Showing 156001 words to 159000 words out of 241367 words

Chapter 53 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1603

jiya, ni kuma kin san bana son irin abubuwan nan na gargajiya shi ne na kawo ko zaki yi amfani da su ke" Momy tayi kuri da ido tana kallon ledan da mamaki, sai kuma ta dauka ta bude da sauri, lkci daya ta saita kanta tana murmushin karfin hali tace "Allah sarki, ai kam nasan halin ka baka san itatuwa, zan ko yi amfani da su dama nawa sun kare tas" Ita dai Khaleesat kasa dago kanta tayi, Momy was shock har cikin ranta amma tayi karfin hali take wayancewa, can ta kalli Khaleesat tace "Amma baki fara amfani da su ba ko" Khaleesat ta girgiza kai ba tare da ta kalli Momy ba tace "A'a jiya ta kawo min banyi amfani da komai ba" Momy tace "To to, hakan yayi" Ta kalli Abdul tace "In dai an samu wasu a dinga kawo min kawai" Mikewa yayi yace "Za mu koma Momy" Momy tace "Da wuri haka? To wai ka koma aiki ne?" Yace "Ban koma ba tukun" Momy tace "Toh shikenan, Allah ya tsare nima in sha Allahu ina nan shigowa in kawo mata turarrukan wuta da na jiki" Shi dai bai ce komai ba ya nufi kofa, Khaleesat ta mike tana yi ma Momy sallama, Momy duk fa a rude take ta gyada mata kai kamar kadangariya tace "To Mamata, sai na shigo, ku gaida gida, maza bi sa ku tafi" Daga haka Khaleesat ta bi bayan Abdul da har ya fita daga parlon, Momy ta dau wayarta har tana tuntube ta shiga dakin dake downstairs ta fara kiran Dr Mariya don family Dr dinsu ce for long, Dr Mariya na dagawa suka gaisa da Momy cikin fara'a, Momy tace "Yanxu Abdul ya zo min da matarsa yace daga asibiti suke, naga duk ba shi da walwala nasan yana da zurfin ciki bazai gaya min ko menene ba, shi ne na kira inji lafiya dai ko Dr? Ko juna biyu gareta? kinsan dama yace bai son haihuwa da wuri, in dai juna biyu ne da ita gwara in yi dubara in dawo da ita wajena don ni dai ina son ganin jikana, kar yaje ya bata wani abu da zai lalata cikin taje ta sha" Dr Mariya tayi dariya sosai, bata boye ma Momy komai ba tayi mata bayanin dalilin zuwansu Asibiti, Momy ta sauke wani irin ajiyar zuciya ba tare da tasan tayi hakan ba, sai kuma ta bige da cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kinsan yarinya ce fa, duka duka Allah yasa tayi shekara ashirin, har da yarinta abun nata dae" Dr Mariya tace "Wallahi nima haka nace masa don dae in kwantar masa da hankali kar ya dinga jin haushinta, amma shekara ashirin ai ba yarinya bace Hajiya, aka ma er shekara sha biyar aure ta zauna balle er shekara ashirin, ni dai na bata shawarwari Allah ya sa tayi amfani da shi, kar tun yana hakuri da ita hakurinsa ya kare a fara samun matsala gaskiya" Murmushi kawai Momy take tana Allah Allah su gama waya da Mariya ta kira Godiya, daga karshe Momy tace "To Allah ya sa ta dau shawaran naki Dr, kuma zan yi ma yayarsa magana ita ma taje gidan anjima ta kara nutsar da ita in sha Allahu" A haka Momy suka yi sallama da likitan, Momy tayi wani dariya tana girgiza kai sannan ta fara dialing number Godiya, a????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ikin miliyan biyu ai ba wasa bane, sun dade suna waya da Godiya a waya, daga bisanni suka yi sallama, Momy na ta murmushi ita kadai bayan Godiya ta sake jadadda mata Malamin yace lokacin ma da ya dibar masu za ayi sakin baza a kai haka ba, don gab ake da yin sakin cikin kwanan nan kuwa, Meemah da ta shigo dakin ta tarar Momy na waya ta zauna duk tana sauraron conversation dinsu har suka yi sallama tace "To shikenan Momy yanxu haka zai saketa ba mu ci ubanta ba na huce haushin abinda yayi min a kanta?" Momy tace "Ke wa ke ta wani cin ubanta? Ance maki shi ne a gabana sai kace wata yarinya? Ni dai in na samu Abdul ya rabu da ita an gama min komai, kuma hakan kadai ne a gabana yanxu ba shashanci irin naki ba, ke kinsan menene hada iri da talaka kuwa? Ke kiji matsiyaciyar kakarta har ta fara shige shigen malamai tana kawo mata asiri banda Allah yasa Abdul din ya gani, to karyarsu ta sha karya wallahi, cikin kwanan nan zai kora masu ita bayan ya saketa" Mikewa Meemah tayi ta fita daga dakin don kwata kwata ba haka ta so ba ita, so kawai tayi a bar ta tayi ma Khaleesat dukan mutuwa ko zata jin sanyin abinda Abdul yayi mata a kanta.
