Showing 3001 words to 6000 words out of 241367 words

Chapter 2 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1594

dai bashi da hankali ne bai san bin komai ake a sannu a kasar nan ba" Khaleesat dai ta dau Noodles dinta ta bar wajen tana kallon Safiyyah tace "Ga Indomie ki dafa mana, ina son inyi magana da Ummanmu kafin Aunty Sha'awa ta fita kasuwa" Safiyyah tace "Ohk to" Khaleesat ta bar kitchen din ta dau jakarta ta wuce dakinta, WhatsApp dinta ta bude ta shiga contact din makociyarsu Sha'awa tayi mata voice note kamar yanda ta saba a duk sanda take son magana da Ummanta. Sai kusan karfe hudu na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zuwa gun Lyft din da tayi ordering don tun daxu Cousin brother dinta ke kiranta ganin bata dawo gida ba, Safiyyah ta shige motar ta kulle tana daga ma Khaleesat hannu, sai da Lyft din ya bar wajen sannan Khaleesat ta juya tana tafiya a hankali ta nufi apartment dinta, dai dai apartment din taga mota yayi parking a space din da aka tanadar don parking for that apartment, bata karasa ba ta jingina jikin fence din dake inda take tsaye tana kallon motar ta little space din dake between the wooden fence din, taga ya fito daga motar ta bi sa da ido har ya shiga apartment din yana danna wayarsa, ta fi minti biyar tsaye a inda take, daga karshe tana tafiya a hankali ta karasa apartment din ta murda kofar parlon taji ya kulle, hade rai tayi tana kallon kofar, daga karshe da ta gaji da tsayuwa kawai tayi knocking, sau uku tana knocking sannan ya bude kofar, yana ganinta yace "Hi" ita dai ko kallonsa bata yi ba fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi gefensa ta shiga parlon, direct gun wayarta dake kan kujera ta nufa ta dauka tare da reading materials dinta dake saman kujeran, har zata dakinta sai kuma ta dawo ta tafi kitchen ta dau goran ruwa daya sannan ta nufi dakin, sai da ta bude kofar tayi masa kallon gefen ido taga he is just busy sorting out some textbooks that were inside a carton he came with, har ta shiga dakin nata bai juya ba balle ya kalli direction dinta....


07087865788
' [4/29, 5:07 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: https://chat.whatsapp.com/KVY8hjs3iNq5ntSN4Z5g6V



('(' HALYSAAH ('('



By _Khaleesat Haiydar_
'



2.....

