Showing 204001 words to 207000 words out of 241367 words

Chapter 69 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1605

taji zaman America din ma ya fita kanta har ma da karatun, shikenan ita daga wannan sai wannan a rayuwarta, hawaye taji ya cika idonta, Safiyyah tace "Ke kuma matsalata dake kenan, komai sai kice kuka kamar wata er yaye, Meye abun kuka kuma? Ni fa ina da strong mind yanda bakya zato" Ita dai Khaleesat goge hawayen idonta kawai take don ta gaji kuma haka, Safiyyah ta tabe baki ta koma gefe, haka suka zauna for almost 10 minutes a wajen kowa da tunanin da yake a ransa, murya can kasa Safiyyah tace "Kin ga kuma gashi can zuwa, wannan mutumi dai bashi da alkibla" Khaleesat ta daga kai tana kallon inda Safiyyah ke kallo, lkci daya ta dauke kai fuskarta a daure, A hankali Safiyyah tace "Ni dai kinga tafiyata...." Daga haka ta dau handbag dinta kamar munafuka ta bar wajen kan Ajay ya karaso, har Ajay ya iso wajen Khaleesat bata sake kallon direction dinsa ba, Yana kallonta yace "Rashin kunyan ki har ya kai ki dinga katse ma mutane waya yanxu?" Ta wani kallesa amma taki cewa komai, sai kuma ta kauda kai, yace "Ba magana nake maki ba?" Bata fuska tayi tana shirin kukan da ya tokare mata a makogwaro yace "Sai dai kiyi ma kanki kuka ba ni ba, and in case u don't know.... work load dake kaina yafi karfin duk wani kananun issues din ki, Jay ne yake iya combining both ni kam bazan iya ba, i will be taking you home ki zauna can har sanda Jay zai dawo ku ci gaba daga inda ku ka tsaya, i don't have much time to be fighting with a tout because of you" Ita dai bata ce komai ba, ya hade rai yace "Baza ki tashi ba?" Mikewa tayi without looking at him, ya juya ya bar wajen ta fara bin bayansa tana hararansa, can apartment dinta ya fara kai ta, bayan yayi parking yace "Kar ki bata min lkci ki shiga ki dauko duk abinda zaki bukata for now, don't waste my time" Bude motar tayi ta sauka ta nufi apartment din, sai da ta Sata kusan minti ashirin a cikin gidan bata fito ba, patient dinsa ya kare ya dau waya zai kirata kenan ya ga motar da ya tsaya dai dai apartment din, kallon motar ya dinga yi don ya gane motar waye, wanda ke cikin motar na ganin motarsa sai yayi gaba ya wuce apartment din yana driving slowly, Ajay ya dinga kallon motar da mamaki, wato uban fist din da yayi masa banda frnds dinsu sun shiga tsakani bai ishesa ba kenan, few a cikin abokan Aymaan are also his frnds shi yasa matter din ma bai yi escalating ba har suka shiga tsakaninsu suna ba Ajay hakuri, amma fa Aymaan ya sha kulli kafin abokan su yi intervening, haushin hakan yasa yaje ya samu su Khaleesat a department dinsu, sai kuma yanxu gashi ya sake biyota gida, Ajay ya gyada kai, ya ci sa'a ba a Nigeria suke ba, wayarsa ne ya fara ring ganin Jay ke kiransa ya daga, daga daya bangaren Jay yace "Yarima me yasa baza kayi respecting title din da kake holding ba pls, why are you like this? menene ya kai ka fada da Aymaan? A America ku ke fa ba Nigeria ba Bruh" Ajay dake sauraronsa yace "Ai ba mu yi fada ba, kilan dai nan gaba za mu yi, don sai na karya masa hannu in bai yi hankali ba, dama naga ba shi da Stamina bugu daya ya tafi kasa don haka karyasa ba wahala zai min ba..." Jay ya ja tsaki yace "Can you hear ur self plss? I will report you to Abba in dai baza ka dena wannan abun da kake yi ba, kai bini bini ka kai fist kamar wani Wan dambe? who does that pls, haba wannan zubar da class dinka kake wallahi" Ajay yace "To wa ya jawo? Ba kai da wannan brat din bane ku ka ja har nake fada? Da baka bar ni da ita ba hakan zai faru ne?" Jay yace "A'a dama can hannunka kaikayi yake, stop using us to cover ur foolishness, sannan ni ban bar ka da ita ba because i know she is old enough to care for her self with no supervision kai ne dai ka maida care dinta hannunka voluntarily for reasons best known to you, Kuma ni ba gashi nayi ma Aymaan din magana ba kuma ya fahimce ni, amma kai