Showing 75001 words to 78000 words out of 241367 words

Chapter 26 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1561

yace "Why? Meye da dakin Halysaah?" Tayi shiru bata ce komai ba, Calmly yace "C'mon Halysaah wannan ma ai yafi wancan da kike ciki" Yana murmushi ya kare maganar, ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya ajiye mata kayanta da wayarsa yace "If you need anything just call my line" Ta gyada masa kai, ya nuna mata hanyar bandakin dake babban dakin yace "In zaki yi sallah ga bandaki can" Nan ma dai ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita daga dakin ta koma ta zauna, gajiya tayi da zama tana son kwanciya amma ta kasa kwantawa saman gadon, ita kanta ta rasa dalili, can dai ta zamo kasa a hankali ta kwanta saman lallausan carpet dake dakin ai ko nan da nan bacci ya dauketa, throughout ranan haka Khaleesat ta yini a dakin ita kadai, tun da Housemate dinta ya kawo mata lunch har lokacin magrib yayi bai dawo dakin ba, sai Cook din gidan ne ya kawo mata dinner, tana zaune saman darduma bayan ta idar da sallahn isha taji an bude kofar dakin ta daga kai, sosai gabanta ya fadi ganin AJ, ta sauke idonta daga kallonsa, shi kam ko kallon inda take bai yi ba fuskarsa a murtuke ya tafi ya dau second phone dinsa da laptop, ya bude press dinsa ya dau pajamas dinsa sannan ya fice daga dakin, sai a sannan ta daga kai ta bi sa da kallo tana mamakin abinda ya shigo yi, don bata san me ma ya dauka a dakin ba, har sannan bata kawo cewar dakinsa bane, har ta fara bacci Jay ya shigo dakin da sallama, ta mike zaune daga kwancen da take a kasa, da mamaki yake kallonta yace "Me yasa kika kwanta a kasa Halysaah?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "C'mon don't do that pls, ga gado zaki wani kwanta a kasa" Ta kalli gadon tace "Zan kwanta" Yace "Good, hope u need nothing?" Tace "Bana bukatar komai" Yace "Alright then, good night" A hankali tace "Thank you" ya mata murmushi yace "In kashe maki wutan dakin ko a maida maki dim light?" Tace "Dim light" Ya mayar mata wutan mara haske sosai sannan ya juya ya fita daga dakin, bayan fitarsa ta koma tayi kwanciyarta a kasa, ita gani take kamar master bedroom din gidan ne, may be that's why she is not comfortable, wajen karfe dayan dare dakin yayi sanyi sosai amma taki daukan duvet din saman gadon ta rufa, kawai ta lullube da Hijab dinta, she was so cold gashi Safiyyah bata hado mata kayanta da Sweater ba, tana ta kwance ta kasa bacci saboda sanyin da ya dameta sai juye juye take taji an bude kofar dakin, a hankali ta sauke Hijab dinta kasa kadan tana son ganin wanda ya shigo don har kanta ta rufe, taga AJ ne ya shigo, kallo daya yayi mata ya tafi daukar abinda zai dauka, zaro ido tayi bayan ta zargi anya ba dakinsa bane nan kuwa, sai bayan da ya fita taji ya kullo kofar ta mike zaune tana sake bin dakin da kallo with shock, dumin da taji dakin ya fara dauka gradually ne yasa ta gane ya kunna mata heatern dakin, ta koma a hankali ta kwanta sai da dakin yayi dumi sannan bacci ya dauketa..... Washegari da safe Jay na zaune main parlor tare da Abba da Aunty, cikin nutsuwa Abba ke masa magana amma shi gaba daya hankalinsa na sama kan Halysaah don tun da gari ya waye bai je wajenta ba, kawai dai Cook din gidan ne ya kai mata breakfast, AJ ya shigo parlon daga reading nook da yake zaune ya nufi dinning area zai yi breakfast, Abba ya bi sa da kallo, after a while yace "Baka yi breakfast din bane" Jay ya Wan kalli AJ, Aunty kanta kallonsa take ita ma, without turning back AJ yace "Ban yi ba" Aunty tace "To ai naga cook din gidan ya kai maka Breakfast din sama daxu" Ko tankata AJ bai yi ba ya tafi dinning ya zauna, Abba na kallon Jay calmly yace "Is he Okay?" Jay ya Wan shafa kai yayi kasa da murya yace "I think supervisor dinsa ne bai yi approving Article din da yayi publishing ba tukunna" Aunty