[6/25, 8:35 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Bayan Khaleesat sun koma gida tayi wanka sannan ta canza kaya tayi sallan azahar ta fito ta dora lunch a kitchen, tana ta zaune parlor bayan ta gama hada komai na girkin tayi tagumi tayi nisa tunanin da take bata san sanda ya fito daga dakinsa ba, ya karaso parlon yana kallonta yace "Burden din mutane nawa ne a kanki da kike tagumi haka" Juyawa tayi ta kallesa tana gyara zamanta amma bata ce masa komai ba, tunda suka dawo gidan sai yanxu yake mata magana bayan ya gama cika da batsewan sa kenan, Yace "I am asking you" Shiru tayi still bata ce komai ba, ya zauna kan kujeran dake facing dinta yace "Mutane nawa kike ciyarwa da kike tunanin yanda za ki yi?" Bata san sanda tayi murmushi ba tana wasa da fingers dinta, kamar bazata ce komai ba, sai dai a hankali tace "Ba ina son zan yi magana da frnd dita Sophie ba kace bazan yi ba" Yana kallonta yace "Kiyi magana da ita ki ce mata me?" A hankali tace "Babu komai, i am just missing her kawai" Wayarsa dake hannunsa ya cire ma lock sannan ya mika mata yace "Speak to her in my front" Amsan wayar tayi ta shiga contact dinsa ta duba number Safiyyah sannan tayi dialing, yana kallonta yace "Sa a handsfree" Ba musu Khaleesat ta saka kiran a Handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga, a hankali Khaleesat tace "Sophie" Safiyyah tace "Omg Khaleesat? Wallahi I've been expecting your call for so long kawata amma shiruu, Ya Allah, number Abdul din ne wannan?" Khaleesat ta Wan kalli Abdul da ya kafeta da ido tace "Um, nasa ne" Lkci daya har Safiyyah ta gane wayar a handsfree yake sanin wanene Abdul, a hankali tace "Ohk then, ki gaida min shi sosai pls, but can i come over in gan ki if he will permit that pls?" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I will speak to him about it" Safiyyah tace "Alright dear, take care of ur self, i will be waiting for ur feedback" Khaleesat tace "In sha Allah" a haka suka yi sallama, safiyyah ta kalli wata aunt dinta dake kusa da ita cike da bakin ciki tace "Wallahi nasan yana gefenta shi yasa ban tofa nawa ba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Her marriage and Abdul is the worst thing that have happened to me last year, yanxu shikenan ta zama matarsa duk guje mata hakan da na dinga yi, ba irin addu'an da ban sa ta akan Allah ya rabata da Abdul ba, nayi ta mata sha'awan Housemate dinta amma Allah ya riga ya kaddara Abdul ne mijinta, dubi yanda take min magana kina jin muryarta kinsan tana cikin damuwa da matsin rayuwa, gashi karshen watan nan za mu koma school ban kuma ga alamar zai bar ta taci gaba ba" Safiyyah ta fara matsar kwallan bakin ciki, ita dai tana jin babu wanda ya kai ta bakin ciki da auren Khaleesat da Abdul, Abdul ya amshi wayarsa da Khaleesat ke mika masa bayan tayi sallama da Sophie, a hankali tace "Thank you" ajiye wayar yayi yace "Sai hankalin ki ya kwanta yanxu tunda kin yi magana da kanwar Baabarki ko" Cikin sanyin murya tace "Plss ina neman favour din ka barta ta zo wajena don Allah, i am missing her so much" A takaice yace "Baza ta zo ba, in barta ta zo ta ji dadin zuga ki kamar yanda ta saba? you think i don't know saboda tasan wayar a Handsfree yake shi yasa tayi composing words dinta without saying anything silly yanxu, duk ba ita bace ta fara ruining tunanin ki, very stupid girl" Khaleesat dai kallonsa kawai take hawaye cike idon ta, kawai tayi deciding tayi masa maganar abinda ya tsaya mata a rai all this while, hoping Allah zai sa yayi considering din request din nata, cike da karfin hali tace "Amma don Allah Yaya Abdul kar kace bazan koma makaranta ba, we are resuming end of this month kuma kasan wannan shekaran kadai ya rage min plss kar ka bari inyi asaran shekarun da nayi a baya, kayi considering expenses din karatun plss, in kuma zai yiwu kawai a min transfer ba lallai sai can kasar ba..." Hawaye na