komai sai ka sako hargagi ciki kamar jira kake ka fara dambe" Shiru Ajay yayi, kawai sai yayi ignoring wasu daga maganganun Jay yace "Ohk, kayi masa magana shi yasa naga motarsa yanxu a kofar apartment dinta ko?" Jay yayi shiru, sai kuma yace "Kai me ya kai ka apartment dinta?" Ajay ya katse wayarsa ya ajiye, sosai yaji Jay ya bata masa rai, and he was boiling from inside, ji yayi kamar ya ja motarsa yayi tafiyarsa ya bar ta da faith dinta a gidan tunda dama ba idea dinsa bane dawowarta America, har ya fara reverse amma kuma sai ya kasa tafiya, ya sake kallon direction din da Aymaan ya bi yaga babu motarsa alamar ya tafi, Jay ya dade bai Sata masa rai kamar haka ba, kawai ya dau wayarsa ya shiga contact dinsa ya danna masa block sannan ya ajiye wayar, sai ga Khaleesat ta fito daga apartment dinta, ko kallonta Ajay bai yi ba har ta gama saka duk abubuwan da ta dauko a back seat don taga bai bude booth ba babu kuma alamar zai bude, bayan ta kulle seat din ta bude front seat ta shiga motar ta kullo kofar a hankali, ita ma bata kallesa ba kamar yanda shi ma bai ko kalleta ba ya fara reverse din motar. Har suka isa gidan ba abinda yace mata ita ma haka, yayi wucewarsa ciki ya bar ta da kayanta, haka nan ta dauka kayan bit by bit tana shiga da su gidan, har sannan yana tsaye parlor waiting for her to finish, sai da ta gama shigo da kayan babu yabo babu fallasa yace "Meet me in the kitchen" Daga haka ya nufi kitchen din ta bi bayansa, Utensils da aka kebe a kitchen din ya nuna mata wajen da suke a takaice yace "That is a no go area, duk ma me zaki taSa a kitchen din nan banda su" Yana kai wannan ya fice daga kitchen din ta dinga kallon Utensils din ba ma sae an gaya mata ba ta gane iya shi ke amfani da su, can ta tabe baki ta juya ta fita, bayan ta kai duk abubuwan ta dakin da ta sauka jiya taji wayarta dake jaka na vibrate, ta dau jakan ta bude ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin number Housemate dinta, duk da tayi deleting number amma tsaf yana kanta don special digits ne bbu wahalan haddacewa....
[7/14, 8:35 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat ta zauna gefen gadon dakin tana kallon screen din wayarta, zata yi picking call din ya katse, it took her almost 2 minutes before returning the call amma har ya katse bai daga ba, ta dinga kallon wayar waiting to see if he will call back amma har bayan minti goma bai kira ba, hakan ya sa ta ajiye wayar a hankali ta mike ta fara gyara dakin, ta sauka downstairs tana dube duben inda zata ga abun shara da goge goge na gidan, har ta fidda rai da samu sai gashi ta gani a under stair storage din gidan, bayan ta gama gyaran dakin da take ciki da Babban corridor din sama sai kuma ta sauko downstairs ta fara gyaran babban parlon hade da goge goge, it took her almost 2 hours kafin ta gama aikin gidan gaba daya, kitchen kuma bata ga abinda zata gyara ba cause it was very neat and tidy alamar yana gyarawa a ko da yaushe, ta maida Household cleaners din da tayi amfani da su a under stair storage din da suke sai gashi yana saukowa downstairs ya canza kayan jikinsa, yi yayi kamar ma bai san me tayi ma gidan ba ya dau makullin motarsa da ta ajiye saman Centre table ya nufi kofa ya fita daga parlon, tabe baki tayi ta tafi sama don ta gaji sosai ba kadan ba, sai da tayi gyaran gidan sannan ta kara tabbatar da girman gidan. Khaleesat na zaune a daki da laptop dinta a gabanta tana studying wani course dinsu da za su yi test dinsa ranan monday, it was a Saturday afternoon, ta juya ta kalli wayarta dake vibrate, sau uku kenan Safiyyah na kiranta taki picking don tasan me zata ce, can dai ta jawo wayar tayi picking ta kai kunne tayi shiru, daga daya side din Safiyyah tace "Haba mana Khaleesat don zaki koya min abu sai kiyi ta min walakanci gashi test za mu yi ranan Monday, is it fail that you want me to fail?" Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To ya kike son inyi Sophie? i said u should be coming kin ki" A fusace Safiyyah tace "A'a wallahi bazan zo wannan gidan ba kinji har na rantse, haka kawai in zo ya koreni, shi ba wai kara garesa ba balle ince zai ji kunyan korata, gaskiya bazan zo ba don zan iya zaginsa idan ya koreni" Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace "Wai ban gane ya kore ki ba, why will he do so bayan yasan wajena ki ka zo" Safiyyah tace "In dai baza ki zo school din ba shikenan kawai i will look for another person to teach me, ni kinsan ba gane lectures nake a aji ba sai in an min bayani dalla dalla gani ga mutum" Khaleesat dai tayi shiru tana jin ta, Safiyyah tace "Sai anjima don Allah...." Khaleesat ta Wan yi murmushi tace "To let me see if i will be able to come, kin ga karfe biyu da rabi yanxu fa, da tun jiya sai ki gaya min ai, kina school ne?" Safiyyah tace "Eh mana, tun 12 na shigo schl ai" Khaleesat tace "Ohk, i will be coming now" Katse wayar tayi, ta sauka daga kan gadon ta canza kayan jikinta ko rigar sanyi bata sa ba don sanyin ya ragu sosai yanxu, ta dau backpack dinta bayan ta saka laptop ciki ta kashe wutan dakin ta fito, downstairs take leke daga passage way din da take tsaye, ta ga Ajay zaune parlon da wasu turawa biyu alamar frnds dinsa ne ga wine a gabansu, she can't even remember the last time da suka hadu a cikin gidan da shi, it is more than a month now da take gidan amma zata iya kirga sau nawa suka yi crossing part da shi a gidan, yawanci yana bangarensa take fita school da safe, kuma daya daga ma'aikatan gidan ne ke dropping dinta sannan ta gaya masa sanda zai je ya daukota kamar dai yanda aka basa instruction yayi, in kuma aka dawo da ita gidan bayan ta gama lectures zata ga babu motar Ajay a compound alamar ya fita, tunda a daki take zama bata sanin sanda yake dawowa gidan, the next day kuma the same process will repeat it self, girki kuwa tunda tayi sau uku da shi taga duk bai ci ba don ko kusa da abinda ta dafa baya zuwa kawai sai ta dena sai dai tayi nata ita kadai, but tayi noticing anyi restocking foodstuffs irin na Africa a kitchen din probably because of her, don ita duk wani ciman turawa ba damunta yayi ba, may be yayi noticing hakan ne yasa ya siyo mata irin wanda take so, gyaran gida kuma tunda workers din are around iya dakin da take ciki kawai take gyarawa, tana saukowa downstairs ta gaida friends dinsa sannan ta kallesa shi ma ta gaishesa, bai amsa gaisuwan ba without looking at her yace "Ina za ki je?" Ta sauke idonta tace "Zan shiga school" Still not looking at her yace "Ki yi me a school on a Saturday?" Ta Wan kallesa, sai kuma tace "Tutorial zan ma Safiyyah" Sai a nan ya juya ya kalleta yace "As per the lecturer you are in John Hopkins ko? to baza ki je ba" Tayi shiru tana kallonsa, ya hade rai yace "Ko baki ji me nace ba?" Bata fuska tayi tana kallonsa, ya ci gaba da maganar da yake da friends dinsa, tana jan veil din jikinta tace "To zata iya zuwa nan?" A takaice Ajay yace "Baza ta zo, leave this parlor Madam" Ta wani tura baki ta juya ta koma sama, tana komawa daki ta kira Safiyyah, a hankali tace "Sophie i met the door locked kuma no one is around...." Safiyyah ta katse ta tace "Har workers din gidan?" Khaleesat tace "Kawai ki nemi wanda zai maki Tutorial din Sophie, ranan Monday before the test zan sake yi maki" Safiyyah tace "Ai shikenan, dama ban saka ran za ki zo ba, in ma Ajayn ne ya hanaki shi ya sani don ko a jikina wallahi, dama tun ranan farko da muka je duba Housemate dinki da na fara ganinsa sam bai kwanta min a rai ba naji tsoronsa, wai don Allah yaushe Housemate din ki zai dawo ne abu almost 2 months yanxu, ko dai anyi awarding dinsa doctorate Degree dinsa ne shi ne ya tafi yayi wasu abubuwan a Nigeria? shi kuma wancan uztaz din ko anyi cancelling work dinsa ne yake sakewa daga farko?" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, magana Housemate din nata yake mata balle tasan sanda zai dawo? Kuma kullum da damuwan hakan take kwana take tashi a ranta, ta rasa gane me yasa communicating din da baya yi da ita ya tsaya mata sosai a rai har yake damunta, well... may be he have his reasons, she is not even judging him, but deep down she knows she misses him so much, she misses everything about him, wani lkcn in ta kasa hakuri takan dake zuciyarta tayi masa magana ta WhatsApp, zai kuma yi mata reply amma casually, in yayi mata haka kuma bata iya daurewa sai tayi kuka, last maganar da tayi da shi almost a week ago ta tambayesa yaushe zai dawo, kawai yace mata soon and that was how the conversation ended, after that basu sake magana ba har yau, dama kuma ita ke yi masa, Safiyyah tace "Ni dai sai anjima, ina ta maki magana zaki min shiru katina na tafiya" Daga haka ta katse wayarta, a hankali Khaleesat ta ajiye wayar hannunta a gefen gado. Few weeks later Khaleesat na zaune ranan friday ita kadai a haraban department dinsu, Voice call suka gama da Aunty Farida ta WhatsApp bayan ta turo mata wasu videos da ta kasa fahimta sai kawai ta kira Aunty Faridan don tana online, tunda suka gama wayar Khaleesat ta kasa kwakkwaran motsi a inda take zaune, she looks so confuse and shock at the same time, kamar ance ta daga kai ta ga Aymaan da wata yarinya suna tafiya, yarinyar na ta masa labari da turanci, bata yi kama da er Nigeria ba duk da kana ganinta kasan er Africa ce yarinyar, Khaleesat ta sauke idonta tana kallon wayar hannunta har suka wuce ta, sai ga Safiyyah ta fito daga Hall din karatu da Backpack dinta a hannu, tana isowa kusa da Khaleesat ta zauna tace "Ke baki ga Aymaan ya wuce ba yanxu?" Khaleesat dai tayi shiru don har sannan bata yi recovering daga shock din da take ciki ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Ni wallahi naji haushi da ya Musty ya neme sa wai har da basa hakuri akan abinda muka masa, me muka masa in ba cowardliness irin na Musty ba? Abinda ma shi ne ya nuna mana halin jakanta, tunda uwata ta haifeni ban taSa ganin matsoraci kamar Ya Musty ba, ni da nake mace ma na fi sa dakakken zuciya, wai ka samu namiji kamar ka kana basa hakuri, wallahi ban so ace case din nan ya mutu da wuri ba na so ayi ta gwabzawa, na tsani in ga an shashantar da Case me zafi irin haka, bayan hakurin da Ya Musty ya basa naga kamar yana shakkar Ajay ma, kinsan na gaya maki frnd dina Sulaiman ya gaya min ashe narka masa duka Ajay ya so yayi aka maza aka shiga tsakaninsu, amma duk da haka ya sha kulli wajen Ajay, to duk har da hakan ya tsoratasa ya kama kansa da mu, amma nasan zai fake da cewa Ya Musty ne ya basa hakuri, kuma yaga Ajay ya daukeki daga apartment din ki ya maida ki gidansu, kinga ai dole ya tsorata da lamarin, Allah ya sa dai Housemate din ki ma bai ba Aymaan din hakuri ba don daga yanda ya sameni yayi min magana ta WhatsApp sanda abun ya faru har da bani lefi wai me yasa zan yi ma Aymaan rashin kunya wallahi babu tantama shi ma Housemate din naki ya basa hakuri, ni fa na tsani in ga maza suna baya baya da case din tashin hankali kamar wasu mata, shi yasa Ajay ya burgeni da ya nuna masa hauka, wo koma yaya ne dai can ta matse masa sh??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ege, ai kinga bai sake bi ta kanmu ba a school din nan, kaiii mun ga jalala ashe lafiyarsa qlau mutumin, sannan bai taSa aure ba sai yawon iskanci..." Shiru Safiyyah tayi ganin hankalin Khaleesat gaba daya baya jikinta, Safiyyah tayi kasa da murya ta kamo hannunta tace "Me ya faru kawata? Is anything the matter? Naga lafiya na bar ki naje dauko Backpack dina, why the sudden change of mood? Ko Aymaan din yace maki wani abu ne?" Khaleesat ta kasa ce ma Safiyyah komai, sai ga hawaye cike idonta, Safiyyah ta dire jakar hannunta a kasa tace "Subhanallahi, don Allah me ya faru? Me Aymaan din yace maki mu kira Ajay yanxu" Khaleesat na goge idonta cike da karfin hali tace "I spoke with Aunty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login