Showing 162001 words to 165000 words out of 241367 words

Chapter 55 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1596

kun ga ai ta dawo taga yanda za ayi da uban nata ko furson din za a mayar da shi ko hukuncin rataya za a yanke masa, ni dai na shiga uku na lalace, Allah ya hada Ali da mata da 'ya yan da basa tausayinsa kuma su za su yi ajalinsa, yanxu in Khaleesat er arziki ce da yace ya saketa ba sai tace babu inda zata je ba tunda bautar Allah take??" Malam Ali ne ya shigo gidan da er taliyar Hausa da ya siyo cikin Bacco bag, Nenne na ganinsa ta rushe da sabon kuka tace "Wallahi ta kashe auren ta dawo taga yanda za su yi da kai Ali" Malam Ali ya tsaya yana kallon Nenne, Nenne na fyace majina tace "Ga ta can dakin uwar a kwance tana jiran taga da wace motar za a zo a kwashe ka, dama wallahi tun da muka je gidan da parida nasan za a samu babban matsala don babu alkhairi a ran Parida, kuma in bata yi hankali ba daga ita har Zahra'un sai dai su koma kasar su, duk wanda baya son kwanciyar hankalin Wa na to kwanciyar hankalina ne baya so wallahi" Malam Ali dai ya nemi tabarma ya zauna ya kasa cewa komai, Mama Zubaida tace "Ikon Allah, kuma abinda ya faru kenan ni Zubaida? Aure wata daya da yan kwanaki amma har an yi saki? Yanxu zawarawa har biyu garemu a gidan nan kenan?" A fusace Nenne tace "Ta zauna tayi ma uban wa zawarci a gida? Ai ko taki ko ta so sai naje na ba Awdul hakuri ya maidata dakinta don kaf zuri'armu babu wanda ya taSa zawarci sai in mutuwa mijin yayi, to ko bakin halinta bai isa ya sa ya korota ba bai shirya ba, Khaleesah ce duk wani mummunan bakar maganar da ya zo bakinta take yaSa ma mutum, ko kuma in ka gaya mata abinda bai gamsheta ba tayi maka wani kallon walakanci da kaskanci da tula tulan idanuwanta, wani lkcn kana mata magana tayi maka banza wannan duk mun san halinta ne ba wai sharri ba, ga nukurci kamar er sarkin kutare, to ai ba ko wani namiji bane zai dau wannan, don haka zan je in basa hakuri ya dubi girman Allah ya maidata dakinta..." Mama Shatu tace "Toh ko samun sa kika yi ai sai yayi niyya zai maidata Nenne, in zai iya ai bazai fara sakin ta ba" Wani zagi Nenne ta kundumo mata a fusace, dai dai nan aka rafka sallama a kofar gida, Malam Ali ya mike tsaye yana kallon hanyar fita gidan, Nenne tayi tsit zufa na keto mata, can ta fara kuka a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Zahra'u dai bata zo mana pamily da alkhairi ba, kun ga har an zo tafiya da shi" Mama Zubaida ce ta yafa gyale ta nufi hanyar fita daga compound din, wani mota taga anyi parking a kofar gidan, mutumin dake tsaye kusa da motan ya nufota yana kallonta, Mama Zubaida ta gaishesa har da risinawarta, ya amsa yace "Mai gidan na ciki kuwa?" Mama Zubaida tace "To Allah ya sa dai lafiya Malam" Mutumin yace "Eh to, ni Dreban Alhaji Musa ne, an bani sako ne in kawo ma mai gidan" Mama Zubaida tace "To ni mai dakinsa ce, ni ce uwar gidansa, ko zan iya karba in mika masa, don baya jin dadi ne" Mutumin yace "To ba damuwa" Hannu yasa a aljihu ya ciro Envelope ya mika mata, ta amsa yayi mata sallama ya koma zai shiga mota, Mama Zubaida ta koma gidan tana juya takardan ita kanta sai da gabanta ya fadi don irin wannan in an kawo ai sammaci yake nufi, Nenne na ganin Envelope din hannun Mama Zubaida ta rushe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, shi kenan Ali a haka zai kare kenan ni Zainabu? wani takardan kotun aka sake kawo masa kenan?" Malam Ali ya amshi Envelope din hannun Mama Zubaida ya yage ya ciro takardan ciki ya warware, "Ni Abdallah Musa, na saki er ku Hauwa saki daya, biyu, uku" content din dake jikin takardan kenan, Shatu ta amshi takardan hannunsa tun da tayi karatun primary, tana duba takardan ta karanto abinda ke jiki amma fa da kyar tana in ina, Nenne ta tsaida kukan da take bayan taji Shatu ta karanto rubutun jikin takardan tace "Ji tsinanne la'ananne matsiyaci? saki har uku kamar warce ta kashe ubansa ko uwarsa? To Allah Ubangiji ya tsine masa albarka, dama banda kaddara uban me Khaleesat zata ci da Wan barawon Gwamnati? ubansa barawon gwamnati shi kuma Wan daba, Ai mu wannan sakin abun farin ciki ne a gare mu gaba daya tunda ba na'am muka yi da auren ba, kuma ko yau Khaleesat ta fita sai ta samu mijin nuna ma tsara da ya fi sa komai wallahi, bakin cikinmu daya zawara da ya maida ta, dama kullum da fargaban aurenta da shegen nake don har raina bana son sa babu yanda na iya ne kawai, banda jarabawa wasu iyayen kwarai ne za su dau er su su ba tsinanne irin Awdul? Khaleesah sai dai kaw????