tace "To banda abun sa ai ba wani abu bane he should add in more effort to his work kawai" Shi dai Jay bai ce komai ba, haka shi kansa Abba, after a while Jay ya mike ya tafi sama, direct part din AJ ya nufa bayan yayi sallama ya tura kofar dakin ya shiga. Wajen la'asar AJ na zaune parlorn dake sama, gaba daya he look moody, dama jiya da daddare a nan parlorn ya kwana tsabar takaici, har zuwa yanzu yaki ce ma Jay komai a gidan, Jay kuwa ko a jikinsa don ko kallonsa ma baya yi, su biyu ne kadai a gidan don Abba ya fita tare da Aunty da autarta zuwa gidan wani prominent friend dinsa a garin, da yake gobe da safe za su bar kasar zuwa Nigeria, AJ ya gyara zama yana bin Jay da kallo trying to be sure of what he is holding in his hand, he was very shock ya dai bi sa da kallo har yaga ya nufi bangarensa, ya tallabi chin dinsa yana girgiza kafa, sai bayan da Jay ya fito for the first time since yesterday AJ yace "Wallahi i will never forgive you for these Jawwad, i promise you am not forgiving you" Jay dai ya dake bai yi dariyar da ya basa ba, kuma yaki tankasa yayi wucewarsa ya bar sa zaune a gun, da daddare Khaleesat na duba laptop dinta Jay ya shigo dakin da sallama ta daga kai tana kallonsa ya zauna kan kujeran dakin yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya sauwake, amma ki tabbatar kin sha maganin so that u get enough night rest" Tace "Zan sha" Yace "Alright Good night Housemate, bacci nake ji" Ta Wan yi murmushi tana kallon agogo dake nuna karfe goma tace "Ai baka ma yi da wuri ba" Yayi murmushi kawai yace "Saura kar ki kwanta saman gadon yau" A hankali tace "Zan kwanta" Yace "Good" Daga haka ya fita daga dakin, shi kansa yasan tunda ta dawo gidan yake tauye ma kansa bacci, kuma ba wai baccin baya damunsa bane kawai daurewa yake yi, har ciwon kai yake yawan yi yanzu saboda baya bacci sosai, Khaleesat ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan ta mike a hankali ta dauko maganin da ya kawo mata daxu ta sha sannan ta kwanta saman gadon, amma fa a dar dar take saman gadon, Jay na isa parlorn dake sama ganin AJ kwance kan kujera yana danna wayarsa yace "Do you care sharing my room with me today?" AJ yaki tankasa yana danna wayarsa, Jay ya daga kafada yayi wucewarsa dakinsa, after like an hour AJ ya mike zaune jin muryar Abbansa, Abba dake kallonsa yace "Is everything Alright Ahmad? Why are you lying down on the Couch?" AJ ya fara sosa kai yace "Eh yanzu zan tafi daki Dad, ban san sanda bacci ya daukeni ba" Yana fadin haka ya mike tsaye ya dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta juya jin an bude kofa don ba bacci take ba, yana shigowa dakin kuma ya kulle kofar ya tsaya nan bakin kofar, rufe har kanta tayi da duvet, ya tafi gaban madubi ya tsaya yana tunanin Jay bai taSa cutarsa ba irin na wannan lokacin, sosai abun nan ya tsaya masa a rai, ita dai Khaleesat tana ta sauraren taji ya bude kofar ya fita daga dakin amma taji shiru, hakan yasa ta sauke duvet din kanta a hankali suna hada ido ya watsa mata kallo yace "Meye kike kallona?" Ta wani kallesa, sai kuma ta juya masa baya bata ce komai ba, after almost 5 minutes ya bude kofar dakin ya fice, tsabar yanda bai yarda da neatness din duk dakunan dake gidan ba ya sa ya gwammace ya kwanta a parlor instead of going into any of the room. Da Asuba Jay ya fito dakinsa kenan zai sauka downstairs su yi sallah da Abba, tunda Abba ya zo tare suke sallah amma banda AJ da baya saukowa ayi sallan da shi sai dai yayi shi kadai a sama, Jay ya hadu da Abba yana haurowa sama, Abba yace "This shows baku sallah tare a gidan nan Jawwad, ma'aikatan gidan nan guda biyu duk Musulmai ne, ga ka ga Junaid, amma ace baza ku hadu ku yi sallah ba?" Da sauri Jay yace "Muna yi Abba..." Abba bai ce masa komai ba ya nufi bangaren AJ, Jay ya buda ido sosai, sai kuma ya bi sa da sauri yace "Zan kira