sauka idonta ta kare maganar tana kallonsa, ya mike yace "You think i am stupid da zan bari ki kara komawa America ki ci gaba da karatu? to ai kai ki can ma da nayi tun farko i deeply regret doing so, nayi da na sanin kai ki karatu America da har ya bude maki ido, kuma tunda ba kudin ki ko kudin wani naki aka kashe ba all this past years ina ruwanki da asaran da za ayi? How is the lost going to affect you da kike nagging akan expenses din? Ina ce kudina ne sai ko kudin mahaifina? So babu ruwanki, na gwammace inyi asaran duk abinda na kashe maki da dai ki koma kasar nan, kuma kika kuskura kika sake kawo min maganar karatu sai nayi mummunan saSa maki wallahi, kuma bari kiji, common University din kasar nan ma baza ki yi ba balle na wata kasar don babu inda aka ce lallai lallai sai kinyi karatu, at first nayi tunanin kina da kamun kai da nutsuwa ne shi yasa confidently na kai ki America, amma sai kika tafi kina rayuwa da wani ?aton Wan iska a gida daya without my knowledge, ya kai ya kawo ko kudi na tura maki sai kiyi kamar baki gani ba for days tunda kin samu Wan iskan dake siya maki abubuwa, not even one guy, kattin maza har biyu kika je kina mu'amala da su a can, ko wanne kuma ke kika san abinda kike basa da yake kashe maki kudi, so ko da kuskure kika sake kawo min maganar karatu wallahi sai na maki abinda har ki koma ga Allah baza ki manta ba" Yana kai wa nan ya dau wayarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo hawaye masu zafi na sauka idonta. Har dare Khaleesat na dakinta abun duniya ya taru ya mata yawa, wajen karfe sha biyun dare har ta fara bacci taji an bude kofar dakinfa, a hankali ta bude idonta, wutan dakin taga ya kunna sai kuma ya kashe, ita dai tana kwance bata juyo ba, ya karaso inda take kwance ya cire duvet din jikinta ya cire hulan kanta yana shafa dogon gashinta ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace "You gave me Neither lunch Nor dinner today, saboda kinfi karfin a gaya maki gaskiya ko?" Ita dai bata ce komai ba duk da tana jin sa, dagota yayi zaune ya rungumeta yace "Then let me have you since you are not giving me what u cook" Bai jira abinda zata ce ba ya fara kissing dinta, Sosai Abdul ya bata lokaci wajen romancing dinta irin yanda yasan zai gigita ta, in ba ita ba ma babu warce ya taSa romancing har haka, ko lube din bai dauko ba yau don baya ganin zasu bukace sa ma, a wannan moment din Frustration dinsa yafi na kullum don sosai ya kai zuciyarsa nesa bai kai mata hannu ba, yana wani irin huci ya fixgota da karfi yace "Why are you doing this to me Khaleesat? Why are you frustrating me?" Kasa ce masa komai tayi jikinta na rawa hawaye na zuba idonta, ta gaji da ce masa ita bata san abinda ke faruwa ba, cikin daga murya jikinsa na rawa yace "Ki bani amsa? Me na maki kike wahal dani kike cutata haka?" Khaleesat dai ta kasa ce masa komai jikinta na rawa don tsoron magana ma take ya gaggaura mata mari, yana wani irin huci ya turata yace "Ki jika abun ki ki sha" Yana fadin haka ya sauka daga saman gadon ya saka Pajamas dinsa ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Khaleesat dai ta jawo duvet ta rufe jikinta har sannan zuciyarta na bugawa ta fashe da matsanancin kuka, bayan kusan minti goma taji fitar motarsa a gidan gaba daya. Da yammacin ranan Momy na parlonta da Godiya sai ga Abdul ya shigo kamar an hankado sa, Momy na kallonsa tace "A'a Babana, sannu da zuwa" Juyawa yayi ya fice daga parlon ganin Godiya, Momy ta Wan zaro ido tana kallon Godiya sai kuma ta mike da sauri ta tafi kusa da kofar ta bude tana leka corridor taga bangaren Abbansa ya tafi, ita ta dade bata gansa cikin irin wannan yanayin ba ma, ta kulle kofar ta dawo tana kallon godiya tace "Anya Godiya Malamin nan ba maye bane kuwa, kin ga dama yace Abdul zai zo yau gashi kuma ya zo din kamar an jefosa" Godiya tayi wani dariya tace "Ke ma dai wallahi sai kace yau Danger ya taSa maki