Showing 135001 words to 138000 words out of 241367 words

Chapter 46 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1601

ruwan dake kafarta sai ga ta a kasa timmm, A fusace Momy tace "Wallahi tallahi kika kuskura kika illata min tiles sai na cire cikin kudin albashinki, yau naga er iskar mata kawai, kullum na kiraki sai kin azabtar min da tiles saboda kauyanci? Wannan wace irin mata Adama ta kawo min haka da sunan me aiki?" Har kasa mai aikin ta zube tana ba Momy hakuri, cikin tsawa Momy tace "Miko min wayata dallah ki fita ki bamu waje, er kauyen banza" Mai aikin ta kalli wayar dake kan center table dab da inda Momy ke zaune, ta karasa da sauri ta dau wayar ta mika ma Momy, Momy ta warce, mai aikin ta bar parlon, Momy ta mika ma Meemah wayar tace "Dubo min lambar Godiya, glasses dina yana daki" Meemah ta amshi wayar ta dubo number aminiyar Momy sannan tayi dialing ta mika mata, a kashe suka ji wayar, Momy tace "Tayi tafiya me muhimmanci kenan, bari zuwa anjima in sake kiranta" Meemah da kanta ya gama kullewa tace "Tabddi jam, lallai nayi babban kuskuren da ban taSa yin irinsa ba Momy, sai ma fa kinga kayan dake jikinta da naje gidan, tana kitchen tana soye soye" Momy dai tayi shiru tana girgiza kafa don bakin ciki da takaici, can tace "Dauko min gyale da jaka a daki, ina zaman zamana kin janyo min kashe kudin da banyi budgeting ba Meemah, duk ke kika ja min wannan masifa da kika ki jin maganata wallahi, in hada iri da matsiyata akan wani dalili? A farko dai na hakura na zuba masa ido da yaki jin maganata, amma yanxu kuwa wallahi sae ya rabu da yarinyar nan, babu dalilin da zai sa in hada zuri'a da ita, ga kuma rashin adalcin da aka yi ma Alhaji ga asara ga biyan tara" Tashi Meemah tayi ta tafi dauko ma Momy gyalenta da handbag, all this while dama ita ke ta shiga malamai don Khaleesat ta shiga hannun Abdul Momy ko bin ta kanta bata yi tunda dama ba son auren take ba, Momy na ficewa daga gidan da driver dinta Meemah ta tafi dakinta da wayarta tayi dialing number Malamin da tasa yayi mata aiki. Runtse ido Khaleesat tayi bayan taji duk maganganun da Abdul yayi, yana rungume da ita saman gadonsa kamar zai maidata jikinsa, it's past 8pm na dare, jin taki cewa komai s hankali yace "Khaleesat" Bude idonta tayi wasu hawaye masu zafi suka silalo fuskarta tace "Um" Yace "Say something" Still tayi shiru hawaye na zuba idonta don bata ma san me zata ce masa ba at this point, ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "Say something pls" Da kyar muryarta na rawa tace "Ban san me zan ce ba" Yace "Say anything" Shesshekan kuka ta fara yi masa tana jin zafi a zuciyarta, me kuma yake son ta ce masa, tunda yace bazai taSa rabuwa da ita ba ko me zai faru, meaning dole ko tana so ko bata so haka zata ci gaba da rayuwa da shi a matsayin mijinta, so me yake son ta ce, ta dai dake da kyar har sannan muryarta na rawa tace "Kawai alfarma daya zan nema wajenka" Murya can kasa yace "Say it Khaleesat" Tayi karfin halin cewa "I don't want you to hurt anyone because of me...." Kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace "Ohk u mean ur Body Guards that sue me?" Ita dai kuka kawai take, Ya Wan yi wani murmushi yace "I don't think i will leave dem cause they started everything first, they intruded in what wasn't der business, basu baki labarin harbin da aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem..." Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace "To su ma ana nan ana targeting din su, amma in kince in kyalesu i will do that under 2 condition..." Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, yace "The first condition is that.... zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu..." Bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Baza ki yi ba kenan?" Muryarta na rawa tace "Ban ce bazan yi ba" Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da kyar tace "Bani da number ai" Yace "Amma aunt dinki na da shi ai... Call her and ask her to send you the number" Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi conditions dinsa, cikin kuka tace "Bani da numberta offhand" Yace "Ni ina da shi, i will call her now sai ki gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number kawai zaki yi requesting ta turo maki" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Why are you doing this plss Ya Abdul" Yace "Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka harba ai yayi surviving, i hope they survive too....." Tana kuka sosai tace "No plsss..." Wayar ya dauka yayi dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta.
