Showing 81001 words to 84000 words out of 241367 words

Chapter 28 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1604

na kallonsa a hankali tace "Pls kar kace zaka siya min ticket ina da kudi a account dina, i will get the ticket" Yayi murmushi yana kallonta yace "To Hajiya me kudi, kudin zai isa ki mana booking har ni da AJ?" Tana murmushi ta fara wasa da gefen gyalenta tace "Sae dai kai kadai, ni ai ban san wani AJ ba" Akan kunnen AJ da ya taho daga parlor zai sauka downstairs, ya tsaya yana kallonta babu fara'a, Jay ya juya ya kallesa yana murmushi yace "Je ki shirya ina jiranki downstairs Halysaah" Juyawa tayi ta tura kofar dakin a hankali, ko da Khaleesat ta sauko downstairs ta tarar da Jay yana jiranta, and it's almost 6pm, ya mike suka fita daga parlon, bayan sun bar compound din a motarsa ya Wan kalleta yace "Kinga kin kara tsokanar AJ ko?" Ta marairaice tace "To ni ai ban san yana wajen ba, why is he always eavesdropping?" Jay yayi dariya yace "Ni dai ba ruwana" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, she can't even wait ta dena ganin AJ she is already exhausted with him and his problem, she can't wait to stop seeing him, suna isa apartment dinta abinda ya faru ya dawo mata fresh, kawai sai take ganin kamar trauma din ya dawo mata sabo a kwakwalwarta, lkci daya duk jikinta ya mutu, haka dai jikinta ba kwari ta tafi dakinta ta fara hada kayan da zata hada shi kuma Jay ta bar sa parlor yana jiranta, sau uku Safiyya na zuwa gidan debo mata kayanta kwanaki kuma duk Housemate dinta ne ke kawota, after a while Khaleesat ta gama daukan abubuwan da zata dauka a akwatinta, sauran kayan dakin duk ta haWa su waje daya, ko zata dawo kasar ko bazata dawo ba ita dai bata sani ba, ta kuma bar ma Allah komai, ta gama tidying ko ina a dakin sannan ta fito wajen karfe shidda tana jan akwatinta a hankali zuwa parlor, kwance taga Housemate dinta kan doguwar kujera ya fara bacci, ta tsaya tana kallonsa, sai kuma ta tafi kusa da kujeran still looking at him ta Wan tapping din jikin kujeran gently, a hankali ya bude ido sai kuma ya mike zaune yace "Kin gama ne?" Tace "Are you sleeping?" Yace "A'a, kawai na kwanta ne ina wani tunani, it's even time for magrib bari inyi sallah, kema kije kiyi" Bandakin dake parlor ya shiga ita kuma ta koma dakinta, sai bayan wani minti sha biyar din suka bar gidan, tunda suka fito gidan Khaleesat tayi shiru, shi ma kuma bai ce komai ba, amma ya lura mood dinta ya canza, kawai ya sa a rai bazai tafi da ita gida a haka ba, after a while ya Wan kalleta yace "Would you mind watching a movie in Cinema tonight?" Khaleesat ta juya ta kallesa, sai kuma ta sauke idonta bata ce komai ba, yace "Ko baki kallo?" Tace "Ina yi, amma ba sosai ba" Yace "To yau za ki yi" Waje ya samu yayi parking, ya dau wayarsa ya shiga website din Cinema din dake Maryland to check their schedules for that day, yayi selecting movie din da za su kalla, da lokacin da za su kalla sannan ya siya masu ticket aka turo masa ta online, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa, without looking at her yace "I hope you will enjoy the movie" Ita dai bata ce komai ba har suka isa Cinema din, ya siya masu popcorn and lemonade, sannan suka nufi cikin Auditorium din da za a haska film din da ya siya masu ticket, in some minutes kuma za a fara haska film din, wannan ne zuwan Khaleesat Cinema na farko a rayuwarta duk da a baya babu irin takuratan da Safiyyah bata yi akan su je tare da frnds din Safiyyar amma ita dai bata yarda taje, suna shiga Jay ya fara cin popcorn dinsa kamar abinda ya kawosa kenan, ita dai Khaleesat dama bata wani damu da popcorn