Washegari har karfe sha daya Khaleesat na dakinta bata fito ba duk da yunwan da take ji, tayi tagumi don gaba daya ta ma rasa what is her problem particularly, ta dau wayarta jin shigowar WhatsApp message, tun daxu suke chatting ta VN da Ummanta ta wayar makociyarsu Sha'awa, da taji shiru ta ma zata an maida ma Aunty Sha'awa wayar nata ne, ta bude VN din tana sauraren voice din mahaifiyarta, Addu'a Ummanta ke mata tana mata fatan nasara a karatun ta, sannan kamar ko da yaushe ta sake jaddada mata ta kula da mutuncinta ta kula da kanta, daga karshe ta ?are da cewa za a kai ma sha'awa wayarta don zata fita kasuwa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar a hankali sannan ta mike ta dau hijab din sallanta ta saka ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita daga dakin don ta gaji da horan kanta da yunwa ita da ke breakfast da wuri, kitchen ta tafi almost bumping into her new House mate shi kuma yana kokarin fitowa daga cikin kitchen din, komawa baya yayi at the same time yace "Good morning" Bata yarda su hada ido ba ta matsa gefe allowing him to pass, ya fito daga kitchen din yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan ta shiga ciki, tsaye tayi tana kallon littered cups da plates din da yayi amfani da su ya bari a sink din wanke wanke without washing them, ga bowl din fruit salad da shi ma ya ajiye bai sha ba, bin kofar kitchen din tayi da kallon mamaki, to wa ya bari yayi masa wanke wanke? Ta fi minti daya tsaye a inda take da tunani iri iri a ranta, wata zuciyar ta ce mata kawai tayi abinda ya kawota ta fita daga kitchen din ta bar unclean utensils din a yanda ya bar su, amma dai kawai ta jawo liquid wash da sponge fuskarta a daure ta fara wanke kayan wanke wanken kawai, bayan ta gama ta goggoge kitchen din ta hada shayi ta debi cookies a plate sannan ta fita daga kitchen din ta wuce dakinta. Wajen karfe uku Khaleesat ta fito daga dakinta, tun da ta gama breakfast take karatu sai sallah kawai ta tashi tayi da azahar, jin ko ina shiru and to be sure baya gidan ta nufi kofar parlon zata bude taji an kulle da makulli, dakinta ta koma ta dauko makullinta ta bude kofar tana duba garage taga babu motarsa a ciki, komawa cikin gidan tayi ta kulle kofar sannan ta tafi kitchen, tun shekaranjiya take son cin shinkafa da miya amma kasancewar she is not comfortable tun da ya dawo gidan yasa ta hakura da girkawa, yanzu da taga baya nan kawai tayi deciding tayi shinkafa da miyar, bayan ta daura shinkafar, ta fara hada miyar dama tana da sauran chicken thighs a fridge, fitowa parlor tayi da sweeper zata yi shara, ta ajiye sweeper din hannunta to tidy the couch first, dukawa tayi tana kallon takardun Housemate din nata da ta gani, sai kuma ta kyabe baki ta bar su nan yanda ya bari a kan kujeran, share rug din parlon ta fara yi bayan ta dauke makullin da ta gani a kasa, ta dinga juya makullin ganin kamar na Bedroom ne, kafin minti arba'in ta gama girkin da take ta tsaftace ko ina na gidan, ta debi abincinta ta tafi daki da shi, sai da ta fara yin sallahn Asr sannan ta dau wayarta tana dubawa, sosai gabanta ya fadi ganin miss call din Abdul, nan da nan taji abincin ya fita ranta gaba daya, ta zauna gefen gado a hankali tana kallon wayar, ta fi minti goma zaune a haka, she was soo worried, to yanzu me zata ce masa ma in ta kirasa, daga karshe ta daure tayi dialing number nasa, har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, duk da yunwan da take ji haka nan taji abincin ya fita ranta, ta tsani duk wani abu da zai sa Abdul ya daga mata hankali, haka tayi forcing din kanta ta ci abincin sannan ta kwanta side din gado, bata san sanda bacci ya dauketa ba a haka.... knocking kofar dakinta da ake yi ne ya farkar da ita daga baccin da take, ta mike zaune da kyar tana murza idonta tana kallon kofar at the same time tana mamakin me zai sa ya dinga bubbuga mata kofa haka, to ko dai bashi da kai ne?? ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe shidda da mintuna, bata yi tunanin ta dade tana bacci haka ba, sake knocking da aka yi yasa ta mike tsaye ta saka hijab fuska daure tace "What is that??" Ta ji yace "Ohk i think i misplaced my keys, just want to know if you saw it while tidying up the parlor?" Sai a sannan ta tuna makullin da ta gani a parlor daxu da take shara, tana tafiya a hankali ta karasa kofar dakinta ta murda key din jiki sannan ta bude door din, tuni har ya bar corridor din ya koma parlor ya tsaya yana jiranta, da alama dawowarsa gidan kenan a lkcn, ta karaso cikin parlon ba tare da ta kallesa ba, shi dai duba message din da ya shigo wayarsa yake with all his attention, ta tafi inda ta ajiye makullin sannan ta dawo ta ajiye masa kan takardunsa