Showing 210001 words to 213000 words out of 241367 words

Chapter 71 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1593

ya bude ya shiga parlon, ta bi bayansa. Jay na zaune gaban mai martaba kansa a kasa yana jin duk abinda yake cewa, Cikin nutsuwa mai martaba ya ci gaba da cewa "I am so disappointed in you Ahmad, kana kallon abinda Wan uwan ka ke yi amma ka kasa gaya min, i am really disappointed, even if you can't tell me directly there are other ways to approach me and i will understand you, to yanxu kana tunanin rufa masa asiri kake yi yana aikata sabo kenan?" Jay ya dago kansa a hankali, after few seconds murya can kasa yace "Abba ba abinda ku ke tunani bane, i promise you Junaid is doing nothing that is against the teaching of Islam, ba ma shi da lokacin da yake kula mata balle har yayi wani doguwar mu'amala da su, ka yarda da ni Abba bazan maka karya ba" Mai martaba dake kallonsa yace "Na je Maryland na ga mace a dakinsa, Auntynku ta je jiya and same thing happened, ta yaya zan yarda da maganar ka Ahmad? What sort of silly coincidence is that?" Jay yace "A gafarce ni Abba, amma nasan ba a dakinsa Aunty ta ga mace ba sai dai a dakin baki, shi Junaid wani irin mutum ne wanda idan yaga mutum stranded be it namiji ko mace bai ki ya ajiye ko ma waye a gidan ba har zuwa sanda mutumin zai yi sorting kansa out, you can confirm this from the workers of the house, wallahi halinsa kenan ba wai don ya hada komai da wa enda yake taimaka ba, Abba kasan bazan maka karya ba wai don in rufe laifin da kake tunanin Ajay ya aikata don in nayi hakan nima Allah bazai bar ni ba, Billah i am telling you nothing but the truth Junaid ba shi da hadi da koma wacece Aunty ta gani a gidan nan" Abba yayi shiru, after a while yace "Na ji, kuma na yarda, but i am afraid hukuncin da na tsara a kansa bazai masa dadi ba, but he still have to accept it cause hakan kadai ne zai sa in samu nutsuwa da kwanciyar hankali" Jay sai kallon Abba yake, a hankali yace "Wani hukunci kenan Abba?" Abba yace "Na yanke hukunci zan masa aure and he just have to accept ko ma wacece matar, you are not excluded also, duk da kai akwai maganar ka da Hadiyah....." Jay ya kwantar da murya yace "Don Allah kayi hakuri Abba, we have just few months remaining da muke saka ran za mu gama karatun nan da muke yi, bamu yi tunanin za mu kawo har warhaka bamu gama ba, plss Abba a saurare mu har zuwa sanda za mu gama, in just 2 to 3 months" Abba yace "Kwanaki ma haka ku ka min dadin bakin nan, kun maida ni kakan ku" Jay yace "Kayi hakuri Abba, mun san ka bamu dama sosai and this will be the last in sha Allah" Murmushi kawai Mai martaba yayi yana kallonsa, kowa yasan sa a mutum mai magana daya, amma ga yara sai juyasa suke yanda su ke so, after a while Abba yace "Yaushe zaka koma Amurkan?" Jay ya sunkuyar da kansa yace "Watan da za mu shiga in sha Allah" Abba yace "Allah ya kai mu" Khaleesat na zaune saman darduma wajen karfe shidda na yamma, tun da tayi sallan la'asar take zaune kan darduman take karatu a laptop dinta don in a month and few days time za su fara Spring semester exams din su, wayarta taji yayi vibrate alamar shigowar text, ta jawo wayar tana duba text din taga number Ajay, "Come out" iya abinda ya tura mata kenan, ta ajiye wayar ta mike ta dau Hijab dinta ta saka, tunda ta dawo apartment din nata kusan kullum zai zo wani lkcn ya gama zamansa a motarsa da yake parking a garage sai kuma yayi ordering ride ya bar motar tasa a garage din ya tafi, wani lkci kuma ya shigo parlon nata bazai dai dade ba zai fita, kuma ba wai magana yake yi mata ba, da ta lura bai son magana iyaka kawai ta gaishesa ta koma ta ci gaba da abinda take, wani lkcn ma sai ta dawo school zata ga alamar ya zo apartment din idan taji kamshinsa a parlor, duk ta lura for security purpose yake hakan, har ma da barin motarsa da yake yi a garage din apartment din, don ko da ya zo da safe ya dau motar ya tafi inda za shi