ba hakan yasa take Wan ci jifa jifa tana kallon film da ake, she is beginning to like the film hakan ya sa ta tattara gaba daya hankalinta kan film din, after almost 35 mins da fara film din ta juya ta kalli Jay taga bacci yake, ta dade abu bai bata dariya haka ba, she couldn't believe he is seriously sleeping abun sa, ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya a hankali, she don't know why she feel relieve a duk sanda take tare da shi, there is never a boring moment with him, gently ta kai hannu kusa da shi ta dauki popcorn dinsa daya, he was still sleeping ta dinga kallonsa maimakon film din da ya kawota ta kalla, idan yana bacci komawa yake so gentle and calm, a nan ne kuma ainahin handsomeness dinsa ke fitowa, if there is the sleeping princess then he will be the sleeping prince, har awa daya da fara film din Jay baccinsa yake kuma ta kyalesa bata tashesa ba, she watched the movie har sai da ya kusa karewa and she really enjoyed every bit of it, ta juya ta kallesa sai kuma ta dau popcorn daya ta matsa dai dai kusa da shi a hankali ta saka masa a baki, da sauri ta gyara zamanta ta maida hankalinta kan movie, ya bude ido, taji yace "What a nice movie" Sai a sannan dariya ya taho mata ta juya ta kallesa tace "Ain't you ashame of saying this?" Yana gyara zama yace "You don't like the movie? But it's nice, i like it" Tana murmushi tace "To in ka gama baccin ka tashi mu tafi, ni na gama kallona" Ya Wan shafa kai trying not to smile yace "Wa yace maki bacci nake, i was only meditating duk nasan abinda ake yi ai, ba gashi an kusa gamawa ba" Ita dai murmushi kawai take tace "Naji, tashi mu tafi, a hanya sai ka bani labarin film din don akwai inda ban gane ba" Yayi shiru yaki cewa komai, tana danne dariyarta ta tashi ta dau sauran popcorn dinta da nasa, tashi yayi ya bi bayanta suka fita daga Auditorium din, lokaci lokaci take juyawa ta kallesa don ta tabbatar he is not walking and sleeping at the same time, da sauri ya jawota ta fado jikinsa bayan tayi missing step saboda waige waigen sa da take sai kuma yayi saurin saketa, within few seconds aka yi hakan, ta rufe bakinta da hannu don ba karamin tsorata tayi ba, yace "Yanzu da kin fadi kika fara min kuka kilan har mu kai gida" Ta marairaice tana kallonsa, Softly yace "Alright Sorry Halysaah" Ta juya ta fara tafiya a hankali, a haka suka fita daga cinema din bata sake waigen bayanta ba, yana biye da ita yana kallonta har suka isa gun da yayi parking. Wajen karfe goma suka isa gida bayan yayi parking ta juya ta kallesa a hankali tace "Thank you so much" Ya mata murmushi yace "You are welcome House mate" A haka suka sauka daga motar tana biye da shi suka shiga gidan, kafin ta shiga daki yace "Get me ur travelling documents" Ta kallesa zata yi magana ya daura fingers dinsa biyu a lips dinsa, ta sauke idonta sannan ta juya a hankali ta shiga cikin dakin, after some minutes ta fito ta mika masa, ya amsa yace "Good job, zan tura maki ticket din ta Email dina, sai da safe" A hankali tace "Allah ya tashe mu lafiya" Juyawa tayi ta koma cikin dakin ta kulle kofar, Jay ya tafi parlon sama yaga AJ kwance kan Couch yayi bacci, shi dariya ma yake basa, kawai mutum ya dora ma kansa wahala, juyawa yayi ya wuce dakinsa, wajen karfe sha biyun dare Khaleesat na ta juye juye ta kasa bacci ita kanta ta rasa dalili, message taji ya shigowa wayar Jay dake wajenta ta mike zaune ta jawo wayar tana duba message din taga Email ne ya shigo, tana bude Email din taga ticket din ya turo mata na Turkish Airline, kuma Business class seat, bata san me yasa taji hawaye ya cika idonta ba, ta ajiye wayar a hankali ta koma ta kwanta.