maka shi Abba..." Abba yace "Jiya da nace ka kirasa ya sauko?" Jay ya kasa cewa komai, duk tunanin Jay za su ga AJ a Parlor a kwance amma sai yaga baya parlon, nan hankalin Jay ya tashi ya tsaya a inda yake tsaye ya kasa ci gaba da bin bayan Abba, he wish Junaid bai cire code din nambobin kofar dakinsa ba, Abba na tura kofan sai ga AJ da ya shiga bandakin dake parlorn da suka baro yayi alwala ya taho zai dau pray mat, shi ma zaro ido yayi yana kallon Abba kamar yanda Jay ma ya tsaya kallonsa, AJ ya juya suka kalli juna da Jay, tunda Abba ya kunna wutan dakin ya tsaya for like a minute bakin kofar dakin yana kallon Khaleesat dake bacci, sai kuma ya juyo ya fito closing the door gently, Daga AJ har Jay suka sunkuyar da kai a tare kamar munafukai, Abba dai sai kallon AJ yake, after 30 seconds of silence, speaking Calmly Abba dake kallon Jay yace "Abinda ke faruwa gidan nan kenan Jawwad, and you told me nothing about it?" Jay ya kasa cewa komai kuma ya kasa barin su hada ido da Abba, cikin nutsuwa babu fada Abba yace "Magana nake maka Jawwad" Da kyar Jay ya girgiza kai yace "I know nothing about it Abba" AJ ya bude baki yana kallon Jay da yaki kallonsa, Abba ya gyada kai yace "Ohk then, ku mu je mu yi sallah lokaci na wucewa" Daga haka ya juya ya bar su tsaye a wajen, Jay ya bi bayan Abba da sauri, AJ ya bi sa da kallo baya ko kiftawa, tuni har Abba ya sauka downstairs hakan yasa Jay ya tsaya Parlor sai ya tuna tuggun da AJ ya hada masa gun Hadeeyah just 3 days back, bai san sanda dariya ya taho masa ba, sai ga AJ da jikinsa yayi sanyi ya shigo parlon yana kallonsa, hakan yasa Jay ya danne dariyarsa ya hade rai ya sauka downstairs da sauri, AJ ya bi sa da kallo, sai kuma a hankali ya zauna saman kujera ya kai hannunsa baki, ganin abinda Jay yayi masa yake kamar a mafarki, bai taSa shiga shock irin na wannan lokacin ba. Da safe kamar babu abinda Abba ya gani a gidan don bai sake masu maganar baz kuma da alama ko Aunty bai gaya ma ba, Jay ma yasan bazai taSa gaya mata ba, karfe sha daya jirginsu zai tashi zuwa Nigeria don haka har sun gama shirin tafiya Airport, Abba ya kalli Jay yace "Junaid bai sauko yayi Breakfast ba ko an kai masa sama ne?" Jay yace "I don't really know" Abba ya dau wayarsa ya kira AJ, ba a dau lkci ba sai ga AJ ya sauko parlor shi dai ya kasa hada ido da Abbansa, Abba na kallonsa yace "Kayi breakfast ne, naga baka sauko ba" Without looking at his Dad yace "Na yi" Abba yace "Ohk, za mu tafi airport ne yanzu, get ready" a hankali AJ yace "Ohk" Daga haka ya juya ya koma sama, sai da AJ ya fara zaunawa a parlon sama for almost 5 mins, gaba daya jikinsa a sanyaye yake, gashi ya tsani shirun Abbansa don ba alkhairi bane shirun, gwara ace ma fada yayi ta masa ba kakkautawa da wannan basarwan da yayi kamar bai ga komai ba, his next move might not be funny, Jay ya cucesa, bai taSa zaton haka daga Jay ba, to ko yace ma Abba bai santa ba ta yaya zai yarda da shi tunda a dakinsa ya ganta ba dakin Jay ba, ganin bata lkci kawai yake ya mike yana tafiya a hankali ya tafi dakinsa don dauko kayan da zai sa, yana shiga dakin Khaleesat na fitowa daga bandaki da hijab dinta har kasa ta fito wanka, ya wani kalleta daga sama har kasa fuskarsa a daure, ita dai tunda suka hada ido ta dauke kanta bata sake yarda ta kallesa ba tana dai tsaye hanyar shiga bandakin, ya dau kayan da zai dauka ya karasa gaban madubi ya dau tsadadden turarensa ya fice daga dakin, ta wani kyabe baki ta karasa shigowa cikin dakin. Har Abba suka isa Airport bai ce ma AJ komai ba akan daxu da asuba, kuma da alamar babu abinda zai ce masa, he was just speaking about something different in the car, a haka suka rabu normal normal a airport kamar babu komai, AJ yaki jiran Jay ya ja mota ya bar airport din ya kama hanyar gida, dole sai Uber Jay ya samu da zai maida shi gida, ko da ya isa gida ya ga AJ zaune a compound da non alcoholic wine a gabansa trying to use it to calm himself down at the same time trying to figure out wani hukuncin Abbansa zai ce zai dauka a kansa.....