Showing 174001 words to 177000 words out of 241367 words

Chapter 59 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1620

kalli Khaleesat tace "Ta yaya za ki fiddo kudaden a account din ki Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Sai naje banki, bani da Atm card, kuma kudin bazai fita lokaci daya ba...." Momy na mata matsiyacin kallo tace "Sai ki tashi ki tafi bankin ai don wallahi kudaden nan baza su kwana a account din ki ba yau, da niyyar ki kin ci bulus tunda ubanki ne ya nema masa kudin ba" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, ita har sannan ta kasa daina mamakin matar nan, kai tunda aka haifeta ma ita ba a taSa shayar da ita ruwan mamaki yanda mahaifiyar Abdul ta shayar da ita ba, yau sati daya da sakin da Abdul yayi mata amma kullum in ta tashi sai ta zauna tayi mamakin uwarsa ganin abun take kamar Drama, ba ayi ranan da zai zo ya wuce da Momy bazata fado mata ba, bata taSa san akwai mutane irin Momy a rayuwar nan ba, muryar Mama Zubaida taji tace "Ai ba zama zaki yi kina zazzare ido ba kamar barauniya, tashi za ki yi ki kama hanya ki tafi banki ki fiddo masu da kudadensu tunda ba gadon Abdul din gare ki ba kuma ba kudin tsohon ki bane, duk wani abu na rashin gaskiya dake da uwarki da kanwarta gaba ku ka basa ba baya ba, banda haka ta yaya za kuyi shiru da makuden kudadensa har Miliyan goma a account dinki? So ku ka yi ku danne kudin ko yaya? Don ma kun samu masu hakuri da kawaici da wasu ne idan ba a zo da motar yan sanda an tafi da ku ba ku ce bani ba, wannan ai rashin gaskiya ne da rashin tsoron Allah kiri kiri, duk kun yi mukus da bakin ku za ku cinye miliyan goma ga banza ta samu" Aunty Farida ta juya tana kallon Mama Zubaida, sai kuma ta nufeta tana cewa "Zubaida idan ban zubar maki da hakora a gidan nan yau ba ki ce bani ba, don kaza kazan ki akwai tsinannen da ya sako bakin ki? Uwarki muka yi ma rashin gaskiya ko ubanki?" Mama Zubaida tayi wani shewa tana tafe hannu tace "To yau kika saba Farida? Ai ke fitsararriya ce dama mara mutunci mara kunya shi yasa ga ki har yau duk kyan ki kin rasa mashinshini sai dai kiyi tuwo tuwo a garin legas kina hadawa da karuwanci, waye bai san wannan ba?" Aunty Farida zata cakumo Mama Zubaida Mama Shatu ta shige tsakaninsu tace "Ke yanxu Farida Zubaida sa'arki ce zaki dinga zaginta haka ta uwa ta uba don kawai tana kishiyar yayarki? Daga dai ta fadi gaskiya banda Wan Adam baya son gaskiya?" Aunty Farida tayi wani wurgi da Mama Shatu sai ga ta a kasa timmm, tuni Mama Zubaida ta shige dakinta ta kulle kofarta da sakata tana cewa "Haka kawai ki shafa min bakin jini irin na ku? Allah ya sauwake in yi dambe dake Farida, ku je can ku ji da rashin sa'ar ku a rayuwa, ku kenan daga wannan iftila'in sai wannan bala'in, ko wani fitinar duniya a kan ku ya kare, daga wannan sai wannan, Allah kadai yasan laifin da ku ka tafka a kasar ku, kilan ma ta zina aka sami ke da yayar taki, ga bakin jini da rashin sa'ar ku ya shafi Malam ya talauce" Da kafa Aunty Farida ta hambare uban miyan da Mama Zubaida ke yi na abincin siyarwanta, miyar duk suka malale kasa, shinkafar ma dake cikin kwando ta kifar da shi a kasa tana zagin Mama Zubaida ta uwa ta uba, Mama Shatu ganin yanda aka yi watsi da kayan sana'an Mama Zubaida ya sa ta ja bakinta tayi shiru ta tafi gun nata miyan ta zauna tana cewa "Hakuri kawai za kiyi Farida, hakan ba dadi kam" Momy ta rike haSa tace "Alhamdulillahi da na yi iya bakin kokarina na ganin ban hada iri da gayyar tsiya ba, ku kuga wannan tsiya haka kamar 'yar tasha, ga talauci ga tashanci, Abdul ya so ja mana abun fade a dangi Allah ya takaita min abun, kuma ba dai kun ce kudade na banki ba, to zuwa yau da daddare in ga alert din Miliyan goma, in kuwa ba haka ba gobe da sassafe za ku gan ni a gidan