dake kan kujera tace "Here" Yace "Ohk" dakinta ta koma ta shiga tana mamakin wai Ohk, ba ma thank you ba kamar irin ya ajiyeta din nan, kwafa tayi ta saka ma kofarta key, bayan Khaleesat ta idar da isha ta sake kiran Abdul bai daga ba, sau hudu kenan tana kiransa tun karfe bakwai bai yi responding ba, yanzu dai tafi tunanin yana bacci don dare ne sosai a can kasar, even at that tasan she is in soup, mikewa tayi ta dau plate din da ta ci abinci daxu ta nufi kofa ta fita daga dakin, a parlor ta ga sabon Housemate dinta yana tattara takardunsa at the same time yana answering phone call taji yana cewa "I am on my way now" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa ya dau takardunsa da makullin mota ya mike tsaye, ido hudu suka yi for the first time tunda ya dawo gidan, ita dai ta dauke kai kamar bata ma gansa ba ta karaso cikin parlon zata tafi kitchen taji yace "I ate a little out of the food you cook, and...." Yayi pointing takeaway din da ke kan kujera yace "I am taking some to my frnd too" duk wannan abun bai kalli inda take tsaye ba yake magana, sai ita ce ma da ta dinga kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, ya dau takeaway din ya nufi kofa cikin hanzari, yace "Good night" Ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle gidan da makulli ta waje, mamaki yasa ta kasa karasawa kitchen din, after some seconds ta tafi kitchen din, da plate din da ya ci abincin, da cup din da ya sha coffee, da bowl din da ya sha fruits salad duk suna ajiye a sink babu wanki, ta jingina da kofar kitchen din ta rungume hannu tana kallon sink din kamar zata fashe don bakin ciki, can ta karasa ciki tana duba shinkafar da ya bar mata, taga da kyar in zai yi spoon uku, gashi duk yayi littering din wajen da shinkafar wajen diba kuma ya bar shi haka, haka nan ta juye er shinkafar da ya rage a karamin bowl, ta wanke duk utensils din, ta gyara ko ina ta goge sannan ta hada shayi ta koma daki da bowl din sauran abincin, zaunawa tayi gefen gado ta dau wayarta tayi dialing number Safiyyah, sai da ya kusa katsewa Safiyyah tayi picking daga daya bangaren tace "Allah da gaske baki da kirki Khaleesah, to ko baki kira ba dai na isa Virginia cikin koshin lafiya" Khaleesat ta Wan yi murmushi tace "Dama nasan kin isa lafiya ai, hope you are doing good?" Safiyyah ta tabe baki tace "Oho dai, wannan ba matsalar ki bane" Khaleesat tace "Amma don Allah ina kika ce ma Ya Musty za ki?" Safiyyah tace "Ahaf tsaya wasa, sai kace baki san ni ba, munafukar matarsa da yake ba son zamana a gidan take ba ita ce ma ta kara convincing dinsa, duk zatonsu ina gidanki muna group reading with some of our Coursemate" Khaleesat tayi murmushi tace "To ai shikenan, yanxu yaushe zaki dawo?" Safiyyah tace "Gobe ne birthday din ai, in sha Allah i will be back on Monday" Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu, kinsan mene?" Safiyyah tace "Aa" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi in gaya maki Abdallah ne ya kirani nayi missing call dinsa as i am speaking to you now tun daxu nake kiransa yaki picking, nasan fushi yayi sosai, ni kuma...." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ke kuma me? Shikenan rayuwa babu uxuri dama?" Khaleesat tayi kasa da murya tace "He warned me times without number kar in sake missing call dinsa Safiyyah, kuma wallahi ina kitchen sanda ya kira wayar kuma na daki ba da gangan nayi missing kiransa ba" Sounding so pissed off Safiyyah tace "Wai don Allah me yasa kika dauki tsoron duniya kika dora ma mutumin nan ne Khaleesat? For how long will things continue this way? Yaushe za ki fara nuna masa ke fa mace ce? yanzu haka za ku yi auren ya maida ki slave a gidansa tunda kin nuna masa kina mugun tsoronsa tun a waje? wannan wani irin gantalallen relationship ne? Gaskiya ina jinjina maki Khaleesat, don wallahi in nice bazan iya ba Allah ma ya gani sai dai duk abinda zai faru ya faru" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I have no choice nor option Safiyyah...." Tana fadin haka hawaye ya fara gangarowa idonta, a Wan fusace Safiyyah tace "To wai ke kadai ce mace a gidanku ne da ya gani? Naga ga Labibah da Lamisah, ina ce sati biyu kika ba Labibah a shekaru, ita kuma Lamisah wata daya, ga kuma yayyinki Samira da salamatu, to wai halan su ba mata bane sai ke??" Khaleesat dai bata ce komai ba tana goge hawayen dake zuba idonta, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai shikenan, but u really need to speak up for ur self Khaleesat, ni dai nasan their worst mistake is sending you to school abroad, aje dai zuwa, ke kuma in har baki waye kin kwatar ma kanki 'yanci daga karshe ba to sorry to say this, wallahi u will live a miserable