*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H? [5/26, 9:47 AM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat na zaune gefen gado tana kallon Jay dake kulle mata akwatunan ta, yana dagowa ta juya a hankali tana kallon window dake dakin, ya dau boxes din biyu yace "Let me get them in the car" Daga haka ya fita daga dakin, ta jinginar da kanta jikin gadon dakin har ya dawo, yana kallonta yace "Hope you didn't forget anything Halysaah" Ta gyada masa kai, yace "Ok, you know what? in dai muka fita kika hadu da AJ thank him and tell him you are leaving" With a smile on his face ya kare maganar yana kallonta, ta sauke idonta tana wasa da fingers dinta a hankali tace "Ohk" Yace "Good gal, mu tafi" Mikewa tayi ta bi bayansa tana rike da karamin handbag dinta walking slowly, suna fitowa walk way din babban corridor din sama sai ga AJ ya taho daga parlorn dake nan sama, Jay ya kalli kayan jikinsa ganin iri daya suka sa kuma tun safe ba wai sun hadu bane kawai coincidence, tunda AJ ya kallesu sau daya ya ci gaba da tafiyarsa, Khaleesat ta Wan kalli Jay, ya gyada mata kai sannan ya nufi stairs, ita dai tana tsaye ta jira har AJ ya iso kusa da inda take sannan ta sauke idonta a hankali tace "Good morning, i want to thank and appreciate you for everything, i will be leaving today in sha Allah" Without looking at her yace "Jay dai zaki ma godiya ni me na maki" Ta bi sa da kallo har ya fara sauka downstairs, sai bayan da ya sauka sannan ta tabe baki ta bi bayansa tana tafiya a hankali, parlor ta tarar da Jay zaune yana jiranta, Jay ya bi AJ da kallo yace "Flight din naka na gobe ne amma?" AJ yace "I am leaving for the airport now" Jay yace "Ohk, zaka jira inyi dropping Housemate dina sai in dawo in kai ka airport din?" AJ yace "No, don't bother" Daga haka ya fita daga parlon tare da daya daga workers din gidan wanda da alama shi zai yi dropping dinsa airport din, Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, ya lura tunda gari ya waye jikinta yake a sanyaye, yana kallonta yace "Are you Okay Halysaah?" ?an murmushi tayi tace "Sure" yace "Kin gaya ma kawarki yau zaki tafi?" Khaleesat ta gyada masa kai tace "Na gaya mata" Yace "Ok, ita yaushe zata tafi?" Khaleesat tace "Yayanta yace ta bari ranan lahadi" Jay yace "Kin tabbatar baki mance komai ba kuwa a sama?" Ta gyada masa kai, yace "Je dai ki sake dubawa Housemate" Bata masa musu ba ta juya zata koma sama yace "Toh ki ajiye jakar taki mana" Ta dawo ta ajiye jakarta a kan kujera sannan ta wuce sama, Mikewa Jay yayi ya tafi gun jakar ya dauka ya bude sannan ya ciro Dala dubu daya a aljihunsa ya sa mata a jakar ya kulle ya mayar ya ajiye mata ya koma ya zauna, ba a dau lokaci ba Khaleesat ta dawo downstairs tace "Ban manta komai ba" Yace "Good" Mikewa yayi bayan yaji fitar motar AJ don dama jira yake yaji sun fita daga gidan, yana kallonta yace "Mu je, ur Flight is in an hour time in sha Allah" Khaleesat ta gyada masa kai ta dau handbag dinta, tana biye da shi suka fita daga parlon gidan, har gari ya fara duhu, suna shiga motarsa ta mika masa wayarsa dake hannunta kar ta manta, a hankali tace "Thank you so much" Ya amshi wayar sannan ya dauko pin a motar ya cire sim card din cikin wayar snn ya mayar mata yace "Your ticket is on the phone, in kin koma Nigeria sai kiyi SIM card replacement, in kuma baki son wayar sai in sa a kai maki sabo a Nigeria" Tayi murmushin karfin hali tace "Saboda me zance bana so, nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "To ai nasan ku mata da son sabon abu" Ta girgiza masa kai kawai tana murmushi bata ce komai ba, a haka suka bar gidan suka dau hanyar airport da tunani iri iri a ran Khaleesat, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya ga wani daren, ko me zata je ta tarar a Nigeria sai Allah, it's now that reality is dawning on her, bayan sun isa airport Jay ya juya ya kalleta yace "You can sort ur self out ba sai na shiga ciki ba ai ko?" Ta gyada masa kai, da kyar tayi karfin halin cewa "Thank you so much Housemate, Allah ya saka da alkhairi da abubuwan da ka min" Kasa ci gaba tayi saboda hawayen da ya fara sauka a idonta she just can't thank him enough, gani take words