to zai maida nan yayi parking da yamma sannan yayi ordering ride da zai kai sa gida, and she really appreciate all this that he is doing for her safety, don farko da ta dawo gidan kusan kullum sai tayi kuka gashi bata iya bacci da daddare don gani take kamar at anytime Aymaan zai iya zuwa gidan, gradually kuma ta hakura barin da ta ga Ajay na yawan zuwa gidan, amma fa duk wannan abubuwan ba shi ne yasa bata tunanin Housemate dinta ba, babu ranan da zai zo ya fadi bata yi tunaninsa ba, wani lkcn har da kukanta ta rasa dalilin hakan, zuwa yanxu kam ta ma hakura ta dena masa magana ta WhatsApp din tana ganin kamar takurasa take maganar da take masa duba da yanda yake amsa mata kamar baya so, tana bude kofar apartment din bayan ta sauka downstairs taga ledojin dake ajiye bakin kofar, sai kuma ta kalli garage ta gan sa zaune cikin motarsa, sai da ta fara shiga da ledojin parlor sannan ta fito ta nufi gun motarsa tana kallonsa ta gaishesa, ya bude motar ya sauka ya amsa without looking at her ya kulle motarsa, sai kuma taga ya nufi lyft din da ke jiran sa, tana tsaye tana kallo har ya shiga sannan ta juya ta koma apartment dinta ta kulle kofar da makulli, kayan shayi ta gani a ledojin da ya kawo mata, gwangwanin madara manya biyu, milo biyu, kwalayen sugar, Lipton, coffee powder, da kuma chocolate, har da bread manya uku da cookies iri iri, kilan ya shiga kitchen ne yaga babu madara shi ne ya siyo mata, kuma lokaci ne bata samu ba tana ta son zuwa taje tayi shopping din kayan shayin.... Bayan kwana biyu Khaleesat na isa school Safiyyah dake zaune lecture hall ta dinga mata wani kallo tace "Wai don Allah baza ki dena yafa manyan mayafan nan ba kina kunyata ni Khaleesat, kin fa gama wannan kadararren iddan ba wai baki gama ba, ko sau biyu za ki yi masa iddan ne?" Murmushi kawai Khaleesat tayi tana kallonta tace "Ni na ce maki na gama?" Safiyyah tace "Ai shi yasa na tambaya ko sau biyu za kiyi don ina nan ina taya ki lissafi wallahi kin gama, duk na kagu inga kin fara cin gayu kina zuba zawarcin ki son ranki, ai yanxu kuma ba da bane kin shiga wani level daban" Khaleesat tace "To bakya lissafi dai dai kuwa..." Safiyyah tace "Wallahi ina yi sai dai in kece bakya lissafin" Khaleesat bata tanka ta ba ta nemi waje ta zauna don yanxu wani sabon gayu Safiyyah ke ji a makarantar ita ga final year student, ko ta zo da mayafi sai ta saka a jaka tayi ta yawo da hula kawai kamar er Enugu, ko kuma tayi azababben English dressing ta daura karamin dankwali a kai, ita dai har ta gaji da yi mata magana ta zuba mata ido, a tare suka koma apartment din Khaleesat ranan don danwake Safiyyah tace zata masu, sai kusan yamma likis Safiyyah ta bar gidan shi ma Mustapha ne ya isheta da kira, Khaleesat na kitchen ta gama wanke duk Utensils din da Safiyyah taki wanke mata tana goge gogen kitchen din taji an bude kofar apartment din, dama tasan dole zai zo tun da taga ya mance charger dinsa a parlor alamar da taje school ya zo apartment din daxu, a hankali take wanke hannunta a pampon kitchen din trying to be sure of what she is perceiving, gently tayi patting hannunta jikin towel din kitchen din tana goge ruwan hannunta, sai kuma ta juya, sai da numfashinta ya tsaya for some seconds tsabar yanda gabanta ya fadi, yana jingine jikin bango kusa da kofar shiga kitchen din ya rungume hannu yana kallonta, ta sunkuyar da kanta, sai kuma ta nufi kofar kitchen din zata fita zuwa parlor, hannunta ya kamo yana kallonta with smile on his face, bata san sanda ta fashe da kuka ba zata kwace hannunta ya jawota kusa da shi murya can kasa yace "Halysaah" Hawaye kawai ke zuba idonta ta kasa kallonsa, slowly ya rungumota jikinsa murya can kasa yace "I am sorry" Bude kofar parlon aka yi, Jay yayi saurin saketa amma tuni Ajay ya shigo, sau daya ya kallesu sai kuma ya sauke idonsa ya tafi ya dau charger dinsa ya juya ya fita daga parlon....

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H?