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H? [5/26, 9:45 AM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat felt so much relieve after leaving AJ's room, tana biye da Jay ta koma dakin da take, ba tare da Jay ya kalleta ba bayan ya ajiye laptop dinta dake hannunsa yace "Kin ji sanda aka bude kofa da asuba ne?" Khaleesat na kallonsa ta girgiza kai tace "I am not sure, may be ina bacci sannan, banyi bacci da wuri ba" Yace "Ohk" Tace "Why are you asking?" Ya juyo yana kallonta, ya Wan mata murmushi yace "Nothing" Tace "But ai frnd din ka yana shigowa ya dau stuffs dinsa wani lkcn" Jay yace "Ohk" Har ya juya sai kuma ya sake dawowa yace "Kince baki yi bacci da wuri, ciwon kan ke damunki har yanzu?" Ta girgiza kai tace "A'a, kawai baccin ne dai bai zo ba" Yace "Ohk" Khaleesat ta bi sa da ido har ya fita daga dakin sannan ta zauna gefen gado a hankali, har cikin ranta take jin kamar ta jawo ranan talata, she is so tired tana bukatar kawai ta ganta kusa da Ummanta, she need her Mom's hug, Jay na fita ya kira ma'aikatan gidan su gyara ma AJ dakinsa, Jay made sure the workers left nothing untouched a dakin duk da babu abinda dakin yayi, amma irin gyaran da aka ma dakin da bandakin ba na wasa bane, sai da ko ina ya dawo yana sparkling tsabar gyara sannan Jay ya koma downstairs, amma still a ranan ma AJ bai kwana dakin ba, yayi kwanciyarsa a parlor kan kujera. Washegari which was monday AJ na zaune usual spot dinsa a compound da Coke din gwangwani a gabansa, har a sannan yaki ce ma Jay komai a gidan, not even Jay hatta ma'aikatan gidan duk ba wanda yake yi ma magana he is just keeping straight face, Jay ya fito daga cikin gida ya karasa har inda yake zaune, ko kallon direction dinsa AJ bai yi ba yana juya counter din hannunsa, Jay na kallonsa yace "Abba wants to speak to you" Yana fadin haka yace "Abba gashi nan" Ya ajiye wayar gaban AJ, Calmly Abba yace "How are you doing Junaid" AJ ya sauke idonsa ya gaida Abba, Abba ya amsa yace "You didn't call to know if we arrived safely" AJ yace "Ayi hakuri" Abba yace "It's fine, yaushe za ku dawo hutu" AJ yace "Ran Thursday zan dawo in sha Allah" Abba yace "What about Jawwad" A takaice AJ yace "I don't know" Abba yace "Hand the phone over to him" Jay ya dau wayarsa sitting in one of the chairs beside AJ yace "Na'am ina ji Abba" Abba yace "Kai yaushe zaka dawo" Jay ya Wan yi shiru, sai kuma yace "Probably next week in sha Allah" Abba yace "Ohk Allah ya kai mu, earlier today you said you have something to tell me unfortunately ina tare da ba?i a lkcn, so what is it Jawwad" Jay ya Wan shafa kansa thinking of where to start, can dai yace "Abba dama it's about the girl u saw yesterday" Abba yayi shiru at first, sai kuma "Ohk, what about her?" Jay yace "Abba ni ne na kawota gidan ba AJ ba, she is a student of John Hopkins also, she is having issue with House rent and she's writing exam, so shine kawai na kawota gidan nan zuwa sanda zata gama jarabawan...." Abba ya dakatar da shi yace "Did you and Junaid birth me or i birth you both?" Jay ya girgiza kai da sauri yace "Billah Abba i am not cooking up stories, believe me, all what i am saying is the truth ai kasan bana maka karya Abba, kawai dai ni na kai ta dakin AJ ne without even his knowledge cause Aunty will definitely see her in the house, part din AJ ne kawai nasan bazata shiga ba, kuma because of this... AJ parlor ya dawo yake kwana, wallahi babu komai tsakaninmu da ita kawai taimako ne, you can even speak to her to confirm ranka ya dade" Abba yace "If she is having rent issue don menene baza ku bata kudin hayan ta biya ba ko kuma ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login