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
ai tayi hakuri don cuta kam Ali ya cuceta, ya cuci Rayuwarta, don duk shi ya ja mata wannan masifa, da suka ce maka er ka suke so bayan an fito da kai furson in kai uba na gari ne sai ka cije kace sam baka yarda ba sai dai a maida ka furson din ka mutu a can, amma saboda tsoron azaban duniya ba na lahira ba ka zabi ka sadaukar da erka don samu encin kanka, to gashi nan bayan ya rabata da budurcinta ya sako mana ita, dama auren sha'awa kawai yayi da ita, Allah ya isa bamu yafe masa ba wallahi" Nenne na kai wa nan ta fashe da kuka ta jawo kujera er tsugunno ta zauna tana rera kuka sai kuma tace "To yanxu ko zuwa za muyi mu basu hakuri ya dubi girman Allah ya maidata tunda malamai sun ce saki uku a madadin daya yake" Wajen karfe goma na dare Aunty Farida ta zauna gefen Khaleesat dake zaune da cup din kunun da Umma ta dama mata tunda ta kasa cin abinci, Aunty Farida tace "Baki shanye kunun bane?" Khaleesat ta dau cup din ta ci gaba da shan kunun a hankali, Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon buhun abubuwan da ita da Umma suka hada zata kai ma Khaleesat gobe, don da gobe zata je wajenta, tun daga dakakken yaji, kubewa busasshe, kuka, kanwa, su citta da kanumfari, gyadar miyar, har da garin danwake da sauran abubuwa da yawa duk su ne a cikin buhun, ga turaren wuta da suka siya mata masu kyau, Aunty Farida ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat da ta kasa shanye kunun hannunta, a hankali ta jawota jikinta, soothingly tace "Kiyi hakuri Daughter, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, kar ki saka komai a ranki kin ji?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida bata sake ce mata komai ba don ita bata ma son ta tambayi abinda ya hadasu don mayar da maganar bacin rai kawai zai kara masu, Ita dai Umma na zaune kan darduma Islam na bacci a jikinta, Maman Salame ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon Umma tace "Wani labari ne wannan nake ji a garin nan Zahra'u?" Umma dai tayi shiru tana kallonta, Maman Salame ta zauna kan tabarma tana kallon Aunty Farida da Khaleesat dake gefenta tace "Farida" Aunty Farida ta Wan yi murmushi tace "Ina yini Maman Salame" Maman Salame tace "Wai da gaske ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Farida tace "A ina kika ji Maman Salame?" Maman Salame tace "Ga labari nan ya baza Mariri? Dawowata daga Wudul kenan kusan mutane biyar suke gaya min haka a hanya tun ban karasa gida ba, wallahi buhun hannuna kawai na ajiye bayan na shiga gida na yo nan" Aunty Farida tace "To Allah ya sa mu dace" Maman Salame tana kallon Khaleesat cike da tausayinta tace "Garin yaya haka Khaleesah?" Khaleesat ta sauke idanuwanta bata ce komai ba, Maman Salame tace "To Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, in kuma auren bai kare ba Allah ya kaddara za ki koma sai ki ga an koma" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai saki uku ne Maman Salame" Maman Salame ta kasa cewa komai tana kallon Aunty Farida, kana ganinta kasan sosai jikinta yayi sanyi, ita dai Umma babu abinda tace a dakin, bayan kusan minti goma Maman Salame ta mike a sanyaye tace "Toh Allah ya sa mu dace, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu duka, sai na shigo da safe in sha Allah" Umma tayi mata sallama, Maman Salame ta fita daga dakin rai babu dadi, sarai Umma tasan kishiyoyinta ne