Showing 96001 words to 99000 words out of 241367 words

Chapter 33 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1602

a kasa, Aunty Farida tace "Kuma ba unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo" Ajay yace "Toh shikenan, jikinta da zafi ne?" Aunty Farida tace "Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta min magunguna in siyo mata" Ajay yace "Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip ayi mata karin ruwa" Aunty Farida tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid" Ajay ya Wan yi murmushi yace "Bari in je in dawo dai" A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya harhado mata magunguna da drip da allurai. Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar kafafuwanta, cikin fada take cewa "Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata? Er talakawa? Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na'am bane kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka? In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya? Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane" Wata matashiya ce er shekara 39 dake zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace "Momy ban gane abinda kike nufi ba? Wai nufinki ya saketa kenan?" A fusace Momyn tace "Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema? Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?" Warce ta kira da Meema ta girgiza kai tace "A'a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy? Ae wallahi bata isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci da tijara haka?" Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace "In har aka ga na saketa to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan ne zata gwammaci bata taSa sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her" Momy ta tabe baki tace "Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar yarinyar nan" Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace "Ai ki ma dena maganar asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji" Momy dai ta tabe baki tana kallon me aikinta tace "Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min naman yatsu" Hakuri mai aikin ta hau bata. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta Wan kishingida a 3 seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya taSa biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta kalli Khaleesat tace "Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?" Khaleesat ta girgiza mata kai, dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace "Tare da brother dina muke" Aunty Farida tace "To ku shigo mana" a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara'a, sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace "Are you feeling better now Housemate?" Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace "Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha Allah, i promise you" Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl din hannunta Softly yace "Take ur soup" Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali, Aunty Farida ta kalli Ajay tace "Baka zauna ba Junaid" Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna, Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace "Mu ma duk ba da son ran mu bane abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za su dau er su su ba Abdul aure"
[5/29, 8:10 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Sai da Jay yaga Khaleesat ta ci pepper soup din me Wan yawa sannan ya mike ya koma kusa da Ajay ya zauna, After a while Ajay yayi breaking din silence din da ya ziyarci parlon yace "Iya daukar nauyin karatun ta kawai yayi Aunty?" Aunty Farida zata yi magana wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin Umma ce ke kiranta ta wayar makociyarsu Sha'awa, ta mike ta tafi dakinta don daga wayar, Ajay dai kallon Khaleesat yake kamar yanda Jay ke kallonta don har ta shanye pepper soup din, ta ajiye bowl din kasa tana kokarin disconnecting drip din hannunta ta yanda zata bar cannula din kawai, Jay ya mike yana kallonta yace "What happened? Do u want to ease ur self" Da kyar tana girgiza masa kai tace "I think i want throw up" Ya karasa cikin hanzari yayi disconnecting din mata, ta tashi ta wuce bandakin Aunty Farida da sauri tana toshe bakinta, sai