aren't enough to thank him, shi dai Jay kallonta kawai yake with surprise, can yace "C'mon Halysaah, to menene abun kuka?" Ta kasa basa amsa ta rufe fuskarta da gyalenta tana kuka a hankali, Jay ya kwantar da murya yace "Pls ki dena wannan kukan, in nasan abinda zaki yi kenan i will have just order either Lfyt or an Uber that will be taking you to the airport" Dena kukan tayi tana goge hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsa, ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido taga Luggages dinta dake booth zai dauko, a hankali ta bude side dinta ta sauka daga motar tana bin sa da kallo, daya daga porters dake wajen ya ba luggages din nata ya shigar mata da shi ciki ya hada masa da tip dinsa, ita dai Khaleesat kallonsa take, ya juya ya dawo kusa da ita yace "Alright safe trip Halysaah, idan kinyi replacing Sim card dinki sai ki min magana ta WhatsApp, my regards to everyone back home" Ta sauke idonta a hankali tace "I will miss you" sai bayan da ta fada haka ita kanta tayi realizing abinda ta fada, sai kuma ta kasa dago kanta, ya Wan yi murmushi yace "I will miss you too Housemate, in sha Allah next week i will be in Nigeria too" Bata iya ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai ta juya a hankali ta bi bayan porter din da ya shigar mata da luggages dinta zuwa check in counter for her Boarding pass, kasancewar Business class ticket gareta all the processes were smooth and straight for her, daga karshe ta nufi waiting lounge don in 15 mins time za su fara boarding jirgi, tunda ta shiga lounge din take kallon wanda ta gani zaune da mamaki, ta kalli boarding pass dinta sannan ta kalli na hannunsa taga iri daya, wayarsa kawai yake dannawa, ganin bai ganta ba ta juya a hankali ta koma wani wajen daban ta zauna ta inda ma bazai ganta ba, bata sake waigen inda yake ba, iya drink kawai ta amsa a lounge din unlike wasu da ke ta cin abinci duk a cikin kudinsu, gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa saboda damuwa, da ta tuna inda zata sae taji har wani juya mata kanta yake kamar bata da lafiya, ta sa?a wancen a ranta ta kwance har daga karshe aka fara boarding din jirgi, sai da Khaleesat ta jira AJ ya fara tafiya sannan ta mike ta bi bayansa walking slowly, Har seat dinta wata Flight Attendance da ke welcoming dinta da fara'a ta kai ta, hada ido Khaleesat tayi da AJ that was sitting few seats away from hers, ta sunkuyar da kanta ta zauna Seat dinta tana mayar da Amenity kit din da aka ajiye mata a gefe, AJ ya kasa daina kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, he can't even explain what he is feeling at that moment don bai taSa ganin wanda ya gama rena masa wayo a duniyar nan kamar Jay ba, jiya wajen karfe sha biyun dare ya farka ya gansa yana duba masa waya ashe ticket din da ya siya yake dubawa, he felt like just leaving the plane at that moment, after a while kawai ya dauke kai yana kara gyara barrier din da zai sa ko hangota bazai dinga yi ba, Ita ma Khaleesat ko by mistake bata sake kallon direction din sa ba, a haka jirgin ya tashi, Khaleesat bata taSa jin motion sickness ba tun da ta fara tafiya a jirgi amma yau ko don saboda pressure din da ta saka ma ranta ne kawai sai ji tayi as if she wants to throw up tun da jirgin ya daga, ta cire seat belt dinta da sauri ta mike ta nufi Lavatory din jirgin almost running, shi dai ya bi ta da kallo, Flight Attendance din da ta kawo mata Hot towel kafin tashin jirgin ne ta bi bayanta tana tambayar if she's okay, Khaleesat ta gyada mata kai kawai bayan ta fito daga Lavatory din, AJ ya bi ta da kallo har ta koma seat dinta ta zauna sannan ya tabe baki, Flight Attendance din ta duka kusa da ita tana tambayarta ko tana bukatar wani abu ne, Khaleesat ta girgiza kai tana murmushin karfin hali tace "Thank you, i am okay" Matar ta sake tafiya sai ga ta ta dawo da ruwa da orange drink, sai kuma wani drink daban duk a glass daban daban akan tray daya, ta duka tana mika ma Khaleesat ta dauki wanda take so, glass din ruwa kawai Khaleesat ta dauka ta mata godiya sannan ta sanar mata bazata ci abinci ba all throughout the flight don ma kar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login