Showing 141001 words to 144000 words out of 241367 words

Chapter 48 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1600

tsaye Momy ta kama hannunta suka fita daga dakin, can bangarenta ta tafi da ita har cikin Bedroom dinta sannan ta nuna mata bandakin dake dakinta tace "Ki shiga ciki kiyi alwala, amma kafin nan let's do a mother and daughter talk first my dear" Khaleesat ta daga kai tana kallon Momy, Momy ta nuna mata kan kujera tana mata murmushi tace "Get sitted Mamana" Khaleesat ta zauna kan 2 seater dake dakin Momy ta zauna gefenta tana facing dinta tace "Kar ki boye min komai mamata, ki daukeni tamkar mahaifiyarki, ki gaya min gaskiya wani abu ya shiga tsakaninku da Abdul ne tun bayan da ya dauke ki?" Sosai Khaleesat taji tambayar yayi mata nauyi a kai, hakan yasa ta kasa kallon Momy ta sunkuyar da kanta kawai, Momy ta kwantar da murya tace "Akwai dalilin da ya sa nake tambayarki haka ne Mamana, kar ki ji kunya ki boye min komai, open up to me" Girgiza mata kai kawai Khaleesat tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, Momy ta kamo hannunta tace "Kar fa ki ji kunyata ki boye min komai mamana, gaskiya zaki gaya min" a hankali Khaleesat tace "Gaskiya na gaya maki Momy" Momy ta dinga kallonta kamar dai bata yarda ba, can tace "To saboda me? Anya kuwa gaskiya kike gaya min Mamana?" Khaleesat bata dago kanta ba tace "Period nake yi ne" Momy tace "Toh kin gama yanxu?" A hankali Khaleesat tace "Daxu na gama" Momy ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "To naji dadin jin hakan mamana, don nasan irin daukan da Abdul ya tafi ya maki bayan dawowar ki daga makaranta, hakan bai ba iyayenki daman yi maki duk abubuwan da ya kamata su maki ba a matsayinki na budurwa kafin ki tare gidan mijinki, basu samu daman yi maki shirin xuwa gidan miji ba, amma tunda ya kawo ki nan in sha Allah zan maki duk abinda ya kamata diyata...." Ita dai Khaleesat tayi shiru har sannan bata dago kanta ba, Momy ta mike tace "Ta shi mu je bandaki ki ga...." Khaleesat ta mike tsaye ta bi bayan Momy har zuwa bandakinta, Momy ta nuna mata wani babban flask tace "Kin ga wannan flask din? To zaki dinga tsiyayan ruwan ciki ki sirka da ruwan zafi a pampo ki dinga tsarki da shi" Momy ta dauko wasu Sakakken sabulai dake nannade a leda ta mika mata tace "Sabulan nan su ma tsarki zaki dinga yi da ko wannensu, in kin yi sai ki ajiyesa inda kika ga na dauko yanzu don naki ne" Momy ta nuna mata wani roba dake rufe a bandakin shi ma tace "Wannan ma diba zaki yi kiyi tsarki da shi, kin ji?" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta dauko wani kwalba dake boye a cikin bandakin, Khaleesat dai bin ta kawai take da kallo ta bude flask din ta tuttule abinda ke cikin kwalban, sannan ta mike tace "Yauwa mamana, duk ki tabbatar kinyi amfani da su yanda nace, sai kiyi alwala ki fito" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Daga haka Momy ta fito daga bandakinta ta shimfida ma Khaleesat darduma, sannan ta zaune kan kujera ta jirata har ta fito daga bandakin, Momy ta mike ta nuna mata darduman tace "In kin idar da sallan kar ki fito, kiyi zamanki zan kawo maki abinci" Khaleesat tace "To Momy" Daga haka Momy ta fita daga dakin ta kulle da key ta tafi da makullin tana Wan murmushi, a corridor ta hadu da Abdul ya taho daga dakinsa bayan ya shiga bai ga Khaleesat a ciki ba, Momy tace "Har ka dawo masallacin Babana?" Yace "Na dawo, tana ina ne Momy?" Momy ta ja kunnensa tace "Yanxu abinda kayi ma yayarka ya kamata Babana? Kasan ta fa wani lokacin ba hankali ya ishi yayar taka ba, da sai kayi hakuri ka kyaleta da halinta kawai" Ya hade rai yace "Dukanta fa take kokarin yi Momy? A ina ta san ta ko kuma me tayi mata da zata zageta kuma ta nemi ta doketa??" Momy ta kama hannunsa suka shiga dakin ba?in dake kusa da su tana kallonsa tace "Ai na mata fada sosai Babana, yanxu ma haushin abinda kayi mata ne yasa tayi abinda tayi a parlor amma kayi hakuri kaji Babana" Yace "Naji, ina Khaleesat din take?" Momy tace "Bazan fa baka matar ka ba sai zuwa jibi in ma zaka cire ido a kanta ka cire, tun da baka bari iyayenta sun gyarata yanda ya kamata ba to ni zan gyarata" With confusion Abdul yace "Gyarata kamar yaya Momy?" Momy tace "Ka taSa ganin inda aka dau mace budurwa aka kai ta gidan miji haka nan? To fin karfin iyayenta da kayi kuma suna shakkar ka shi yasa suka baka ita haka babu yanda suka iya maka, amma a al'adar mu ta Hausa babu inda ake yin haka, ni kuma kaga bazan baka ita ba sai nayi mata duk abinda ya kamata na gyarata, in kuma rashin kunya