Showing 114001 words to 117000 words out of 241367 words

Chapter 39 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1544

jiye masa tsoron kar idonta ya bude, to gashi nan bayan karatun har da karuwanci ta dinga yi da manyan kasar nan tunda gashi har ta samu wanda zai tsaya mata da lauya ya biya makudan kudin da aka kashe mata kilan yace har da miliyan 100 da ubanta ya salwantar, abun arziki dai bai amshe mu ba a family din nan, ban ga laifin ki da baki son talakawa ba Momy, shi yasa nima bana son su na tsane su" Momy dai girgiza kafa kawai take tsabar takaici da bakin ciki ta kasa cewa komai, Meema ta kalli Abdul daka safa da marwa a parlon yana Wan murmushi tace "Ka kwantar da hankalin ka Abdul, as far as ina numfashi kuma uwar mu na numfashi ko don ka rama duk abinda yarinyar nan tayi maka za mu shiga mu fita har sai kotu ta baka ita, in sun san wata ai basu san wata ba, koma waye ke taka mata baya daga karshe kashe kudadensa kawai zai yi a banza don sai ta shigo gidan nan mun ci ubanta da izinin Allah, banda kaddara me ma zaka yi da er gagurumin barawo kuma makaryaci, daga basa dukiya ya kai Lagos yace an kwace mota" Sama Abdul ya wuce kamar zai tashi sama, Momy ta bi sa da kallo cikin bacin rai tace "Kai Allah Ubangiji ya tsine ma mutanen nan albarka, yanda suka sa Wa na a damuwa Allah ya saka duk zuri'arsu a damuwa, ita kuma yarinya Allah ya kasheta ma duk mu huta, tun da lamarin nan ya faru ko abincin kirki Abdallah yaki ya zauna ya ci a gidan nan, in ya fita tun safe sai dare muke ganinsa gaba daya ba shi da sukuni akan er talakawa, wannan wani irin iftila'i ne ya same mu" Meema tace "Tashi tsaye kawai za mu yi ayi abinda ya kamata Momy, gidan nan ai kamar ta shigo sa ne in sha Allahu, da bakinta zata ce ita ta hakura a kai ta gidan mijinta kawai, kuma ta shigo nan ta same mu muna jiranta" Daga haka Meema ta mike ta bi bayan Abdallah. Jay na zaune tare da Ajay a office din lauyansu suna sauraron sa, lauyan yace "He is trying to re-litigate a case already resolved in court, don an riga an rufe case din a kotu tunda yace ya yafe, har lauyoyinsa sun yi filing notice of discontinuance kuma kotu tayi approving sannan ta kulle case din ta yi releasing debtor dinsu from any further liability, but like seriously ban san wani irin lauya bane Wan sa, don har da written confirmation of debt forgiveness da suka yi a kotu duk yana nan, why let them arrest the man again? Ko dai Wan nasa bai gaya masa consequences din hakan da yayi bane cause this is pure abuse of process and malicious prosecution" Jay yace "To yanxu meye abun yi Barrister?" Lawyern ya ajiye pen din hannunsa yace "Za mu yi Filing motion to dismiss the already forgiven case, and we will plead abuse of process, sannan muyi Raising estopped from pursuing the debt again in near future, just that za mu yi presenting documentation of the original debt forgiveness and court records to the court, wannan ma ai sun yi breaching court order ne kuma hakan laifi ne me zaman kansa" Ajay yace "That is because suna ganin ba shi da wanda zai tsaya masa ko shekara nawa zai yi a kulle, his family have no voice to do so, that was why the breached the court order for their selfish interest" Lauyan yace "Babu matsala in sha Allah za mu shigar da kara kotu, and the man will be bailed out while the case is going on, they will even have to pay him damages...." Bayan la'asar Ajay yayi parking a kofar gidansu Khaleesat, dai dai inda yayi parking ranan da suka yi dropping dinta da daddare, a bayansu kuma wata mota ce ita ma tayi parking, Guard uku ne suka fito daga cikin motar dukkansu suka yi tsaye jikin motar da suka sauka, shi dai Jay kallon unguwan kawai yake, Ajay ya bude mota ya sauka, ya jingina da motar ya rungume hannunsa, Jay ma ya sauko sannan ya zagayo inda Ajay yake tsaye yace "Where is the house?" Ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Gashi nan kana kallo" Jay ya kalli gidan dake opposite dinsu, wani almajiri ne ya zo wucewa Ajay ya kirasa, yaron ya taho da sauri Ajay yace "Shiga cikin gidan can kace ana sallama da Maman...." Sai kuma ya kalli Jay alamar ya fadi sunan, Jay na kallon almajirin yace "Kace ana sallama da Maman Halysaah" Almajirin yace "Toh" Da sauri ya nufi gidan, Ajay yace "Meye kuma Halysaah? How is that even a name? In zaka kira sunanta na asali kawai ka kira" Jay na kallonsa yace "Meye sunan nata na asali?" Ajay bai kallesa ba har sannan yace "Ka fi ni sani ai, tunda ka fi kusa da ita" Jay ya Wan yi murmushi bai sake ce masa komai ba, Nenne ce ta leko kofar gidan tana zazzare ido kuma bata yarda ta fito waje ba, tana yin ido hudu da su Jay sannan ga wasu samudawa da ta gani har uku tsaye jikin wata motar ta juya ta koma cikin gidan da sauri har tana tuntube, sai ga Mama Zubaida tana gyara gyalenta da ta yafa akan daurin kirjin da tayi, Mama Shatu na bayanta tana kokarin saka hijabinta ta bai bai, tsaye duk suka yi daga cikin gidan suna leko su Ajay da samudawan dake jikin mota a tsaye, Mama Shatu tayi karfin halin cewa "Ina wuninku?" Jay ne ya karasa har inda suke tsaye, shi dai Ajay na rungume da hannunsa yana kallon ikon Allah, Jay ya gaishesu duk suka amsa kamar munafukai suna gwale ido, Jay yayi kasa da kai yace "Mahaifiyar Halysaah mu ke son gani" Da sauri Mama Zubaida tace "A'a to ku shigo mana, Bismillan ku ai tana ciki, fakewa kawai suka yi da cewar bazata iya fitowa ba bata da lafiya, lafiyarta lauz ku shiga har dakin ku sameta" Duk tunaninsu an zo tafiya da Umma ne kamar yanda aka zo aka tafi da Malam Ali, Jay ya juya ya kalli Ajay dake jin duk conversation din su daga inda yake tsaye, ko ba a gaya masa ba yasan stepmom din Khaleesat ne matan, ya kulle motarsa yana kallon wa enda ke tsaye jikin mota yayi masu alamar da cewar za su fito in 5 mins sannan ya karasa har inda Jay ke tsaye yana jiransa su shiga gidan, su Mama Zubaida kuwa har sun koma tsakar gidan sun tsaya cirko cirko suna jiran su ga yanda za a shigo a fitar da Umma, da hannu suka nuna ma Jay da Ajay hanyar dakin Umma, Jay ne yayi sallama bakin kofar dakin, shi dai Ajay na tsaye a gefe yana kallon white t-shirt dinsa to be sure ruwan taSon da yayi gaja gaja a compound din bai fallatsar masa a jiki ba, Mama Shatu da Mama Zubaida a tsakar compound din suke zubar da duk wani ruwan da suka yi aiki haka ma yaransu, sun maida compound din kamar na mahaukata, gashi simintin da aka masa duk ya dagargaje ya kusa komawa kasa, shi yasa in suka zubar da ruwa sai ya cabe, kudaje sai safa da marwa suke ta ko ina, ga kwanuka gaja gaja, igiyoyin gidan kuwa duk an rataye kaya, Ajay na ganin Jay ya shiga dakin Umma shi ma ya shiga ciki da sallama, dukawa Jay yayi daga bakin kofar ya gaida Umma da Maman Salame dake dakin, Ajay ma yayi hakan ya gaishe su, ganin haka Maman Salame ta tashi da sauri ta shimfida masu darduma a kan ledan dakin tana masu sannu da zuwa, duk tunaninta ita ma zuwa aka yi za a tafi da Umma amma sai bata ga alamar hakan a tattare da su ba duba da yanda suka yi gaisuwa cikin girmamawa, Jay ne kawai ya zauna kan darduman Ajay kuwa ya kasa zama ga wani zafi da yake ji a duk jikinsa, ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan goshinsa, Mama Salame ta dau mafici ta mika masa, ya Wan yi murmushi ya amsa yace "Nagode" Mama Salame ta dage labulen dakin tana cewa "Yau mun fi sati biyu basu kawo wutan ba, ance tiranspoma tayi bindiga" Nenne dake makale kofar bandaki rike da buta ta dinga leka dakin Umma bayan Maman Salame ta daga labulen, haka su Mama Zubaida da suka ji shiru ba a taso keyar Umma an fito da ita ba, Jay na kallon Umma dake zaune don ko ba a gaya masa ba yasan ita ce mahaifiyar Khaleesat duba da kalan fatarta sannan babu ta inda Khaleesat ta bar ta, ba karamin kama Khaleesat ke yi da mahaifiyarta ba a nan ta samo asalin kyanta, Yayi kasa da murya yace "Ya