nan ba kuma zuwan lumana zan yi ba, ai shi ramin karya kurarre ne, kuma ko kwabo daya yayi ciwon kai a kudaden nan wallahi sai an daure er ku..." Momy na kai wa nan ta bude handbag dinta ta ciro takarda dauke da account details dinta ta jefa ma Khaleesat sannan ja tawagarta suka yi waje tana cewa "Haka kawai Meemah zata ja min bala'i ta hada ?ashi da wannan iri na fitina, irin tsiya, to kiyi dambe da ita ki ce kin yi dambe da wa? Kina ganin yarinya kamar mahaukaciya, A'a wallahi Allah ya maki tsari" A haka duk suka fita daga compound din, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma komawa dakinta tayi tayi tagumi ranta ba dadi, ita kam ta gode Allah da jarabawa iri iri, daga wannan sai wannan, Khaleesat ta dau takardan da Momy ta jefa mata ta juya ta shiga dakin Umma hawaye na zuba idonta, Aunty Farida kuwa bata fasa zage su Mama Zubaida da Mama Shatu a tsakar gida ba, Mama Zubaida taki fitowa kuma taki tanka Aunty Farida, Mama Shatu kuwa tayi tsit kamar bata san da wa Aunty Farida take ba, daga karshe bayan Aunty Farida tayi masu wankin babban bargo ta shige dakin Umma tana huci, Umma ta daga kai tana kallonta tace "Yanxu ban isa ince ki bari ki bari ba Farida?" Aunty Farida ko tanka Umma bata yi ba ta dau Hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace "Ki tashi ki shirya mu tafi bankin" Mikewa Khaleesat tayi tana goge idonta ta dau hijab dinta ta saka, a haka suka kama hanyar banki da Aunty Farida, amma suna isa bankin suka tarar an tashi aiki sai ran Monday don karfe hudu har da rabi a lokacin, Aunty Farida na kallon Khaleesat bayan sun fito bankin tace "Goben karfe nawa ne tafiyar naku?" A hankali Khaleesat tace "Flight din karfe daya zuwa Abuja, daga Abuja kuma jirgin yamma ne" Aunty Farida tace "Kuma bazai yiwu a daga tafiyar ba Khaleesat? Kinga banki dole fa sai Monday idan Allah ya kai mu" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, ita kanta she is just confuse bata san yanda zata yi ba. A haka suka koma gida kusan karfe biyar da rabi, Umma na kallonsu tace "An tashi a banki ko?" Aunty Farida bata ce komai ba ta cire hijab dinta ta nemi waje ta zauna, Khaleesat ta zauna tana kallon Umma tace "Banki sai ranan litinin, sun tashi yau" Umma tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Kema kin san bai amshi kudinsa ba me yasa zaki yi shiru har na sati daya Khaleesat? Yanxu da kinyi magana tun yaushe za a san yanda za ayi a cire kudin a mayar masa kayansa, yanxu rashin mutuncin da suka zo suka mana makota na ji ina amfanin sa?" Aunty Farida tace "A'a ta min maganan kudin fa ranan Alhamis, a lkcn ma tayi zaton yau ne tafiyar ashe gobe ne, kuma kema kinsan Khaleesat bazata taSa ko biyar a kudin nan ba tunda ba nata bane, kawai dai dama matsiyata ne yan iska daga Abdul din har iyayensa" A hankali Khaleesat tace "In ma an cire kudin an basu bazan iya tafiya babu kudi a account din ba, don baza a bari in shiga kasar ba, they wilk see i am not financially capable idan babu kudi a account dina, shi yasa ma ya bar kudin a account din all this years" Aunty Farida tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, haka ma Umma da ta rafka tagumi tun shigowarsu, after a while a hankali Umma tace "Ni tsorona kar su dawo goben da suka ce bamu san kuma da me za su zo mana ba" Aunty Farida ta mike tace "Sai su zo su amshi babu tunda su yan iska ne" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma na kallonta a hankali tace "Kiyi hakuri Jiddah, wataran duk hakan zai zama labari, Allah ya bamu ikon cin jarabawan mu, in ma kin koma makarantar in ma baki koma ba duk yanda Allah yayi dai dai ne" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata ta mike ta dau tsintsiya zata yi gyaran dakin Umma tana goge hawayen dake sauka idonta....