zaka yi min to yi Babana, Khaleesah dai bazan baka ita ba sai zuwa nan da jibi in sha Allah, zan mata duk abinda ya kamata a matsayin ta na 'ya ta" Abdul ya kasa cewa komai yana kallon Momynsa, Momy tace "Mu je ka ci abinci" Bata jira cewarsa ba ta fita daga dakin, bin bayanta yayi ya fita amma duk tsaurin idonsa sai yaji nauyin ce ma uwar tasa komai, haka nan Momy ta dauko masa abincinsa da ta hada masa da kanta ta jera masa su a dinning sannan ta koma kitchen zata hada abincin Khaleesat, Abdul ya zauna kujeran dining amma ya kasa cin abincin, shi fa bai yi niyyar ma kwana gidan da Khaleesat ba don irin burin da ya ci a kanta yau ai sai Allah, nan da nan yaji ransa ya baci, ya mike ya shiga kitchen ya samu Momy ta sa mai aikinta ta jera ma Khaleesat abinci a tray, don irin abin da ta hada mata har ya fi na Abdul, Momy na kallon mai aikin tace "Tafi ki kai mata bangarena ki jirani ina zuwa" Mai aikin ta fita daga kitchen din da tray din, Abdul na kallon Momy a fusace yace "Toh wai menene yasa Meemah zata ce min Daddy ba shi da lafiya critically bayan ma ashe baya kasar?" Momy tace "To ai ganin likita yaje a Amurka, ko bai gaya maka bane? Karfe hudu na yamma jirginsu ya tashi, shi yasa kaji nake cewa baka taho da wuri ba don duk zatona zaka tarar da shi" Abdul yayi shiru yana kallon Momy, Momy tace "Ni dai bari in je wajen diyata, kar ka wani huce kan Meemah don ba ita ta hanaka matarka ba" Daga haka Momy ta bar sa tsaye a kitchen din, tsaye ta tarar da Mai aikinta a bangarenta tana jiranta don kofar a kulle yake, Momy ta bude mata suka shiga ciki, Mai aikin ta ajiye abincin gaban Khaleesat, Momy na kallon mai aikin wanda ranan ne ranan farkon da ta shigo mata daki tace "Toh fita ki ban waje...." Mai aikin ta fita da sauri ta kullo kofar, Momy tayi murmushi tana kallon Khaleesat tace "Ga abinci nan Mamata" Momy ta tafi ta dauko handbag dinta ciro wani kulli ta dawo kusa da Khaleesat ta bude kullin ta barbada mata abinda ke ciki a farfesun kayan cikin dake cike a bowl tace "Maza ki shanye har romon kin ji" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Momy ta tafi ta zauna kan kujera tana murmushi ta dau remote ta kunna TV din dakin, a hankali Khaleesat ke shan farfesun tunani iri iri na yawo a kanta, to yanxu kenan hakuri kawai zata yi da auren Abdul, since gaba daya family dinta sun nuna sun yi accepting auren, sannan ga Mum dinsa ma ta ga tana sonta, kilan zaman aure da Abdul a kaddarar rayuwarta yake, she should just accept it with good faith, most important of all gashi mahaifiyarsa na sonta, his sister won't be an issue tunda mamansa na sonta, kawai ta saka ma ranta salama ta amshi auren tunda haka Allah ya kaddara mata, Housemate dinta ne ya fado mata, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, da sauri ta sunkuyar da kai kar Momy ta gani cikin dubura ta dinga goge hawayen tana jin wasu masu zafi na sakkowa, sai da Momy ta tabbatar ta ci abincin sosai, sannan ta umarceta da taje tayi wanka ta tabbatar ta sake tsarki da duk abubuwan da ta nuna mata a bandaki, kafin Khaleesat ta fito Momy ta dauko mata kayan bacci da inner wears, Khaleesat ta shirya tayi sallan isha'i, Momy bata tashi barin dakin ba sai kusan karfe tara da rabi, bayan ta sa Khaleesat ta kwanta kan gadonta sannan ta kashe mata wutan dakin ta bata remote din Ac a kusa da ita, tayi mata sai da safe ta fita daga dakin, har ta kulle kofar ta sake budewa ta shiga tana kallon Khaleesat tace "Ko tashi kika yi zaki kama ruwa cikin dare kiyi tsarki da abubuwan nan fa Mamana kar ki manta" Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta kara mata sai da safe sannan ta fita ta kulle kofar da makulli ta sauka downstairs, Abdul kadai ne zaune parlor yana kallon kwallo amma kana ganinsa kasan ransa a bace yake, Momy tana kallonsa tace "Sai da safe Babana" Ciki ciki ya amsa mata, ta juya ta koma sama zuwa dakin da su Meemah suke, duk suka dinga kallon Momy bayan ta shigo, Aunty Karima tace "Ya dai Momy duk ta yi?" Momy tayi wani murmushi tace "Tun yaushe kuma" Meemah tace "Alhamdulillahi, shi Abdul din fa?" Momy tace "Shi ai dama a miyar shinkafa aka ce na zuba masa maganin, sai ruwan lipton, na kori mai aikin taje bakin pampo tayi wanke wanke shine na samu duk na zuba masa nasa" Meemah tayi murmushin mugunta tana gyara zama sanin Momy bata bin malaman banza, kai in malami yace zai amshi kasa da 1M a wajenta ma bata yarda da ingancin aikinsa ba, inda ake aikin da gaske take zuwa, ko da kuwa miliyan biyar zata kashe bata kyashi don tasan aiki na gaske ake mata.
