Showing 108001 words to 111000 words out of 241367 words

Chapter 37 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1555

abincin talla hayakin icce duk ya cika ko ina na gidan, Mama Zubaida sai mita take an siyo masu jikakken icce, gaishesu Safiyyah tayi suka amsa ana mata wani kallo kasa kasa, Safiyyah ta tsaya suka gaisa da Labiba dake wanke robobin da za a zuba abincin siyarwa, sannan ta nufi dakinsu Khaleesat ta daga labulen ta shiga da sallama, zaune ta tarar da Umma ta jingina da bango hannunta rike da carbi ga kawarta Mama salame da wata Zaliha makociyarsu sai Sha'awa ita ma makociyarsu zaune dakin ko wanne yayi jigum, zaunawa Safiyyah tayi tana kallon Umma ko gaisheta bata yi ba ganin yanayinta tace "Umma baki da lafiya ne?" Umma tayi karfin halin cewa "Sannu da zuwa Safiyyah" Safiyyah ta gaisheta sannan ta gaida sauran mutanen dake dakin, ta sake maida dubanta kan Umma kan tace komai Mama Salame da ta san kawar Khaleesat ce ita tayi kasa da murya tace "Tsakaninki da Allah Sapiya baki san inda kawarki Khaleesah take ba?" Safiyyah ta zaro ido tace "Kamar yaya Mama?" Sha'awa ta gyara zama tace "Ae tun ranan asabar rabon da a saka Khaleesat a ido, daga ta dawo kasar waje ta tarar an daura mata aure da audallah washegari Asabar aka nemeta aka rasa, babu inda ba a shiga neman Khaleesah ba amma babu ita babu labarinta, jiya jiya yan sanda suka zo suka tafi da Malam Ali" Safiyyah da ta shiga wani shock jin wai an daura ma Khaleesat aure da Abdul ta ajiye jakarta a gefe ta dafe kirji tace "Wani Abdul din aka daura mata aure da?" Sha'awa na gyara barkakken zaninta tace "Audullah saurayinta dai da kika sani, ranan juma'an nan da ta wuce aka daura masu aure, tana dirowa kasar aka sanar mata shine ta gudu har yau babu ita babu labarinta, gashi an tafi da Malam Ali an kullesa" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mikewa tayi tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba tsabar shock din da ta shiga maganganun Sha'awa na yawo a kanta, hawaye ne ya cika idonta tana girgiza kai ta kasa cewa komai, ina jin bayan Khaleesat da tayi bakin cikin auren da aka daura mata da Abdul idan aka cire su Jay babu wanda yayi bakin ciki kuma irin Safiyyah, don ji tayi kamar an aza mata katon dutse a kirji tsabar bakin cikin wannan labarin, kawai ta fashe da kuka cike da tausayin kawarta, Abdul fa?? Housemate din Khaleesat ne ya fado mata a rai, nan Safiyyah ta dinga rera masu kuka kamar ita ce Khaleesat din, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana kunduma ma su Mama Shatu da Mama Zubaida zagi tana cewa "Wato har sararin kunna rubabbun murhun ku kuka samu a gidan nan baku dubi bala'in da ake ciki ba, ai in dai Wa ne kowa ma ya haifa wallahi, yanda ku ke nuna halin ko in kula da abinda ya samu Wa na ku ma dai kun haifi 'ya yan nan naga, shegu masu fararen kafafuwa tunda Wa na ya auro ku yake shiga bala'i sinka sinka a duniya amma saboda baku da imani da tausayi ko wacce ta zauna bakin shegen murhun ta" Mama Zubaida ta kauda kai tana tabe baki tayi kasa da murya tace "Sai kuma yunwa ta kashe mu saboda yan sanda sun zo sun dauki Malam" Ita dai Mama Shatu sai juya miyarta take kar ya kone taki ko kallon inda Nenne take, Nenne na huci ta nufi dakin Umma ta dage labulen tana kallon cikin dakin tace "Saka dogon hijabi da rike carbi ba shine mafitarki ba Zahra'u, duk inda kika tura yarinyar nan waya kawai zaki buga masu ki ce ta dawo tun lamari bai lalace mana gaba daya ba, in ko ba haka ba wallahi sai a wanke daya daga kanninta a ba ma Awdul din tunda abinda yayi ta shi yayi su, in jar fata da gashi irin ta buzaye ne su ma duk suna da shi, babu abinda zata gwada masu sai shekaru tunda ta basu shekaru