[23/07/2025, 1:50:42/ PM] Khaleesat Haiydar =???
'?: https://chat.whatsapp.com/I5vo38MH2jH8pDvzVF0Q4w



Khaleesat ta bi Jay da kallo ganin ya nufi parlor, kana ganinsa zaka gane shi ma bai so abinda yayi ba don bai yarda ya sake hada ido da ita ba, kamar bai san sanda ma yayi hakan ba, ganin ya zauna a parlon ta sauke idonta daga kallonsa, sai kuma ta juya ta koma kitchen, Jay yayi dialing number AJ amma har ya katse bai yi picking ba, bai yi zaton zai shigo parlon ba don har yana ce masa kar ya bata masa lokaci, ya mike ya tafi window din parlon yana duba garage amma sai yaga ya tafi don babu motarsa a garage din, komawa yayi ya zauna ya cire face cap dinsa, Khaleesat na fitowa kitchen ya maida face cap din without raising his head, ita dai kanta a kasa ta karaso parlon tana rike da bottle water da glass cup ta duka gabansa ta ajiye masa, still not looking at him a hankali tace "Sannu da zuwa" Sai a sannan ya Wan kalleta, ganin ba kallonsa take ba with calm in his voice yace "How are you Halysaah?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah, ya hanya?" Yace "Cool" Tana wasa da fingers dinta tace "Yaushe ka dawo?" Har sannan bai cire idonsa a kanta ba yace "Not less than an hour ago Housemate" A hankali tace "Ya su Mama da mutanen gida?" Yace "They are all good Halysaah, ya karatu? In few weeks time za ku fara Spring semester exams ko?" Ta gyada masa kai, shi dai kallonta kawai yake, can yace "How is Safiyyah?" Ta kwantar da kanta saman gwiwowinta har sannan tana jin kamshin turarensa na tashi a jikinta tace "She left not long ago" Sai kuma ta daga kai ta kallesa, sauke idonsa yayi daga kallonta, ita ma ta sunkuyar da kai tace "What should i make for you? Daxu danwake Sophie tayi mana and it's finished, should i make you pasta or rice?" Yace "No don't worry Housemate, Ajay made some food for me back home" Ta Wan bude ido tana kallonsa tace "Can he cook?" Kawai yayi murmushi wanda iyakarsa lips bai bata amsa ba, sai kuma ya nuna mata trolley din da ya shigo da shi parlon yace "I got you some stuffs, hope you will love it" Shiru tayi tana kallon akwatin, yace "Check them" Ta sauke idonta sai kuma ta mike ta bude akwatin, tsadaddun Abaya ta fara cin karo da tana bude akwatin, ta daga kai ta kallesa suka hada ido ya sakar mata murmushi, sauke idonta tayi ta rufe akwatin kawai, cikin sanyin murya tace "Thank you soo much, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara budi" Yace "Ameen Halysaah" Still bata dago kanta ba a hankali tace "And i also want to appreciate you for what you did to my parent, Allah Ubangiji ya sa kafi haka, Allah ya biya maka duk bukatun ka na alkhairi...." Bai tanka ta ba yana kallon agogon wrist dinsa ganin bakwai saura yace "I will take my leave now Housemate, it's late already" Ita dai bata ce komai don sai taji babu dadi da yace zai tafi, ya mike yana kallonta yace "Kina da lectures gobe ne?" A hankali tace "Sai karfe daya na rana" Yace "Ohk, i will come before then in sha Allah, Aunty Farida ta bada sako a kawo maki, yana mota kuma Ajay ya tafi da motar" Ita sai a sannan ma ta tuna ashe Ajay ya shigo gidan fa, ta kallesa tace "Ohk, but how are you going back home tunda ya tafi da motar? Kayi order din Uber ne?" Jay yace "Ohh, na ma manta" Komawa yayi ya zauna yana danna wayarsa yace "Let me order the ride now" Ita dai tayi shiru tana kallonsa babu ko kiftawa, har ya gama order din ya daga kai suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi tana jan yatsunta tace "Toh baza kayi sallah ba kafin ride din ya karaso?" Yace "Ohk bari in yi alwala" Mikewa yayi ya nufi bandakin dake parlon, ita ma ta tashi ta tafi sama dauko masa darduma, bayan Jay ya idar da sallah Khaleesat na kallonsa daga bayan kujeran da take tsaye tace "Or should i make you tea?" Yace "My ride is waiting Outside Housemate" Ta gyada masa kai kawai, tana biye da shi a