aiki da zaki yi mamaki? Yanxu dai sai ki tashi kije ki dora masa girkin da ya fi so da maganin" Momy tace "Ikon Allah, in dai kana da kudin ka zaka ga aiki da cikawa kawai, yanxu ki dubi yanda ya shigo mana a firgice kamar mara lafiya" Godiya tace "Ina kuwa lafiya dama an hanasa angwancewa da amarya, sai kace baki san maza in suka kwallafa rai kan wannan lamari ba" Suka kwashe da dariya gaba daya har da kyakyatawa, Momy tace "Toh yanxu zan tura cikon aikin nan na karshe, yaushe zaki koma wajensa mu je tare in masa godiya" Godiya tace "Nan da kwana uku in sha Allah, kin ga bari in tashi in tafi mai gidana na hanyar dawowa yau" Momy tace "Haka fa kika ce, toh shikenan sai mun yi waya dai kawai" A haka Momy ta raka Godiya har gun motar ta sannan ta dawo cikin gidan ranta fari ?al, bangaren Alhaji ta nufa ta tarar da Abdul kwance a parlor idonsa a lumshe, zaunawa tayi gefensa tana kallonsa cikin kwantar da murya tace "Babana baka da lafiya ne?" A takaice yace "Hutawa nake yi Momy, i need privacy pls" Momy tace "Toh shikenan, bari in sa a daura maka favorite din ka, ina Mamata fa?" Shiru yayi yaki ba Momy amsa, Momy ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo kofar, sai a sannan tayi wani murmushi ta koma bangarenta zata dau maganin da Godiya ta kawo mata wanda zata zuba a cikin girkin abinda Abdul ya fi so, sai da ta kori mai aikinta can compound sannan ta fara girka masa Pounded yam da Vegetable soup, cikin miyan ta zazzage duk maganin da kyauta ta kawo har kala uku, wajen karfe bakwai ta gama ta dau abincin ta kai masa dining table ta ajiye, dama iya cin sa kawai ta girka wato malmala daya kuma ba babba ba, miyar ma Wan tsut yanda zai cinye gaba daya, sai bayan isha Abdul ya ci abincin da Momy tayi masa, ya bar ma mai aiki ta kwashe sannan ya wuce sama zuwa dakinsa, Momy ta fito dakin Meemah kenan ta bi sa da kallo har ya shiga dakinsa sannan ta bi bayansa, tana shiga dakin tace "Wai lafiya Babana? Ko dai akwai wani matsalan da kake boye min ne" a takaice yace "Ba komai, zan shiga wanka" Yana fadin haka ya fara cire kayan jikinsa, Momy tace "To ka ci abincin?" Yace "Na ci" Momy na murmushi tace "You like it?" Yace "Miyan yayi dadi, but it's little" Tana murmushi tace "To maa sha Allah, amma ai ya isheka dai" Yace "Ya isa" Tace "Toh je kayi wankan ka nima bari inje in ci abinci" Fita tayi daga dakin ya shiga bandaki, Momy na zaune parlonta tana cin farfesu dake cike cikin bowl din hannunta Abdul ya shigo, kallonsa tayi ganin yanda ya shirya sai zuba azababben kamshi yake, tace "Har zaka tafi Babana" Yace "Eh, sai da safe" Tace "To ko in zuba maka farfesun ka kai ma Mamata" A takaice yace "A'a ni ba gida zan kwana ba" Momy tayi murmushi tace "To Allah ya tsare Babana" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga gidan. The next 10 days a gidan Abdul was a living hell for Khaleesat, gaba daya Abdul ya sauya mata a gidan ya dawo kamar wani monster, dukanta da yace ya dena sai dai bai samu slightest opportunity din yin hakan ba, kawai ya maida ta punching bag dinsa a gidan barin in ya zo gareta bai samu biyan bukata ba, kuma bai fasa zuwa mata da bukatar tasa ba amma as usual sai dai kawai ya doketa ya fita bai cimma burinsa ba, kwata kwata ya dena cin abincin gidan, ya dena kwana sai sanda ya ga dama, duk wani ingredients din girki ya dena siyowa sai dai tayi ta cin indomie, hatta bottle water ma da ya kare yaki siyowa, kuma ko Satchet water yaki siya ya ajiye, sai dai ta sha ruwan pampo, gaba daya Khaleesat ta fita hayyacinta a gidan ta dawo kamar ba Khaleesat ba, ga karyewa da gashinta ya dinga yi sosai saboda tsananin damuwa, kana ganinta kasan tana cikin jarabawan rayuwa, bata da aiki sai kuka sai kuma addu'a da sallan dare, gaba daya ta maida duk lamarinta ga Allah, kullum haka take kwana ta tashi da zazzabi amma ina taga fuskar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login