bakwai, don bazan zuba ido a karo na biyu Wa na ya koma fursin ya tagayyara ba, Allah kadai yasan nawa na kashe wajen shige shige har Allah ya bamu mafita a wancan lokacin da aka kullesa, tun asali bata san bata son Awdul din ba sai bayan da ya kashe mata uban dukiya da bazai lissafu ba? Wace masifa ku ke son ja ma Wa na ke da er ki a garin kano? Shi kadai fa ya rage min namiji sai mata, wallahi ki fito da ita Zahra'u in ya so su riketa a sake min Wa na, nasan har da hadin bakin makirar tsohuwar can Gaje, yanxu kuma zan kama hanya in tafi Hotoron duk inda ku ka boye Khaleesah sai kun fito da ita baza ku kara ja min salalan tsiya ba, sha'awa taso ki rakani gidan tsohuwar banzan can Gaje" Da sauri Sha'awa ta mike ta figi ba?in gyalenta ta fita daga dakin ta bi bayan Nenne dake huci suka fita daga compound din gidan, Mama Zubaida da Mama Shatu suka saki guda a tare bayan Nenne ta fita, Mama Shatu ta kyalkyale da dariya tace "Ana yi muna hura murhu, ma ga dai karshen wannan dirama me dadin kallo a gidan nan, su buzuwa sai a koma dajin da aka shiga aka nemo maganin farin jini ayi ma Malam bayanin lamari ya kwabe, ba dai 'ya yanmu bane munana masu ba?in jini, maji ma gani dai" Umma dake jin duk abinda suke cewa ta jinginar da kanta da bango hawaye na sauka idonta Mama Salame na bata hakuri, Safiyyah dai jingina tayi daga bango a inda take tsaye hawaye na zuba idonta ita ma, ganin abun take kamar a mafarki wai an daura auren Khaleesat da Abdul, to amma ina Khaleesat zata tafi tun ranan Saturday ita da tasan Khaleesat ko kawaye bata da su a kano, Housemate ne ya fado mata, ta dau jakarta da sauri tana share hawayenta ta fita daga dakin Umma, Umma ta bi ta da kallo hawaye masu zafi na bin idonta daga ranan asabar zuwa yau har ta rame, ko abinci bata iya ci ta kira Aunty Farida yafi a kirga akan ta zo gareta ko zata ji saukin radadin da take ji a zuciyarta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi Safiyyah da wani kallo suna tabe baki har ta fita daga compound din, Mama Zubaida ta matsa kusa da Mama Shatu da yake murhunsu kusa da kusa yake, tayi kasa da murya tace "Kin ga ki hakura da dafa waken nan da kika ce don gaskiya zai bata mana lokaci ga waje da nisa, gwara mu je a kara kada hankalinta taji ta tsanesa da auren kuma taki dawowa, in ya kama a kadata ta shiga duniya duk sai mu ce ayi, kudi ne dai zai yi kuka ba wani abu ba, kinga daga karshe in ma Labiba ko Lamisah duk wanda yace a basa duk daya ne a wajen mu babu banbanci, babu abinda zata gwada masu sai farin fata da uban gashi kamar na doki, in idanuwa ne su ma suna da shi, sannan suna da hancinsu dai dai gwargwado, tun asali kece kika yi ta makon fiddo kudi da ba a kai ga haka ba ma wallahi" Mama Zubaida ma tayi kasa da murya tace "Wallahi ban taba zaton aikin mutumin na ci haka ba Shatu, kinsan Malaman Jabu sun yi yawa yanzu sai dai ka kai masu kudinka su yi cefanen gidansu, shi sa kika ga ina ta ja da baya naki sakin kudi dama jarina ba jarin arziki ba, kinsan tun bayan rasuwar Malamin nan da yayi mana aiki kan Parida naki sakewa da Malamai don asaran kudi kawai mutum yake shi din dai ne malami gangariya amma mutuwa ta dauke mana shi kwatsam, gashi har yau duk uban kyan parida babu mashinshini tana can tana tuwo tuwo a Legas tana aiko ma yayar kudi kuma in sha Allahu a haka zata kare ga dai kyan da diri da komai amma babu mashinshini, to in anyi duniya don manzon Allah haka Khaleesar ma zata kare, amma yanxu tunda muka samu sabon Malamin nan naga aiki da cikawa kema kin san fiddo kudi bazai kara min wahala ba, ba gashi har na sa an amso min adashina ba daxu, in sha Allah sai mun karkato da hankalin Abdul kan 'ya yan mu, ko Labisah ko Labibah, ba dai kyau suke