[6/19, 8:55 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Washegari da safe bayan Khaleesat ta shirya cikin tsadadden Abayan da Momy ta bata, Momy ta gama hada mata shayin da take yi cikin cup tace "To zo kiyi breakfast din kar ya huce Mamana" Khaleesat bata ce komai ba ta karasa ta zauna kan darduman da aka jera mata breakfast din, Momy tayi murmushi tace "Idan farfesun bai isheki ba sai ki bude warmer ki ?ara, dankalin ma akwai saura a warmer in bai ishe ki ba" Ita dai Khaleesat kai kawai ta gyada mata, tana juya shayin gabanta a hankali da spoon din ciki, Momy ta koma kan kujera ta zauna tana kallonta tace "Duk da ma ina lura jiya baki wani ci abincin da aka kawo maki da yawa ba, ko maganin cin abinci zan sa a samo maki mamana" Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba ta dau shayin tana kallon ciki, sai tayi tunanin lipton din ne kilan ya fashe a cikin ruwan shayin, sipping din shayin tayi kadan ta ajiye sannan ta fara cin irish din, Momy dai kallonta kawai take kasa kasa, Bude kofar dakin aka yi Momy ta juya, ganin Abdul tace "Sai yanxu ka tashi Babana" Bai ce mata komai ba ya karasa ya zauna saman kujera, Khaleesat ta Wan kallesa taga kallonta yake, sauke idonta tayi a hankali tace "Ina kwana" Ya kauda kai yace "Lafiya" Momy tace "Ka tashi kaje kayi breakfast din ka" Yace "Momy za mu je shopping ne, bata zo da kaya ko daya ba" Momy na kallonsa tace "To wanda ka gani a jikinta yanxu kai ka siyo mata?" Shiru Abdul yayi yana kallon Momy, Momy tace "To har na tura ma Meemah kudi su je su yi mata siyayya ita da Karima tunda kai baka da ?ara" Mikewa Abdul yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Momy ta bi sa da kallon gefen ido, sai da Momy taga Khaleesat ta gama cin abinda zata ci na breakfast din sannan ta mike ta fita ta kira mai aikinta ta fitar da sauran abubuwan da Khaleesat ta rage, bayan mai aikin ta fita Momy ta bude bayan labulenta ta dauko wani karamin jarka ta kawo ma Khaleesat tace "Wannan tsumi ne Mamana, daga yanxu har zuwa dare nake son ki shanyesa gaba daya" Ita dai Khaleesat kallon jarkan take, Momy tace "Kin ji ai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Toh Momy" Momy ta dauka ta mayar bayan labule sannan tace "In zaki yi kallo sai ki kunna TV abun ki, bari in je zanyi bakuwa ban san ko ta iso ba" Khaleesat tace "Toh" Momy ta fita daga dakin ta kulle da makulli tana rike da makullin ta sauka downstairs don aminiyarta godiya ta kirata ta sanar mata tana hanya, tana shigowa parlor taga Abdul zaune dinning area da breakfast din da Khaleesat ta rage a gabansa, da karfi Momy ta kwala masa kira, ya juya yana kallonta, ta karasa wajen da mugun sauri tace "Banda abun ka ba ga naka a kitchen ba Abdul me zaka yi da wanda aka rage? Ko har kaci wannan din ne?" Abdul dake kallonta yace "Ban ci ba, amma menene idan na ci?" Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da sauri Momy ta kunduma mata wani ashar tace "Nan nace ki ajiye sauran abincin er iska kawai er neman jidali? Me yasa ke dakikiya ce? Wallahi zan kore ki fa a gidana na gaji da maganar da kike sa ni kamar kanwar uwarki, yau ga shegiyar mata kawai" Abdul ya kalli Momy yace "Ni fa nace ta kawo min nan, beside what is wrong with the food da bazan ci ba?" Momy ta mata tsawa tace "Dauka ki wuce ki ban waje guntuwar banza kawai" Mai aikin na ba Momy hakuri ta dauke jiki na rawa ta tafi kitchen da breakfast din, Momy ta kalli Abdul dake kallonta, yace "I want to