ga Aunty Farida ta fito daga daki, ta kalli inda Khaleesat ke zaune ganin bata nan ta kalli kofar bandaki, zaunawa kan kujera tayi a sanyaye tana kallonsu tayi kasa da murya tace "Yanzu yayata ta kirani wai an zo an tafi da mahaifin Khaleesat" Da mamaki Jay da Ajay ke kallonta, Ajay yace "Kamar yaya kenan?" A sanyaye Aunty Farida tace "Baban Abdul din ne yasa aka je aka tafi da shi" Daga Ajay har Jay kallonta suke with confusion da kuma mamaki, fitowar Khaleesat daga bandaki ya sa Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, bayan Khaleesat ta kwanta kan 3 sitter din Aunty Farida ta juya tana kallonta tace "Ko zaki shiga daki a maida maki drip din?" Khaleesat ta gyada mata kai don ita ma ta gaji da kwanciyar kujeran, Aunty Farida ta mike tace "Bari in ma makociyata magana sai ta sa maki a daki" Daga haka ta fita daga parlon, after some minutes sai ga ta ta dawo da Neighbor dinta Bayerabiya, Khaleesat ta tashi ta koma dakin Aunty Farida, Bayerabiyar ta bi ta ciki ta sa mata drip din, ita dai Aunty Farida na zaune parlor tayi nisa tunanin da take har makociyarta ta fito ta tafi, Aunty Farida ta kalli su Ajay a hankali tace "To abinda yayata ta kirani ta gaya min kenan" Ajay yace "So suke a biya su kudin makarantar da ya dinga biya mata?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai ba iya kudin makaranta bane Junaid" Ajay yayi shiru yana kallonta, Jay yace "Bayan makaranta akwai wani abu na kudi da ya hadasu ne?" Aunty Farida tace "Kwarai kuwa.... Shekarun baya Malam Ali wanda shi ne mahaifin Khaleesat dreban babban mota ne, babu garin da baya zuwa da kaya a babban mota a fadin Nigeria, kuma motar tasa ce iyaka idan kana da lodi ya kai maka kayan ka har inda kake so sannan ka biyasa, har Nijar ya sha shiga da kaya daga nan Nigeria ta haka ma ya hadu da yayata Aunty Zahra'u warce ita ce mahaifiyar Khaleesat, don mu yan Nijar ne mahaifinmu har yanzu yana nan da ransa mahaifiyarmu ce dai Allah yayi ma rasuwa shekarun baya, to bayan ya auri yayata ya kawota Kano Nigeria ya ajiyeta cikin matansa biyu, bayan en watanni da auren shine na dawo wajen yayata tunda bata da kowa a Nigeria bata san kowa ba, nan rikona ya dawo hannunta a lkcn ina da shekara goma, tsangwama da kyara babu irin wanda ban sha ba a wajen kishiyoyin yayata, gashi bata iya ce masu komai tunda ita ma ba barin ta suka yi ba, mace ce me hakuri da kauda kai, in zanyi magana ma sai ta hanani, a haka ta samu makaranta ta saka ni tunda a can kasarmu ina karatu aka daukoni aka kawo mata, sai da tayi shekara biyar a gidan sannan Allah ya bata Khaleesat, Mahaifin Khaleesat na da rufin asirinsa sosai don haka bamu rasa komai a gidan ba sai zaman lafiya da kwanciyar hankali daga kishiyoyinta wani lokacin har da uwar mijin, jifa jifa mu kan kai ziyara Nijar gun iyayenmu da yan uwa da abokan arziki, bayan shekaru 12 da auro yayata a lkcn Khaleesat na da shekara bakwai sai abokan Mijin yayata da yan uwa suka dinga zugasa akan ya shiga siyasa ya nemi wani babban mukami zai samu tunda yana da jama'a sosai, kuma ba laifi yayi karatunsa, matansa ma suka dinga zugasa akan ya fito takara, yayata tayi kokarin ganin ta hanasa tunda bai rasa komai ba a sana'arsa ta dreban mota amma ya ki, haka nan ya daga babban motarsa ya siyar har da sabon gidan da ya fara ginawa a nan ?an Ladi na sidi, ya daga duk en kadarorinsa ya siyar ya shiga siyasa gadan gadan, duk matansa sai da ya biya masu Hajji suka tafi da mahaifiyarsa, ya kuma canza ma ko wacce kayan daki, ya ba kowa kudi a hannu, kusan mutane goma sha biyu ya biya ma Hajji a lkcn, banda matasan anguwa da ya dinga biya ma kudin makaranta, yayi ta facaka da kudi a karshe dai ya zo ya fadi zabe, duk wa enda suka dinga zugasa suka juya masa baya, Allah ya rufa masa asiri bai amshi bashin banki da wani abokinsa ke ta zugasa ya amsa ba kasancewar da zaben ya gabato bashi da kudi kuma a hannu, bayan faduwarsa zabe aka shiga yanayi na babu a gidan, cin yau da kyar na gobe da kyar ga yayata na da cikin yan biyu, dama gidan da yake haya me tsada tuni ya saki bayan kudin hayan sun kare muka dawo mariri gidan gadonsa da ya bari a walakance don saura kadan ya kyautar lokacin da yake campaign sai gashi gidan ya mana amfani ya rufa mana asiri, makaranta me tsada da yaran gidan ke zuwa duk ya