kusa da ita da daura kanta a saman cinyar Ummin, ba tare da Ajay ya kalleta ba ya gaisheta a takaice zai wuce sama Hadeeyah ta gaishesa ya amsa yana haura stairs, Jay ya zauna parlon ya gaida Ummi ta amsa tace "Sai yanxu? Ko dai ba Bar beach din ku ka je ba?" Jay ya Wan buda ido yace "Mun fasa" Yana magana ne yana kallon Hadeeyah da ta hade rai tana danna wayarta kamar bata gansa ba, Ummi ta kalleta tace "Ke baki ga yayanki bane" Hadeeyah na ci gaba da danna wayarta tace "Oh, ok, Good evening" Jay yace "Ya hanya?" Tace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Mami tana sama" Jay ya mike yace "Ohk" Sama ya wuce, Hadeeyah ta bi sa da kallon gefen ido har ya fara hawa stairs, bayan ya tafi Ummi na kallon Hadeeyah tace "Fadan ku ka sake yi kenan?" Hadeeyah ta Wan yatsine fuska taki cewa komai tana danna wayarta, Ummi ta kyabe baki tace "Kun fi kusa dai" Jay na bude kofar dakin da yasan Maminsa na ciki ya sameta zaune tana waya, ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi mata side hug ya jinginar da kansa a shoulder dinta a hankali yace "Mami" Mami tayi ma warce suke wayar sallama ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa tace "Ina ka je tun safe Son? I was thinking zaka zo airport kayi picking din mu" Jay ya Wan kalleta yace "Karfe nawa ku ka iso Mami?" Tace "Karfe sha daya da rabi na safe" Jay yace "Mun fita ne da Ajay, Ummi bata gaya maki ba" Mami tace "Kaga da ubansa ne zai sauka Lagos duk abinda yake yi barin sa zai yi ya tafi ya taro sa, amma kai uwarka ta sauka Lagos ya ja ka kun tafi gantali" Jay bai ce mata komai ba, Mami na kallonsa tace "Duk karatun ne yasa ka fada haka? Are you okay?" Jay yace "Stress din tafiyar da nayi zuwa Nigeria ne" Mami tace "Nasan shi zai zugaka ku dawo Nigeria kar ka biyo min ta UK" Jay ya Wan hade rai yace "Ya fa riga ni dawowa Nigeria Mami, ni ba jiya na dawo ba, shi kuma ai tun last week yake Nigeria" Mami ta tabe baki bata ce komai ba, Jay ya mike ya nufi kofa yace "Zan je inyi wanka" Mami tace "Dama gobe ka shirya mu tafi Bauchi ban san gantalin da yake jan ka ku ke yi a Lagos ba, kai da ko ance ka sauka Lagos baka taba yarda sai gashi saboda Junaid na lagos kai ma ka zauna a lagos, to gobe za mu tafi Bauchi kuma Hadeeyah ma a can zata yi hutu" Jay ya juya ya kalleta yace "Mami ni ban gama abinda nake yi ba, kawai ku yi tafiyar ku" Bai jira me zata ce ba ya fice daga dakin. Wajen karfe biyar da rabi Jay da Ajay suka sauko downstairs, dakin dake kasa suka nufa don Mami na ciki tare da wata bakuwarta warce suka hadu da dadewa a Saudia suna zumunci sun zama kaman en uwa, jin Mami ta shigo Lagos sai matar ta taho gidan gaida Mami tunda ita ma a Lagos din take, Ajay ya zauna kan 1 sitter dake dakin ya gaida Mami sannan ya gaida frnd dinta, Jay ma ya zauna ya gaida kawar Maminsa, matar me suna Hajiya Batula ta amsa da fara'a tana kallonsu sai kuma ta kalli Mami tace "Wanne ne son din naki a ciki Hajiya?" Mami tayi pointing Jay tace "That is my son" Matar na kallon Jay tace "Maa sha Allah, ai kuwa ga kama na gani" Shi dai Ajay danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba, Jay ya mike yace "Mami za mu je Gym ne" Mami ta kallesa tace "Da yamman nan ga uban traffic din Lagos ne zaka je Gym?" Jay yace "Ai ba nisa Gym din" Hajiya Batula tace "Nan Area din ma ai da Gym ba sai sun je da nisa ba" Jay ya kalli Ajay yace "Mu je" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa Jay ya bi bayansa suka fice daga dakin, Hajiya Batula tace "Amma Wan uwansa ne wannan din ai ko, naga suna yanayi sosai" Mami tace "Eh Cousin dinsa ne" Hajiya Batula tayi kasa da murya tace "Ko dai shi ne Wan sarkin dai?" Mami ta tabe baki tace "Shi ne" Hajiya Batula tace "Ya sunansa?" Mami tace "Sunansu daya Ahmad amma Junaid ake kiransa" Hajiya Batula tace "Ikon Allah, shi kam Jawwad babu ruwansa..." Cike da takaici Mami tace "Ni babban bakin cikina yanda har yanxu Jawwad bai san ciwon kansa ba, hakan na ci min tuwo a kwarya wallahi, controlling dinsa kawai yake yana bin sa, ko a America din ma Junaid????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? din ne ke juyasa" Hajiya Batula tace "A'a gaskiya bai san ciwon kansa ba naga alama, shi ko kishi baya yi, kuma gaskiya Mai martaba ya nuna son kansa a fili karara nada Wan sa da yayi Yarima me jiran gado a maimakon Jawwad, ina ce Jawwad din ya girmi Wan sa?" Mami tace "Ya basa watanni har uku" Hajiya Batula ta rike haSa tace "Amma in tambayeki mana Fulani, bayan rasuwan mahaifin Jawwad wato me martaba Sarki Ahmadu Yusuf shi brother din nasa wanda shi ne sarkin yanxu bai nemi rikon Jawwad a gabansa ba?" Mami tayi shiru, can tace "Cikin Jawwad na da wata bakwai mahaifinsa me martaba ya rasu aka nada kaninsa wato mahaifin Junaid, dama su uku ne gun babansu Sarki Yusuf Ibrahim, daga Mahaifin Jawwad wanda shi ne babba sai Mahaifin Junaid sannan Maimuna warce nake gidanta yanxu suna kiranta da Ummi...." Hajiya Batula tace "Ikon Allah, to amma...." Shigowar Ummi dakin ne yasa Hajiya Batula tayi saurin canza topic din tace "Yanxu goben za ki koma Bauchi kenan Hajiya?" Mami tace "In sha Allah" Ummi ta ajiye plate din hannunta tace "Sannun ku, gashi nan kaza na tsaya gasa maku" Hajiya Batula na murmushi tace "Allah sarki, sannu da aiki" Ummi tace "Bari in kawo maku drinks din, a can parlor mai aikin ta ajiye" Daga haka ta fita daga dakin, Mami tace "Da ma kin ci gaba da maganar ki, ita ma ai bata so Junaid din da aka nada Yarima me jiran gado ba" Hajiya Batula tace "To ke sai kika zuba ido aka yi hakan Fulani? In uban Jawwad din bai mutu ba a ina kanin nasa zai samu har yayi sarauta? Kuma shine bazai yi kara ya nada Wan yayansa da ya mutu ya bar masa sarautan Yarima me jiran gado ba sai ya nada Wan cikin sa?" Mami tayi wani murmushi tace "Ni fa ko a jikina hakan da aka yi, Jawwad is doing fine beside shi mulki ma baya gabansa, as far as my son is okay, i think da a nada sa Yarima da kar a nadasa duk daya..." Hajiya Batula tace "To halan Junaid din kadai sarkin ya haifa?" Mami tace "Wani Junaid? Amaryarsa da suke kira da Aunty na da Wa me shekara 29, ita in son samu ne ma a nada Wan ta Yariman ai" Hajiya Batula ta rike haSa tana kallon Mami. Ajay yayi parking kenan bayan sun dawo gida wajen karfe bakwai na dare ya kalli Jay zai yi magana wayarsa ya fara ring, ya dauka yana duba me kiransa ganin number wani abokinsu ne da kamar bazai yi picking ba kawai sai kuma ya daga ya kai kunne, after few seconds of listening to what the frnd was saying ya zaro ido yace "What???" Kallonsa Jay yayi da sauri don intonation din da yayi using ya nuna ba lafiya ba, Da kyar Ajay ya cire wayar a kunnensa yana kallon Jay dake kallonsa shi ma babu ko kiftawa, Nan da nan Jay yaji hankalinsa ya tashi don babu inda mind dinsa