understand meye da abincin da bazan ci ba Momy?" A takaice Momy tace "Kayan gyaran mata mana? Ko kai na mace ne?" Bata jira cewarsa ba ta bar wajen ta shige kitchen ya bi ta da kallo, Tuttular da shayin tayi a sink sannan ta juye sauran irish din da kwai da farfesun duk ta cakudesu waje daya tace "Gasu nan ki kai ma karnuka, in kuma kwadayin ki ya ja ki kika ci ke kika jiyo" Mai aikin ta risina ta amsa tace "Toh Hajiya" Sai da Momy ta jirata har ta dawo bayan ta kai ma karnukan can cage dinsu sannan Momy ta dau breakfast din Abdul ta kai masa kan dining din tace "Ga naka nan" Daga haka ta juya ta bar wajen, dai dai shigowar Godiya gidan, da fara'a Momy ke mata sannu da zuwa Abdul ya dauke kai kamar bai ganta ba don ya tsani matar with passion, tun asali dama baya gaida ta, Haka Momy ta ja ta zuwa sama tana cewa "Mu je ki ga surkar tawa ku gaisa" Da ido Abdul ya bi su har suka haura sama, Momy na isa kofar dakinta ta bude da makulli suka shiga, Khaleesat dake gyara gadon Momy ta mike tsaye tana kallonsu, Momy na murmushi ta kalli godiya tace "Kin ganta" Da fara'a sosai Godiya tace "Maa sha Allah, ai ko ga ta kamar balarabiya Maa sha Allah, sannu amarya, ya sunanki?" Momy na murmushi tace "Sunan Baabata gareta, Hauwa sunanta" Khaleesat ta zame kasa ta sauke idonta ta gaida Godiya, Godiya ta karasa kusa da ita ta dafata tare da Wagota ta zaunar da ita gefen gadon Momy tace "Lafiya lau diyata, ya bakunta?" Khaleesat bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Momy na kallon Khaleesat tace "Kin sha tsumin da nace ki sha kuwa?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Na sha" Momy tace "To maa sha Allah, Allah ya maki albarka Mamana, zuwa anjima sai ki kara sha kin ji" Khaleesat tace "To" Bayan few minutes Momy da Godiya suka fita dakin, Momy ta sake kulle kofar da makulli sannan ta cire makullin suka tafi wani daki dake sama, bayan sun shiga Momy ta kulle kofar tana kallon Godiya tayi murmushi tace "Duk tayi amfani da abubuwan babu gardama godiya, iya na jarkan nan ne kawai ya rage yanzu" Godiya ta zauna gefen gado tace "To madallah, shi ma Abdul din duk kinyi yanda aka ce kiyi da na sa?" Momy tace "Kwarai kuwa" Godiya tayi wani murmushi ta bude handbag dinta ta ciro wani babban laya bakikirin da shi ga er karamar kwado a jiki ta mika ma Momy tace "To aikin karshe kenan wannan Hajiya, Malam ya ce ki samu inda kika san baza a taSa tono sa ba ki binne a cikin gidan nan" Momy ta zauna gefenta tana murmushi ta amshi layan tace "To laya nawa na binne gidan nan ba a tono ba godiya, ai wannan karamin aiki ne a wajena don ba sabon abu bane" Godiya tace "Yauwa, bayan kin binne Malam yace ki basa yarinyar kawai, wallahi yace min in har ta wuce sati biyu Abdul bai rabu da ita ba to bazata wuce sati biyar ba a gidansa" Fara'ar fuskar Momy ya bace tace "Har sati biyar Godiya? Ni da yace min sati daya kacal a waya" Godiya tace "Halan bai gaya maki irin abubuwan dake ?an dan ki ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  bane? Da yaya ma aka samo kansa har asirin nan yayi tasiri? Ai abubuwan ?an Abdul sun fi karfin wani asirin wallahi kiji in gaya maki" Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "An taSa gaya min haka da dadewa wallahi, don ni akwai malamin da yace min ma yanda asiri ke cin ubansa shi sai an wahala asiri zai ci sa" Godiya tace "To wallahi Malam sai da ya tura masa aljanu don ma ki ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login