[7/2, 6:55 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat har ta fara bacci wajen karfe goma da rabi Aunty Farida ta tasheta tana mika mata sabuwar wayarta dake vibrate, mikewa tayi zaune tana gyara hulan kanta ta amshi wayar taga Safiyyah ce ke kiranta, Wagawa tayi ta kai kunne, daga daya bangaren Safiyyah tace "Ko har kin fara bacci ne" Khaleesat tace "Um, da wuri na kwanta ne" Safiyyah tace "Ayya sorry for waking you up, dama Housemate din ki ne yace in tambayeki wani account zai maki funding, cause nasan definitely Abdul ya amshi kudinsa dake account din k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ko?" Khaleesat tayi shiru ta kasa ce ma Safiyyah komai, har sai da Safiyyah tace "Hello" a hankali Khaleesat tace "Ina jin ki Sophie" Safiyyah tace "To naji kin yi shiru" Khaleesat ta daga kai ta kalli Aunty Farida dake kallonta, goge hawayen dake makale idonta tayi cikin sanyin murya tace "Daxu Mom dinsa suka zo za su amshi kudin, ni kuma bazan iya transfer ba kuma bani da Atm card, shi ne ta ajiye min account number wai in tura masu kudin yau, and today is Friday, mun je banki sun tashi, yanxu tace zata dawo gobe da safe idan ban tura mata kudin ba" Safiyyah dake ta sauraron Khaleesat cikin bacin rai tace "Allah ya sauwake, ke kiji wani tsiya don girman Allah, akan miliyan tara ne ko goma uwar ta kamo hanyar gidan ku da kanta? Can you imagine fa? A'a gaskiya sai yanxu nake sake tabbatar da su Abdul were once poor in this life, all of a sudden kawai Allah ya basu arziki sama ta ka, nobody can change this my perspective wallahi, banda tsiya meye kuma miliyan Goma a irin yanda suke show casing arzikinsu, what is 10M to them? wannan ai abun kunya ne a garesu, Ke kuma maimakon ki kirani tun daxu ki gaya min shi ne kika yi shiru? Yanxu ba don Housemate dinki yayi reason cewar dole sai da sufficient fund a account dinki za ki iya tafiya ba da shiru zaki yi kenan sai gobe da za mu tafi ki gaya min? Allah ya sauwake, ita kuma uwar Abdul wallahi matsiyaciya ce er wahala, har ta iya kamo hanyar Mariri akan kudin da ba ita ta bada ba, in kin bibiya ma Wan nata bai sani ba ta kamo hanya, ki min sending shegen account din nata da ta bar maki" Daga haka Safiyyah ta kashe wayarta, Khaleesat ta jawo handbag dinta tana goge hawayen da ya taru idonta, ta bude jakar ta ciro takardan account details din da Mom din Abdul ta bar mata, tura ma Safiyyah account din tayi ta message sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta koma ta kwanta, ita dai Aunty Farida bata ce komai ba don duk ta fahimci conversation din nasu. Washegari Khaleesat na idar da sallan asuba kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tayi picking call din ta kai kunne, a hankali tace "Good morning Safiyyah" Safiyyah tace "How was ur night?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah tace "Na tashi yanzu naga Housemate dinki ya tura min receipt din 10M da ya tura a account din da kika turo min jiya, he sent the receipt via my WhatsApp, ba ki yi activating WhatsApp dinki ba da sai in tura maki ki tura masu, sai su san su ne matsiyata" Kasa cewa komai Khaleesat tayi hawaye ya fara sauka idonta, Safiyyah tace "Ko kuma bari in tura ma Aunty Farida receipt din kawai since she is on WhatsApp" Khaleesat ta gyada mata kai da kyar tace "Nagode" Safiyyah tace "Kuka kike yi ko? Kina da aiki, ni dai sai anjima, make sure ki fito gida da wuri kin san Flight dinmu zuwa Abuja karfe daya ne" Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Umma na kallon Khaleesat tace "Wai me ya faru?" Khaleesat na share hawayen da yaki tsaya mata tace "Ta ce ya tura masu kudin ne, zata tura ma Aunty Farida receipt" Shiru Umma tayi ta rasa abun cewa, kana ganinta kasan jikinta yayi sanyi sosai, Aunty Farida dake zaune kan darduma tace "Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi ya kare sa sharrin masu sharri, Allah ya mayar masa da dubban abinda ya kashe maki, yanda ya rufa maki asiri Allah ya rufa masa shi ma" a hankali Umma tace "Ameen ya Allah" Mikewa Khaleesat tayi don dama ta gama azkar din da take yi, ta kwanta kan gadon Umma har sannan hawaye yaki dena sauka idonta. Da