life in the nearest future Khaleesat, this is just the fact i am saying, na gaji da lamarin so called Abdul din ki" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Ki daina cewa haka pls Safiyyah, ke me tayani addu'a ce kan Allah ya kawo min komai da sauki amma ba ki dinga fadin wa ennan maganganun ba...." Safiyyah ta taSe baki bata dai ce komai ba, a hankali Khaleesat tace "Pls ko zuwa gobe da safe ki masa magana ta Whatsapp ki tayani basa hakuri cause nasan bazai daga kirana ba no matter what..." Safiyyah tace "To naji, Allah ya kai mu goben" Khaleesat tace "Ameen" Sallama suka yi, Khaleesat ta ajiye wayarta. Karfe goma saura na safe Khaleesat ta fito daga dakinta rike da wayarta don kar ma Abdul ya kira by mistake tayi missing call dinsa, tun jiya take makale da wayar duk don kar ya kira bata sani ba, kuma sau uku tana kiransa bayan da tayi sallan asuba bai daga ba still, yanzun ma da ta tashi sae da ta kirasa sau daya nan ma no answer, zaune taga new Housemate dinta a Wan reading nook da aka tanadar a living Room din studying with a huge textbook dake gabansa, she had no idea ma ya shigo gidan, don bayan da tayi sallan asuba ta fito ta hada shayi ta sha da cookies a nan parlon sannan tayi karatu har zuwa bakwai na safe, daga nan ta shiga daki ta kwanta sai kuma yanzu da ta tashi feeling hungry, sau daya ya kalleta yana ci gaba da duba Textbook din gabansa yace "Good morning" Ta karaso cikin living room din a takaice tace "Ok" Ajiye wayarta tayi kan 1 sitter ta nufi kitchen, Ya daga kai yana kallon direction din da ta bi da harshen turanci yace "In baki yi breakfast ba, ga wani nan ki dauka....." Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kalli Centre table da yake nuna mata, ledan abinci ne kan table din duk da bata san wani kalan abinci bane a ledan, ta kallesa taga ya ci gaba da karatun da yake, girgiza kai tayi with no interest tace "No, tnx" Daga haka tayi wucewarta kitchen, ta fi minti uku tsaye kitchen din tana tunanin me zata yi, seeing her House mate sitted in the living room yasa ta zama uncomfortable to cook anything, hakan yasa kawai ta dauko kwalin cereals da bowl zata hada cornflakes, wayarta ta ji yana ring a parlor don tun jiya ta cire wayar a silent, bata san sanda ta saki both d bowl and the Cereal din hannunta ba ta fito daga kitchen din within few seconds, House mate dinta ya bi ta da kallo har ta nufi gun wayarta ta dauka da sauri, sai da gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, babu bata lokaci ta daga call din, zuciyarta na bugawa tayi masa sallama, jin shiru tace "Hello" kallon wayar tayi ta sake maidawa a kunnenta har sannan bata daina cewa Hello ba, House mate dinta dai ya ajiye Textbook dinsa gefe ganin yanda ta rude ya maida duk concentration dinsa akan ta, Khaleesat ta sake kallon Screen din wayar jin shiru Abdul ya ki ce mata komai kuma tana jin maganar mutane a background, marairaicewa tayi ta duka nan kasan living room din ta saka wayar a handsfree tace "I know u can hear me pls, don Allah kayi hakuri, i am making u this promise hakan bazai sake faruwa ba wallahi, don girman Allah kayi hakuri" Sai a sannan yayi magana da husky voice yace "Hold on to ur promise malama, sau biyar kenan kina missing call dina within a short period, are you out of ur senses or is anything wrong with ur brain?" Da sauri ta girgiza kai kamar zata yi kuka tace "Wallahi ina kitchen ina girki san da ka kira jiya, kuma...." Cutting dinta yayi yace "ke, bana bukatar jin komai daga gare ki, none of ur lies and excuses will convince me, naga kamar u are beginning to take me for granted this days.... Kinsan Allah kika sake missing call dina zaki sha mamakina wallahi cause it will take me nothing to be in America...." Hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Amma me yasa baka min uxuri?" Yace "Baza ayi uxurin ba, ni za ki gaya ma uxuri? A kanki aka fara karatu?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Wato ke kin fi karfin ki bude baki ki bada hakuri ko" Kasa cewa komai Khaleesat tayi don tun da ta daga kiransa ta fara basa hakuri bata kuma san wani hakurin yake nufi ba, A takaice yace "Anyway, i called to warn you to stop disturbing me with unnecessary calls, na biyu kuma ki ja ma kawar??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ki kunne she should never come into my DM and tell me nonsense again don zan dau mummunan mataki a kanta, ke kuma duk sanda yayi suiting dina i will call you, don't try calling my line again" Yana kai wa nan ya katse wayar, Khaleesat ta dinga kallon screen din wayar hawayen dake makale idonta ya gangaro, House mate dinta ya Wan yi murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login