yaje immediately sai gun Khaleesat, Ya fixge wayar hannun Ajay yace "What's happening plss?" Ajay ya kasa cewa komai tsabar yanda ya girgiza, Jay ya shiga call logs din wayar da sauri yaga Adams abokinsu ne ya kira nan yaji hankalinsa ya Wan kwanta don yasan ba abu bane da ya shafi Khaleesat, dialing number yayi amma har ya gama ring ba a daga ba, a hankali Ajay yace "Salim aka harba" Jay bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba yace "What? Harbi kuma? Is he dead?" Ajay ya dau wayarsa shi ma ya kara dialing number Adams amma har ya katse bai daga ba, available flight to kano ya fara dubawa immediately.....
[6/3, 9:01 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Washegari sai da rana Ajay da Jay suka samu ganin Salem a hospital din da aka yi admitting dinsa, iya kafadarsa ne kadai aka nannada ma bandage alamar a nan aka harbesa amma duk kamanninsa ya canza alamar ya ci duka ba na wasa ba, Jay ya zauna kujeran dake kusa da gadon yana kallon Salem that was in pain yace "Hasbunallah, How did this happen Salem?" Shi dai Ajay na tsaye ya rungume hannu shi ma yana kallon Salem ganin yanda aka canza masa kama, ya ma kasa cewa komai, Salem dake kishingide jikin pillow da kyar don ko iya motsa kafadarsa daya baya yi ga duk jikinsa yayi tsami yayi karfin halin cewa "Ban san su ba suka yi attacking dina" Jay yace "Har gida suka same ka?" Salem ya girgiza kai yace "I stayed out late yesterday in wudil naje gurin wani abokina, he insisted i stay till the next day amma saboda ina da abun da zanyi washegari da safe a kano sai naki kwana a garin muka yi sallama da shi, bayan na kusa unguwan da nake da zama sai na lura da wata mota na biye dani a baya amma ban yi tunanin komai ba na zata ya shigo layin ne bai san hanya ba shine yake bi na ko nima fita zanyi daga unguwan mun fita tare, bayan na shigo layin mu babu kowa saboda dare yayi tun kan ma in sauko daga motata in shiga gida in bude gate sai nake ma motar alama da hannu ya tafi gaba zai samu hanya, sai kawai matukin motar ya fito ya nufo ni, duk da haka ban wani damu ba na zata direction zai tambayeni, na tsaya har ya iso dai dai gabana ban ankara ba kawai sai jin saukan naushi nayi ta ko ina a fuskata ina kokarin defending kai na sai sauran mutane ukun dake cikin motar suka fito su ma suka hau dukana ta ko ina at the same time they were asking me about a girl i know nothing about, wai inyi providing dinta ko su kashe ni" Da wani expression Jay ke kallonsa, sai kuma ya mike da sauri ya dafa gadon da Salem yake kai yace "A girl?" Salem ya gyada kai da kyar yace "Wai Khaleesat, ni ban ma taba jin sunan ba wallahi, suka yi ta dukana wai sai na fadi inda take ko su harbeni" A tare Ajay da Jay suka kalli juna, Salem yace "Kashe ni suka yi niyyar yi banda Allah ya rufa min asiri kururuwan da nake yi wani soja dake kusa da gidanmu ya fito da bindiga, da wani makocina da ya fito da adda, kafin makota na su fito ne suka min harbi har biyu daya ya sameni a kafada daya kuma bai sameni ba ya sami gate, sojan da makoci na suna fitowa suka shige motarsu suka tsere, ni wallahi ban taba jin sunan yarinyar da suka ambata ba ma" Aunties din Salem biyu ne suka shigo ward din da sallama, Ajay ya gaida su sannan ya fita daga ward din ya tafi haraban asibitin ya zauna, after almost 10 mins Jay ma ya fito, inda Ajay ke zaune ya nufa ya zauna bai dai ce masa komai ba, Ajay yayi breaking silence din yace "He is tracking me, ni yake nema ba Salem ba, but tana da number Salem a wayarta ne?" Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Yawanci shi take kira ya bani waya if there is anything she wants to tell me, ko number ka ma ai Salem ne ya tura mata, instead cewa zaka yi he is tracking the both of us tunda nima ta kira layina ai ranan, but how did he get Salem's line?" Ajay yayi murmushi yace "Definitely layinta ya sa a duba masa numbers din wa enda take waya da, and he is using that to track us" Jay ya mike yace "We need to take down our sim card AJ, decidedly zai samu information mun shigo kano since we are in his list, sannan i think before anything ya kamata mu fara fighting for her innocent father's release tunda ita Halysaah yanxu bai san inda take ba and she is safe where she is, but the Man needs help" Ajay yace "No, i don't think she is safe with her aunt, although aunt din tace bai san inda ta koma ba amma as far as yana da number wayarta zai iya sakawa ayi tracing din inda take ita ma" Jay ya juya yana kallonsa yayi shiru, he just realize of course hakan zai iya faruwa cause ya daina underrating Abdul yanxu, Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "That guy is something else Ajay, duk wata salon mugunta ya sani adding it to his career skills, ina jin kawai a duba mana if there is flight zuwa Niger republic a biya masu kawai su tafi can da aunt dinta har zuwa sanda za mu gama da Case din dad dinta, in the other hand shi kuma mun yi sue dinsa requesting for divorce for her" Ajay yayi shiru, can yace "But what if she is needed in court?" Jay yace "For now her lawyer will represent her, in ma an bukace ta a court we will sort that out" Jay yace "I think that's cool, amma ya kamata mu je gidan su gun mahaifiyarta" Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace "Is that necessary?" Jay yace "Of course, kasan aunt dinta tace mana the mother is not medically fit, kada wannan damuwar yayi weighing dinta down" Ajay yace "Sai mu je a matsayin su wa?" jay ya mike yace "Human right" Abdul na tsaye rike da takardan da mahaifiyar sa ta mika masa daga shigowar sa parlor idonsa na kan takardar yana karanta content din jiki, Meema yayarsa ma na zaune parlon tana kallonsa fuskarta dauke da bacin rai karara, wani murmushi Abdul yayi ya cukuikuye takardar ya jefar kan kujera, Mahaifiyar sa dake ta kallonsa ta tabe baki tace "To yanxu menene amfanin wannan tozarcin da kaskantar da kai da ake yi? Sam kace kai baza ka ji maganata ka dau shawara ta ba Abdallah?" Meema ta katse ta tana kallonta a fusace tace "Haba Momy ta yaya kike son ya ji maganarki bayan uban kudin da ya kashe ma tsinanniyar shegiyar yarinyar? Ai jin maganar ki ba nasa bane wallahi, kuma don an kawo masa sammaci ba shi ke nufin ya hakura zai saketa ba, kotu ce kawai za a shiga ayi ta gwabzawa, kuma in sha Allahu duk inda kafafuwana za su shiga sai na shigar da su don Abdallah yayi nasara a wannan case din, bazan taSa bari a tozarta min kanina ba ga mari ga tsinka jaka bazai taSa yiwuwa ba wallahi, alamar koma waye ya zugata ta yarda aka yi karansa zai iya biyan ko nawa aka ce ya biya a kotu, kai jama'a amma yarinyar nan anyi babbar er iska butulu, dama ni tun asali ban goyi bayan da yace zai kai yarinyar nan Amurka ba ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login