safe wajen karfe tara Aunty Farida na bude WhatsApp dinta taga Receipt din da Safiyyah ta tura mata, tana kallon Khaleesat tace "Yanxu ta ya za a tura masu receipt din su gani Khaleesat?" Umma tace "Ba kina da number Abdul din ba? Ki tura masa ta WhatsApp din kawai" Khaleesat dake cin wainar da Umma ta sa aka siyo mata ta daga kai ta kalli Umma, sai kuma ta girgiza kai a hankali tace "A'a Umma kar a tura masa, ba sun ce za su zo da safe ba, in sun zo sai a nuna masu receipt din" Umma tace "Saboda me? Ba kudinsa bane kuma shi ya aiko su karbar masa?" Aunty Farida ta kalli Umma tace "Suka aiko kansu dai Umma, don Abdul dai a yanda yake ji da kansa bazai ce a zo a amsar masa miliyan goma ba, dama sun san da kudin kuma kilan sun san bazai ce zai amsa ba shi yasa suka taho su amsa" Khaleesat tace "Shi yasa nace kar a tura masa receipt din, don nasan ba shi yace su zo ba" Umma tace "To ko ma dai yaya ne ai kudinsa ne, ni bana son su sake dawo mana nan su mana tijara makota na ji shi yasa nace a tura masa kawai, idan yaso sai yayi ma uwar tasa magana tunda zai ga a account dinta aka tura kudin ai, tonan asirin bai ishe mu bane da har za mu sake yarda su dawo gidan nan" a hankali Khaleesat tace "Umma ni bana son abinda zai sake hadamu magana da shi balle har yace zai dawo da wata magana kuma" Aunty Farida tace "Ya dawo da wani magana? Saboda ba shi da hankali zai dawo da wata maganar? Ai yanxu ba mu da abinda zai sake hadamu da shi da ya wuce kudin nan nasa, saki uku ya aiko maki balle ace zai dawo da wata magana" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya tace "Aunty ba fa shi ya aiko da takardan sakin nan ba, ba rubutunsa bane, iya saki daya yayi min" Daga Aunty Farida har Umma kallonta suka dinga yi, a hankali tace "Shi yasa bana son a tura masa receipt din balle har hankalinsa ya dawo kan mu..." Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya tace "To Allah ya kyauta, yanxu su suka rubuto takardan suka aiko kenan? To su dai suka sani Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu da ke baki daya, idan sun kwaso kafa sun sake dawowa sai a nuna masu receipt din" Umma dai bata ce komai ba don bata ma san me zata ce ba.
Meemah na bacci Momy ta shigo dakinta wajen karfe goma na safe ta tasheta tana mika mata wayar hannunta, Meemah ta amshi wayar tana kallon screen din, sai kuma ta kalli Momy tace "Kudin suka sako?" Momy ta tabe baki tace "Gashi kuwa kina gani, nima yanxu naga alert din ashe tun daren jiya aka sako" Meemah tace "To a gidan uban wa ta samu ta turo bayan tace bata yin transfer kuma bata da Atm card" Momy tace "Ke baki ga sunan wanda ya turo kudin ba? Ai ba ita bace ta turo" Meemah ta kara kallon wayar da kyau taga sunan namiji, taSe baki tayi tace "To wai ke Momy da nake ce maki iskancinta ta dinga yi da maza a Amurka kin zata wasa nake? Ai ba abun mamaki bane don kin ga ta samu wanda ya turo miliyan goman, harkar iskancinta kawai ta dinga yi a Amurka da 'ya yan masu kudi, kuma karya take babu miliyan goman nan a account dinta wallahi, to dai gashi nan daya daga farkanta ya turo kudin nan take" Momy tace "Oho dai koma wa ya turo kudin ta matse masu can, ni dai ba na amshi kudin Wa na ba, da ban yi haka ba har a tashi duniya in dai Abdul ne wallahi bazai yi maganar kudin nan ba, kin ga da shikenan sun ci bulus, to ni da na haifesa ba asararriya bace da zan yarda ya bar masu makudan kudaden nan" Meemah tace "Wallahi Momy ni so nayi mu ce sai sun biya kudin sponsoring dinta da Abdul yayi, ke kinsan nawa Abdul ya kashe akan yarinyar nan kuwa? Wallahi idan na fara maki lissafi sai kin rike baki don mamaki, kudade ne ba na wasa ba da, duk kanta dukiyarsa ya dinga tafiya kamar kin masa baki, yaushe rabon kiji Abdul ya siya wani asset nasa ya ajiye? Tun da ya hadu da tsinanniyar yarinyar nan ya dena yi ma kansa komai sai dai yayi mata, ranan a gabana ya siya mata Abaya har biyu ko wanne dubu dari da hamsin, nayi masa magana ya nemi ya min rashin kunya cikin jama'a, handbag din nan shegiya sai Abdul ya siya mata na dubu kusan dari har fin haka, komai designer yake siya mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login