suka baza labarin a garin, don ko Nenne bazata gaya ma kowa wannan labarin ba ita da ta tsani tonan asiri, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya don exactly tunanin da Umma take yi ita ma shi ne a ranta, Khaleesat ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty kina da number Safiyyah?" Aunty Farida tace "Ina da shi" Khaleesat tace "Ina son zan kirata ne" Aunty Farida tace "Babu kati a wayar, kuma yanxu dare yayi, ki bari gobe da safe sai kiyi magana da ita" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike tayi kwanciyarta saman gadon Umma, yaron Mama Shatu ne yayi sallama bakin kofar dakin Umma ya daga labulan yace "Wai Babanmu yace Khaleesat ta je" Umma da Aunty Farida dai sai kallon yaron suke, ya juya ya bar bakin kofar, Khaleesat ta mike zaune bayan taji abinda step brother dinta yace, tun dawowarta gidan ita ko haduwa da baban nata bata yi ba, ta sauka daga saman gadon tana gyara hulan kanta ta fita daga dakin Umma ta bi ta da kallo taji hawaye na taruwa idonta, Khaleesat na tafiya a hankali ta karasa har bakin kofar Babanta don yana zaune kan tabarma shi kadai a bakin kofar nasa, dukawa tayi daga gefen tabarman ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta gaishesa, maimakon ya amsa sai taji a hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, i failed you as a father, i caused you all this, but everything happened because I am a nobody, everything happened because...." Shirun da taji yayi ya sa ta daga kai ta kallesa taga hawaye a idonsa, bata san sanda ta fashe da kuka ba, yace "I am sorry for failing you daughter, albarkacin biyayyan da kika min baza ki taSe ba in sha Allah, my wish for you since u were born was to give you the best of everything i could amma Allah bai nufa hakan ba kaddara ta fada min...."
[6/27, 8:51 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Washegari da safe har karfe goma saura Khaleesat bata tashi baccin da take ba, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya tasheta don duk sun san bata yi wani baccin kirki ba daren jiya, daga wayewar gari zuwa lokacin mutanen da suka shigo dakin Umma yi mata Allah ya kyauta da abinda ya faru sun fi goma, don gaba daya labarin ya gama bazuwa garin, Aunty Farida ta kalli Umma bayan wata makociyarsu da ta shigo jajen ita ma ta fita, a fusace tace "Don Allah ki dena tanka masu Umma, ki nuna ke baki ma san jajen uban me suka shigo yi maki ba, wallahi banda ke in ban ci kaza kazan mace ba ta sake shigo mana dakin nan ace ba ni ba, wannan ai iskanci ne" Umma tace "To ya kike son inyi Farida? kinga ai muna mutunci sosai da su shine har ya sa suke shigowa, duk warce kika ga ta shigo dakin nan to muna mutunci sosai ne da ita, kin ga ai bazan masu rashin mutunci ko wani abu ba, wanda ya yaWa labarin a garin ai shine vabvan munafuki ba wanda ya shigo jajenta maka ba, kuma naga dai ba kan Khaleesat farau ba mutuwar aure" Aunty Farida ta mike tace "Ban taSa ganin inda ake shigo ma mutum jajen mutuwar aure ba sai a garin nan, kuma wannan ba komai bane banda salon gulma da munafurci" Daga haka ta fice daga dakin zata duba ruwan zafin da ta dora kan wuta, Umma ta kalli Khaleesat da tayi backing dinsu tana bacci, ta kai hannu ta dafata, tayi kasa da murya tace "Har yanxu baccin dai Khaleesat?" Juyowa Khaleesat tayi tana murza ido, sai kuma ta mike zaune, Umma na kallonta tace "Jiya da daddare baki ci abun kirki ba, ki je ki wanke baki ki zo ki karya, ga wainar shinkafa na sa an amso maki tun daxu, kar ya huce" Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta tafi gun akwatinta da ta dawo da shi daga America ta du?a ta bude jakar ta ciro Shower gel dinta da sponge, sai toothpaste da Brush, Umma dai kallonta kawai take har ta mike zata fita daga dakin Umma tace "Tunda wanka za kiyi kice Farida ta juye maki ruwan zafin, tana waje" Khaleesat tace "To Umma" Daga haka ta fita daga dakin Umma ta bi ta da ido, Khaleesat bata ko kalli inda kishiyoyin Ummanta