jikin Umma?" Cikin sanyin murya Umma tace "Alhamdulillah da sauki" Ajay ma yayi mata ya jiki ta amsa tana kallonsu gaba daya don jira kawai take taji me ke tafe da su, in ma cewa za su yi tafiya suka zo yi da ita dama a shirye take tunda hijab dinta na jikinta, shiru ne ya biyo baya a dakin, don Jay bai san ta inda zai fara introducing kansa ba ma, haka ma Ajay da yayi shiru zafi na neman hallaka sa, after few seconds Ajay yayi karfin halin breaking silence din a hankali yace "Makaranta daya mu ke tare da Jidderh a can America, so kawarta ta sanar mana abinda ke faruwa shi ne muka nemi ta bamu address mu zo nan duba ki" Sosai hankalin Mama Salame ya kwanta jin abinda Ajay yace, Mama Salame tace "Allah yayi maku albarka, kuma mun ji dadi mun kuma gode da zuwan da ku ka yi" Jay ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Umma kuma ki kwantar da hankalinki, muna tabbatar maki in sha Allah komai zai wuce nan ba da dadewa ba, don za ayi duk abinda ya kamata, mahaifinta ma in sha Allahu za mu yi abinda ya dace a sakesa a yan kwanakin nan, ita kanta Halysaah zata dawo gida in sha Allah" Maman Salame ta daga hannu sama cike da farin ciki tace "Alhamdulillah ya Allah, gaskiya mun ji dadin jin hakan daga gare ku, don bamu da wanda zai tsaya mana sai Allah, Alhamdulillah" Ita dai Umma kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ajay yace "Zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Mama Salame tace "To Allah Ubangiji ya kai mu goben lafiya, mun gode, mun gode" Mikewa Ajay yayi ya kara yi ma Umma sallama sannan ya fita daga dakin kar yayi suffocate, heat wan finish prince, don in akwai abinda baya shiri da shine zafi, baya son zafi ko yaya yake, Nenne na ganin Ajay ya fito daga dakin Umma ta sake komawa cikin bandaki da sauri, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi sa da kallo har ya fita daga compound din, to su waye wannan kuma su da suka baza ido da kunne su ga an fito da Umma tana kuka, bayan fitar Ajay da few minutes sai ga almajirai suna shigowa gidan da buhun shinkafa biyu, carton din taliya biyu, carton din indomie biyu, manyan gallon na manja da mangyada, da carton din maggi duk kuma aka dinga dire su a kofar dakin Umma, daga Nenne har su Mama Zubaida haka suka saki baki suna kallon ikon Allah, Maman Salame ta taso zuwa bakin kofa tana kallon kayan abincin da mamaki tace "Ikon Allah, har da uban hidima haka??" Jay ya ajiye ma Umma 100k yace "Gashi Umma ayi cefane da wannan, in sha Allah gobe za mu shigo da izinin Allah" Bai jira cewar Umma that was speechless and shock ba ga hawayen dake sauka idonta kawai ya fita daga dakin.....
[6/6, 5:08 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Jay na fitowa dakin Umma, Nenne dake tsaye tsakar gida bayan ta fahimci ba yan sanda bane ta rushe da matsanancin kuka ta nemi er kujera ta zauna tana kallonsa tace "Da wannan uban kudaden da ku ka kashe na siyo kayayyakin abincin nan ai da belin Wa na ku ka yi, wallahi maraya ne ba shi da kowa, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya rube a can, wancan karan ni kadai nasan wahalan da na sha na ganin an sako sa, babu inda kafata bata shiga ba wallahi, na dinga bi gida gida ina neman taimakon kudi" Jay ya kwantar da murya yace "In sha Allah za mu yi bakin kokarin mu na ganin an sako sa kaka, ki kwantar da hankalin ki" Nenne na matsar kwalla da gefen haSar zaninta tace "?an nan ina hankalina zai kwanta Wa na na can furson? In dai daga gidan radio da talabijin ku ke ni dai na amince ku zo ku dau muryata da fuskata in nemi taimakon al'ummar musulmai ku watsa ni duniya ta gan ni ina jawabi, kilan gwamna ma in ya gani yaji tausayina ya saka baki a sakar min Wa na" Jay yace "Ba sai anyi haka ba Kaka, ina tabbatar maki nan ba da dadewa ba zai dawo gida in sha Allah" Nenne tace "To daga ina ku ke? Ko dai kungiyar kare ha??in en Adam ne" Jay ya Wan yi shiru, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun yi cirko cirko a tsakar gida suna gwale ido suna kallon Jay, Jay yace "Makarantar mu daya da Halysaah a can Amurka, shi ne muka samu labarin abinda ya faru mu ka zo" Nenne ta mike da sauri tace "To ai yau kusan sati daya kenan ana neman ta ko sama ko kasa, wallahi bamu san inda take ba, ita uwar ta na daki tana jimamin ta, ni kuma ina nan ina jimamin Wa na, haka muka raba abun, amma tun da yarinyar nan ta samu labarin daurin aurenta da annoban nan Awdul ta shiga duniya, wallahi bakina da nata tace min bata son sa bazata iya auren sa ba, tun da uwata ta haifeni ban taSa ganin inda ake auren dole ba" Nenne na kai wa nan ta fasa sabon kuka, Jay dai ya ma rasa abinda zai ce mata, beside baya ma son yayi magana gaban su Mama Zubaida da suka wangale kunnuwa suna saurare, kawai ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu ashirin din da yayi saura, yaje har gaban Nenne ya mika mata da ladabi yace "Ga wannan Kaka, in sha Allah za mu shigo gobe" Nenne ta daga hannu da sauri tace "A'a, gwara ku hada kawai ku kai furson a sako min Wa na, don yafi min ko wani kudi a duniya" Jay yayi murmushi yace "Ki amsa kaka, na maki alkawarin za a sako sa nan ba da dadewa ba in sha Allah" Nenne ta amshi kudin da hannu bibbiyu tana sa masa albarka cikin rawan murya tace "In ma Allah ya sa kun zo gobe ba ku sameni a nan ba ku sa a raka ku gidana babu nisa daga nan" Yana murmushi yace "In sha Allah Kaka" Daga haka yayi mata sallama sannan ya fita daga gidan su Mama Zubaida suka bi sa da kallo babu fara'a ko wacce da abinda ke yawo a ranta, Nenne ta kulle kudin a habar zaninta ta soke tace "Dama gobe da asuban fari zan je gun Malam Na ta'ala, Allah ya sa in samu kwale kwalen da zai tsallakar da ni da sassafe" Dakin Umma ta nufa tace "To ke Salame kike ko wa? Ki fito mana ki shigar mata da dukiyar nan dake bakin kofa kar a faki ido a sungume mata wani abun, kayan abinci ai dukiya ce me zaman kanta a yanxu, Allah kadai yasan dubu dari nawa suka kashe wajen siyo kayan abincin nan...." Maman Salame ta fito daga dakin Umma ta fara shigar da kayan abincin ciki, Mama Shatu ta shige dakinta fuska a murtuke, Mama Zubaida ma ta tabe baki ta shige nata dakin ta sako tsumman labulenta dake rataye da kyauren dakin. Jay na fita waje ya tarar da Ajay cikin mota yana zaune a kujera me zaman banza ya kwantar da seat din kujeran idonsa a lumshe, Jay ya bude driver seat ya shiga yana kallon Ajay jin yanda ya kure AC din motar gaba daya, Ajay ya gyara zamansa yana kallonsa, Jay dai yayi murmushi ya fara driving motar Ajay ya nuna masa hanyar da suka bi suka fita ranan da yayi dropping Khaleesat, motar dake bayan su ma ya bi su, Ajay sai sake kare ma unguwan kallo yake with distress har suka isa main road, bayan sun hau saman titi ya kalli Jay yace "In za a samu gida ko na 30M zuwa 50M ne a siya pls su bar wannan vicinity din" Jay yace "I think that will be okay idan anyi releasing mai gidan but not now" Ajay yace "Duk daya ne Bruh, plss kayi ma Salisu magana a fara duba gidan daga yau zuwa gobe, that house isn't healthy for a living thing, ta yaya me rai zai dinga rayuwa a gida irin wannan? This is so pathetic, or am i exaggerating pls?" Jay yace "But haka kawai baza mu yanke decision without the release of the head of the House ba, so kake mu kara triggering saurayin nata bayan har yanxu ba mu yi achieving ko abu daya ba, we are following everything step by step Ajay, we will reach der in sha Allah" Ajay bai sake cewa komai ba, amma da gaske hankalin sa ya tashi kwarai ganin condition din cikin gidan most especially the compound, in ba dole ba shi kam babu abinda zai sake kai sa gidan nan, it's not about the house structure or where it's located but the hygiene of the house, sai kace cikin prison, ji yake kamar har ya kamu da cholera don har wani zazzabi zazzabi ya fara ji, ya kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login