[6/17, 7:43 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Har Aunty Farida ta Waga kiran Khaleesat bata amshi wayar da Abdul ke mika mata ba hawaye na zuba idonta, lkci daya ya hade rai yana mata wani irin kallo, babu shiri ta amshi wayar hannunta na rawa, a sanyaye tace "Aunty" Cikin rikicewa Aunty Farida tace "Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, hankali tashe Aunty Farida tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Khaleesat kina ji na? Don Allah kiyi magana, Hello Khaleesat" Khaleesat ta kasa ce mata komai hawaye masu zafi na sauka idonta, kiris ya rage ta fashe mata da matsanancin kuka a wannan lokacin, Abdul ya fixge wayar yayi a hannunta ya katse yana mata wani mugun kallon da ya tsorata ta sosai yace "Are you daring me?" ta fashe masa da kukan da take dannewa tana girgiza masa kai, a fusace yace "Ohk then, since abinda kika zabar masu kenan to ina me tabbatar maki zan aikata hakan nan ba da jimawa ba kuwa, sannan bayan nayi zan sanar maki, don bani da imanin kyale duk wani mahalukin da yace zai shiga hurumina, i don't mind sending that person to his early grave, and mind you.... i will so deal with them yanda in their next life baza su kara shisshigi akan abinda bai shafesu ba, if you think i am bragging watch and see, bani da conscience...." Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "Duk ba sai ka masu komai ba, zan yi abinda kace" Wayar ta amsa a hannunsa ta cire a Flight mode din da ya saka sannan ta sake dialing number Aunty Farida, yana fara ringing Aunty Farida ta daga da sauri tace "Khaleesat, kina ji na Khaleesat?? Hello" Khaleesat ta dake ta hadiye sauran kukanta cike da karfin hali tace "Na'am Aunty" Cikin tashin hankali Aunty Farida tace "Kina ina Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta daga kai ta kalli Abdul taga ya wani murtuke fuska yana kallonta kamar bai taSa fara'a ba a rayuwarsa, ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na zubo mata cikin sanyin murya tace "Aunty Number Ahmad za ki turo min yanxu plss" Aunty Farida da duk ta rude tace "Ahmad kuma Khaleesat? Wanene Ahmad? Kina ina ne yanxu?" Shi dai Abdul wani devilish look kawai yake mata, tayi kasa da murya tace "Aunty Number Junaid zaki turo min" Da sauri Aunty Farida tace "To bari in turo maki yanxun nan" Katse kiran Aunty Farida tayi cikin rawan jiki ta tura ma Khaleesat number Ajay, number na shigowa Abdul ya amshe wayar a hannunta yana kallon number for almost 5 seconds, can yayi wani murmushi ya mayar mata da wayar, cike da isa yace "Kirasa ki gaya masa abinda nayi instructing din ki" It took Khaleesat almost 30 seconds kafin ta iya dialing number Ajay, shi ma saboda irin kallon da Abdul ke mata ne, exactly irin kallon da yake mata in zai gaura mata mari, cikin muryarsa dake tsoratata taji yace "Kika kuskura kika yi magana da wata muryar da ba normal voice dinki ba zaki sha mamaki wallahi, and immediately he picks just go straight to ur point, do not give him a breathing space to say anything to you, go straight and tell him kin hakura zaki zauna da mijinki, kin ji me nace maki?" Ita dai bata ce masa komai ba hawayen takaici na zuba idonta, sai da kiran ya kusa katsewa Ajay ya daga, ta Wan kalli Abdul da bai fasa mata wani irin kallo ba, da kyar ta daure tace "Hello, good evening....." Mikewa Ajay yayi jin muryarta, bata jira ya gama processing ba ta ci gaba a hankali tace "Dama ina son in ce maka ni na hakura zan zauna da mijina, and i appreciate all what you've done for me kai da Yaya Jawwad, thank you so much" Ajay ya juya ya kalli Jay da shigowar sa dakin kenan, as if counting his words yace "Come again!" Yana fadin haka ya saka wayar a handsfree sannan ya