baya har suka fita daga apartment din, ta rakasa har gun Lyft din dake jiransa, yana kallonta kafin ya shiga motar yace "Sai na zo gobe, take care of ur self" Ta gyada masa kai don har cikin ranta take jin da ma kar ya tafi, sai yanxu ta kara tabbatar da irin missing dinsa da tayi, memories dinsu tare na old apartment dinta ya dinga dawo mata a kai, and she misses every bit of those moment, she wish it's gonna happen again, a hankali ta juya bayan ya shiga Lyft din tana tafiya kamar mara lafiya ta koma apartment dinta ta kulle kofar. Jay na komawa gida ya bude kofa parlor ya tarar da Legend zaune bakin kofar alamar shi yake ta jira, tun da ya dawo gidan daxu bayan Ajay ya daukosa a airport Legend ke ta tsalle kansa yana haushi kamar zai rungumosa wanda hakan ke nuni da yayi missing dinsa ba kadan ba kuma ya bi sa har daki yana wagging tail dinsa yana kada kai alamar farin ciki ya nemi waje ya zauna a dakin, kafin su fita daxu kuwa sai da Jay ya kullesa a Cage dinsa don bin sa ya so yi yana ta haushi, Jay ya kalli Ajay dake zaune parlorn yana danna wayarsa ko dago kai bai yi ba, dukawa Jay yayi gaban Legend yana patting kansa ya bude steak din da ya siyo masa a hanya ya ajiye masa a pack din sannan karen ya kyalesa ya maida hankali kan Steak din, Jay ya mike ya karasa cikin parlon yana kallon Ajay yace "Didn't you see my call?" Ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "I didn't" Jay bai sake ce masa komai ba ya nufi kitchen, bayan wasu yan mintoci ya fito yana kallon Ajay yace "Where is the food you said you made?" Still not looking at him Ajay yace "Nayi zaton can zaka kwana ae, i gave all the food to the workers" Kallonsa kawai Jay yake, can ya juya ya koma kitchen din to make a cup of tea for him self, ko kafin ya fito kitchen din Ajay ya bar parlon. Washegari wajen karfe sha daya Khaleesat ta sauko downstairs jin ana danna bell, bayan ta tambayi waye ta bude kofar parlon, gaishesa tayi tana kallonsa, ya amsa da murmushi, zata amshi ledan hannunsa yace "Don't worry Halysaah" Juyawa tayi ta koma cikin parlon, ya bi bayanta, bayan ya ajiye ledan yana kallonta yace "Sakon Aunty Farida da tace a kawo maki" Khaleesat ta karasa ta dau ledan ta kallesa tace "Thank you so much" Kitchen ta tafi da shi ta duba taga cin cin ne me yawa aka yi packaging sai alkaki da dublan, a wani ledan kuma ta ga kayan kamshi na dafa shayi, sai flour, kuka da kanwa, da dakakken yaji me yawa, tana gani ta gane saboda danwake aka aiko mata, Wan murmushi tayi sai kuma ta dau take away a kitchen ta dibi cin cin din da su alkaki ta saka a wani ledan ta dawo parlor da shi, dukawa tayi gefensa da ledan, yana kallonta yace "What's that?" Tace "Cin cin ne da alkaki da Aunty Farida ta bada a kawo, i fetch some for you" Ya Wan bude ido yace "No, ta bamu namu ni da Ajay, it's at home wannan naki ne" Ta wani kallesa tace "Ban yarda ba" Yace "I am serious, har da tea spice da grounded pepper duk ta bamu" Khaleesat tayi murmushi tace "To na yarda" Mikewa tayi ta maida cin cin din kitchen, sannan ta fito tace "I made you some food in kawo maka yanxu?" Yace "I had breakfast before leaving home Halysaah" ?ata fuska tayi tana kallonsa, yayi murmushi ya sauke idonsa yace "Ohk... amma kadan zaki zubo min ba da yawa ba" Juyawa tayi ta koma kitchen din, ba a dau lokaci ba ta kawo masa shinkafa da stew din kaza da tayi, yana kallon abincin yace "Wannan ai yayi yawa" Tace "Eat and remain" Shi dai murmushi kawai yayi, ta koma kitchen ta dauko masa ruwa da glass cup ta ajiye masa, yace "Karfe nawa kika ce kina da lectures?" Tace "Karfe daya" Yace "Ohk to ki shirya idan na gama sai inyi dropping dinki nima zan shiga school din" Tace "Ohk, nagode" Sama ta wuce ta bar sa a parlon. Ko da Khaleesat ta sauko downstairs wajen karfe sha biyu da rabi ta gansa kwance kan 3 sitter idonsa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login