ciresu suka dawo gida suka zauna babu karatu, iyayen basu yi dubaran mayar da su na gwamnati ba, duk muka shiga mawuyacin hali a gidan, sai sanda ya samu mota yake lodin kaya ya kai a biyasa, sanda babu mota kuma sai dai kowa ta ciyar da kanta a gidan, yana kuma fin wata da watanni bai samu ko da karamar mota ba, duk ka zo kofar gida zaka gansa a zaune babu abun yi shi ma duk ya fita hayyacinsa, tuni yayata ta siyar da kayan dakinta ta fara sana'a ina taimaka mata, ta kuma saka Khaleesat a makarantar da zata iya biya don Khaleesat ta taso da kwazo da hazaka ga ta yarinya ce me shiga rai ko don kalan fatarta, don a unguwan ma gidan buzaye ake kiran gidanmu, hatta Mahaifinta kiri kiri yake nuna yafi sonta a cikin sauran yaransa wanda hakan ya ja mata tsana da kyara a gun matansa da yan uwanta, ko sanda yake da mota a hannu tsaraba na musamman yake ma Khaleesat ko da bazai yi ma uwarta ba, ana haka yayata ashe duk cinikin da nake sai ta kwasa ta ba mijinta a boye ban sani ba, ga dai matansa duk da hali na babu da aka shiga a gidan basu bar yayata ba, kullum cikin hada mata tuggu da makirci ake wajen miji da uwarsa, cikin wannan yanayi yayata ta haifi yan biyunta wanda haihuwan da tayi na karshe kenan a gidan, a lkcn matsaloli har sun fi na da, jarin yayata ya karye kuma babu wani abu da zata siyar ta tada jarin, ga jegon yan biyu tana yi ga yunwa wani lkcn sai makota ke zubo abinci a kawo mata, iyayenmu a can Nijar ba masu karfi ba balle su taimaka mana, a haka na bi wata kawata zuwa nan garin Lagos tana siyar da abinci, kafin nan fa nayi aure har na fito, duka auren bai cika shekara daya ba, na auri wani abokin mahaifin Khaleesat, karayar arziki na samun Malam Ali na dinga fuskantar matsaloli gun mutumin da matansa uku wanda daga karshe ya sakeni dama ba saboda Allah yayi auren ba saboda kalan fata ta yayi, ina nan Lagos nake tallafa ma yayata da 'ya yanta uku, don bana son karatun Khaleesat ya tsaya duk da ta samu Foundation sosai sbda makarantar da ubanta ya sa ta ma a sanda yake da rufin asirinsa yafi na sauran yan uwanta tsada, na zo Lagos da yan shekaru yayata ta kirani wataran wai gashi an ba Baban Khaleesat babban mota har zai kai kaya kudu, matsaloli sun fara warwarewa tunda har an biyasa kudin kai kayan kuma kudade masu tsoka gashi har ya siya kayan abinci masu yawa ya ajiye a gida, tace in Maza in dawo gida kawai dama ita hankalinta ba a kwance yake da zamana a lagos ina sana'a ba, a haka ta takurani har sai da na dawo Kano, a sannan Khaleesat na da shekaru sha shidda tana kuma gab da gama secondary don da wuri aka sakata a makaranta, na dawo da wasu kwanaki ranan muna zaune tsakar gida da yamma sai ga mahaifin Khaleesat an shigo mana da shi ranga ranga ko motsin kirki bai yi, wanda duk gaba daya mun zata yana hanyar kudu har ya kusa Lagos, ga dai shi babu ko kwarzanen ciwo a jikinsa kuma wa enda suka
kawosa suka ce ai daga asibiti ma aka taho da shi a can wajajen garin yarbawa, sannan kwanansa uku a asibiti aka sallamosa wasu mutane da suka shaidasa tunda dreba ne suka biya kudi aka sako sa a mota aka dawo da shi Kano, sosai hankalinmu yayi mugun tashi a wannan lokacin, sae da Malam Ali yayi kwana biyu a gida ana ta addu'a da neman taimako kafin ya farfado gaba daya har yana iya magana, nan fa yake sanar mana barayi ne suka kwace Trailer da kayan mutane a ciki bayan sun shaka masa wani farin abu, tashin hankalin da duk muka shiga bazai misaltu ba a lokacin, daga Trailern har kayan cikin trailern ya doshi miliyan dari da tamanin" Shiru Aunty Farida tayi tana goge hawayen dake zuba idonta, Jay that was shock ya kalli Ajay dake kallon Aunty Farida babu ko kiftawa jin zunzurutun amount din da ta kira, Aunty Farida na share idonta ta ci gaba tace "A ranan yan sanda sun kusa goma suka zo a motoci, a haka aka sa ma mahaifin Khaleesat ankwa ana jan sa kamar barawo aka fita da shi yaransa da matansa na kururuwa suna ihu, Khaleesat kadai ce bata motsa daga inda take zaune da littafi a hannunta ba sai hawaye kawai, duk aka cika kofar gidanmu babu masaka tsinke kai kace barawon gaske aka zo dauka, mun shiga tashin hankalin da baya faduwa a wannan rana, kuma duk mutanen da yayi ta biya ma Hajji a sanda yake da hali, da kuma mutanen da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login