nufi Jawwad yana kallonsa, Khaleesat ta kalli Abdul, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Cewa nayi ni na hakura yanxu, zan zauna da mijina, and thank you for all what you've done for me...." Wasu sabbin hawaye suka hau zarya a fuskarta tana ji kamar ta fashe da kukan dake cin ta, Abdul ya fixge wayar a hannunta ya katse sannan ya kashe wayar gaba daya, Ajay ya kalli Jay that looks speechless and shock at the same time, lkci daya ya jefar da wayarsa saman gado, cikin nutsuwa yace "Nayi da na sanin bata lokacina akan yarinyar nan, i regret wasting my very precious time...." Jay ya ma rasa me zai ce, walking slowly ya karasa gaban window din dakin yana kallon Ajay that was boiling from inside, a hankali yace "Look Ajay, i think those words are not coming from her heart, sakata yayi ta fadi hakan pls mu yi mata uzuri, she is forced to say all what she said, ba mu san situation din da take ciki ba let consider that plss" Ajay ya masa wani kallo yace "Billah na cire hannuna a lamarinta kaji na rantse Jay, i have nothing to do with her case again, after all i was just doing it just for the sake of humanity not because of her, ko kasheta yake ya kamata ta gaya mana haka? Mu zata dauka for granted? Beside she spoke confidently meaning she is okay with what he asked her to say, i am leaving this state first thing tomorrow morning, so unfortunate i waste my time on the brat, don taga mun yi stooping kan mu so low shi yasa ta dauke mu for granted" Yana kai wa nan ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Jay ya lumshe ido ya bude don bai san me zai sake ce masa ba da zai sa ya sauraresa, kuma tunda har ya rantse magana ta kare, ya zare hannunsa kenan babu abinda zai sa ya sake involving kansa, zaunawa yayi gefen gado ya dafe kansa da yaji ya masa nauyi, at the same time letting out a sigh, kalmomin Khaleesat ne suka dinga dawo masa kai, he felt really disappointed in her too, but can kasan zuciyarsa tausayinta ne ya mamayesa ya kuma yi mata uxuri, ya rasa menene yasa shi shiga yanayin da ya shiga a wnn lkcin, da kyar dai daga karshe ya mike ya fita daga dakin yana tafiya a hankali. Daren ranan nan Khaleesat bata yi baccin awa biyu ba cikakke, da bacci barawo ya saceta zata farka a firgice, bata taSa jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Abdul ya sa tayi ma su Housemate dinta ya tsaya mata ba, gashi ko digon hawaye yaki fita idonta, her heart is just heavy, but did she have a choice? In bata yi hakan ba yayi ma su Housemate dinta wani mugun abu ai bazata taSa yafe ma kanta ba, tunda har yake ikirarin ba shi da imani babu abinda bazai iya aikatawa ba, tasan kuma sarai zai iya aikatawa din, tunanin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa take, is she going to survive this at all? Is this not going to be her end? A ranta taji kilan lokacin mutuwarta ne ke tinkarota, sai a sannan taji hawaye masu zafi for the first time a idonta, ta kai hannu a hankali tana sharewa ta juya tana kallon Abdul dake baccinsa hankali kwance, dai dai nan alarm din wayarsa ya kada, ta juya da sauri tayi backing dinsa tana goge hawayen da ya fara zubo mata sosai, after some seconds taji alamar ya tashi yana karanto addu'an tashi bacci, ita dai hawaye kawai take, sai da taji yayi sallah ya fita daga dakin sannan ta mike zaune tana kuka a hankali. Nenne ta bude hannu tana kallon su Aunty Farida cikin nutsuwa tace "To kun ga ai baza mu shiga hurumin Allah ba, ko akwai me tsaurin idon da zai shiga a cikin ku? Allah Ubangiji ne kadai yasan daliliin da ya maidata hannun mijinta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, to don me za mu shiga hurumin da ba namu ba? A'a gaskiya banda ni tunda ni dai