suke ba da dukun dukun din zannuwan jikinsu kamar masu yin kuli kuli, ta jira Aunty Farida ta juye mata ruwan zafi a bucket ta surka mata sannan ta kai mata har bandaki, bayan ta shiga wankan Aunty Farida ta dora wani ruwan ta koma dakin Umma, Mama Zubaida ta taSe baki tana murmushi ta kalli Mama Shatu tace "To kuma yanxu ko da uban me za ayi mana takama?" Mama Shatu ta kwashe da dariya tace "In kin tambayeni in tambayi wa? Ba ke kike kokwanton maganar Malam ba da yace auren karkari ayi wata daya ya sakota, to kin dai ga kwalliya ta biya kudin sabulu, sai ki dena cewa kinyi asaran kudin ki, ji yanda hankalinki ya tashi ranan da muka je gidan da Nenne kin ga katon gida ta shiga dakin can ta fito ta shiga wancan ta fito kin zata watayawa take a gidan, ni dama ina kallon kwayar idonta nasan ubanta take ci a gidan, sam ban ga alamar kwanciyar hankali ba don duk a firgice na ganta" Mama Shatu ta sauke ajiyar zuciya ta rike haSa tace "Ohhh.... Ba karatu a Amurka, ba Miji, ga zawarci, wannan asara da yawa take ni Aisha, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, an ga samu an ga rashi, ina Zahra'u zata saka ranta ta ji dadi" Mama Zubaida tace "Ke baki ga haka ya korota daga ita sai kayan jikinta ba, ko er jakar hannu da ake saka waya fa bata taho da shi ba, dama a haka ya dauketa, kuma kinga ko tsinke ba a kai mata ba dama" Duk suke kwashe da dariya har da kyakyatawa, Mama Shatu tace "Sai a dawo a ci gaba da alalan da aka watsar, don ita kanta Faridan Allah ya sa Wan zaman da ta dawo suka yi ba a cinye jarin nata ba, nan nan a gabanmu aka yi ta hade haden garin Wanwake da su kuka da kubewa za a kai ma Khaleesat ashe ashe korota zai yi, ni anjima ma zan shiga a tsam min garin danwaken don naga da yawa suka yi" Tana dariya ta kare maganar, Mama Zubaida tace "Ae wallahi ko tsirara zan yi na gwammace inyi da dai Zahra'u taji dadi da 'ya yanta, in ke kin manta irin cin ?ashin da Malam ya dinga mana bayan ya aurota ni ban manta ba, duk muka zama bora a gidan nan, baya ganin kowa sai Zahra'u tunda da asirinsu na buzaye ta shigo gidan, banda dai dama tun asali idonmu ya bude da Malamai ai da tuni ya sake mu tun bai samu karayar arziki ba, hatta kayan dakin da ya siya mata sai da na zaga na koma kasuwa na tambaya aka ce min nata duk yafi namu tsada, gashi yaranta su ne 'ya yan so barin Khaleesat din nan ai mun sha bakin ciki iri iri Shatu, Ita fa har Umra tayi sannan ga Hajji, mu kuwa iya Hajji kawai muka je mu ka yi tsabar ya maida mu 'yan iska" Mama Shatu ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ki bar tuna min wannan takaicin Zubaida, banda a tsaye muke ai da wani labarin ake yanxu ba wannan ba, haka mu ma muka yi ta hadata da Malam da taimakon asiri, amma shegiyar bata yi zuciya ta koma kasar su ba da ya fara cin ubanta a gidan, in sha Allahu yanxu ta fara ganin bala'i ita da zuri'arta su da jin dadi ko farin ciki har abada, hatta yan biyun nan ya kamata mu fara mi?a sunansu yanxu kar lokaci ya kure, don naga wani farin jinin jama'a da suke da shi, duk inda suka shiga sai an tankasu ayi ta nan nan da su" Shigowar Nenne gidan yasa suka yi shiru, duk suka gaisheta ta amsa ba tare da ta kallesu ba ta nufi dakin Umma da er ledanta a hannu, duk suka taSe baki suna bin ta da kallo har ta shiga dakin, Umma da Aunty Farida suka gaida Nenne bayan ta shigo dakin, Nenne ta amsa bayan ta ajiye ledan hannunta tace "Ina Khaleesar take?" Aunty Farida tace "Ta shiga wanka" Nenne tace "Atoh dai, dama ina zata tsaya bakin cikin shege ya kasheta, harkar gabanta kawai zata ci gaba da yi kamar babu abinda ya faru, da auren wannan gansamemen mutumin da rashin aurensa ai duk daya, kuma mu muka cusa mata shi ba sonsa take ba wallahi, yanxu banda ni da ku waye yasan tayi wani gantalallen aure ko da wani ya fito yana son ta, banda dai gulma tayi ma jama'ar Mariri katutu, ai kawai ce ma Ali zan yi ya siyar da gidan nan da nawa gidan mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login