takama da shi ba wai su buzaye, to wallahi sai dai su ga ana aure....." Shiru Mama Zubaida tayi ganin Salame ta fito daga dakin Umma ta ci gaba da juya miyarta with serious face, Safiyyah na fita kofar gida ta ciro wayarta a jaka don tana da number Housemate, tayi dialing numbersa gabanta na faduwa tana hoping yasan whereabout din Khaleesat, jin Khaleesat take a ranta kamar er uwarta ta jini, she can't imagine halin da take ciki yanxu, yana fara ring Jay dake mota tare da Ajay ya daga wayar ganin Safiyyah ke kiransa yayi picking ya kai kunne calmly yace "How are you Safiyyah?" Da kyar Safiyyah tace "I am fine, ina kwana?" Yace "Lafiya lau, kin dawo Nigeria kenan?" Ta gyada kai da kyar tace "Pls tambaya nake son in maka Ya Jawwad" Jay yace "Ina jin ki Safiyyah" Safiyyah tace "Don Allah kasan whereabout din Khaleesat, wai tun Saturday ta bar gida har yanxu ba a san inda take ba, yanxun nan na zo gidansu nake samun labarin" Hawaye na zuba idonta ta kare maganar, a hankali Jay yace "Halysaah?" Lkci daya Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma ya fixge wayar ya katse ya ajiye, Jay dai kallonsa kawai yake, can yace "Kawarta ce fa" Ajay yace "And so? Assignment din announcing whereabout dinta aka baka ne? Me yasa baka da sirri ne kai?" Jay yace "But it's nothing, kawarta ce kuma tana sonta sosai, nasan bazata gaya ma kowa komai ba" Ajay ya dau wayar jin ya fara ringing, yayi rejecting call din Safiyyah sannan ya saka wayar a silent ya zura a aljihunsa yace "Dama ka saba tona ma mutane asiri kayi ruining plan dinsu ai" Jay yace "Bani wayata malam" Calmly Ajay yace "Bazan bayar ba" Dai dai sanda Ajay yayi parking a kofar gidan Aunty Farida ya kashe motar ya sauka ya bar Jay a ciki. Nenne na isa kofar gidan Gaje tare da Sha'awa er rakiyarta suka ga yan sanda biyu kofar gidan Gaje da motarsu, ga yan unguwa sun tsaya cirko cirko ana salallami, Nenne ta ja burki inda take tsaye tana gwaggwale ido sai ga wata er sanda ta kado keyar Gaje sun fito daga cikin gidan, Gaje na rusa kuka cikin rudewa take cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wallahi ban san inda take ba tsakanina da Allahn da ya halicce ni, in nasan inda take Allah ya tsine min albarka, Al-qur'anin Allah babu abinda na hada da ita ba dangin iya ba na Baba haduwar gidan duniya ne kawai, don manzon rahama ku min rai ban hada komai da ita ba" Er sandar tace "Amma ai an ganta ta shigo gidan ki ranan asabar da daddare, iya gaskiyar ki kadai ne zai cece ki a wannan case din aki kai ki furson, in kuma kika ce zaki ci gaba da karya zaki ga illar karya kuwa" Cikin tashin hankali zufa na keto ma Gaje ta ko ina tace "Wallahi zan fada gaskiya ku tsaya ku saurareni, tsakanina da Allah ta zo gidana da daddare wajen karfe goma tace in rufa mata asiri amma bata gaya min abinda ke faruwa ba, ni kuma da na tashi sai na kai ta gidan wata er dakina Sadiyah Chamo, Sadiyah ce ta bata mafaka a gidanta ta kwana, kashegari kuwa ta kira wani gingimemen mutumi a wayarta ya zo da katuwar motarsa ya dauketa suka tafi inda ban sani ba, idan na maku karya a wannan zance kada Allah yayi min rahama" Er sandar tace "Ina gidan Sadiyar yake?" Jiki na rawa Baba Gaje ta nuna hanyar gidan Maman Fu'ad, er sandar tace "Shiga mota mu je ki nuna mana gidan" Gaje ta rushe da kuka tana cewa "Na shiga uku na lalace ni Al-haqqatu na ja ma kaina masifa a garin kano" Bayan mota aka bude ma Gaje tana kuka ta shiga er sandar ta dago mata yakunannen gyalenta dake jan kasa ta dora kan cinyarta sannan ta shiga bayan motar ita ma, tuni Nenne ta juya sum sum tun ba a lura da ita ba ta shige wani layi, sai juyawa sha'awa tayi taga gefenta wayam babu Nenne.....


Next update at night in sha Allah.