nasan wanene Allah, kuma shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan, da yasan Khaleesah zata cutu hannun Awdul da bazai fara basa sa'ar sungumeta ba don bamu fi sa sani ba, ko ba komai Wa na zai samu kwanciyar hankali ya ci gaba da sabgogin rayuwarsa kamar ko wani Wan adam, mu mun yarda da kaddara mummuna ko kyakkyawa tunda mu musulmai ne, kuma duk abinda Allah yayi mu din banza za mu ce don me, domin haka nake cewa Allah ya bata zaman lafiya da mijinta, Wan halayyarsa da yake yi mara kyau Allah ya gyara sa ya dena, ai babu wanda bai da taSon wani mugun abu a rayuwar nan, in sun dawo kano mu kuma sai mu je ganin daki mu sa albarka, duk sanda ya bar ta ta zo ta gaida mu a Mariri sai ta zo bakinta alekum, shi kuma Ali Allah ya sa karshen wahalarsa kenan a duniya" Wani irin kallo Aunty Farida ke ma Nenne zuciyarta na tafarfasa, Umma dai kanta na sunkuye bata ce komai ba amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Mama Zubaida tace "Amma dai Nenne ai ya kamata a bibiyi halin da take ciki, an taSa tarewa haka kawai a zo a sungumi yarinya a mota da asuba ba a san ko shi din ne ba ko ba shi ba amma duk a rasa me bibiyar hakan, wannan ai abun dubawa ne, tun da mu dai har yanzu bai ce mana shi ya dauketa ba" Nenne tace "To er bakin ciki, shi din ne ya sungumeta ba kowa ba aniyarki ta bi ki, kuma ai halaliyarsa ya sunguma ba wata ba, duk wanda ya sake cewa zai bada shawara a wannan lamari idan ban sa Ali ya sallamesa ba shegiya uwata da ubana suka haifeni, kwata kwata bakwa neman ma Wa na sauki a rayuwar nan, burin ku kawai tashin hankali ya kashe Ali ku huta ni kuma in shig????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a uku, ita uwar da ta tsugunna ta haifi yarinyar bata da bakin magana sai ke me baki kamar ta dorinar ruwa?" Mikewa Mama Zubaida tayi ta shige dakinta, Mama Shatu ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta, in ya dawo mana da gawar ta ai sai mu zauna mu yi zaman makoki ba shikenan ba" Nenne tace "Sai dai ki ga gawar er ki Labeebah amma ba Khaleesah ba, kuma bakin cikin da ku ka kasa boyewa ne zai kashe ku ke da Zubaida" Mikewa Umma tayi hawaye cike idonta ta shiga dakinta, Nenne ta kyabe baki ta mike tana kallon Aunty Farida tace "In Ali ya dawo ki ce masa nace ya zo ya amshi tuwo da miyar taushe zan ajiye masa, wallahi wata guda zan yi ina masa girki ya marmaro" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida tayi tagumi hawaye cike idonta.
Meemah ta shigo parlon Momy ta zauna tana Wan murmushi, ta jira har Momy ta gama wayar da take yi da aminiyarta godiya sannan tace "Momy na samesa a waya" Da sauri Momy tace "Ya daga kuma?" Meemah tace "Eh ya daga bayan yaga text din da na tura masa kenan" Momy na gyara zama tace "Toh Alhamdulillahi nagode ma Allah, sai yace maki me?" Meemah tace "Kema kinsan dole zai taho ai, amma tsorona daya kada ya kira Daddy kuma ya daga waya yace masa ba haka ba" Momy tayi wani murmushi tace "Bazai daga ba, tunda na riga na gaya masa abinda ke faruwa ai" Meemah ta sauke ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, in ya samu flight yau za mu iya ganinsu a gidan nan" Momy tace "Me zai hana ya samu jirgi, ai da sauran lokaci dole zai samu" Mai aikin Momy ce tayi sallama tana makale jikin kofar parlon duk da a bude yake amma bata shiga ba, hannunta rike da tray me dauke da plate din gasasshen kaza da lemon kwali biyu, Meemah ce ta amsa sallaman tana mata wani kallo tace "Tun da kika ga kofa a bude ba sai ki shigo ba, kin wani raSe jikin kofa kamar munafuka, don Allah ki dena wannan kauyancin yana damun mu a gidan nan" Momy ta hade rai tana kallonta har ta karaso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login