[6/2, 8:30 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: A hankali Khaleesat ta Wan bude curtain din dakin Aunty Farida tana leko cikin parlon ta hada ido da su gaba daya, sauke idonta tayi ta shigo parlon walking slowly ta tafi ta zauna kan kujera kanta a kasa, tun da taji sallama ta tashi ta tafi dakin Aunty Farida don saka Hijab dinta, gaishesu tayi still not looking at them, Jay ne kawai ya amsa yana kalllonta calmly yace "How are you feeling now Housemate?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a hankali tace "I am much better now" Kallon Ajay tayi suna hada ido ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini?" Yana danna wayarsa yace "Fine" Aunty Farida ta shigo parlon daga kitchen ta ajiye masu tray din Can drink da ruwa da taje dauko masu, sannan ta zauna kan kujera tana kara gaishesu, Jay yace "Ya me jiki" Aunty Farida tace "Da sauki, abinci ne dai bata ci har yanxu" Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, sauke idonta tayi ta dau plate din abincin da Aunty Farida ta zuba mata not long ago, ta bude murfin ta ajiye sannan ta dau spoon ta fara cin abincin a hankali, Aunty Farida na kallonsu tace "Bari in kawo maku abinci" Ajay ya kalli Jay, Jay yace "A'a mun yi breakfast Aunty, mun gode" Aunty Farida tace "To ai rana tayi yanzu" Bata jira taji me zai ce ba ta tafi kitchen zata zubo masu abincin, ita dai Khaleesat a hankali take cin abincin hannunta, mikewa Ajay yayi, Jay ya sa hannu a aljihunsa ya ciro wayarsa, Ajay yace "Zan yi waya a waje" Daga haka ya fita daga parlon kafin Aunty Farida ta fito daga kitchen, Jay yayi murmushi bai dai ce komai ba, bude wayarsa yayi yaga miss calls din Safiyyah har shidda, yayi dialing number dinta ya saka handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga kamar jira take, yayi kasa da murya yace "Can you hear me Safiyyah?" Tace "Ina jin ka, plss ba a san inda Khaleesat take bane tun ranan asabar, kuma ni nasan bata da inda zata je a garin kano" Yace "Where are you at now?" Da sauri tace "Nima a kano nake ai, jiya da yamma na dawo daga Maryland shi ne na zo gidansu yau nake samun labari she is away from home tun ranan Saturday after receiving the news of her marriage with Abdul, wai Abdul fa aka daura mata aure da" Safiyya na kai wa nan ta fashe da kuka, Jay yace "I mean are you at home or where?" Cikin kuka tace "A'a yanxu na baro gidansu, ina bakin titi ma haka, i am just confuse, Khaleesat bata da kawaye bata zuwa ko ina, i don't know where she will be now, i am disturb don Allah in kasan inda take kar ka boye min plss Ya Jawwad trust me" Calmly yace "Look, this should be confidential Safiyyah, i trust you are saying nothing to anybody about this...." Da sauri Safiyyah tace "Na rantse babu wanda zan ce ma komai Ya Jawwad, trust me, i am also not in support of the fruitless marriage" Jay yace "Ohk, here is ur frnd speak to her....." Mikewa yayi ya mika ma Khaleesat wayar, ta amshi wayar tana kallon screen din dama tun jiya take wishing ace Sophie na kusa da ita ko ba komai zata dinga Consoling dinta tana karfafa mata gwiwa da bata assurance, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Sophie" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Khaleesat, i am so happy you are safe and sound, dama fatana kenan, plss kina ina haka yanxu in taho don Allah" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Bana kano Sophie" Da mamaki Safiyya tace "To kina ina?" Khaleesat ta daga kai ta kalli Housemate dinta dake kallonta, sauke idonta tayi da kyar tace "Ina Lagos" Safiyyah tace "Lagos wajen wa? Ko wajen Aunty Farida?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Amma Umma bata san kina nan ba" a hankali Khaleesat tace "Bata sani ba" Safiyya ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Pls kar ki tada hankalinki kinji kawata, i know ur Housemate won't allow u do that, kuma in sha Allah babu zaman aure tsakaninki da Abdul don bai yi deserving din ki ba, i can't imagine what he will turn you into, in Allah ya yarda bazai ci nasara akan ki ba, Allah zai raba auren cikin gaggawa, shi kadai yasan mugun Intention din dake ransa akan ki shi yasa yayi haka, amma Allah ya fi sa" Khaleesat dai gyada mata kai kawai take hawaye na sauka idonta ta kasa cewa komai, Housemate dinta ya mike ya nufeta ya amshi wayar a hannunta ya koma ya zauna yace "Safiyyah" A sanyaye Safiyyah tace "Na'am Ya Jawwad, Please kawata bata da wanda zai tsaya mata akan issue din nan, ba da intention me kyau ya saka aka daura auren ba wallahi, mugu ne azzalumi, har abusing dinta yana yi" Jay dake sauraronta yace "In sha Allah we will try our very best ki taya mu da addu'a" Safiyyah tace "In sha Allah, but how can i be reaching her?" Yace "Don't you have her aunt's number" Safiyyah tace "Sure ina da shi, i will be calling her ta wayar Aunty Farida" Jay yace "Keep this confidential pls Safiyyah" Safiyyah tace "Trust me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login